Showing 9001 words to 12000 words out of 22316 words

Chapter 4 - Ameenatou Yar Kaka Hausa Novel Complete

Takori   

23 Nov 2024

495

Ameenatou ta kwashe da dariya, "Yoo ni wasa ce? Wallahi ko Aljanu ban bari su tabani su sha lafiya bare bil Adam,hhhhhhhh ai aradu in dai muguntace yanzu aka fara indai za a taba ni a makarantar nan, Allah sa duwawun ma ya rufe ya kasa zama da gasken."

Zama tai akasa ta dinga jibga uban dariya tana Sambatu tamkar zautacciya.


Shi ko Uncle na can ana fama,ko da yaje staffroom aka tambaye shi miye cewa yake, "Zasu kashe mun duwawuna wallahi alluraine akan kujerar can."


Hakan ya sa Wani Malami zuwa ajin domin duba meke faruwa

Aikuwa ana duba kujerar nan da kyau ƙayoyine jeri ba adadi yadda duk mutum ya zauna sai ya ji ajikinsa.


"Ku fadamin waye acikin ku ya yi wannan aikin ko kuwa dukkaninku laifi ya hau kan ku."

Ameenatou ce tai karaf ta ce, "Onkul Aradun Allah Aljanune duba ka gani yadda suka zuba kayoyin fa kuma onkul bai gani ba sanda zai zauna saida suka tarwatsa masa duwawu,tab ni dai wallahi ba ruwana fita zan yi a ajin nan ma in zakuyi binciken domin aljanun na fitowa mutuwa zamuyi duka,kakata ta ce mun duk randa mutum ya ga aljani to wallahi mutuwa zai yi,ni dai ba ruwana na tafi wallahi."


Kasancewar Ameenatou ta san Uncle Kabiru da tsoron Aljanu ya sa ta yin wannan shawarar.

Nan da nan kuwa ya zaro ido.

"Subhanallah nima ko kaman fa tabajin labarinan to kun ga afita da kujerar waje kawai."

Ya karasa maganar yana sakawa bujensa iska.


Ameenatou ta zo gaban aji tana, "Aradun Allah ba wani Aljanu nice nan kuma duk wanda ya ce nice sai na masa addu'ar mutuwa,kun san dai Kakata ta iyeee eheee,yara ku fada ku ga aradu kun sanni ai." Ta karasa maganar tana kyalkyalewa da dariya.



_____A kwana a tashi Ameenatou za su zana jarabawar kammala primary daman kamar yadda Baba Audu ya tsara a binni za ta yi karatun secondary kasancewar kaka ta ce sai Ameenatou ta kammala makaranta zasu koma binni.


Ameenatou ce ta fito da sassafe tana, "Kaka Aradun Allah ki cewa baba Audu gobe su zo da Onkul Al-ameen dina yanzu zamu tafi zana jarabawa kuma yasin ko mun kammala ba zan dawo da wuri ba,dan sai na yiwa kowa sallama a agarinnan Hatta mai garin ma kowa sai ya sallameni yasin eheee."




Ba tare da ta jira amsar Kaka ba ta baiwa bujenta iska.


Yau da kanta tabiyawa su Furera da Lantana.

"Ku wallahi yau dinnan sallama za mu yiwa yan gari har fada zamuje kun ga muje mu zana jarabawar karshennan da sauri yasin yau mun girma mun huta da Onkul Wasi mie si niem.



Haka kuwa akayi abun mamaki Ranar Farko da Ameenatou ta shiga makaranta ta zana jarabawa ba tare da rigimar komai ba.


Suna fitowa daga jarabawa ta cire jibinta ta daura a kugu, wandon nan kuwa aka kara jan shi sama aka janyo safarnan ku san cinya.


"Yawwa kuzo yasin ta gidan mai gari zamu fara."


Nan kuma suka dau hanyar Fadar mai gari.

Suna zuwa Ameenatou ta ce, "Baba Mai Gari Sallama na zo ma gobe zamu koma binni."


