Showing 15001 words to 18000 words out of 22316 words
da yar uwarsa amman yana gudunta dan bakin hali, ansha a nonon gyatuma."
Dady ya ce, "Hakuri za ka yi ka dau excuse in kun dawo kaje yanzu kam tun da anyi break kuje kawai i think yanzu 10:pm ma ta wuce."
Ba yadda Al-ameen ya iya haka ya tashi babban tashin hankalin sa shine maganar siyo bra a kasuwa bai ma san ta yadda xai kwatanta ba ga kuma wannan aljanar yarinyar abun da kunya anganshi yaje siyan bra kuma da ita.
"Onkul jirani insa takalmi na , "ta fada tana washe baki.
Kaka ta ce, "Yawwa ka kulamun da ita kuma axaɓo mata bra mai Bala'in kyau ehee."
Tun da ta shiga motsr nan ban tabe tabe da tambayoyi ba abun da take yiwa Al-ameen bai kulata ba ita ko ko ajikinta ta ci gaba kamar ana zugata, "Onkul yaushe za ka yi aure? Ka haihu kana daukan jinjiraye zannsma yaranka wanka da kaina aradu na iya har kai ma zan iya ma fa ko kashi kayi zan ma tsarki."
Daidai da isowarsu kasuwar kenan ya yi paking tuni ta fito kamar an jefota.......
*Me kuke tunanin zai faru?*
*Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments*
_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_
_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_
[12/1, 4:28 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_
_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_
_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_
_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_
_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_
*FREE PAGE-15*
_nayi mistake fejin baya maimakon 14 nasa 13 so take note wannan 15 ne dayan 13 din 14_
_*Afwan Ameenatou fans bana da lafiya ne kuka ji shiru🙏*_
_*Wannan fejin naku ne Harbeebbty da Aminiyata Ada kuji dadinku kadan domin namijin jajircewata yasa na baku fejinnan mai kama da ku😁*_
Free Page na daf da karewa wa inda suka biya sun huta😆
_____
Dai dai isowan wani mai mashine gashi ya shigo da gudu, Al'ameen bai san lokacin da ya dira a motar ba ko rufewa baiyi ba ya janyo Ameeenatou suka tafi tamkar zasu faɗi gaba ɗayan su yayi sauri ya dafe Motar ta tashi.
Wiki-wiki Ameenatou tayi da ido ta lafe a jikin shi, tuni har Mutane sun fara taruwa kowa na tofa albarkacin bakin shi, finciko ta yayi ya jefa a Mota yana huce ya shige Motar bai saurari Mutanen da ke gurin ba ya figi Motar ya harba kan Titi, Sai da sukayi tafiya mai Nisa ba wanda yayi magana a cikin su gaba ɗaya Ameenatou a tsorace ta ke don ta sadaƙar da mashine ɗin nan ya bige ta sai tayi rugu-rugu, kawai Hausi ta tuna maƙociyar su da Mashine ya bige sai dai a ka cire mata ƙafa, tana gama wannan tunani sai kawai ta fashe da kuka.
Parking Al'ameen ya yi dai dai wani guri da ba Mutane, ya fito a fusace ya jawo ta ya wanke ta da Mari, yana faɗin, "ke wacce irin mahaukaciya ce yanzu da Mashine ɗin ca ya bigeki fa,! banza wawiya ƴar ƙauye kawai,! kuma wallahi ko ki mun shiru ko in tafi in barki a gurin nan masu satan mutane su harbeki kowa ya huta da jaraba, kawai Daddy ya tashi ya jawo mana Annoba a gida.!
"Onkle ya fa isheka don ba tsoron ka nake ji ba da zaka tasani kana mun masifa, kuma Yasin muka koma gida sai na faɗa ka da kaka ba dai ni ka mara ba, wallahi sai na ce ka mun shegen duka, ka turani titi kuma wai Mota ya kasheni saboda ba ka ƙauna ta."
Ameenatou ta ƙarasa maganar tana juyawa ta shige mota ta cigaba da kukan ta.
Takaici gaba ɗaya ya gama cika Al'ameen ya rasa mai zai ma yarinyar nan ya huce ne, ji yayi har kan shi ya fara ciwo don shi har ga Allah bai son dogon magana balle hayaniya amma wannan mayyar yarinyar ta sa shi yana ta buɗe murya a titi.
Komawa motar yayi ya ja ya kama hanyar komawa gida da ita yace sai dai duk abun da zai faru ya faru, Muryan ta yaji tana cewa.
"Onkle ya zaka maidani gida baka siyamun rigar Nonon ba.?
