Showing 15001 words to 18000 words out of 33950 words

Chapter 6 - Mr Romantic Book 2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

384

Zaka tafi da ita ba sai ka jira Wata Uwani ba , Nan wata zuciyar ta danne da da cewa " Idan Momy ta fahimci wani Abu to tabbas mafarkin ka ba zai taɓa cika ba . Dole kayi zurfaffan tunani akan lamarin . To amma kuma tayaya Hasile ta shigo cikin gidan nan? . Maleek.! Muryar momy ya katse masa tunanin sa . Ok mum ni na tafi kawai . Tom . Ta furta tana bin bayan sa da kallo har ya fice ,bayan fitar sa ne Ta kalli Nihla kana tace " Dole sai Uwani ta gyara wannan baƙauyiyar , saboda Idan taje a haka maleek ko ruwa ba zai iya haɗiya ba da sunan sha". Caɓe baki Nihla tayi tana furta " Gaskiya fa kam . Nima Bara na haye sama na kwanta sai zuwa Anjima na sauko . Ok . Mummy ta furta tare da juyawa Nihla na barin falourn tana barin ta da Hasile dake ta bin ko ina da kallo . Uwani...! Mom ta kwaɗa kiran sunan Uwani tare da ware idanun ta tana duban hanyar shigowa , gigif tayi tana saurin kara buɗe idanun ta tare da murzasu tana mutsika su ganin fuskar Hasile a hanyar shigowan Uwani...Rufe idanun ta tayi cikin sauri tana buɗe su tare da ƙara kallon wurin da kyau , ganin ba kowa yasata juyawa bayan ta nan ta tadda hasile riƙe da Hannun ta a rakuɓe babu alamar ta motsa daga inda take tsaye ma . What's going on? Mam Rahinat ta furta dai dai Uwani na shigowa.
**
What? Maleek mene kake cewa? . Yes! Yau fa na ganta Rayyan, da gaske na ganta kuma da idanuna itace ba gizo ko mafarkin nan dana saba yi ba. Kai Maleek wannan ban yarda da zancen ka ba sam . This can't be possible, yarinyar da ka santa tun tana ƙarama can ƙasa , kar ka manta gani daya kayi mata fa a rayuwa Kum....katse Rayyan Maleek yayi yana cewa " Of course yes Rayyan , kallo ɗaya ya zama kallon da har duniya ta naɗe ba zan manta da fuskar ba , kallo ɗaya ta samu gurbi mai ƙarfi a Zuciya ta , tausayin ta shi yafi komai tasiri a zuciya ta . Tabbas wannan ba mutum bace Maleek , yau Nima na bi rakiyar Momy da kullum take cewa" Aljana kake so ba mutum ba . Yanzu har abin ya kai ta fara bayyana maka kan ta a zahiri...? Dafe kai Maleek yayi yana furta " Ohhhh...! Rayyan You Are a man , kar ka zama mace mana! Kana kokarin gino tunanin ka irin nasu Momy .....!

Wai shin kuma me kuke gani da wannan labarin Wacece Hasile ? Mutum ce ko Aljana? #Bonus .

*Littafin mr romantic it's paid book ₦500 regular payment Vip payment ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank. For more enquiry contact 08081202932*
[11/30, 7:40 PM] 🙂🙂🙂🙂: 💋💋💋💋💋
*MR. ROMANTIC*
💋💋💋💋💋

_*Story and Written by:*_
_Anty Aysha Mohammed_
_(Maman teddy) ._

_Page 20-21_

*Ban yarda wani ko wata su juya mun wannan labari ta ko wani siga ba , domin kuwa wannan labari ƙirƙirarre ne daga memory ɗina ,ban rubuta shi don wani ko wata ba , haka ban yarda a ɗaura mun wannan littafi a ko wani manhaja ba tare da sani na ba , yin hakan kuskurene , idan kunne yaji gangar jiki ya tsira.*

*Labarin nan na kudi ne Regular payment₦500...Vip payment₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 , ban yarda Wani ko wata su karanta ba tare da sun biyani gumi na ba , Idan ka karanta ki karanta Kema keda Allah*

