Showing 24001 words to 27000 words out of 33950 words
ki ɗaya babu daɗi ganin al'amarin yake tamkar ba a gaskiya ba ,koda wasa bai taba kawowa Amiinin sa zai yi masa irin haka ba a rayuwa . To shi ake ce mawa wanda ka yarda dashi kake masa kallon masoyi shine macucin ka mai kuma san ganin bayan ka . Ya ilahi kayi mana tsari da abokai masu hali irin na Ruslaan. Tabbas wannan izina ce gare mu da mu himci sau da yawa wanda muke masa kallon su muke So basu ne masoyan mu na gaskiya ba . wani ƙayataccen falo ya shiga inda na hango komai na wurin kalan milk mai haske . Ga wani farin carpet da aka shimfiɗa tun daga farkon saka ƙafarka har zuwa tsakiyar falon . Hango Daddy yayi zaune hannun sa Ɗauke da Magazine gyefe guda kuma fruits ne a wani basket bowl ƴar madaidaiciya mai ƙyaun gaske ,domin shi ma'abocin son kayan itatuwa ne . Gyefen sa guda kuma ruwa ne na shan sa domin lafiyar sa ta yau da kullum . Cike da Rashin karsashi Maleek yayo masa Sallama kana ya tako zuwa inda Daddy ke zaune bisa Cushine din falon .
Mamaki ne ainun ya bayyana bisa fuskar Daddy ganin yanda Maleek ya zube a ƙasa tamkar bashi ba , yana ƙasa da kan sa cike da ladabi tare da cewa "Daddy Barka da Warhaka . Ya aiki Maleek? An dawo kenan ?. Daddy ya katse shi cike da son ganin bai tirsasa son Sanin me ya jefa Maleek cikin damuwa haka ba , sannan bangare guda na zuciyar sa yana mamakin ganin sauyi irin haka daga gare shi . Nan take Daddy ya fara tunanin ko Abdul ya amince da Auren sa da Nihila ne ?.
Daddy magana nake so muyi idan ba damuwa don ALLAH . Hummmmm..... Ajiyar zuciya Daddy yaja mai ƙarfi kana yace " Maleek ina sauraren ka . Meke tafe da kai haka ?.
Shiru Maleek yayi tamkar mai tunanin abin da zai fadi na kusan mintuna biyu Daddy na jiran tsammanin maganan tasa amma shiru wannan yasa shi cewa " Maleek ina sauraren ka , yau kuma tunani kake yi don zaka faɗa mun magana . Ni mahaifin ka ne ,ka faɗa mun koma menene idan magana ce akan Hajiya kaka da matsayar da muka zartar akan ka , kana da damar kayi duk abin da kake so ba zamu tursasa maka kan dole sai ka Auri Nihila ko ita Wancen Baturiyar ba. Ko a musulunci ba'a hana Auren ka da Christian ba . Dad...! All is not". Ba wannan maganan ya kawo Ni ba A yanzu . Maleek ya katse Daddy yana ɗago da idanun sa tare da kallon shi sai kuma ya kara kasa da kan sa . Daddy don Allah kayi hakuri ka yafe mun duk abin da nayi maku nakin amincewa da Auren da kuke so nayi . Daddy a yanxu a shirye nake da na amshi ko wani abun da kuke so nayi . Ko auren Nihla ko Jenny . Hummmmm ....Daddy Amma Ina rokon alfarma daya ,ku taimaka mun a yanzu ku Aura mun wacce nake So ,zan rike su duka amana .
Ban gane ba Maleek meke faruwa? Yimin yanda zan fahimta kana da wacce kake so ne ?.
