Showing 90001 words to 93000 words out of 94091 words
Sosai takaici da hayaniyar papa ta sake rufe Yoohan ɗin, amma sai ya daure cikin taushin murya da sanyayata yace, “Papa Please relax. Ina lafiya fa”.
Da sauri ya rungumeshi yana sauke numfashi a jajjere. Su dai su Solo suna kallon ikon ALLAH daga gaba. A haka suka ƙarasa hotel ɗin da har yanzu akwai sauran yaran Ema... Da taimakon papa Yoohan ya fita, shine ya kamasa har ɗakin da yake. Su kuma su Solomon suka dakata wajen manager ɗin hotel ɗin suna musu bayani akan anga Yoohan ɗin su kwantar da hankalinsu.
Papa na zaune kusa da Yoohan dake kwance idanu a lumshe, hannunsa har yanzu dafe yake da kansa. Yama rasa wane kalar tunani ya dace yayi akan matsalarnan guda biyu. Alaƙalar Papa da Baba malam. Abinda ya aikatama Nu'aymah a karo na biyu. Buɗe idanunsa yay a hankali kan papa da yay shiru shima yana wani tunani can daban, sai da yay masa kusan kallon sakan goma kafin cikin nuna kulawa ya kamo hannunsa cikin nashi da faɗin, “Papa!”.
Firgigit ya dawo hankalinsa tare da kallonsa. Yoohan ya sake lumshe idanu ya buɗe a kansa. “Papa dama kasan malamin nan ne?”.
“Yoohan! Wannan tambayar taka bata da muhimmancin samun amsa. Kai ya kamata nasan minene alaƙarka da shi?”.
Kamar Yoohan ya faɗi ainahin gaskiya sai kuma wata zuciya ta gargaɗesa dayin hakan. Yunƙurawa yay ya tashi zaune sosai ya jingina da fuskar gadon. Hannunsa ya sake maidawa cikin na papansa, cikin kwantar da murya yace, “Papa akwai abinda nake buƙata a wajensa, shiyyasa na kwantar da kaina nake binsa a sannu harna cimma burina. Sai dai kuma gashi kai kazo cikin mintuna goma kacal kana shirin rusamin shiri na. Miyasa zaka biyema su Solomon da shirmensu? Ai koda suka sanar maka na ɓata ko tunanin inda za'a'a sameni kamata yayi ka jira harna dawo kaji ta bakina. Haba papa da girmanka a ƙasarnan amma kake abu tamkar wani mara.......”
Saurin katsesa papa yayi ta hanyar ɗaga masa hannu. hakanne ya saka Yoohan haɗiye sauran maganar tasa. Papa ya gyara zamansa sosai da cewa, “Naji nayi kuskure, amma kaima harda laifinka. Miyasa tun tuni baka sanarmin ba, bayan kasan niɗin mai baka goyon bayane akan kowanne irin business naka musamman a wannan yakin”.
“Nima naji nayi kuskure to. Amma ina da dalilin ɓoyewar ai. Da ace na sanar maka mi nake shirin yi zaka iya ɓatamin aiki dan kanada gaggawa papa. kai kafi son komai da zafi-zafi a lamarinka. Hakan kuma na taɗiyeka daga nasarorinka. Yanzu da ace bakazo ba da cikin satin nan zan kammala aikina. Amma yanzu kaga ka kawo min togaciya dan zai fara kokwanto a kaina. Kaga kenan saina sake sabon ginin da zai ƙara yarda dani hundred percent kamar farko”.
Cikin tsananin jin daɗi papa ya rungume Yoohan yana faɗin, “I am sorry my sweetheart, kai ɗinne ba'a gane kanka sai kaso. Yanzu dai na maka alƙawarin da kaina zan gyara abinda na ɓata a yau ɗinnan kaji”.
Ɗagowa Yoohan yay da sauri, yace, “Papa da gaske kakeyi?”.
“Ƙwarai kuwa my dear son”.