Ransa duka babu daɗi tunanin abubuwan da suka faru yanzu yake yi . Wuce ma'aikatan Mom Rahina yayi yana nufar Up stairs din ta inda Bedroom din ta yake , kai tsaye ya murɗa Handle Door tare da Shigewa . Kai Mashaallh. Ko ba'a faɗa maka kai daga jin yanda Wurin ke tashin ƙamshi zai tabbatar maka da Momy mace ce mai tsafta ƙwarai bata shiri da ƙazanta . Komai na Bedroom din ta mai launin duhuwa Arsh colour , Window manya biyu na kallon junan su . Ga bedroom din babba yalwataccen Gaske . Hatta cottns ɗin ta (labulaye) suma kalon ruwan toka ne masu kyau .

Jan wani numfashi yayi a hankali yana saukewa tare da zuba manyan idanun sa bisa wani ƙaton frame da ya kusa mamaye rabin bangon Bedroom din , Wanda frame din ke dauke da hoton sa dana Daddy sai Mommy Rahinat. Takawa yayi yana isa Gaban frame din tare da kai hannun shi yana shafa Hotunan iyayen nasa da yake jin zafin son su a zuciyar sa . Me yasa Daddy ya sauya ne ? Yayi maganan yana kallon Fuskokin su a wancen lokacin dake fidda Annuri , Gimtse fuska yayi tamkar wanda Dad ke a gaban sa kana ya furta " Dawowan sa Nigeria shi ya sauya shi , lokacin xaman mu a America ba haka yake yi ba ai sam . Yanzu wai har Nine za'a yi ma Auren dole ana ƙoƙarin ƙaƙaba mun Ragowar ƙwarata mtsww! Yaja guntun tsaki yana cigaba da kallon hoton . Maleek".

Muryar Momy Rahinat ya katse shi wanda bai ji motsin shigowan ta ba sai dai maganan ta daga bayan sa da yaji . A hankali ya Juyo yana zuba mata idanun sa da suke tsaye babu alamun tsoro ko nuna damuwa don jin zancen iyayen nasa da kuma na Hajiya kaka . Na'am Momy ".

Maleek yanzu abun da kayi kana kyautatawa? Yanzu fa ga baturiyar mutane can na kaita ƙaramin Falour na , wannan wani irin Abu kake yi ne ? Yanzu me kuma kake nufi? .

Ohhh ..!
Ya furta tare da dafe kan sa yana kallon Mommy idanun sa na kaɗawa lokaci guda. Cikin Arrogant voice din sa ya fara magana da cewa " Mom ke ma tension kike son ɗaura mun? Nifa babu ɗayar su da nake so . Kin san wace nake so momy! Kin san itace kaɗai mafarki na , Tayaya zan so nayi rayuwa da Wa'annan sam basa lissafi na. Ina Jenny take ???. Yayi Maganan yana ƙoƙarin wuce Mom Rahinat tare da jiran jin me zata ce masa game da inda Jenny take , don ya kuduri ci mata mutunci wanda da ƙafarta zata bar Nigeria ta koma inda ta Fito.

Dakata!

Muryar Mom ya katse sa tana saurin kallon sa tare da cewa " Ina zaka tafi a wannan yanayin? Maleek yarinyar nan fa Zuwan ta abun tausayi ne ,baka ga inda tazo ba ,Allah ma ya kiyaye ta iso nan Lapiya. Tausayin ta ne yasa Dad din ka cewa a barta tayi kwana biyu sai ta juya .

Ohk Daddy ya tausaya mata ,amma Ni kuma ya faɗa mun magana That means Bai damu da tashin hankalin da zan shiga ba . Cox....ya isa Maleek please. Ya isa haka! Yanzu koma ka zauna, idan ma barci zaka yi ga Bed can , ka huta dai , zuwa Anjima zamuyi magana . Ta ƙare maganan tana kai hannun ta tare da zaunar dashi Gyefen ƙayataccen gadon ta .

