Showing 69001 words to 72000 words out of 94091 words
ta ƙanƙameta tana faɗin, “Wayyo Ummuna, nayi kewarki wlhy”. Umm dake murmushi ta amshi ɗiyar tata da hannu biyu ta rungumeta itama, sai da ta tabbatar sunji ɗumin juna kowa na sauke ajiyar zuciya kafin ta ɗagota da ga jikin nata. “Nu'aymah! Yaushe ne zakiyi hankali kisan kin girma ne? Bakisan yanzu ba da bane, shekararki goma sha bakwai fa kina shirin shiga sha taƙwas”.
Cike da shagwaɓa ta saka kanta a kafaɗar Umm tana faɗin, “Umm ni indai ina gabanki wlhy jaririyace sabuwar haihuwa, nayi kewarki ne sanyin idaniyata. Ina Muhammad yake?”.
“Nayi cinikinsa” Umm ta bata amsa tana janyeta daga jikinta ta fice domin shiga tawagar masu tarbar surukar tasu.
Baki Nu'aymah ta tura gaba, ta ɗaga ƙafa zata biyo Umm tajiyo muryar Muhammad a bayanta yana faɗin, “Marhaban biki Aunty na”. Saurin juyowa tai garesa, sai kuma ta nufe da sauri kamar yanda yake nufota suka rungume juna cike da kewa da ɗoki.
Haka gidan ya kasance a hargitse ranar saboda shagalin bikin salla, Nu'aymah bataje ko inaba, dan bayan tayi salla taɗanci abinci sai ta shiga ta gaida kowa na gidan, kafin ta koma ɗakin Umm tai kwanciyarta, duk wanda yazo musu yawo a ranar bai samu ganinta ba, dan ta ɓoye kanta a cewarta saita huce gajiyarta da ƙyau tunda dai tasan zasu zaga gari yawon sallar gobe idan ALLAH ya kaimu ai.
___________
Kiran sallar la'asar ne ya tada Nu'aymah dake kwasar barcin gajiya. Ta miƙe da ƙyar dan jikinta ko ina ciwo yake faman mata. Wanka ta farayi, ta saka ɗaya daga cikin kayan sallarta. Tayi ƙyau sosai cikin shaddarta ruwan hoda, taji aikin stones da yay ƙyau sosai. Kayan sun mata ɗas ajiki, tare da sake fiddo haskenta saboda ƴar ramar da tayi.
Lokacin data fito Umm kanta sai da tace, “Masha ALLAH”. Hakama ƴaƴan yayun Umm ɗin su uku da sukazo mata yawon salla duk sai da suka yaba ƙyawun da Nu'aymahr tayi. Ta zauna fuskarta da murmushi tana gaidasu cike da girmamawa. Dan dukansu matan aurene, kuma duk suna da yaransu. Cike da kulawa suke amsa mata, kowanne na mata ƙorafin rashin zuminci, musamman babbarsu.
Nu'aymah tace, “Lah Aunty Zulfah wlhy ba rashin son zuminci bane, ni abinda yasa banason zuwa gidanki wannan ƙanin mijin naki takuramin yake wlhy. ya cika shegen kallo kamar ɗan daudu”.
Dariya suka sanya gaba ɗayansu, aunty Zulfah tace, “To kwantar da hankalinki, indai Fa'iz nema aurensa zaiyi, tunda ke kinƙi. Kinga nima dakin yarda ai dana samu ƴar uwata kusa dani ko.......”
Da sauri Nu'aymah ta katseta da faɗin, “Taf, aunty daina faɗa dan ALLAH, wlhy ya cika iyayi, banason namiji yayta gwalli kamar wani mace, shiba ɗan daudu ba shiba mata maza ba”.
“Amma Nu'aymah baki da kirki wlhy, kin gama ɗebema ƙanin mijin aunty Zulfah albarka gaba ɗaya”. Aunty Rafi'a ta ta faɗa tana dariya. Ita kanta Nu'aymah dariyar takeyi, Umm dai batace musu komaiba. duk da kuwa tana zaune tana jinsu.
Sai da suka tsagaita da dariyarne Nu'aymah ta miƙe tana faɗin, “Umm yunwa nakeji, ALLAH yasa akwai waina dai?”.
“Kin kuwa makaro, dan su Basira na ɗeboma ita gaba ɗaya, kinsan zakici wainar kikaƙi ɗiba ki ajiye?”. Kamar Nu'aymah zatai kuka tace, “Kai Umm! ALLAH yanzu kin daina sona, amma yanzu duk wainar dana gani ace ta ƙare? Su su aunty Basiran miyasa basu zauna sunci a sashen Addah b.......”