"Ah To Alhamdu Lillah Ma sha Allah ɗiyar kaka mun gode Allah,Allah tsare hanya yar albarka."cewar Mai gari da har cikin ransa yake hamdalar barin Ameenatou a karkarar domin ita da kakarta sun addabi kowa shi kan shi basu bare ba bare yan garinsa.



Ameenatou ta ce, "Amin din wato ma dadi kake ji ko? To wallahi sai in fasa tafiyan ma ehee ai naga kaka ta ce asalin garin nan dinma namune ehee."



Mai gari ya zaro ido, "Subhannallah kar ki fasa,ai ni so nake kije binni ki zama yar binni kixo ki dauke mu muma ki kai mu can."




Ameenatou ta ce, "To sallameni mu tafi."


"Yoo Ameenatou wace sallama ce kuma bayan wadda mu ka yi?"


Ameenatou ta ce, "Kambalaasss lallai ma mai garinnan ka cika son duniya,kudi fa za ka ciro ka ce ungo nan Ameenatou yar albarka Asiya magarya asha amota,in da hali ma ka siyamun harda alewar malam tanko,ni ko sai in ce na gode baba mai gari, Allah ya ma albarka, Allah ya shirya ka kadaina sa ana satan abincin gona,kuma Allah sa amutu ana kashi a bayi."



Mai gari ya san tsaf Ameenatou zata iya kunce masa zani a kasuwa domin ita da kakarta in suka fara zuba tamkar wa inda suka kone aka suke.

Da sauri ya ce,"Ungo nan jakka biyune asha magarya a hanya , Allah tsare hanya."


Ta karba tana, "Yawwa mai gari mai kumatun cincin wallahi kumatun ka sak irin na cincin din da kaka ke soya mana, yanzu saura alawar."


"Oh Allah na gode ma ku dakata in shiga gida ina ganin da kwai alawa."cewar mai gari yana ba yan fadarsa hakuri.



Yana shiga gida Ameenatou ta ce, "kin ga furera rike mun kudinnan ha in zaga fitsari ina ji."


Ta zaga bayan gidan mai gari ta tsinko karkashin sai da ta jajjaga shi tas agun kan ta dibo.


Sai da ta bari kowa baya kallonta kan ta fara shafa leda gun zaman mai gari da karkashi.

Tana gamawa kuwa sai ga mai gari ya fito da alawa.

Da sauri Ameenatou ta karasa ta karba tana, "Ina Godiya Mai garinmu zan Turo adaukeka a gyarama kumatunnan ysn ya dawo na mutane."


Shi dai mai gari bai ce komai ba ya nufi gun zamansa domin damuwarsa kawai Ameenatou ta bar wajen kan ta gama tona masa asiri.



Lanatana ta ce, "Yawwa to Goggo ki zo mu tafi."


Ameenatou ta ce, "dalla tsaya mu sha dariya na masa na bankwanane so inke in ga kukan mai gari yau Aradu."

Tana gama magana kuwa sai ga mai gari dam akasa.


Mai Ameenatou za ta yi ban da dariya.

"Wayyo Allah kunkumina na shiga uku ya balle ku dagani waziri ku dagani." Cewar mai gari.


Ameenatou ta ce, "Hhh wayaga mai gari akasa,kato da gemu a kasa."



"Daman na sani sharrin ja'irar yarinyar cen ce ai gwanda ku koma binni ko ma huta."


Yan fada suka bisu tuni su Ameenatou suka tsere.


Ihu mai gari yake yana, "ku dawo ba iya kamosu zakuyi ba sai dai su kara targada ku a zo adumamamun kuguna wayyo ni zai balle."


Ameenatou kuwa Kafa mai naci ban baka ba


*Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments*

_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_
[12/1, 4:28 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_



*FREE PAGE-10*

🤍🤍🤍 *KALAMAN SOYAYYA*

_Wani Hamshakin Murmushi ya sake mata tare da gyara zama yana kallon cikin idanunta, " *Hayatiy* ki sani duk da cewa na san kin sani amman ki kara sani cewa aduk sanda zan furta kalmar *INA SONKI* ba abu daya nake nufi ba,tamkar na ce Ina so in rayu da ke ne,kuma da ke zan rayu haka kuma kece Farincikin Rayuwata, aduk sanda kuwa zan ce *KE CE RAYUWATA* ba wai ina nufin ba zan rayu in babu ke bane aa,amman zan iya ba da rayuwata gareki aduk sanda bukatar hakan ya taso, ba wai so na soyayya kadai nake miki ba,kauna ta rayuwa tare nake miki,kuma zan ci gaba da hakan har karshen numfashi na, kin san meyasa?"_