Shigowa Falourn Nihla tayi tana gaba Hasile na biye da ita a baya , a tsorace Hasile ke tafiya don tsaruwan Falourn da kayan alatun da aka zuba wanda ko a labari bata taɓa ji ko ganin irin su ba yasa ta yin ɗar² tana biye da Nihla dake ƙwada kiran sunan "Momy..........!
[11/30, 7:40 PM] 🙂🙂🙂🙂: 24-25






Kar ku manta masoyana wanda basu san da budewar channel dina ba yanzu zaku iya shiga YouTube naku kuyi Subscribing channel Dina mai suna MAMAN TEDDY mun gode! https://youtube.com/@mamanteddy4123?si=1cwxAAGsGEzYkelS

Ga kuma link zaku iya shiga ta hanyar clicking kai tsaye👆🏻.

Ga masu bibiyar littafaina kuma ga list din su 👇🏼.

*SOME PRICE OF OUR NOVELS:*
📚MAMAN TEDDY NOVELS

1. KWARTON MANYA N500

2. FYADE N1000

3. SIYASATA N300

4. THE SEXY BOSS N500

5. WALIJAM N500

6. MY LADY BOSS N500

7. YAR AIKI NA N200

8. BINTOTO FREE

9. THE VIRGIN MAID N500

10. GIDAN KWARATA N300

11. SEXXIES HOUSE N500

12. YAR WAYE N300

13. KWARYAR SAMA N300

14. DIJAMA YAR FULANI N300

15. SADAKA YALLA N500

16. BAFULLATANAN RUGA N300

17. ZUMA DA MADACI N300

18. DUNIYAR SHAHARA N600

19. YAR MAULA N300

20. TABARAH N500

21. YAR TSAKAR GIDAA N600

*WhatsApp no_08081202932*
*Zaku iya shiga manhajar ku na YouTube channel domun samun Audio books na maman teddy, zaku same su a channel Dina mai suna MAMAN TEDDY https://youtube.com/@mamanteddy4123?si=1cwxAAGsGEzYkelS*
*©AISHAT MUHAMMAD*
*(MAMAN TEDDY)*



Please be like a rigid person namiji tsayayye....No"Maleek that is not the best way for us , sometimes ka zama flexible ma yana da amfani . Kar kayi ƙoƙarin zama mutum da ba'a iya tanƙwara shi kayi tunanin rayuwar ka will be Okay, Hakan ba zai yiwu ba , Momy dole tafi mu sanin Wasu abubuwan musamman abun da ya shafi Rayuwar mata ,mufa maza ne , sannan kuma ita..... It's Okay please! Ya ishe Ni hakan Rayyan , at the first time nayi tunanin kana da Ƙwaƙwalwa ashe kaima mata ka rako , Har kaima ka yarda Hafsat ba Mutum Bace kenan . To ko Aljana ce ina Son ta , kuma zan Aure ta! ƙoƙarin masa magana yake yi ƙitt yaji ya datse kiran , dakatawa Rayyan yayi yana kama kan sa tare da lumshe idanun sa , Motsa laɓɓan sa yayi yana cewa " Tabbas da akwai matsala, Nima na fara sensen wani abu gami da Wannan Yarinyar, Gaskiya bana jin yarda da ita a zuciya ta. Amma kuma kai ne baka yi masa bayani yanda zai fahimta ba . Wata zuciyar ta katse shi ta hanyar furta masa wannan zancen . "Humm"Numfasawa yayi kana yace" Kwarai nine nayi Kuskure, Amma Wannan Wacce irin soyayya ce yake yi ma wannan yarinyar ? A takaice ma ina so na ƙara sanin labarin shi akan wannan yarinyar, Duk dukiya da ilimi ga gayu na Maleek ya shirya Auren wannan yarinyar har yana faɗa akan ta ,tare da shirin yin koma meye akan tabbas da akwai Matsala, Ni ban yarda Maleek zai iya rabuwa da Jenny ba , shi da bakin sa yake faɗi bai taɓa jin daɗin mu'amala da ko wacce mace ba kamar ta ba , amma a yanzu ya gummaci ya fasa Auren ta ya Auri yar Ƙauye jahila? Mara wayewa? Humm , Tom ya Auri Nihla mana. Duk maganan Rayyan yake yi kana ya lumshe idanun sa yana maganan zuci da cewa "tabbas so masifa ne , Nima nayi wannan Rayuwar, still har yanzu zuciyata bata Warke daga Wannan famin ba , sannan Kuma har abada bana tsammanin Zan iya rayuwa da Wata mace bayan............... Magana sa ce ta ɗauke sakamakon jiyo knocking da ake masa wanda babu shakka yasan Sectariyan nashi ne da Sakina wacce tun da ta shigo Idanunta ke akan Sir Rayyan,wanda a yanzu ta gama yarda da zancen Mama kan cewa " Ba Rayyanun ta bane".