Yes Daddy . Hafsat itace nake so . Wacce dai ka sani a yau na ganta ,gashi ba zan yi naga na mallake ta ba Daddy zaku amince wallahi a yanzu ko waye zan Aura indai zaku Aura mun Hafsa . Hannu Daddy yakai yana dafa shi tare da kokarin kwantar masa da hankali kana yace da shi ya masa bayanin komai tun daga farko ne Maleek ya labarta masa komai Babu abun da ya rufe mawa mahaifin nasa ,wannan yasa Daddy jan dogon ajiyar zuciya kana yace " Alhmdlh Allah na gode maka da ka nuna mun wannan rana . Maleek kasani Allah yana son ka da Rahma da har kasan kayi laifi kuma ka gyara ka tuba. Allah yayi maka Albarka . Sannan ka sani Ni ba zan maka dole ba , ka bayyana mun wacce kake so ,don haka ita ce zan tsaya don ganin ka Aure ta . Daga yau zuwa gobe ku shirya zan koma da ita inda aka dauko ta . Sannan magana ta gaba , Nihila zata fidda miji ita kuma Jenny ta koma America inda ta taho . Allah Ubangiji yayi maka albarka ya kuma saka ayi wannan Aure lafiya . Ya kuma shiryar da matasa wanda suka dauko dabi'a irin taka a da . Yanzu kaje zan yi magana da Hajiya Rahinat da Ammie , zuwa safe zan nemeka . Allah ya maka albarka .
Amin Daddy . Maleek ya furta tare da miƙewa yana ficewa da ga falon.
**
Tun daga Wannan rana Daddy ya maida hankali sosai akan lamarin yaron nasa . Kaman kuma yanda yace a washe gari yasa aka maida Jenny ƙasar ta , bayan nan tsawon kwana uku bai yi ma kowa magana ba ,har su Momy da har yi wannan lokacin basu san komai ba . Abun yana juyawa ne a iya tsaknini mahaifi da Ɗan sa . Sai a kwana na hudu ne yasa su Ammie suka taho . Anan yake labarta masu komai ,sannan kuma yace zai samu Malam Aminu don suyi tafiyar maida Hasile ruga da su dashi duka . Kuma a yanda ya kudurta ba zasu dawo ba sai da Auren yarinyar don shine fatan shi da burin shi . Tun da ta zamana silar gyaruwar al'amara da dama . Tabbas a da baya momy yar a dawa ce a soyayyar Hasile da Maleek amma a yanzu sai taji ta fi kowa son ganin anyi hakan . Zuciyarta yayi zafi kwarai da jin abun da Nihila aka hada baki da ita don ayi ma yaron nata . Anan ta kara ƙaimi wurin ganin tana kai kukan ta ga Allah da ya tsare mata yaron nata a duk inda yake.
Kwana bakwai hasile ta ɗiba a cikin gidan , a yanzu ta saki jikin ta sosai da Maleek , sai dai tsawon wannan lokacin babu abin da yake gani na Firgici ko a razana shi sai idan buƙatarsa ta motsa masa ,wanda ya yanzu yake kokarin yawan yin azumi da jumuri da shan lemun tsami . A Wannan lokacin safe rana da yamma Mommy ke lekowa don ganin Hasile har suyi fira , Duk abin da ke faruwa Nihla tana sane amma ta rasa wa zata yi maganan da shi . Hakan yasa ta kullum cikin kukan zuci .
**
Ke Wacece kike ? Muryar Sectariya ne ya katse sakina wacce ta ɗago tana kallon ta hannun ta rike da kyalle na goge goge . Sakina sunana". Ok wannan iskancin da kike yi kamar mara jini a jika fa? Nan fa ba wasa muke yi ba . Yi ne ko bari . Ɗagowa Sakina tayi tana kallon Rayyan da idanun sa sam baya akan su . Juyawa tayi tana cigaba da goge gogen tare da share sakatariyar , wannan yayi matukar hasala Sakatariyar. Sir...! Ta kira sunan Rayyan tare da cigaba da cewa ' Ya kamata a sallama wannan yarinyar ji da kan ta yayi yawa . 'Duk yanda kika yi hakan yayi ba laifi. Ya furta yana cigaba da taɓa system din gaban sa . Takowa tayi cikin fushi tana fuzgo Sakina tare da sharaara ma fuskar ta Mari tasssssssss. Wani irin duhu Sakina ta gani ,wannan yasa ta juyawa tana kallon inda Rayyan yake a wannan lokacin ita yake kallo . Kuka ta fashe dashi tana takawa cikin zafi zuwa inda yake kawai itama sai ta daga hannu tana wanke fuskar shi da mari ....................!
