Showing 18001 words to 21000 words out of 22316 words

Chapter 7 - Ameenatou Yar Kaka Hausa Novel Complete

Takori   

23 Nov 2024

494

ihu, "Kaka Kin gani Onkle Al-ameen ya siyomun rigar Nonona irin na Antu Naura."

Washe baki Kaka tayi tana faɗin, "to ko kaifa ɗan albarka, in da haka kake kula da ƴar uwar ta ka marainiyar Allah yaushe zan damu, Amma da yake an biyo baƙin halin Uwa shiyasa, tashi muje ɗaki ki gwada muga yanda ya yi na san ma dai zai miki kyau, ƴan baƙin ciki sai dai su mutu."
Kaka ta ƙarasa maganar tana hararar Hajiya ƙarama da ta fito daga kicin.
"Oh yanzu Al'ameeen saboda rashin aikin yi ne da taya ɓera ɓari ka siyo ma wannan beran yarinyar bereziya har kala goma, tabdijam to ina Nonon da za'a saka abu kaman allon mayu, Allah ya kyauta ƙauyanci irin na ƴan ƙauye kuwa."

Hajiya ƙarama ta ƙarasa maganar tana hayewa sama da sauri, don ta san in har ta tsaya sai kaka tayi mata zagin ƙare dangi.

"Eh lallai wuyar ki ya isa yanka, tabbas za ki ga tijara don kin samu na haƙura ranar ban sa an kaɗaki gidan mai dattin hula ba ko, shiyasa har ni kike zagi bari Audun ya shigo zaki san kin zageni."

Kaka ta ƙarisa maganar ta mai fashewa da kuka.
"Kaka kiyi shiru ki barni kawai ni da ita zan miki maganin ta a gidan nan, zata san waye Ameeenatou kaka tabbass."
"Yauwa ƴar albarka, shiyasa nake alfahari da ke ai, navsan kevɗin jinina ce ban ce ki ragawa kowa ba gidan nan ehe kowa yayi miki ki mishi."

"Angama Kakan Ameeenatou ikon Allah, tashi muje in gwada rigar nono na kinji."



ASIBITI
"Sister Surayya ni abun ya ɗauremun kai, ko dai Dr Al'ameen aure zaiyi,? to in ba aure ba mai zaiyi da breziya, saboda tsaban cin fuska ma ni zai aika in siyo mai bresziyar kayan aure, ni kaina gaba ɗaya ya kulle a lokacin da na ƙarɓi kuɗin saƙon shi."

"Hhhhh sister Rukayya kenan, ke dai kawai ki ce kin ga kuɗi ya ruɗaki kin mance da kishi sai yanzu hankalin ki ya dawo jikin ki, kika sani ko wannan yarinyar da suka zo tare ya siyan ma."

"Yarinyar da ko ƙirgan dangi bata fara ba balle nonuwa."





Cewar Rukayya.


Surayya ta ce, "Ko ma yane dai tunda kin samu rabonki ai shikenan yanzu abani rabona."


Harara Rukayya ta bi ta da shi kan ta tashi tana, "Wannan kudi kam ai ya shiga kuma ba fita Allah sa gobe yazo ya ce asiyo masa pant ma,kuma in sha Allah indai na cika Sunana Rukayya kamar Anyi an gama na Auri Al-ameen."


Ta shige tana rangwaɗa.


Dariya Surayya tai tana, "To ai shikenan Allah ya tabbatar da alkairi."



******Kaf sai da Ameenatou ta gwada breziyoyinnan suna shewa da kaka kai kace sabin kamu ne.

Tana cikin sa kaya taji alamar maganar Hajiya Karama na fitowa.

Ko bari ta karasa sa rigar ba tai ba ta ce, "Kaka ina zuwa."


Da gudu ta nufi kitchen, robar yaji ta ɗauka,ta nufi ɗakin Hajiya Karama sidif sidif ta shige toilet.


Buta ta dauka saida ta ciketa da ruwa dam kan ta juye yajinnan aciki.

Ta fito tana dariya.