Wani lallausan murmushi Yoohan ya saki najin daɗi. Dan ya fahimci lallai sai ya nunama papa akwai manufa a tafiyarsa da baba malam sannan zai samu nutsuwar samun damar fahimtar ilimin addinin islama da zai kare kansa anan gaba a wajensu dama duk wani dake a cikin ahalinsa da yasan zai kawo masa togaciya. Amma a yanzu yasan duk yunƙurin da zaiyi sai sun taɗesa saboda rauninsa na kasancewa sabo cikin addini mai ɗunbin haske irin musulinci. A yau kawai daya kasance a ciki jinsa yake tamkar sabon mutum. Tamkar darajarsa ta ƙaru. Duk wani nauyin zuciya da ƙunci da yakan tsinta kanshi a ciki a baya yau sai yaji tamkar ansa kwano an kwashesu tas.
Jikin papa ya sake lafewa tare da lumahe ido. Papa ma dake jin daɗin Yoohan ya fara ɗaukar huɗubarsa ya shiga shafa kansa cike da jin daɗi da annashuwa. Dan shima har zuciyarsa ta gama shirya masa babban aiki akan baba malam tsaf............✍
Tofa masu karatu. Yanzu za'a fara wasan😎 dan haka kumuje zuwa filin daga😉😱🚶🏻.
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/20, 9:01 PM] Amina Mama: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 32
............Tun isowarsu asibitin aka fara bama Nu'aymah dake a sume taimakon gaggawa. Sai dai harsu baba malam suka isa asibitin bata farfaɗo ba. Hakan sai ya sake ɗaga hankalinsu. musamman ma Hajjo dake ta faman sharɓar hawaye. Cike da kulawa baba malam ya zauna kusa da ita duk da kunyar ɗan fari dake tsakaninsu. Murya a tausashe da nuna ɗunbin kulawa da ladabi ya fara lallashinta da faɗa mata kalamai masu taushi da nutsuwa irin na masu ilimi. Ya nuna mata koda rasa Nu'aymah sukayi su zama masu haƙuri da godema ALLAH. Dan lokacin da ya basu ita baiyi shawara da suba. A yansu kuwa idan ya karɓeta ya fisu bukatarta ne.
Haka ya cigaba da mata nasiha harta samu nutsuwa tai shiru. Abba Musbahu yazo gabanta ya durƙusa tare da saka handkherchief ya share mata hawayen.
Ana haka Doctor ya fito daga ɗakin da aka sanya Nu'aymahn. Ya buƙaci ganin ɗaya daga cikinsu cikin nuna girmamawa a garesu. Abban Abdallah da Abban su Adawiya ne suka bisa office. Dan baba malam ya nuna kawaicin nasa da ya saba kamar ko yaushe. Amma zuciyarsa cike take da tsoro da rauni. Yana ta dai ƙoƙarin danneta ne da ambaton ALLAH wajen ƙarfafa imaninsa.
A office ɗin likita kuwa ya nutsu ne wajen rubuce-rubuce a wata takarda kafin ya maida hankalinsa gasu Abbah.
“ALLAH ya gafarta malam zan fara da muku albishir ɗin farfaɗowarta. Sai dai kuma kamar yanda kuka sani raunin dake a cikin ƙwaƙwalwarta shine ya motsa mata. Kuma gaskiya a bincikenmu yarinyarnan tana matuƙar buƙatar son ganin babban likita. Idan ba hakaba a koda yaushe zata iya fuskantar gogewar komai na ƙwaƙwalwar ta. saboda tana ƙara girma ciwon na daɗa faɗi. Musamman ma daya kasance kamar tana sakama kanta abubuwa masu nauyi a cikin rai. A duk kuma lokacin data shiga ƙunci ciwon na mata kuɗa a cikin kanta, ba dan ma tana samun kulawa da kuma addu'oi ba da gaskiya bana zaton yarinyarnan zata kai wannan shekarun batare data tsinci kanta a ciwon hauka ba. Duk da komai na ALLAH ne, babu wani bawa daya isa canja ƙaddarar wani bawa daga yanda tazo a littafinsa. Amma a wannan karon ayi himmar sadata da likitan daya dace da matsalarta, munan taimako kawai muke bata na dakatar da raɗaɗin a gareta a lokacin daya taso. Amma matsalarta sake hauhawa takeyi gaskiya”.
Su Abba da duk jikinsu yay sanyi sukaima Doctor godiya sosai. Tare da tabbatar masa insha ALLAHU a wannan karon zasuyi abinda ya dace.