Harar da Umm take jefo matane ya sakata yin shiru, dan su Basiran ƙannen Adda ne. “ALLAH ya shiryeki to, to ance miki sune kaɗai suka cinye. Ga yayunki nan suma duk ita sukaci, sannan Abbanku da yay baƙo duk da baya a gidan shima ita yace akai musu kafin ya iso gidan”.
Komawa tai ta zauna kamar zatai kuka, su Aunty Zulfah nata tsokanarta wai ta amshema Muhammad guri tana shagwaɓa bayan shine auta.
Umm tasan yanda Nu'aymah keda jarabar son waina, dan haka ta dubeta sau ɗaya ta ɗauke kanta tana faɗin, “ki wuce sashen hajjo idan bata ƙareba”. Aiko zumbur ta miƙe, a ranta tana fatan ALLAH yasa ta samo.
Duk da takalman data gani na maza a ƙofar falon na hajjo kusan ƙafa biyar bata damu ba, sallama tayi kawai, kafimma su gama amsa mata ta shige dan duk zatonta yayunsune a ciki, tunda tasan duk suna gidan. A shagwaɓe ta buɗe baki zatai magana. sai dai cin karo da fuskar da batai zato ko tsammanin gani ba ta sata waro manyan fararen idanunta waje cike da al'ajabi.
Yoohan dake zaune shima cikin Suit ruwan babypink kallon nata yake cike da mamaki, a ransa faɗi yake, ‘Dama yarinyarnan ba'a cikin Orphanage ɗincan take ba? No wander ɗazun baiga komai kama da itaba a cikin yaran’. A fili kuwa sai ya ɗauke kansa cike da shan ƙamshi kamarma irin bai ganta ba ɗin nan shi.......
“Lafiya wai kika tsayama mutane ƙerere a kai Zainabu?”. Maganar Hajjo ta katse mata tunaninta. Juyawa tai inda hajjon take, har yanzu mamakin ganin Yoohan ɗin bai barta ba, “Hajjo wannan mutumin kuma ina kika sanshi?”.
“Wa ɗin?”. Cewar Hajjo tana kallon inda Hamza Manager, Yoohan dasu baba ƙarami ke zaune.
Maimakon Nu'aymah tai magana sai ta je ta zauna kusa da hajjon, matsar da bakinta tai dai-dai kunnen Hajjo tace, “Hajjo arne ne fa wlhy”. “Aina sani” Hajjo ta bata amsa cikin nuna halin ko in kula.
Sosai mamaki ya kume Nu'aymah, tai tsai tana kallon Hajjon, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta sake maida dubanta ga Yoohan daya maida dukan hankalinsa kan wayarsa.
“Wai lafiyarki kuwa? Kina ganin mutane baki iya gaisuwa bane? Sai shegen kallo malama”. Yah Ahmad ya faɗa idonsa akan Nu'aymah. Sai da taɗan tura baki kafin ta duba Hamza manager data wuce da dukanin imaninsa tace, “Ina yini”. Cikin narkakkiyar murya da shi kansa baisan ta fitaba ya amsa mata da “Lafiya lau ƙanwarmu, kinyi salla lafiya?”. Kai ta gyaɗa masa kawai, dan duk sai taji kuma ta takura da kallon da yake mata. Ganin bata gaida Yoohan ba ya saka Malam ƙarami hararta, yace, “Shi kuma fa?”.
Yanzun kam baki ta kumbura sosai, ta kalli Yoohan ɗin da yay tamkar baisan da zaman kowaba a falon tace, “Good evening.
Sarai yajita, amma sai ya share baiko motsaba. Sai da Hamza ya ɗan taɓasa da faɗa masa ana gaishesa sannan ya ɗago manyan idanunsa farare tas ya sauke a cikin nata. Karan farko da sukaima juna kallon ido cikin ido. Kusan lokaci guda kowanne gabansa ya faɗi. Nu'aymah tai saurin fara janye nata da ƙoƙarin juyawa daga saitinsa.
Shima ɗan lumshe nasa yay ya buɗe (dan hakan ya zame masa kamar wata ɗabi'a) cikin muryarsa mai amo ɗin nan yace, “Kina lafiya?”.
A mugun razane Nu'aymah ta sake waigowa inda yake, har taune harshenta take wajen faɗin, “What?! Dama kanajin hausa?”.
Yanda tayi tambayar sai da ya saka su hajjo yin dariya. Hakan sai ya ƙarama Nu'aymah takaici, musamman ganin yanda Yoohan ɗin ya wani yamutse fuska, tare da miƙewa saboda wayarsa da aka kira, dama shi baiyi dariyarba. Sai da yazo daf da ita a hankali yace, “Yeyye girl”.
