Showing 21001 words to 22316 words out of 22316 words
dubo Alhaji Adam mu tattauna in sha Allah hakan za ayi."
Yana fita Hajiya ta kira Al-ameen a waya nan take kuwa ya xo.
"Al-ameen na san ka fiye da kowa na san wanene kai da kuma kudirin ranka amman ka da ka manta farincikin iyayenka a kullum shine gaba domin inganta rayuwarka cikin aminci, ka da ka bijire mana,kuma ka da ka ce mun zalinceka kamar yadda Inna ta bukata gobe in sha Allah za adaura ma Aure da Ameenatou."
Wani irin faduwar gaba Al-ameen ya ji wanda sai da hanjin cikin sa suka haɗe waje guda.
"Momy! Me ki ke fada? Aure ni? Aure ni fa? Kuma Ameenatou Momy wallahi bana da buƙatar auren kowacce mace a duniyar nan bare Ameenatou, Momy me na maku kuke son hukunta ni da auren yarinyar nan." Karasa maganar ya yi hawaye na zubowa daga idanunsa.
"Al-ameen ban san ka da bijirewa umarni na ko na Dadyn ku ba, ina so kasa aranka wannan kaddara ce da muke fatan kasancewar ta mai kyau,dole sai kayi hakuri ka yi hakuri Al-ameen."
Share hawayen ya yi kan ya ƙaƙulo murmushin dole wanda azuciyarsa yana tuna yadda zai ladaftar da Ameenatou ne kawai,"In sha Allah da kanta zata gudu ta barni."
A zahiri kuma ya ce, "Bakomai Momy."
Murmushin ita ma ta bisa da shi, "Allah ya yi maka albarka."
Da Ameen ya amsa kan ya tashi ya fice ba tare da ya ce komai ba.
Yana fita ya nufi ɗakinsa kwanciya ya yi kawai ban da saƙe-saƙe ba abun da yake,babban tashin hankalinsa yadda ya ga da gaske safiyar nan fa yi take kuma wai aure za a daura masa da yar ƙauyen cen.
Washegari
Da sassafe Kaka ta fito tana kwaleleto , "Audu na ce za ka fito Aɗaura Auren Ameenu da Yar Uwarsa ko kuwa ?"
Dady ne ya fito yana, "Inna Gani za adaura in sha Allah,jiran Alhaji Adam nake zai tawo da goro."
Kan Kaka tai magana kuwa sai ga sallamar Alhaji Adam.
Amsawa sukai a tare Kaka ta ce, "Yawwa Dan albarka in ce kaine Waliyin Ameenu ko?"
Murmushi ya yi, "Eh in sha Allah Inna."
Kaka ta washe baki, "Yawwa to maza adaura zam zam."
Dadyne yasa Al-ameen ya kirawo masa wasu daga cikin makotansu domin sheda daurin Auren.
Haka Al-ameen ya kasance sam ba kumahari da ka gansa za ka san takaici fal cikin ransa amman abun mamaki wani lokacin sai ya sake murmushin da shi kadai ya san ma'anarsa.
Ameenatou kuwa na ɗaki ban da tsalle tsalle da murna ba abun da take taso fitowa Kaka ta hanata wai ai ita Amaryace kuma boye amare ake hakan ya bata damar tiƙan rawa tana murna aɗaki yau tayi aure.
A gaban Kaka aka daura auren Al-ameen da Ameenatou abisa sadaki Dubu ɗari da Alhaji Adam abokin Dady ya bada.
Ana daurawa wata irin guɗa da Kaka ta yi saida ya zagaye illahirin gidan.
"Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah an daura Auren Ameenatou da Al-ameen yan bakin ciki sai dai su mutu."
Nan take Dady suka fice da abokansa.
Ita kuwa Ameeenatou ta fito da gudu ta rungumi Kaka tana, "Kaka da gaske wai yanzu ni matar aure ce kuma Matar Unkle Al-ameen?"
Kaka ta ce, "Eh mana yan bakin ciki kam sai dai su mutu."
Hajiya karama ce ta fito tana, "Cab Lallai Al-ameen ya shiga kaddarar rayuwa wayaga kwaila wannan kam fanko aka aura masa."
Kaka ta ce, "me kika ce? Na ce kin ci gidanku da shegen baki kamar an taune gafiya bani waje ni."
*****
Ranar ko zuwa breakfast Al-ameen bai yi ba.
Bayan an gama kowa na hutawa Kaka ta ce, "Audu ince yaushe za a kai Ameenatou gidanta dana Al-ameen ne?"
Dady ya ce, "Inna na ce ko za abari ayi mata siyayya kafin lokacin bikin Nauwara sai akaisu duka."
"Aa aa na ce maka Audu haka kawai yara da aurensu kuma suna zumudin juna ace za arabasu? Sam ban lamunci daukan hakki haka ba,in ma za ka sani ka sani daren yau za akai Ameenatou gidan Al-ameen eheee."