_*Hayatiy* da ta durkusar da kanta kasa ba tare da ta dago ba ta girgiza masa kai ya yin da take wasa da yatsun hannunta._

_"Ke din tauraruwatace kuma haske ga rayuwata, ana yawan fadin kalaman soyayya karyane,amman aguna sam ba karya domin abun da ke cikin raina kawai nake fiddawa, Ina son farincikinki tamkar yadda kowace shuka ke bukatar ruwa domin tsirowa,ina sonki,zan ci gaba da sonki kuma bana fatan dainawa,kasancewar rayuwarmu atare ita ce burina akullum."_

_A hankali ta dago da fuskarta ya yin da ta sake masa murmushi,cikin sanyayyar murta ta ce, " *Ruhiy*." Shiru ta yi kan ta ci gaba da magana , "Nima ina sonka kuma ina so inyi rayuwa da kai,ka mun alƙawari cewa ba zaka barni ba kaji,ina so in rayu da kai kaji,kar ka barni kai din Farincikin rainane,ka tausayawa zuciyata,ko da zanma laifi na zabi da cewa ka mun fada komin zafinsa bana son kalmar rabuwa,domin tamkar rabuwa da bangaren rayuwata ne."_

_"ba zan bar ki ba *Hayatiy* na miki alƙawari in sha Allah,indai ina raye ba zan taba barinki ba."_

_"Na gode *Ruhiy* ka da ka manta da abu biyu Kasancewar ka cikin murmushi a kullum shine Farinciki da burina ,haka kuma kasancewar ka cikin kamshi shine walwalar ruhina,zan kasance mai alfahari da kai akullum."_
______
"Wai Wannan Wace Irin Mahaukaciyace a gidannan?"



Fisge Hanunta ta yi ta kalle shi kan ta murguda baki, "Aradun Allah ni ba Mahaukaciyace ba sai dai kai eheee."


Kaka Da Baba suka karaso Tana, "Kai Al'ameen kanwar taka ce Mahaukaciyace? To ahir dinka wallahi."


Ameenatou ta ce, "Yooo ni bama dani yake ba wallahi eheee ni ba Mahaukaciyace ce ba."


Baba ya ce, "Ameenatou ba kyau rashin kunya bai san ke ce, Al-ameen wannan yar gidan Goggonkuce Ameenatou."


Kau da kai Al-ameen ya yi yana cizon yatsa aransa yana tunanin yadda zai seta yarinyar nan can kuma ya ce, "Barka da zuwa Kaka." Daga nan bai Kara cewa komai ba ya wuce cikin gida.



Tsaki Kaka tayi kan ta ce, "Kai Audu wai har yanzu 'Dannan naka bai bar wannan shegen nunkufarcin ba? Ko da yake ba laifin ka bane na uwarsa ne da ta hana abani shi mu zauna a kauye da tuni na seta shi,wai yana gaidani kamar ya ga kashi?"



Ameenatou kuwa ina ko kula su kaka ba tai ba tabi bayan Al-ameen duk inda ya yi nan take shiga.
Ba tare da ya san tana binsa ba.

Baba ya ce, "Iya ina Ameenatoun kuma?"


Tabe baki tai kan ta ce, "yoo waya sani muje ciki nikam hanjin cikina sun fara bayani."



Al-ameen ba inda ya nufa sai toilet yana kyankyamin rike hannun Ameenatou da ya yi gabadaya ya tsargu da kayan tubewa ya yi ya fara wanka kawai.


Ita kuwa zama tai kan kujerar dressing mirror tana kalle kalle, man shafawansa cream ta gani fari sol atunaninta abun sha ne budewa tai tana ta lasha abun ta hankali kwance.