[11/30, 7:40 PM] 🙂🙂🙂🙂: Mr.Romantic
#mamanteddy.
Ɗauke wuta yayi daga jin kalaman nata , Me hakan ke nufi kenan? Yayi maganan yana tambayar zuciyar sa . Wacece Wannan Bilkisun? Meye halaƙarta da Nihla? Tabbas da akwai Rina a ka ba , it's Sense like itace take ɗaura Nihla a duk wani hanya , in ba haka ba Menene Nihla zata yi da Camera vedio duka don taga rayuwata ko ta samu wata hujja da take son samu don ganin ta shigo rayuwa ta da karfin tsiya , Yess " yanzu na samu amsata Bilkisu itace ta bayan fagen da duk ta ke ƙulla wannan shaiɗanan , but who is she? Wacece ita ? Me kuma take bibiya a gare Ni da ita ma kanta Nihla, Ya akayi ta shiga Rugar su Hasile dole tana da Basira! Ya furta yana mai furzar da huci mai zafi . Rintse Lulun idanun sa yayi yana ware su akan Hasile da idanun ta suka fara zubda Ƙwallah . A cewan ta ita sam fa ba za'a taɓa mata jiki ba .
My Hafs.
Ya kira sunan ta tare da kai hannun sa yana shafa gyfen kuncin ta . Sorry ba Zata yi Miki komai ba, ita wannan mutuniyar kirki ce ba kaman su ba . Kallon sa tayi cike da Yarinta tare da Haukan rashin tauna magana irin na fulanin jeji ta furta "ai kaima Haka kake . Saboda.....Saurin katse ta yayi a dabara ganin Hanne dake watsa masu ido ita dai har yanzu ta rasa fahimtar Wacece Hasile? Sai dai abin dake bata mamaki shine Mom Rahinat ta sanar dasu cewa " Ta dauka ma Abdoul Maleek sabuwar ma'aikaciya , amma kuma sai taga ya neme ta don yin aikin sa . To ina Wancen mai aikin nasa take ne? Sannan kuma watannan Wacece?. Tambayar da ita kan ta ke mawa kan ta kenan . No Hafsat ni kaina ki yarda dani na chanja i totally change, duka na sauya , yanzu Ni fa yayan ki ne , yaya ba zai cutar da ƙanwarsa ba . Lumshe ido tayi tana gyada masa kai alamun ta amince . Hanne please be patient, Take good care of my wife .Ok sir . Hanne ta furta tana bin sa da kallo har ya fice daga Bedroom cikin zafin jini irin nasa .
Hummmm.
Numfasawa Tayi yana ƙare ma Hasile Kallo, cike da mamakin kalaman nasa ya fara dawo mata " Be patient take good care of my wife ". Wife? Aaa. Ta yaya yaushe ne yayi Auren ? Whats going wrong? Meke faruwa ne ko nace yake shirin faruwa? . Hummm Gaskiya Abdoul lamarin sa da bambanci dana mutane . Dole nasan Wacece wannan domin na kaima Momy Rahinat rahoto. Keee Hattara! Baki da hankali ne , kika sani ko matar nasa ce . Daga nan sai ki ma kanki salalan Tsiya aikin da kike ciyar da Ahalin ku dashi sai ki rasa ku koma Bara a titi. Taji ɗakin ya amsa mata yana wani irin juyawa da ita . Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una ta furta tana kankenewa da bangon cike da tsoro don almara da Firgici abun ya bata wanda bata taɓa expecting ko jin sa a labarai ba . Ɗaki yana magana kaman mutum . Bin Hasilen take da kallo a lokacin da Juyawar ya fara tsagaitawa . Bakin ta ɓame babu alaman ita ce tayi wannan maganan . Wannan yasa Hanne cikin rawar murya cewa " Wacece Ke? Da gaske ke din matar sace? Mutum ce k........Keeee! Hasile ta daka mata Tsawa yayin da sai da dakin yayi Girgiza kaman zai zube . Ni shiriyarsa ce .! T..ttt...to to kiyi Haƙuri. Hanne ta hau maganan cikin rawar murya .