Adaidai kofa ta ci karo da Hajiya karama .

"Ke bagidajiya mai kikazo mun aɗaki?"


Ameenatou ta murguɗa baki kan ta ce, "Hassana da Hussaina na zo nema muyi wasa ko da gaba ne?"



"Iyeee Ni kike fadawa hakan da shegen ido kamar na bera." Cewar Hajiya Karama.


Ameenatou ta sheƙe da dariya, "oho dai ni ban da duwawun akuya." Ta zura aguje.


Hajiya karama na shiga ɗaki tana, "Wannan yarinya dole in dau mataki akanta wallahi cikinama ya murɗa bara in shiga toilet in fito kan dai in tafi anguwar nan."



Aiko Hajiya karama ta shiga toilet cikin nishaɗi ta zabga uban kashinta tana nishi.


Tana gamawa ta janyo buta domin tsarki.


**Ameenatou kuwa na can na zabga uban dariya.


Kaka ta ce, "ke wai lafiyanki kuwa?"


"Hhhh Kaka ba za ki gane bane bari bomb din ya fashe ka......


Kan ta karasa suka jiyo karar Hajiya Karama tana.

"Na shiga uku jamaa......







_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthu[12/8, 1:06 PM] Xayyeesherthou: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_



*FREE PAGE-18*

_*Anata tambayata wai ba kalamai ne?😹to tabbas akwai su yaku fans dina masu kwamushemun kalaman love ku saurara:*_


_*KALAMAN SOYAYYA🤍💫*_


_Ban yi karyar cewa ba zan rayuwa in babu kai,amman ina so kasani cewa rayuwata ba za ta taba samun walwala ba har sai da kai cikinta, ka rayu dani Ruhiy! Domin inganta mun rayuwata,ina sonka_



"Zan Mutu,Na shiga uku,ku kawo agaji."


Nan da nan Kaka,Hajiya Babba da Ameenatou aka nufo ɗakin Hajiya Karama domin dubawa ko lafiya.


Suna shiga suka tarar da ita kan gado tayi goho tana ihu, "na shiga uku ya shige mun ciki, can ciki wallahi ina jin macijini acikin ruwannan wayyo Allahna shikenan ya shige,ko yaushe zai fito oho."sai hawaye.



Hajiya Babba ta karasa tana dafa ta, "Momyn Husaina lafiya kuwa?"


Ƙaraf Ameenatou ta ce, "Wallahi ni ce nan nasanya mata yaji acikin buta tayi tsaki duwawun ya soye, waya ce ta na rainamun Kaka." Ta kyalkyale da dariya har tana rike ciki.



Kaka ta ce, "Au to Ma sha Allah Ameenatou na shiyasa nake sonki maganin mara kunya ai kenan gwanda da akayi maganin takashin maga yadda za ayi rashin kunyar."


Ta yi tsaki kan ta fice.

Ameenatou ta bita tana dariya.


Hajiya karama ta ce, "Wallahi ba zan yafe ba, Allah ya isa,Allah saka mun shegiyar yarinya mai kama da aljanu."

Hajiya Babba ta zauna gefen gado ta dafa Hajiya ƙarama ta ce, "Momyn Hussaina na faɗa miki ki daina shigar harkar Inna da yarinyar nan, kwata-kwata inna bata da daɗi kina dai gani ka mata biyayya ma ya aka cika balle, don Allah duk abun da zasuyi a gidan nan ki daina kulasu sai a zauna lafiya."
"Amma Momyn Al'ameen kina gani haka zamu zura ido matar nan ta zo har gida ta dunga mana tijara jikar ta ma tanayi, ni ba abun da ke ƙonamun rai irin wannan shegiyar ƴarinyar mai kama da zubin buzaye, duk ita take ƙara in giza kakar take ma mutane wulaƙanci."

"To ni dai na baki shawara ki kiyaye musu, kina ganin gashinan yarinya tana neman naƙasaki ta illataki."