Yaji daɗin hakan sosai. Ya sake ɗan musu wasu bayanan da suka dace akan yanayin kula da Nu'aymahn kafin ALLAH yasa a dace da samun Doctor ɗin daya faɗa. Dan ya basu note dazai taimaka musu samun ganin makusancin likitan da lokaci-lokaci yake shigowa cikin kano. Baya kuma duba marasa lafiya a ko ina sai a General hospital. Dan haka ya basu abinda zai taimaka musu ganawa da wata likita dake aiki a General hospital ɗin, wadda yake da tabbatacin ta hanyarta zasu iya ganin Doctorn.
Godiya sukai masa sosai, sannan suka fito. Sai dai basu ma su baba malam bayanin komaiba, a ƙoƙarinsu nason yin wani hoɓɓasa akan jinin yayan nasu da a kullum hidimarsa ke ƙarewa a kan su da nasu iyalin. Suma wannan karon sunason nuna tasu bajintar akan ɗaya daga cikin jininsa guda biyu da ALLAH ya bashi.
________★★
Ganin lokacin sallar la'adar ya gabato Yoohan ya buƙaci kaɗaicewa dan ya huta. Hakanne ya saka papa fita ya barsa shima ya nufi ɗakin da aka kama masa.
Yoohan ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana miƙewa. Zuwa yay ya sakama ƙofar ɗakin key. Kafin ya nufi bayi yayo alwala kamar yanda baba malam ya koya masa. Duk da zuciyarsa na kwaɗayin zuwa massallaci yay salla cikin jam'i kamar yanda suka gabatar ɗazun a massallacin juma'a haka ya haƙura ya daure yin tasa shi kaɗai a cikin ɗakin kamar yanda aka koyar da shi.
Bayan ya idar da sallar a tsanake yay addu'a gwargwadon abinda ALLAH ya hore masa. Waya ya jawo yay kiran baba malam. Cikin sa'a kuwa bugu biyu aka ɗaka. Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke wadda har baba malam ya jiyota.
“Banyi zaton zaka ɗagaminba Uncle. Nazata zakayi fushi dani bisa kuskuren papa”.
Baba malam da fitowarsa kenan daga massallacin cikin asibiti sun idar da salla kiran ya shigo masa yay sassanyan murmushi, ƙaunar Yoohan ɗin da ƙyawawan ɗabi'unsa na sake dulmiyasa a ƙaunar yaron. Cikin kulawa yace, “Haba Yahya! Mizaisa nayi fushi da kai? Ai koshi bazanyi fushi da shiba dan ya fini gaskiya. Da farko ina fatan dai ka gabatar da sallar la'asar. Na biyu kuma ina fatan babu wata matsala tsakaninka da mahaifinka a dalilin ganinka da yay a wajena?”.
Lumshe idanu Yoohan yay a hankali yana jingina bayansa da kujera, cikin so da ƙaunar baba malam dake ratsashi shima yace, “Alhamdulillahi Uncle. Yanzun nan na idar da salla, sai dai banje massallaci ba, ina fatan hakan ba laifi baneba. Dan nayi hakanne saboda ahalina, banason su fahimci ni musulmi ne tun yanzu dan zasubi hanyoyi da dama wajen kaini ƙasa. Amma idan na sami wadataccen ilimin addini musulinci duk ta inda suka ɓullo zan kare kaina”.
Baba malam dake murmushi ya sauke ajiyar zuciya. “Tunaninka mai ƙyau ne Yahya. Sai dai salla cikin jam'i tanada matuƙar muhimmanci, dan haka kar kayi sakaci da samun ladan dake cikin jam'i kaji”.
“Zan kiyaye Uncle”.
“Alhamdulillahi haka ake so. Mahaifinka fa?”.
“Karka damu da shi Uncle. haka yake da zafi, amma da an fahimtar da shi yanada saurin fahimta. Munyi magana da shi ya kuma fahimceni, kafin ma ya wuce zai shigo wajenka yacemin”.
Hakan ya bama baba malam mamaki matuƙa. Amma sai bai nunama Yoohan ba ya amsa masa kawai. Sannan sukai sallama.
