Showing 93001 words to 94091 words out of 94091 words

Chapter 32 - Saran Boye Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

270

akan damuwar ciwan ɗiyarsu.

WASHE GARI.

          Washe gari papa ya matsa akan sai Yoohan ya bisa sun koma Abuja. Badan yaso hakanba ya amince zai bisa, dan dama yau ɗinne zai kammala abinda ya kawosa kanon. Yaso komawa wajen baba malam dansu tattauna game da neman iliminsa amma papa ya tsare ko ina ya hanashi matsawa ko nan da can. Asibiti ma binsa yay sukaje tare, ya kuma zauna a office ɗinsa har sai da ya kammala komai suka fito.
      Da ga asibitin airport suka tafi kai tsaye, sai da jirginsu ya ɗaga sannan guards ɗinsa suka ɗauki hanya suma a motocin.

      Baba malam na asibiti wajen duba jikin Nu'aymah da jikinta Alhmdllh saƙo ya shigo masa. Buɗewa yay ya duba ganin Yoohan ne. Murmushi baba malam yayi saboda ganin abinda saƙon ya ƙunsa, a ransa kuwa yana tsananin tausayi da ƙaunar Yoohan, insha ALLAH yayi alƙawarin zai taimaki yaron nan har ya zama HASKEn da zai zama HASKE ga waɗansu.
    Ajiye wayar yay ya maida hankali ga Nu'aymah da Hajjo take lallaɓawa taci abinci amma sai shagwaɓa take ita ta ƙoshi. Ya ɗan murmusa tare da kamo hannunta cikin nashi. “Mamana daure kici ko kaɗanne kinji, inba hakaba fa kinsan Doctor yace allura zai miki, idan kuma kin fison allurar to sai a kirashi kawai”.
     Da sauri ta shiga girgiza kanta idanunta cike da ƙwalla. “Abba dan ALLAH a'a banaso”.
      “To ki daure kici abincin sai kisha magani ki kwanta ki huta. Kinga kince dama kanki na ciwo har yanzu, Doctor kuma yace kina buƙatar hutune sosai”.
      Kanta ta sake jinjina masa. Hajjo da batace musu komaiba ta miƙama baba malam abincin. Babu musu ya amsa ya fara bata da kansa. Batafi spoon huɗu ba su Ahmad suka shigo ɗakin bayan sunyi sallama an basu izini. Ba Nu'aymah kawai ba hatta Hajjo da baba malam da ɗunbin mamaki suke kallon wanda ya shigo tare da su Ahmad ɗin. Ba kowa bane face Nasir jikan yayar Hajjo.
     Babu kunya idonsa fes akan Nu'aymah da mamakin ganin nasa ya sakata masa kallo mai nisan zango. Hajjo ce ta katse su da faɗin, “Naseru yaushe a gari? Inji maƙi baƙo?”.
          Goshinsa yaɗan sosa najin kunyar kallon da baba malam ke masa. Kafin yace, “Hajjo yanzun nan muka iso”.
       “Kuka iso? To kai da wa kuma?”.
Kansa tsaye yace, “Rufaidah”.
      Baba malam da tun gaisuwar daya amsa musu baice komai ba sai yanzu yace, “Lafiya dai ko Naser? Yau ka tuna damu a duniya”.
        “Ayi haƙuri Kawu, ni ɗin mai laifine kam, mun tahone saboda ga biki nata gabatowa, ganin mun sami hutun makaranta mu duka sai kawai nace bara mu taho maɗan huta ai”.
      “Oh to masha ALLAHU, ALLAH yayi jagora to”.
     A tare suka amsa da amin. Nu'aymah dai bata tanka ba, tama ɗauke kanta tamkar batasan mi akeyiba. Sai da Naser ya tambayeta yaya jikin sannan ta gaidashi batare data kallesanba yanzun ma. Shiko yanata so su sake haɗa ido ko zaiji ɗan sanyi a ransa da ruhinsa.
     Miƙewa baba malam yayi yana faɗin, “To ni bara naje gida hajjo, dan ina saka ran zuwan wasu baƙi ɗan anjima kaɗan idan ALLAH ya kaimu. Idan sun wuce insha ALLAHU zan dawo muji ko zasu bamu sallama, banason zama asibitin nan sam”.
      Amsa masa hajjo tayi tare da binsa da addu'a. Nu'aymah ma ma dasu Ahmad sukai masa sallama ya fice. Hajjo ce ta sake cigaba da bama Aymah abincin, badan yana mata daɗi ba take amsa, sai dai mayataccen kallon da Naser ke mata duk ya sake takureta matuƙa, sannan ya tuno mata da wasu shuɗaɗɗun abubuwa dake tdakaninsu a lokacin ƙuruciyarta, hakan yasa taketa cuno baki gaba da ɓata fuska duk da ƙasan ranta cike yake da mamakin ganin nasa ya dawo bayan barinsu na tsahon shekaru da yayi akanta.
          Idan bata manta ba shekara kusan takwas kenan rabonsa da kano. Dan tunda tace masa ita Yah Abdallah ne zaɓinta yay zuciya saboda goyon baya da Hajjo ta bama Abdallah a wancan lokacin. Anyi bukukuwa kashi-kashi a gidansu shi kaɗai ne baya zuwa sam.
    Ta ɗan sake satar kallonsa da jijjina ƙyawun daya ƙara da cikar kamala tamkar ba Yah Naser ɗin data sani ba a shekarun baya. Kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yanzu kam kuɗi sun zauna a garesa da hutu, dan sai ɗaukar ido yake kamar gasashshiyar kazar gidan gona.

    *_Naser yaro ne wajen Alhaji Kabeer Usama dake a garin katsina. Jikane ga Yayar hajjo da suke uwa ɗaya uba ɗaya, dan aurene ya kaita katsina ta zuba zuri'a kuma a can mai albarka. Ita kaɗai kuma ta ragema hajjo a yanzun, shiyyasa take ɗaukarta tamkar uwa. Naseer ya zauna a gidan su Nu'aymah sosai, dan rashin yara a gidan lokacin da su Abdallah sukai Accident yasa hajjo ɗakkosa. A wajensu yay primary ɗinsa har secondary. Jami'a ce kawai ta maidashi garin jos. Yaso nu'aymah shima tun tana ƙarama, dan lokacin takara suka dingayi da Abdallah a kanta duk da kowa bai furta ba saboda ƙuruciya. To sai kuma yazam sanda suka furta ɗin ya zam lokaci guda, sai dai Abdallah ya riga Naser. Dama kuma ya fisa nuna damuwa da Nu'aymah. Hakan ya haddasa rigima sosai tsakaninsu, da Hajjo taga lamarin zai girmama ne tai musu shari'a a tsakani da shaidar cewar Abdallah ya riga Naser ɗin. Wannan shine sanadin yin zuciya ya tattara komansa yabar kano ya koma gidansu. Bai kuma sake zuwa ba sai yau ɗin nan da suka gansa tsulum. Har yanzu kuma baiyi aure ba._*..........✍

      To ga dai Naser tsohon masoyin Nu'aymah a kano bayan gudun hijira na shkara takwas da yayi. Ko da wane shiri ya dawo yanzun kuma? Dan da alama kam akwai motsawar tsohon tsumi tattare da shi dama ita kanta, sai mu cigaba da binsa muji YAYA TAKE NE?!!🤗.

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login