Banza Hasilen tayi mata , nan Hanne ta zauna kusan mintuna biyar a haka ,kana ta motsa cikin rashin kuzari a cewar ta " Maleek ya dauko Aljana bai sani ba , tabbas rashin jin sa ne yazo Ƙarshe . A zuciyar ta babu abin da take fadi sai Hasbunallahu wani'imal wakeel. Malama Hafsa taho muje na nuna Miki yanda Abubuwan ake aiki dasu ,idan mun fito sai ki ci Abinci . Gani tayi Hasile ta mike tamkar ba itace ta daka mata Tsawa ba , a wannan lokacin ta dawo mata cikakken yar Ƙauyen ta . Baki sake cike da mamaki Hanne ta tasa ta suka yi na privacy don tsaftace Hasile . A zuciyar Hanne cewa take " Dama komai yayi farko zai yi karshe , Maleek yara nawa yake lalata da su yanzu ya dauko wanda ba Mutum ba , dama ina yawan jin haka a labarai sai kuma gashi i see the real. Da idanuna na ga Gaskiya , kai naka ƙiyamar ta tsaya kenan ,mu kuma Allah kasa mu cika da imani idan namu ta zo .
Ohk sir .
Lemme inform him ".
Wani irin kallo Maleek yayi ma John kana cike da mulkin nan nasa yace ' No bana buƙatar hakan , yo don xan shiga private room na Ruslaan sai ya zama dole sai an sanar dashi a yau ?. Jikin John na ɓari ya furta " I'm sorry sir . Girgiza Kai Maleek yayi a Miskilance ba tare da ya tanka John ba ya fara nufar direct to Ruslaan's private room .
Muryar ta yake ji mai cike da Amo suna wani irin sakin Dariya wanda rabon da yaji Ruslaan na irin ta ya manta tsawon shakarun . Murmushi Maleek yayi cike da ƙarfin gwiwa yasa hannun sa yana murɗa Handle Door din da sunan ya bude , but unfortunately sai ya fara jin abin da bai tsammani ba ko zato . A rayuwa ta ,tun ina yaro babu wanda na tsana sama da Maleek , Abdool Maleek na tsane shi Tun a yarintar mu har ixuwa yanzu girman mu . Bama taɓa yin abu bai sha gaban mu ba . Ga kafiya kullum he pretend like a king , kaman sarki haka yake rinƙa son juya mutane , akwai wanda ya haifa ne .? Yau zai san sharrin Abota! Na haɗa masa plan da jinin sa a halin sa , don ganin bayan sa . Kin tabbata an saka mata Wannan Camera din . Of course my boss ". Billy ta furta tana kwantar da kan ta bisa ƙirjin sa tare da shafa masa a hankali tana lumshe idanun ta kaman mai jin barci . Motsa laɓɓanta tayi tare da cewa " kai dai ka natsu ka zuba ido , a kwana biyu kacal komai zai tashi .kasan shi Hariji ne mayen mata , baya duba kyau ko muni burin shi yayi aiki ....bare kuma ya ga wannan zazzafan ai bance maka a wunin yau yayi komai ya gama ba yanzu haka . Don haka vedion nan na Tsaraicin sa da Yanda yake lalata mata zamu watsa shi a duniya . Ce masa da ake yi mutumin kirki daga wannan lokacin ya kare . Amma hanzari ba gudu ba . Tayi Maganan tare da saurin kallon Ruslaan . Gyada matakai yayi yana kai cup din lemu bakin sa tare da dan kurɓa kana yace " Menene? .