"Morning Sir "

Muryar Sectariyan ya katse shi , yayin da ya gyaɗa mata kai ba tare da ya amsa ta ba yana cigaba da Aikin sa tare da tsagaitawa da tunanin da yake yi .

Kallon Sakina Sakatariyar tayi tana caɓe baki tare da cewa"Tom Hajiya nan dai shine Office din da zaki na rinƙa gyara shi kullum , Bama son ganin abun da ba dai dai ba , sannan yanda kikayi shigar ki ta yau kullum haka zaki na rinƙa yi , kar bayan kwana biyu ki fara zuwa mana da datti a jiki ko kaya babu guga, idan aka fara hakan zamu Koreki . Shiru Sakina tayi don gaba ɗaya Ƙwaƙwalwar ta ya daina fahimtar komai ,idanun ta duka ta suba su akan Sir Rayyan,wanda yayi tamkar bai san da Dasuwar ta ba . Aikin banza! Muryar Sakatariyar ta katse ta cike da doka Tsawa ,kana tace " anya ke kina da hankali ba dabba Bace ? , Nan kin san ina kike kuwa? Dama idan talauci yayi yawa hauka da doɗewar basira sai ta shigo ciki . Kina ganin Sir Rayyan baki san ki gaishe sa ba ke ga hamshaƙiyya. Kiran sunan ta Rayyan yayi tare da dakatar da ita da cewa"Ki tafi zatayi aikin ta".Ok sir. Ta furta tana barin Office din cike da jin tarin takaicin Sakina a zuciyar ta .

Cigaba yayi da Aikin sa idanun sa na akan system din dake gaban shi .

Jikin Sakina sosai yayi sanyi , haka zuciyar ta na wani irin kuka mara amo, tabbas yau idanun ta na ganin mata abun da ko a mafarki bata taɓa tunanin mafarkin ganin hakan ba . Sam bata san lokacin da bakin ta fara furta " Rayyanu kaine kaine wallahi...Ko a makanta na ganka zan gane ka ba tare da sabarmun ba! Rayyanu Tsafi kayi ne? Tsafi kayi......Keeeeee!!!


Muryar Rayyan ya katse ta yana doka mata Wani irin Tsawa ,wanda sai da wurin ya amsa haka bugun Zuciyar ta ya ƙara tsananta. Tsafi nayi , wace kike ? Sakina ko? . Ai ko baki sanarmun nasan a duk inda kika ganni ba zaki manta dani ba , amma Ni kuma zan faɗa Miki ki mance da kin san Rayyan, nan aiki kika zo yi, So na baki nan mintuna biyar ki kammala aikin ki ,ki fice mun daga Office .....!