Dady zai yi magana
Hajiya Babba tayi saurin fadin, "Bakomai Inna Yanzu zan bincika mata sabin kayan Nusaiba a hada mata kawai su tafi zuwa lokacin bikin in aka hada wasu sai akai mata."
Kaka ta ce, "To Uwar azagwaigwai yau kam kinyi hankali ba shakka har kin fi mijin naki, hakan zai fi daren yau akai yara gidansu na sunnah."
Hajiya karama ta ce, "Hmm akwai kallo,wayaga zumuɗin juna."
Dady ya ce, "Nauwara ki kira mun Al-ameen awaya ya zo ɗaki ya sameni."
Yana fada ya tashi awajen.
*****
Jiki sam ba kwari Al-ameen ya nufi ɗakin Dady.
Da sallamarsa Dady ya amsa.
"Yawwwa Ameenu ga Keyn gidan cen nan domin a ciki zaku tare zuwa dare in sha Allah na san baku da bukatar komai hatta kayan abinci akwai sai dai inyi maku fatan alkairi,kayi hakuri da halin Yar Uwarka ka yi hakuri ka danne zuciya Al-ameen watarana sai labari, sannan maganar skul dinta kuma kaje ka karbo mata uniform din ta fara zuwa ranar Monday in sha Allah, Allah ya yi maka albarka."
Al-ameen ya amsa da Ameen kawai kan ya fice batare da fadin komai ba.
Dare na yi Ameenatou ta tsalla kwalliya,jan baki har kasan labba,girar kuwa har kunne,kamar dodonniya, ta zauna gefen gadon Kaka ana jira atafi.
Aiko Dadyne ya yi sallama yana , "Inna in kun shirya ku fito,ga su Hajiya ma,mu rakata sai mu dawo ko?"
Kaka ta ce, "To, to to gamu nan yanzun nan ma kuwa kasan amare sai da rarrashi ga mu nan tafe."
A motar Dady suka je aka kai Ameenatou har gidanta ban da kalle-kalle da tabe-tabe ba abun da take,domin a kyau da komai wannan gidan ya ninka na Dady kai ka ce Aljanar duniya.
Ba ka ce Amarya aka kawo ba domin tuni ta ware tana zagaye gidan.
Hajiya Babba ta nuna mata wasu ɗakuna biyu masu kallon juna.
"Yawwa Ameenatou wannan shine ɗakinki,wancen kuma na Al-ameen."
Kaka tai karaf ta ce, "Au har raba masu ɗaki ake? To ahir irin haka ke janyo kishiya a banza baku iya tattalin miji ba, Ameenatou kar ki kuskura ki kwana ɗaki daban maza kuna kwana ɗaki daya,haka kawai acuceku to ban lamunta ba."
Hajiya karama ban da ummm ba abun da ta iya furtawa.
Dady ya ce, "to mun rakota,Inna ku zo mu tafi gida."
Ameenatou ta washe baki "to Kaka da Hajiya, Baba Audu sai da safenku ban da waccer hajiya karamar kuma karta kara zuwamun gida ma."
Kaka ta ce, "kar ki ji komai maza nemi waje ki zauna, Yanzu Ameenu zai shigo kin san dai me na fada ko? To a kiyaye sai mun zo zaman jego kuma."
Ameenatou ta sheƙe da dariya.
Kaka ta fita tana, "yanzu nan da wata tara za amun kawa Ah Alhamdulillah yo ai wannan aure ni akawa."
Dady ne ya kira Al-ameen ya sanar da shi sun kai Ameenatou ya je gidan kar abarta ita ɗaya.
Ita ko tanan ta ɗane kan kujera ban da tsalle-tsalle ba abun da take yi.
Al-ameen na sallama taje da gudu oyoyo uncle ta rungumesa.
Tsaki ya yi kan ya finciketa gefe.
Dakinsa ya nufa kawai.
Da gudu ta bisa ɗakin ya kara cillota waje.
"Unkle Wallahi Kaka ta ce tare zamuna kwana ta ce kar in barka."
Ko kulata bai yi ba ya share.
Can ya shiga har ya fara barci Kasancewar ya gaji Ameenatou ta lallaɓa taje ta kwanta kusa da shi ji ya yi kawai ana taba masa baki.
"Ji bikin unkle dinnan mai kyau kamar irin na yan tv da muke kallo gidan Baba Audu,bari in masa yadda suke."
Ta kai bakinta za tai kissing na shi kenan kawai........
*😹💔 Ameenatou za tai kissing unkle ya kuke ganin rayuwar Auren Al-ameen da Ameenatou xai kasance? Maza ku hanzarta biya domin karanta naku cikin sauki yanzu aka fara ko ince har yanzu ma da sauki akan na gaba*
Littafaina na kudi ga duk mai bukata
Matar Police 200
Ashe haka so yake 300
Jameel 200
Ameenatou 300
Duk mai son duka hudun 800 maimakon 10000
_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_
_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_o🤍*_huo🤍*_