"Tab gaskiya Abunnan da dadi su Onkul aradu an iya shan kayan dadi,ysin ko kadan ba zan rage ba shanye kayana zan yi nikam."


Ya Gama wankansa tsaf ya tuna towel dinsa na falo, da sauri ya fito domin dauka ya goge jikinsa kan ya duba wani kayan.


Wata irin kara da Ameenatou ta sake sai da ya karade dukkanin bangaren gidan.

Azabure Al-ameen ya juyo ya kalleta.
Ganin jikinsa take kallo tana ihu yasa shi yin tsaki tare da janyo towel dinsa ya sanya ajikinsa.
"You! Meya kawo ki dakinnan?"

Kan tai magana sai ga su Kaka,Baba,Hajiya,karama da Babba.


Ameenatou ta fara, "Kaka Aradu Onkul Dan iska ne tsirare yake yawo fa."

Kaka ta kalle Al-ameen kan ta ce, "Yoo Daman ban da tambada da rashin kunya yaushe mutum zai zauna daga shi sai wani guntun zani mai kamar famfas ajiki,da shegen kai kamar kwallon mangoro."


Tsabar takaici Al-ameen janye kayansa ya yi ya fice adakin batare da ya ce komai ba.


Kaka ta ce, "Maza muje ciki ku kuma iyayen Kwainane da iyayi aba Ameenatou abinci daga zuwa har mun fara gamo oh ni Indo tabbas sai na gyara maku zama daga ku har 'Ya'yan naku."


Hajiya Babba ta ce, "Ayi Hakuri Iya In sha Allah hakan ba zai kara faruwa ba."

Hajiya karama kuwa ficewa tai ba tare da ta ce komai ba.


"Ban waje yo duk ba ke kika koyawa dan naki futsara ba,oh kin ga wancer tsigen mai kama da farantin Dan malale wato hakurin ma ban isa ta bani ba?" Cewar Kaka.


Ameenatou ce ta katse ta da maganar, "Kaka Aradu ina jin yunwa kuma ni da Yaya Al-ameen zan..........


*Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments*



_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_
[12/1, 4:28 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_



*FREE PAGE-11*

_*KALAMAN SOYAYYA🤍*_

_Aduk in da zaka kasance ina so ka tuna da cewa Ina sonka, Kuma bana fatan bari, kasan dalili? Kai ne hasken rayuwata zan kasance da farinciki ne kawai in har ina tare da kai, ina kaunar ka_


_________

"Zan ci yana bani abaki ai haka yayu suke ma kanne ko?"ta karasa maganar tana goge hawayen fuskarta.



Kaka ta ce, "Muje Ciki dai."


Suna zuwa falo kuwa suka tarar da Al-ameen zaune yana aiki a system.



Aminatou ce taje ta zauna kusa da shi tana, "Onkul Ka zo mu ci abinci ka bani abaki kaji Allah yaso ma nikam dazu fa ban ganka ba rufe idanuna na yi nikam bab ga komai ba kaji ko."



Hajiya ce ta shigo da sallama tana, "To Ameenatou ga abincinki in bai isheki ba sai akaro.


Ihu tasa tana , "Kaka? Kaka? Kaka kin gani dan abincinnan mai na ci bare in ba hanjin ciki da hantar kwakwalwata Kaka Ni da Onkul kuma zamu ci fa tab wallahi ni akaro Mana."


Karaf Kaka ta ce, "Yoo daman ban da jarabbabiyar rowa wannan dan abinci wa zai ci? Kar ki manta fa ina sane da yadda aka auroki kamar tsinken gazari amman yanzu anzo anci ba iyaka sai hawa kamar fulawa, a tarihin danginku kaf tun daga yayan kakan kakanki ba wadda ta shiga gidan arziki sai ke ko ince ma ku da aka barwa gadon tusa? To ahir wallahi dibo mata abinci iya son ranta ta fiki gadara da gidan."


Ameenatou ta kyalkyale da dariya, "Laaa Kaka daman ana gadon tusane?"


Kaka ta murza ido kan ta ce, "Yoo ba ga shi kinji ba,ban da tusa ba abun da gidansu suka iya yanzu ma Allah rabamu da wannan tusa dan in tayita ina ga sai mun suma sau tamanin batare da sanin inda muke ba."