*Littafin mr romantic it's paid book regular payment ₦500 vip payment ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank WhatsApp number 08081202933*
[11/30, 7:40 PM] 🙂🙂🙂🙂: "Sir Maleek".
Ya furta yana mai ƙafeta da Tsayayyun idanun sa , Jikin Hasile ne ya hau kyarma kar-kar-kar . So take ta ƙara furta wani maganan amma kuma ta gaza don laɓɓan ta da harshen ta sunyi mata nauyi Matuƙa. Cikin rawar Murya tare da son janye jikin ta daga gare shi ta furta " Sir Da Hausan ku ai Shanu kenan ko? Kai Meye haɗin ka da dabba ?. Malaak ko malaam kace kana dan malamai kake taɓa mun jiki? Hakan ba kyau ...Ko mace ne ba abu ne me kyau suna taɓa jikin junan su ba .
"Hum"Wani Gwauron numfashi ya sauke , kana ya ƙara ɗaura tausasan taffan sa yana kwanto da kumcinta bisa , yana kafe ta da manyan Lulun idanun sa da suke da shape din ball eyes gasu a warwaje . "Good". Ya furta yana ɗan cizan laɓɓan sa kaɗan kana yace " Eh Ba abu bane me kyau Mace tana rinƙa taɓan jikin yar uwar ta mace da sunan Feelings. Amma ba laifi idan namiji yayi don zai iya yiwuwa ko Ni na kasance mijin ki".
Saurin Jah da baya Hasile tayi kana tace " A'a duka babu kyau liman yana yin wa'azi akan mu guje ma maza , basa da kirki, amma dana zo nan sai naga Adda Bilkisu da Watannan yar nan gidan suna Iskanta junan su tare . "Damm" Ƙirjin sa ya buga a hankali yake kallon ta kana taga ya saki Murmushi yana wata yar dariya a hade tamkar na basawa . Hannun sa ya kai yana jawo ta jikin sa tare da yin ƙasa da Muryar sa yana furta " Baxan cutar dake ba", sai kuma taga ya ɗaga Muryar sa yana cewa" Barka Nihla wannan Shiri naki yayi matuƙar ƙayatarwa , Ko ba komai kin sakani cikin farin ciki sanadiyar ki naga abun da na daɗe ina marari . Amma ki sani daga rana mai kaman ta yau kin fara nadama tare da danasani mara iyaka . Gittttttttt Hasile taji ya fuzge Wani Abu daga bisa kan ta . Wanda tun shigowan ta jikin sa ke alamta masa akwai wani Abu a tare da ita . Wannan yasa shi matsowa gare ta , ashe recording ne ɗan ƙarami Nihla ta sanya mata Wanda ita Hasilen ma bata san dashi ba . Bin Abin yake da kallo ,wanda ko mun ruwa baya lalata shi . Takaici ne ya kamasa . A zuciyar sa yana cewa " Wannan yarinyar mene take nufi? Ya akayi suka dauko hasile daga Inda suke? Gyefen sa ya kalla inda Hasile ke tsaye . Sam bata yi masa kama da Mutanen da suka yi rayuwa a birni ba . Humm " Dan Numfasawa yayi kana yace"Dukan su sai na saka su cikin bakin ciki yanda kullum suke jefa rayuwa ta . Dole dole nayi Rayuwa da Hasile , ko su so hakan ko ba su So ba .
"Saa Malaak magana kake yi Kai ɗaya kuma Sannan kana kiran sunan Adda Nihila Wacce take can a waje ba anan take ba".
"Humm".
Numfasawa yayi ba tare da ya bata Amsa ba , Yana katse duk wata hanya ta na'uran kamin ya fuskantota yana cewa "Sunana Maleek Ba wannan kalmar da kike kirana ne sunan ba". An baki labari na kamin kizo?.
Kallon sa Hasile tayi kana ta Girgiza kan ta tare da cewa " A'a Aradu ban san komai akan ka ba ,amma nasan zaka kasance Mutumin kirki".
Girgiza kan sa yayi yana Cewa" No ,ni Sam ban kasance Mutumin kirki ba , forget all people said , Wancen ba zahirin waye maleek kika sani ba , A yanzu ne zaki fahimci Ni Wanene? .
Kallon sa Hasile tayi maganan sa ya fara Mata tsauri gashi ta gaza fahimtar manufar sa . Wannan yasa ta juyawa tana kokarin barin Wurin tare da cewa " Adda Nihila tace Aiki zana yi kaman gyaran banɗaki da Sauran su . Bari na fara ina ne ....Shiiii "Ya ɗaura yatsarsa bisa laɓɓan sa tare da katse ta ,yana bin ta da Wani irin kallo .
"ba zaki aiki a matsayin mai aikina ba , face matsayin mata ta".
Hasile zaki Aure Ni?
Wani irin bugawa ƙirjin hasile yayi tana bin sa da Wani irin kallo . Zuciyarta na tuno mata da Samarin rugar su tabbas irin haka suka saba mata zance , tana ci masu mutunci amma kuma a wannan karon jin abun take tamkar ba kunnuwar ta dai dai suka ji ba .
"Yallaɓai ina ne banɗakin da zana gyara".
Hafsa baki bani amsa na ba?. Ya kuma katse ta yana neman Wuri tare da zama a ɗaya daga kujerun falon, still idanun sa bai dauke su daga gare ta ba".
"Saurin Girgiza kai Hasile tayi kana tace " Ban fahimci Hausan ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login