Lokacin da Yoohan ke waya da baba malam a can papa ma yana ɗakinsa suna waya da Uncles ɗin Yoohan ɗin su Uncle Godwin. Ba akan komai suke wayarba sai akan baba malam. Kamar yanda papa ya girgiza da ganin Yoohan da farko haka suma suka girgiza dajin Yoohan a wajen baba malam. amma daga baya sai bayanin da Yoohan yayma papa ɗin yaɗan sanyaya musu rai.
Uncle Mike yay wata dariyar mugunta yana faɗin, “Wannan ɗan nakafa shegen kansane, inaga akwai aikin da yakema turawan nan ta ƙarƙashin ƙasa shiyyasa kullum bai damuwa da lamarin kowa sai wannan aikin nasa. A da ba ƙaramin haushi yake baniba akan hakan, amma jin wannan maganar ta yau sai naji ƙaunarsa da son haɗa tafiya da shi. Sai dai matsalar ɗaya ce yaron yanada taurin kai, nasan bazai taɓa yarda musan cikinsa gaba ɗaya ba. Amma ni a ganina mizai hana muma muyi namu aikin akan wannan hausa man ɗin, dan fa multi millions ne. Kawai dai baya nunawa ne”.
Papa ya kwashe da wata dariya, kafin yace, “Mike! tunaninmu ɗaya, dan haka ku bari sai na shigo Abuja mu tattauna da ƙyau. Yanzu dai matakin farko zanbi shawarar Yoohan zanje har gida na bashi haƙuri. Daga haka na ƙulla alaƙa mai ƙarfi da shi. Sauran bayani kuma sai mun zauna a tebirin shawara”.
Duk sunyi na'am da hakan suma. Dan haka yay musu sallama ya kashe wayar cike da zumuɗi a ransa. Kaɗan-kaɗan sai ya ƙyalƙyale da dariya. Dan gaba ɗaya zuciyarsa ta gama tsara masa yanda komai zai kasance.
______________★★
Bayan Baba malam sun shiga sun duba Nu'aymah dake barci suka bar Hajjo da Abba Musbahu a asibitin. Koda suka iso gidan sai su Umm suka shirya su kuma suka tafi duba Nu'aymah. Wanka yayi ya zauna a falonsa yaci abincin da Umm ta shirya masa kafin su wuce. Abincin kawai yake ci a zahiri, sai dai zuciyarsa sam bata tare da duniyar mutane. Yayi zurfi matuƙa gaya a tunanin Pastor Goshpower (Papa). Ba komai ya kaisa ga tunaninba kuwa sai mamakin dama Papa nada babban ɗa a duniya kamar Yoohan? Ga shi dai a zahiri akwai kamanni tsakaninsu, sai dai baisan miyasa zuciyarsa ke kawo masa wani al'amari mai kama da kokwanto a cikin zuciyaba. Musamman da zuciyar tasa ke tariyo masa wani shuɗaɗɗen al'amari daya faru a shekarun baya tsakaninsa da Papan.
Haka yayta saƙawa da kwancewa har lokaci yaja bai farga ba. Sai da Abban Abdallah ya shigo dubasa sannan ya fahimci yayi zurfi sosai a tunani ashe. Alwala yayi suka fice massallaci dan lokacin sallar magriba ya gabato
Suna fitowa su Umm na dawowa gidan. tambayar jikin Nu'aymah sukayi. Suka sanar musu har yanzu tana barci, batama san sunje ba balle tahowarsu.
Baba malam yabi Umm da kallo harta shige. tausayinta mai tsanani ne ke sake shigarsa. Tanada haƙuri da kawaici matuƙa, shiyyasa yake tsananin ƙaunarta fiye da zaton mai hasashe. Yanzu haka inba shi daya gama sanin kayarsa ciki da bai ba bazaka taɓa fahimtar tanada damuwa ba a fuskarta. Ta dake ta shanye komai, baka ganin komai akan fuskarta sai tsananin jarumta da tarin haƙuri da juriya.
Haka ya tafi massallaci da wannan tunanin na Umm.
Bayan idar da sallar isha'i suna shirin zaman karatu kamar yanda suka saba ɗaya daga cikin ƴan agajin massallacin ya shigo ya sanar masa cewar yayi baƙi.