Tsaki Al-ameen ya yi,yana kokarin tashi.

Kaka ta ce, "Kai Ja'iri ni kake yi yiwa tsaki dan gyatumarka, kana sunkuyar da kai kamar munafikin kwarto har ni za'a kawowa raini a cikin gidan d'ana ni da idan na so zan iya hana kowa zama a cikin gidan nan. Ace daga zuwar yarinya har anfara yi mata hassada da ba'kin ciki abincin ma ba za'a saka mata wanda za taci ta 'koshi ba. Shi kuma wannan me zubin aljanun yana min tsaki saboda ya raina ni"


Dariya Ameenatou tayi sai kuma lokaci guda ta d'aure fuska ganin Al-ameen ya bud'e 'kofa ya fita ta fashe da wani irin kuka tare da kwanciya a 'kasa tana birgima kamar wacce taji wani mummunan labari, lokaci guda hankalin Kaka ya tashi dan a tunanin wani abu ya faru da Ameenatoun.



Hajiya Babba dake tsaye a gefe ma ta matsu kusa tana 'kokarin ta'ba Ameenatou, da sauri Kaka ta karasa kusa ta bige hannun Hajiya Babban ta fara magana cikin kuka tana fadin "Ba ga irinta nan ba anyiwa yarinya mugunta, yanzu haka ma mayu suka kamata dama tunda muka shigo gidannan na ga ana nuna alamun ba'ayi murna da zuwarmu ba, wayyo ni Indo na shiga uku ya zanyi da ha'k'kin marainiya"


Gefen zani ta saka ta fyace majina ta cigaba da cewa''Kin tsaya kina kallona ne ba zaki wuce ki kiramin d'ana ba yazo asan wacce za'ayi dan ni ba zan lamunce haka ba."

Jiki a sanyaye Hajiya Babba ta mi'ke za ta fita sai dai kafin ta 'karasa ta jiyo murya Ameenatou tana magana cikin shesshe'ka ta ce" Ni fa Kaka ba abinda aka yi kawai yunwa ce inaji yasin kamar hanjin cikina zasu tsinke na mutu haka nakeji."

Kaka ce ta mi'kar da ita zauna ta ce" Bayani zakiyi ai 'yar lelena ga abinci maza kici a 'karo miki dan wannan ba isarki zaiyi ba nasani."

Kuka Ameenatou ta fashe da shi tana fad'in" Ni wallahi ba zanci ba tare da Onkul Al-ameen za mu ci ya dinga bani a baki."

Shiru Kaka tayi kafin ta ce'' Yo ai wannan ba wata matsala bace bari a kirashi ya baki ai kema 'kanwarsa ce"


Kallon Hajiya Babba tayi wacce ke tsaye tana kallon sangarta irin na Ameenatou, Kaka tace"Ke Mero maza je ki kiramin yaron nan Ameenu ya zo ya baiwa 'yar uwarsa abinci a baki."


Cike da ladabi Hajiya Babba ta ce" Mama yanzu kamar Ameenatou ace sai Al-ameen ya bata abinci a baki saboda sangarta ina gani hakan kamar bai dace bawai dan wani abu ba sai dan saboda girmanta yanzu ai abun kunya ne wani ba'ko ya shigo ya tarar ana bata a abinci a baki ba ciwo ba komai kawai dan shagwaba."



Aikuwa me neman kuka an jefe shi da kashin awakai, nan Kaka ta fara surfa bala'i tana fad'in Hajiya Babba ta raina ta daga zuwa gidan d'anta zata fara zaginta, hakuri Hajiyar ke bata amma Kaka ta runtse ido sai masifa take yi.

"Yoo zan ga yau ni da ke wayafi wani mahimmaci awajen Audu in kuma ke kika bani Nonon da na shayar da shi sai ki fadamun."
Ameenatou dake gefe ganin fad'an Kaka ba tsayawa zaiyi ba ya sa ta isa ga plate din abinci ta fara ci hannu baka hannu kwarya dan abincin ya mata dad'i

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login