Hajiya babba ta ƙarasa maganar tana mai fita daga ɗakin, tana kuma dariya ƙasa-ƙasa ganin in da Hajiya ƙarama ta yaye zani tai ɗai-ɗai a kan gado tana jin iskar fanka na shigan ta, duk ta fita hayyacin ta duk wannan gayun ya gudu a lokaci guda, ga hawaye shaɓe-shaɓe da majinu.

Duk abun da ke faruwa Al'ameen naji kasancewar yana ɗakin momynsu suna magana da ita jin ihun hajiya ne yasa ta fita da gudu don ganin meke faruwa ta bar Al'ameen a ɗaki, bayan ta dawo ne take faɗa ma Al'ameen abun da ya faru shi kanshi sai da yayi dariya.

"Wallahi momy yarinyar nan bata da hankali, zanyi maganin ta kuwa a gidan nan."
"Kar ka kuskura ka jawomin bala'i gurin kakan ku, karka taɓa ta domin ka taɓata kasan a kaina tsohuwar nan zata huce saboda haka naka ido."

"Shikenan sai a bar yarinya ta dunga hauka da rashin kunya baza'a tsawatar mata ba, shikenan Momy na rabu da ita,amman tabbas ta kuma shiga gaba gonata ba zan mata da sauki ba."
Ya ƙarasa maganar yana mai tashi ya shiga kicin yasa abinci ya wuce ɗakin shi.


**********


Suna Shiga ɗaki Kaka ta ce, "Allah miki albarka Diyar kwarai ai kin birgeni wallahi maganinta kenan."



Ameenatou ta kyalkyale da dariya "Ai yasin ka dan ma ta gani ba ita yar gayu ba za ta ga gaye ai, Yauwa kaka tun da na gama gwadawa bari in ɗauka in je ɗakin Onkle in gwadamai shima yaga in da yamun kyau ko Kaka.?

"Sosai ma kuwa Ameeenatoun kaka yi sauri kije ki gwada mai na san zai ce kinyi kyau Watakil ma ya kyasa."

Ameenatou ta washe baki, "Kaka Miye Kyasa?"


"Ina nufin watakil ma ya fada ramin soyayyarki?" Cewar Kaka

Ameeenatou ta ce, "Iyee kuma fa wallahi nima ina son shi Kaka ki cewa Baba Audu ya Auramun shi kinji."


Kaka ta ce, "Yar baɗo ba kunya, tabbas haka za ayi,bari audun ya dawo,yanzu dai jeki nuna masa ki dawo."

Ameenatou ta kwashi bereziyon ta fita da gudu zuwa ɗakin Al'ameen don ta gwada ma Al-ameen.

Zaune yake yana cin abinci kamar daga sama ta hankaɗo kofa.

"Onkul ka ga yadda ya mun kyau ko? Ai kaka ta ce za ka kyasa ni."


Wani irin takaici ne ya kama Al-ameen bai san lokacin da ya zaro belt ya fara jibgarta ba.


Ihu take tana, "Kaka zai kashe ni, na mutu nikam wayyo cikina,wayyo maxaunina ya balle.........



_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_
[12/9, 3:35 PM] Xayyeesherthou: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_



*FREE PAGE-19*

_*KALAMAN SOYAYYA🤍💫*_

_Ina Sonka! Kalmar sam bata mun wuyar furtawa gareka,kasan dalili? Ina rayuwa ne da soyayyar ka araina,amman duk da hakan xan so ace ana so bayan numfashi domin kuwa zan ci gaba da sonka a ko ina,a ko yaushe Noorry_


*_SAURA FEJI ƊAYA FREE PAGE YA ƘARE WA INDA BASU BIYA BA SU HANZARTA BIYA TABBAS DOMIN YANZU AKA FARA AMEENATOU KO INCE YANZU ZA A FARA😹😹💔💔_*



************


Kaka ta fito da gudu ta fincike Ameenatou tana, "Ƙaniyarka Ameenu na ce ƙaniyarka ka ci gidanku, a hakan zan aura ma ita? Lallai ma wato ka samu jakar duka to ahir dinka wallahi, kaf danginmu ba wa inda sukai wannan mummunan Hali na duka sam."