Banza yayi da ita, da ta fasa wani uban ihu ta tuma akan kujerar Motaar bai san lokacin da ya taka wani wawan birki ba, kaɗan ya rage ya bigi na bayan shi.
"Wayyo Allah na ni Al'ameen yau Allah ya haɗani da jaraba.!
wani tunani ne ya zo mishi a rai sai ya juya Motar ya nufi Asibitin shi da ita, ita kuma ta cigaba da birgima da bige-bige a motar kamar mahaukaciya.
Suna isa ya fito ya buɗe gurin da take ya jawo ta yayi hanyar Office ɗin shi da ita, Sister Surayya ce ta hangoshi da sauri ta taɓo wacce take kusa da ita ta ce, "Sister Rukky ga mutumin ki can ya shigo da wata ƴar ƙauyen yarinya, yanzu ya shige Office ɗin shi."
"Uhmm ni wallahi na haƙura da Doctor Ameeen kullum ina bin shi yana wulaƙanta ni."
Wayar ta ce tayi ƙara da take ajiye a tebur ɗin gaban ta, jawo wayar ta yi, zaro ido tayi ganin mai kiran na ta.
"kinga wai yau ni Doctor Ameeen ke kira da ma yana da Number ta ne.?
Ta faɗa fuskar ta ɗauke da mamaki.
" To ki ɗauka mana kar ta yanke kin san bai kira biyu shi."
Da sauri Rukky ta ɗauka ta kara a kunnen ta.
Amsa sallamar da tai mai yayi ya ce mata, "ki zo Office ɗina ina son ganin ki."
Yana gama faɗa mata haka ya katse kiran.
"Kin ji wai yana son gani na bari inje in ji."
"Ok sai kin dawo."
"Ke Meena ki mun shiru wallahi ko yanzun nan in miki Allura."
Ai bai gama rufe baki ba Ameenatou ta ɗauke wuta, don duk rashin jin ta Allah ya saka mata tsoron Allura.
"Alhamdulillah yarinya tun da na gano lagon ki kin shiga uku kuwa, mara kunyar ƙarya."
Duk a zuciyar shi Al'ameen yake wannan maganar, bai gama tunani ba sai ga Rukky ta shigo tana wani karairaya kamar zata karye dama gata ita ta tafi kaman one sai fuska ta ci bleching ga kafar ta da hannun ta baƙinƙirin.
Tun da ta shigo Ameenatou ke kallon ta, can da ta tuntsire da dariya har ta na faɗuwa ƙasa daga kujera, gaba ɗaya suka bita da kallo suna mamakin mai ya bata dariya haka.
Ita ko in ta ɗago ta ƙara kallon Ruƙayya sai ta ƙara kwashewa da dariya.
"Meeenah! will u shut up! ya zaki ta samu gaba kina mana dariya kamar kin ga mahaukata.!
Al'ameen ya ƙara sa maganar cikin fushi.
"To Onkle ba dole in dariya ba naga abun dariya, dama a mutane ma akwai Muchiya da zani ban sani ba, gani nayi wannan Matar tayi kama da muchiyar kaka da take tuka mana tuwo, kuma wai ƙonewa tayi naga fuskarta fari kafan ta da hannun ta baƙi."?
Ameenatou ta ƙarasa maganar tana kara kwashewa da dariya.
Gaba daya kunya ya lulluɓe Al'ameen saboda irin tijarar da Ameenatou take ma Rukky ya rasa ma mai zai ce mata.
Ita ko Rukky ji take a duniya ba'a taɓa mata cin mutunci irin wannan ba, gashi yarinya ƙarama tana muzanta ta a gaban wanda ta fi so duk duniya, a yau taji tana da ta sanin yin bleaching, da sauri ta juya zata fita Al'ameen ya miƙe da sauri ya bita yana kiran ta,
"Rukky please ki tsaya kiji don Allah."
Ko waigowa ba tayi ba, riƙe kanshi yayi da yaji yana sara mai ya koma Office ɗin, samun ta yayi tana ɗaɗɗaga takardun da ke kan tebur ɗin office ɗin.
"Meeeeeenah! wai ke baki san darajar ɗan adam ba ne, baki da hankali wannan ba ta girmeki ba."
"To ni ina ruwa na, ni na ce ta zo tana ma fari da ido tana wani girgiza jiki kamman sandar suluka shine naji ta ban haushi kuma naga kana kallon ta meyasa ni bazaka kalleni ba, ban fita kyau ba ma ni ƴar duma duman Kaka Nono ne kawai ta fini kuma ni ma ya fara fitowa kuma bari ka ganshi."
Ta miƙe tana ƙoƙarin ɗaga mai riga.
"Ke baki da hankali ne na ce miki ina son gani ne.?