Jimm yayi alamar tunanin baƙi daga ina a wannan lokacin? Bai gama kaiwa ƙarshe ba ya hango Yoohan dake ƙoƙarin shigowa massallacin. Bai tashi ba, sai ya jira harya ƙaraso inda suke. Yoohan da kallo ɗaya zakai masa ka fahimci damuwa da rashin walwalarsa kamar ko yaushe ya ɗan bama na kusa da shi hannu sukai musabaha kafin ya ƙarasa inda baba malam ɗin yake. Cike da girmamawa ya risina ya gaishesa. Amma sai baba malam ɗin ya kamo hannunsa cikin nasa sukai musabaha kamar kowa. Cike da jin nauyi Yoohan yay masa bayanin tare yake da baƙi, wannan ya saka baba malam miƙewa bayan ya bama ɗalibansa haƙuri ya barsu da Abbansu Abdallah shi kuma suka fito.
Duk da dai yayi mamakin ganin papa ne sai baice komaiba. Da kansa yay musu iso gidan saukar baƙinsu. Sannan ya kira Umm ta bada abinda ke akwai a gidan cikin su Omar wani ya kawo.
Papa dake ta waya tun ɗazun ya ajiye yana kallon baba malam da murmushi, shima bai gazaba wajen maida masa murtani. A ƙasan ransa kuwa yana neman tsarin ALLAH da ga kowanne irin sharri papan ke tare da shi ko yake shirin ƙullawa. Duk da shi mutum ne mai ƙyautatama mutane zato zuciyarsa ta kasa ƙyautata zaton akan papa, dan shi shaidane akan sanin papa bayahude ne na gaske, sai dai bai saniba ko yanzu ya canja daga yanda ya sanshi a da ɗin.
Hannu ya bashi suka gaisa, hakan yay dai-dai da shigowar Omar ɗauke da basket da Umm ta shiryo abincin motsa baki. Sai da ya gaida Papan, suka gaisa da Yoohan da alamar sanayya tsakaninsu sannan ya fice. Papa ya gyara zamansa yana wani ɗan basarwa, fuskarsa da murmushi har yanzu ya duba baba malam da faɗin, “Kayi haƙuri da kuskurena na ɗazun, ina fatan zaka dubesa akan rashin sani na aikata. Bansan alaƙarka da yarona mai daraja bace irin haka sai bayan mun barka ne yaymin bayanin da har na fahimta, ina fatan zakamin afuwa”.
Sosai mamaki ya kama baba malam, dan duk zatonsa Yoohan ya ma mahaifinsa bayanin ya musulunta ne. dan haka ya ɗan dubi Yoohan ɗin. Da sauri Yoohan ya girgiza masa kai yanda papa bazai fahimtaba, hakanne ya saka baba malam fahimtar akwai abinda Yoohan ya sanarma mahaifinsa daban kenan. Sai kawai ya murmusa abinsa ya fuskanci papan shima.
“Karka damu komai ya wuce. Dama kuma ni ban ɗaukesa wani abuba. A inda ya faru anan na zubar da shi, nima ina fatan kaimin afuwa ka kuma fahimci alkairine ya haɗani da Yahya ba sharriba. Sanin shi wanene kuma bazaisa na taɓa cutar da shi ba insha ALLAHU. Saɓanin dake tsakanina da kai kuma bana fatan ya zama sanadin ɓata alaƙata da shi, dan sanin kai ne mahaifinsa bazai canja komai ba daga yanda na ɗaukesa a raina”.
“Naji daɗin haka, na kuma gode sosai da wannan girmamawa”. Papa ya faɗa yana sake faɗaɗa fuskarsa da murmushin mugunta.
Daga haka dai suka ɗan taɓa hirar da bawani tsaho taiba, shi dai ma Yoohan ba saka musu baki ya keba, yama maida dukkan hankalinsa ne ga wayarsa kamar baya falon. Kusan awarsu ɗaya da rabi sukai masa sallama suka fito inda su Solomon suke. Sai da baba malam yaga barin motocinsu anguwar sannan ya shiga cikin gida ransa taf da wasiwasi akan wannan ziyara ta Pastor Goshpower, amma sai ya bar abinsa a zuciya bai faɗama kowa ba, ya ma maida hankalinsa wajen kwantarma matarsa hankali