Ficewa ya yi yana tsaki ba tare da ya ce komai ba.


Hajiya Babba kuwa tana jin su taƙi fitowa domin ta san tana fitowa abun zai koma kanta ne.



Ameenatou ta kalli Kaka.

"Ni wallahi Kaka kar afasa auren ina son shi fa ni kar ki ce zaina dukana aradu son unkle ina yi kumq in ba a aura mun shi ba mutuwa zan yi fa."



Kaka ta buɗe baki, "Iyee bar batunnan in ce yau Audu zai dawo daga tafiya? In sha Allah adaren yau za ayita ta kare za ki aureshi amman tabbas Sai nayi mai sharadi da kashedi kan dukanki yana fama da kai kamar na bazawarar agwagwa."



Ameenatou ta share hawaye, "Yawwa Kaka kuma wallahi sai na rama abun da ya mun nima kuma sai na rama Ai."



Kaka ta ce, "Yo nasani ai ba acin bashin mu a zauna lahiya ko da ta tusa ce."



_____Dare


Zaune suke Afalo duka nin su Dady ya dawo daga tafiya.


"Yawwwa Al-ameen gobe Monday ya kamata Ameenatou ta fara zuwa makaranta."cewar Dady.


Al-ameen ya ce, "To in sha Allah Dady,Amman da Nawwarata ta kaita in zata wuce Office."


Karaf kaka ta ce, "To anƙi Nuauran ta kai ta, ka ci gidan ku na ce, kai zaka kai tan, Audu kai kuma daman ina da magana da kai."


Dady ya dago kan ya ce, "To Inna ina saurarenki."


Kaka ta yi gyaran murya kan ta gyara zama, "So nake A aurawa Al-ameen Ameenatou!


Wani irin jin kaf yan falon sukai Mussamman Al-ameen da ya ji wani hatsabibin sauti na ratsa masa zuciya.


Hajiya karama ce kawai ta iya furta, "Wonder Shall Never End!!"


Kaka ta ci gaba da magana, "Tun da naga alamun suna son junansu kuma yarinyar nan dai ta isa Aure shi ko kokarin tsufa ma yake ina laifi dan ta taimaka masa ta aureshi."

Ameenatou ban da washe baki ba abun da take.


Al-ameen bai san lokacin da ya fara magana ba, "Haba Kaka arasa da wa za a haɗani sai wannan mahaukaciyar kazamar yarinya, Never wallahi ban ma da ra ayin aure bare ma ko da ace ina da wallahi ba zan auri wannan mahaukaciyar ba." Ya fada yana nuna Ameenatou kan ya fice afusace.



Wani irin ihu Ameenatou ta sake, "Kaka ni wallahi onklu ina so,Kaka shi ina So ni Wallahi shi ina so."

Nan take Kaka ta fashe da kuka, "Yanzu Audu kana gani? Na ce kana gani 'Ɗanka yake zagina? Yo zagina mana tunda ya zagi Ameenatou ai dani ya yi nice mahaukaciyar Kuma kazamiya? Kuma Wallahi in baka Aura masa Ameenatou ba,ba abun da zai hanani tsine ma."


Ta fada tana face majina.


Hajiya Babba na ganin haka ta tashi da Nusaiba,Naurawa ma ta bita,Hajiya Karama ta ce, "Hassana,Husaina maza Oya kuje ku kwanta wannan lamarin yafi karfin kunnuwanku muje daki maza."


A hankali Dady ya ce, "Inna Dan Allah kiyi hakuri in sha Allah ba abun da zai hana a hada Ameenatou da Ɗan Uwanta kiyi hakuri Dan Allah."



Gyara zama ta yi ta ce, "Audu,Audu,Audu sau nawa na kiraka?"


"Sau uku." Cewar Daddy.



"To ina so a ɗaura Auren Ameenatou da Al-ameen a gobe.........