"Wallahi ni sai na nuna ma."
Dafa kai Al'ameen yayi saboda tsananin sara mai da kan na shi ke yi..........✍️✍️✍️
TEAM AMEEENATOU HOW MARKET🤣🤣🤣
ni dai na fece Ameeenatouo tabbas tafi ƙarfi na nan fa kishi Ameenatou kaka keyi ikon Allah🤣🤣🤔🤔🏃♀️🏃♀️🏃♀️
IN GA RUWAN COMMENT KU GA RUWAN TYPING YASIN🙄🙄
_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_
_*Urs Xayyeeshert[12/2, 10:01 AM] Xayyeesherthou: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_
_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_
_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_
_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_
_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_
*FREE PAGE-16*
_*MAH GROUP MEMBERS MA SU SHARHINNAN ANTIES BA GOGGOS DIN BA FA😹👋IN SHA ALLAH ZA KU KARANTA AMEENATOU ABAGAS AMMAN MUTANE UKU KACAL🤸♀️💃*_
Ita kuwa Ameenatou da gaske ban da kokarin tuɓe riga ba abun da take yi.
Ganin abun nata ba wasa ya sa Al-ameen saurin riƙe mata hannu yana, "Please Meena duk na miye wannan ki bari kinji."
"Onkul,Onkle Wallahi ni ka sake mun hannu sai na nunama ai nima na ce ina da shi,Yasin ina da shi kuma in na girma ma sai sun fi nata kyau."
Wata gigitacciyar tsawa ya yi da Ameenatou ba ta san lokacin da fitsari ya fara zubo mata a jiki ba.
"I said You should stop it , ki mun shiru awajen ko in miki allurar nan."
Kallon jikinta ta yi ta ga fitsari na zuba cikin rawar murya ta ce, "Onkul ni bana son rigar Nonon ka kai ni gida gun kaka."
Wani irin kallo ya bita da shi cike da tsaki, a zuciyaarsa tunanin yadda za ta shigan masa mota da wannan kazantar yake wata irin tsanar yarinyar ne ya kara shiga zuciyarsa.
Wayarsa ya dauko ya kira waya cikin minti biyu kuwa sai ga wani ya shigo .
"Yawwa Ibrahim taimako Please ka kai mun wannan yarinyar gidan mu ku shiga keke nafef in ka kaita sai ka dawo."
"Ok Sir An gama ."
Ameenatou ta bisu da kallo.
Al-ameen ya ce, "Oyaa follow him."
Tsayawa tai tana kallonsa
Dafa kai ya yi ganin bata ma fahimci me yake faɗi ba ya ce, "I said ki bi sa ku tafi zai kai ki gida."
Ta shi tai kamar sabuwar bazawara tana wiƙi-wiƙi da ido ta bi bayan Ibrahim sai da su ka je bakin kofa tuyo tana, "Onkle ka tawo mun da rigar Nonon kar ka manta."
Wani takaici ne tsantsa da kunya ya damƙe Al-ameen.
Ita ko Ameenatou tsayawa tai tana, "Onkle ka ce to ba ka amsa ba fa kuma wallahi mai kau ina so in ba ta mun kyau ba aradun Allah Sai an maida an samo mai kyau."
A fusace Al-ameen ya ce, "Oh My God Ibrahim take her out please."
Rike hannunta Ibrahim ya yi suka fita tana mita, "Nima ai kuma na iya turancin irin na onkul wasi mi si niem in ka zo gida zan rama kuma."
Suna komawa gida kuwa Aguje Ameenatou ta shige kaka ta fara, "Ina rigar Maman kuma ina Ameenun na ganki ke ɗaya."
Taɓe fuska ta yi kamar za ta yi kuka, "Kaka fa munje kawai wani mai mashin ya jo zai bige mu, onkul ya riƙe ni kin san wani irin riƙo ya mun? Hmm yasin irin yadda muka kalla a tabijin dinnan jiya na masoya." Ta sheƙe da dariya tana miƙawa kaka hannu.
Miƙa mata Kaka ta yi tana, "Ban baɗo ga dukkan Alamu Ameenu son ki yake munafurci ne da iya shege irin nasa kawai."
Ameenatou ta ce, "Eh mana Kaka kuma wata mai bleaching fa ta zo tana ta wani kanne masa ido Kaka yasin inna kama ta ko? Sai na mata targaɗe a kumatu aradu."
_______A gogon hanunsa ya kalla da mamaki ya ga saura 30minut atashi a office da sauri ya tashi da kan sa ya nufi office din Rukayya.
Tana ganinsa ta sunkuyar da kai.