Ina jin tsoron wannan yarinyar kwarai? Naga abubuwa da dama da yawa akan ta , tun da na dauko ta . Ibeg shut up please.! Bata da komai duk da ban ganta ba , kila kinji tsoron ta ne , sannan kuma kin san shi haka yake tamkar mai siddabaru . Mai bada taimakon Asibiti a ga Vedion sa yana cin ya'yan jama'a hahahaha........... Ruslaan ya wani fashe da Dariya . Well said . Ya furta yana kai hannun sa tare da Rungume Billy jikin sa . Kayi mun Alƙawarin Aure idan na cika maka burin ka , yaushe ne bikin mu . No there's time to....Akwai sauran lokaci Billy , mu bari ya faɗa tarkon namu tukuna.
Zafin zuciya ne yasa Abdool Maleek murɗa Handle din yana shiga falon kaman mayunwacin damisa . Wani irin bugawa ƙirjin su yayi da karfi tare da mamakin ganin Maleek a tsakiyar wannan lokaci . Abokina mai ya faru ka shigo haka kaman kana da......Ya isa! Stop pretend! Ya kamata ka dakata da wannan wasan kwaikwayon naka . Now I see and I understand who you are? N fahimci Waye kai Ruslaan na kuma ji duk abin da ka fadi da kuma son ganin ka tarwatsa mun rayuwa . Ruslaan You Are the First person da ka fara koya mun Yanda zanyi Zina da mata , ashe tsawon lokacin nan don plaan din ka kake yin min haka ? Ashe burinka bai wuce kaga na tozarta na wulaƙanta ba? Mene ne damuwar ka akan ganin sai kaga bayana Ni Maleek? Bayan ka manta Ni babu mai ganin bayana sai ALLAH. Ku sani plan din ku ya rushe . Ba zaku taɓa samun wata illa ko abin da kuke so na sharri ba . Sannan nazo ne nayi maku godiya, domin kuwa daga yau maleek ba zai ƙara zina ba har abada .kun san dalilin godiya ta gare ku? Hummm....Sanadin ku yau gashi kun kawo mun matata har gida! Hasile itace yarinyar da nake so tun tana yar shakaru bakwai zuwa takwas a duniya Yau gashi na ganta matsayin cikakkiyar mace wanda zamuyi rayuwar aure ,mu hayayyafa ..ko a yanzu abota tayi mun . Thanks one again Ruslaan na gode Ƙwarai .
Cike da borin kunya da tacewa Ruslaan ya wani mike tsaye yana cewa " A'a Ni ban fahimce ka ba ,wai duk maganan naka mene kake nufi? Wani ne ya bata maka rai?.
Zuciyar Maleek ne ya harsala kunsan shi da zafi ga fushi . Ba tare da Ruslaan yayi Aune da isowan sa gaban sa ba ,shi dai kawai yaji saukar damtsan Abdool Maleek ne a fuskar sa ta Gyefen dama ,ji kake bummmmm! Kaman ya dagi bango . Baya Billy tayi jikin ta na kyarma tana furta Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una na shiga uku Maleek ka taimake Ni kar ka kashe mu . In kashe ki in kashe banza! Do mun kaf dangin ku Babu mai arzikin bi Miki haƙƙin ki . Ko wannan dabban Bai isa ba ko da shi ne kuwa naga bayan sa baya da Arzikin da zai iya yi mun wani Abu ,don na fishi kaman sama da ƙasa . Maleek hakori na ne fa a ƙasa? Muryar Ruslaan ya katse shi wanda bakin sa ke tsiyayar da jini . Yess wannan kaɗan