_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_
[12/12, 9:15 AM] Xayyeesherthou: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_



*LAST FREE PAGE-20*

_*Wannan shine fejin kyauta na karshe duk mai son ci gaba da karanta AMEENATOU zai biya 300 kacal tsarin yadda za a biya na kasa😹💔Masoya a hito ahadamun kudin tafiya dubai, ku nuna mun soyayyar ku ta hanyar siyan littafinnan eheeen masu sata😰🙏🏼 kuyi hakuri in kinsan zaki siyane dan ki fitar mun dan Allah kar ki siya*_

Dady ya zaro ido

"Inna Gobe fa ki ka ce? Gobe kuma? Ina laifin Ki bari a hada dana Nauwara karshen watannan?"


"Audu na ce adaura Auren Ameenatou da Ameenu gobe in dai ni ce uwar da na haifeka."


Cikin firgici Dady ya ce, "Inna ki mun wannan alfarmar Dan Allah."


Kara fashewa da Sabon kuka kaka tai tana yi Ameenatou na tayata.

"Yanzu ni ban isa da kai ba kenan ko Audu? Matan ka sun shanyeka sun baka Nono ka sha ince bani ba?

Ta janyo zani tare da face majina.

"To na rantse sau saba'in da bakwai harda digo biyar in baka Aurawa Ameenatoun dan uwanta ba,bani ba kai ."


Dady ya ce, "Abun bai kai ga haka ba Inna,In Sha Allah za a yi yadda ki ka ce."


Ba tare da ya jira maganar Kaka ba ya tashi kawai cikin sarkakiya ya nufi ɗakin Hajiya Babba.


Dafa kansa ya yi tare da zama agefen gado .


Karasowa Hajiya Karama tai ta dafasa tare da fadin, "Alhaji lafiya kuwa? Ka san dai ba cikakkiyar lafiya gareka ba,kada ka daurawa kan ka damuwa dan Allah,komai ya yi zafi maganinsa Allah."


"Maryam ya Inna take so inyi da rayuwata Don Allah? Ina zan sa kaina, yanzu Al-ameen ya zai yi da Ameenatou wai cewa take fa Gobe adaurawa Al-ameen Aure da Ameenatou."


Duk da kasancewar abun ya taɓa ta har cikin ranta amman sam bata nuna ba.

Zama tai daf da shi tare da sake masa murmushi, "Wannan sam ba abun damuwa bane Dadyn Al-ameen ni duk tunanina ma wani abune, Ameenatou da Al-ameen duk ɗayane awajen mu,miye laifi dan Inna ta ce a haɗasu aure? Jifan tsuntsu biyu zamu yi da dutse daya,mu taimaketa na maraici sannan mu zaba mata miji wanda ba zai cutar da ita ba,ko ma ya Ameenatou take dole haka Al-ameen zai yi hakuri Yar uwar shi ce ba yadda zai yi."



Dady ya gyara zama "Hmm Maryam! Al-ameen bai kula matan nan bama sai Ameenatou? Kuma wai aure a gobe? Ni na ce ma ta bari zuwa karshen wata a hada dana Nauwara amman sam taki na rasa ina zan sa kaina zuciyata zafi take mun."


Hannunsa ta rike tana, "ka nutsu dadyn Al-ameen akwai lokacin da komai zai sauya,yanzu ba duk wannan ba biyayya ga Inna shine farko,ka kirawo Alhaji Adam anjima ka sanar da shi komai, gobe a daura auren, Al-ameen kuma in sha Allah zan kirasa cikin darennan mu tattauna ,ni dai kawai ayiwa Inna biyayya duk sauran abubuwan masu sauki ne, kuma dama ga gidan cen naka an kammala komai ina jin har kaya ansa so ba ma da wata matsala mu mu zauna anan ba sai mun koma ba shi Al-ameen da Ameenatou su koma,ina fatan watarana muyi alfahari da biyayyar da mukai wa Inna."




Ɗagowan da Dady ya yi ya sake wa Hajiya Karama Murmushi, "Maddala da samun mace ta gari mai son farinciki da inganta rayuwar Ahalinta,yanzu bara naje na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login