"Excuse me Please,Ruky ki yi Hakuri kanwata ce daga kauye so kin san yanayin su."cewar Al-ameen.
Rukayya ta ce, "Ba komai Sir na fahimta." Ta karasa maganar tana sakin wani murmushi da ita kadai ta san ma'anarsa.
Ya ci gaba da magana, "I need your Help please Ruky."
Da mamaki
Wai yau Al-ameen ke mata magana asanyaye kuma har yana neman alfarma agareta ashe akwai ranar da za ta yi amfani wa Al-ameen.
Murmushi ta kara sakewa tana, "Ba komai Sir ka fada duk abun da ka ke so As you wish za a yi."
Al-ameen ya ce, "Thank you,so nake kije kasuwa ki siyo mun........
Sai kuma ya kasa fada ya rasa ma ta inda zai fara.
Ya ci gaba, "Um wannan Abun what ma...." Ya dafa kan shi a zuciyar sa yana fadin wannan yarinya ta haɗani da aiki yanzu in koma gida babu ya zama matsala amman tabbas ba abun da zai hanani hukuntata.
Ruky ce ta katse shi da fadin, "Am waiting Sir lafiya dai ko?"
"Am totally Confuse Ruky." Ya fada yana kara dafa kansa.
Can kuma tunani ne ya zo masa takardda ya dauko ya rubuta breziya ya mika mata.
Tana karantawa cike da mamaki ta dago tana kallonsa asaninta dai Al-ameen ba ya da aure kuma ba ya shirin yi.
Kau da kansa ya yi,ya ciro kudi dim akalla in bai kai dubu hamsin ba ya yi arba'in.
Ya ce, "Ki siyo ko guda biyar ne."
Washe baki tayi ace brar da bata wuce 1k 2k shine za abata dumin kudinnan ta siyo guda biyar? Aranta take fadin , "Oho dai koma wa zai siyawa ni gaba ta kai ni gobara titi a jos."
Fita tai da rawar jiki ta nufi kasuwa.
Bra guda 12 ta siyo yan 800 kuwa hankalinta kwance ta sanya sauran kudin a ajaka, tana zuwa Office ta miƙa masa.
Karba ya yi yana fadin, "Thank you." Kan ya ciro bandir din dubu goma ya miƙa mata, RUKAYYA idon naira baki har wuya ana washewa an samu duniya.
Ledar ya dauka cike da takaici ya fita a office din da niyar tafiya gida.
****#
Kaka ce zaune tana surfa uban masifa wa Hajiya Karama.
"Na faɗa miki Aradu in Ameenu bai shigowa da Yar Uwarsa rigar Mama ba gidannan za ku sha mamaki sai na ɗaga gidan na juyashi ta yadda kowa zai zazzage Mussamman waccer ta ɗakin mara kunya sai na mai da tsinke kamar yadda aka aurota."
Daidai lokacin Hajiya karama ta fito tana tauna cingam da tafiyar kasaita, "Yoo mu kam kuma ai mun shige sai yadda Allah ya yi da mu, gida gabadaya ya sauya ban da wari ba abun da ke tashi,ke jummala fito ki sanya mana turaren wuta ko ma ɗan ji sanyi arai."
Kaka ce ta dakatar da ita, "ke ƙaniyarki na ce ƙaniyarki kinji ko wa ya sanya maku gidan bashi? Yoo ke waya kai gyatumar uwarki bashi Matar da in ta zabga kashi tun ada sai an kira kamfanin iska da turare sai waje ya shekara ba a shiga amman yanzu har kina da bakin magana da shegen goshi awajen kamar jirgin sama,ni na rasa ma me Audu ya gani ajikinki Aradu, sai shegen faɗi amman ko irin lankwasar kwankwason nan ma mai fidda kyau baki da ke da slifas ba maraba ana tallan kugu ke kina tallen faranti bani waje agun."
Ɓata rai Hajiya Karama tai ta nufi daƙi.
Kaka ta ci gaba da magana, "Ji yadda ta kumbara kamar audugar sawa yara aɗuwawu taji fitsari in ce ai dukana za ai."
Ameenatou ko ban da dariya ba abun da take.
Sallamar Al-ameen ne ya katse su duka Ameenatou ta tashi aguje....
_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_
_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_
[12/7, 2:16 PM] Xayyeesherthou: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_
_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_
_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_
_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_
_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_
*FREE PAGE-17*
Ameenatou ta nufesa tana, "Oyoyo Onkle ka siyo mun rigar Nonon ko?"
Kau da kansa ya yi cike da ɓata rai ya miƙa mata ledar batare da ya jira ta ƙara fadin uffan ba ya shige ɓangaren shi.
Ameenatou kuwa tsalle tasa tana