Showing 33001 words to 33950 words out of 33950 words

Chapter 12 - Mr Romantic Book 2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

385

Yana furta hakan ya juya yana kallon Inna kana yace " Duk tsawon Wancen lokacin da banyi Aure ba , Inna ce take dakatar dani daga yin hakan ,saboda a kullum Maganan ta shine na dawo gareki,amma nayi fushi a lokacin bisa abin da kika yi mana , wannan yasa nayi jinkiri da ma duk abin da kika ga nayi Miki a Compani na . Ba wai ban san ki bane , sanin kan ki ne har abada ba zan taɓa son wata ya mace kamar yanda naso ki ba Sakina ....shiru yayi yana jin saukar kukan ta a hankali wanda ta rasa bakin magana , tabbas karanci da halarci Bata taɓa ganin irin Rayyan ba . Gani tayi ya juya yana cewa " Inna a yau za'a dawo mun da Sakina gudana,zuwa Anjima zansa.....to yayi mara kunya! Fice ka bani wuri ,wannan ba huruminka bane sai abin da Sakinan ta yanke hukunci.......!

**
Zaune Asabe take a cikin madafi tana fyare Dankalin hausan da Ɗanjinjiri ya kawo masu suci da wannan safiya . Hannun ta takai tana matse cinyoyin ta wanda take jin gaban ta na mata Wani irin ƙaiƙayi ga fitar da farin Ruwa sakamakon cutar sanyin da ta dauko wurin neman Mazan da Ƙawarta ta daurata a hanya . Kallon Magungunan da Mijin ta Ɗanjinjiri ya sayo mata tayi ,maganin sanyi ne kasadan kwana biyu da take amfani dashi ne yasa ta taji sauƙin al'amuran . Shi a tunanin shi cuta ce kawai daga Allah,abin ka ga miji mai adalci bawan mace irin dan jinjiri fita shiga sai ya kawo mata maganin sanyin Nan . Wasu irin ƙwallah ne suka fara bin Kuncin Asabe , Tabbas na zalunci mijina . Na yi kallon kyalkyal na duniya ,naje na yasar da mutunci na dana y'a'yana . Asabe ...! Asabe...!


Muryar Malam Ɗanjinjiri ya katse ta wanda cikin sauri tare da biyayya ta amsa shi da na'am malam ".

Kan sa tsaye ya shigo ciki yana miƙa mata baƙar leda wanda ke dauke da kayan cefane . Amshi Wannan ,doya ce da kayan yaji na saya mana , Ko zuwa Anjima kwa girka idan kuna buƙata '. Ɗago ido Asabe tayi tana kare ma mai gidan nata kallo ,tare da bude baki zata yi masa godiya kawai sai hawaye ya fara bin kuncinta . Muryar ta na rawa ta kai Gwiwowin ta ƙasa tana fara cewa " Malam Don Allah kayi hakuri bisa Saɓanin da muka yi ta samu ka yafe mun abubuwan da nayi maka na rashin tausayawa da cutar da kai da nayi......kayyya! Haba Asabe , menene haka kuma ? Tashi maza kar yara suxo suga hakan . Komai ya wuce Allah ya kara bamu zaman lafiya. Da ma duk wasu iyalai da suke cikin Matsalar da muka shiga a da baya Allah su ma ya fidda su ya nesan ta su daga kaidin shaiɗan . Amin malam na gode.!

**
Ɓangaren Mr romantic kuwa Malam maleek yanda yake yi ma Hasile shine ya bata damar sakin Dan jikin ta dashi , duk da ganin farko da tayi masa Taji tabbas tasan shi a rayuwar ta amma kuma rashin sanin inda Tasan shi din yasa ta Yin masa shiru sai dai duk abin da yace da ita babu musu . Abinci ya fara bata ,kana ya riƙo ta suna nufa Privacy . Bin Toilet din take yi da kallo don ita bata san nan ina ne ba , Su sun saba shiga mai daɓe . Yaya na ina ne nan? . Lulun idanun sa ya zuba mata kana yace " Nan Toilet ne ,anan zamuna Rinƙa Wanka da alwala da sauran su . Ɗagowa tayi tana kallon sa sosai kaman mai tunanin Wani Abun kana tace " to Ni me zanyi anan yaya na ? . Murmushi yayi mata kamin yace " Wanke amarya ta xanyi tasssss yanzu nan . Ɗago da kyawawan idanun ta tayi tana dan narke masa idanun ta na yin rau-rau kana tace" A'a Ni nayi Wanka kamin nazo nan . sorry my Hafs . Wannan gashinnnan ki mai cika zan wanke da man jikin ki sai muyi barci ko? Ki saki jikin ki babu abun da zan Miki .

Ya za'a yi na yarda da hakan yaya na?.

Tayi maganan tana mai cuno dan ƙaramin bakin ta tare da ja baya tana yin dan nesa dashi . Ba zan cutar dake ba Hafsa . Kin manta Ni ? Amma ki yarda Ni yayan ki ne ,idan muka gama zan baki labarin yanda akayi na sanki har na fara jin soyayyar ki a zuciya ta . Amma Ina so kisa ka a Ranki Da ina mugun ƙaunar ki Hafsa, soyayyar tayi mun yawa . Harshe ba zai faɗi dai dain ta ba . Kayi mun alƙawari zaka kula dani sosai..............? Me yasa ba zan kula dake ba Hafsat nayi Miki Alƙawarin hakan .Saboda ina matuƙar ƙaunar ki . murmushi tayi tana cewa " Tom Shknn taho ka gyara min gashin nawa ,amma kamin A hankali. Murmushi yayi yana isowa ixuwa inda take , kana yakai hannun sa yana dafa ta tare da tallabo kuncinta. Hafsat kece shiriyata sanadin ki Allah yasauya al'amura da dama . Ina Son ki...! Ina ƙaunar ki har abada ba zan daina hakan ba inshallah . Murmushi tayi masa wanda sai da side dimples din suka loɓa . A hankali ta sunkuya tana zama yana fara Warware gashin nata wanda yawon shi da tsawo ba'a magana . Sabulan wankin kai yayi mata amfani dasu iri iri kamin kace mene wurin ya hautsine da ƙamshin sabulai masu tsada da Daɗi . Cike da Bara ya shigar da ita cikin baf din yana Warware zanin ta tare da cire rigar jikin ta................!

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login