Kafin wani ya sake magana a cikinsu, ko ita ta bashi amsa Abban su Adawiya da Abban Musbahu suka shigo falon da sallama. Shi kuma ya fice yana amsa wayar.
Daurewa tai ta shiga gaishesu tana ɗan harar ƙofar da Yoohan yabi ya fice ta gefen ido, a ranta kuwa sai cewa take, ‘Oh ALLAH, amma dai gayen nan akwai munafurci, dama yanajin hausa amma duk sanda suka haɗu yake nuna mata bayaji, jibesa da wani shegen aski kamar kan zakara, sai kuwa yaga yeyye kafin yabar gidan nan yau’.
Duk kallon harar Yoohan da take Manager yana kallonta ne ta gefen ido shima, sai da Abban Musbahu ya kira sunansa ne sannan ya maida hankalinsa garesa, a ransa yana mamakin yanda alamu suka nuna akwai sanayya tsakanin Yoohan da wannan Zuƙeƙiyar budurwar data gama tafiya da dukkan imaninsa a kallo ɗaya.
Ita kam Nu'aymah da batasan yanayi ba sai ta lallaɓa ta fice dan jitai tama fasa cin wainar, yau duk yanda za'ai sai taji dalilin shigowar wannan kahirin cikin gidansu, harma falon kakarsu...........✍
😜Kina ruwa Aymah😸.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/18, 12:14 PM] Amina Mama: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 30
................Lokacinda su Solomon ke acan cikin tashin hankalin tsoron cikar lokacin da papa ya basu akan sanin inda Yoohan yake, shi yana nan suna shirin tafiya massallacin juma'a shi da su baba malam.
Kowa ya kalli baba malam ɗin a yau zai fahimci yana cike da tsantsar farin ciki. A cikin nishaɗin daya shiga da shi cikin gidan nasa ya sake fitowa shi da Umm data taimaka masa yay shirin massallaci.
Ƴar tsokanar da ya kema Umm yasa Nu'aymah dake zaune a falon tana gyaran fruit ɗin da Umm ta sakata ɗagowa tana kallonsu. Cikin washe baki tace, “Abbah yau dai kana cikin farin ciki ALLAH, naga tun safe fuskarka sai annuri takeyi”.
Da ga Umm har baba malam dariya sukayi, ya matsa kusa da ita tare da kai hannu ya shafa kanta. “Tabbas yau ina cikin farin ciki mamana, saboda wannan farin cikin yau har ƙyauta ta musamman na shirya miki ke da Muhammad, dan haka kafin na dawo ki shirya faɗa mini abinda kike so”.
Sosai farin ciki ya sake kamata. Ta shiga jera masa godiya da addu'ar fatan dawowa lafiya. Daga shi har Umm amsa mata suke cike da kulawa. Kowannensu najinta a ransa sosai, dan daga Umm har Baba malam ba ƙaramin so sukema Nu'aymah ba. Suna dannewane kawai saboda ƙarfafama kansu tarbiyarta. Ga ɗunbin tausayinta dake mamaye da ruhinsu game da matsalarta. Dan har yau da muke ɗin nan baba malam bai gajiya ba wajen cigaba da neman likitan nan, yana kuma gayama UBANGIJI da neman taimakonsa a kowane daƙiƙa.
Bayan Umm tama baba malam rakkiya ta dawo. A inda tabar Nu'aymah nan ta sake isketa tana ƙalular gyara fruit ɗin.
“Nikam naga takaina da wannan hali naki Nu'aymah! Mutum yayta abu sanyi-sanyi tamkar bazai ƙaresa ba. Yanzu maimakon ki zauna kiyi aikin nan a kitchen shine kika taho nan kuma dan salon neman ɓata guri?”.
Baki ta tura gaba tana ɓata fuska, “Yoni Umm idanfa na zauna a kitchen wlhy Rabi damuna zatayi da surutun ta, kin sani dai ko redio haka ta ganta ta ƙyale akan zanc........”
Bammm!. Umm ta make mata baki, hakanne ya hanata ƙarasa faɗa. Da sauri ta saki wuƙar hannun nata hawaye na taruwa mata a ido. Umm dake hararta tace, “Saunawa zan faɗa miki karna sake jin wannan maganar banzan a bakinki Nu'aymah? Rabi bata girmeki ba? K wai yaushe ne zaki bar tsiwa da rashin kunya? Itaɗin sa'arki ce?”.
“Kiyi haƙuri Umm bazan sakeba ALLAH ”.
“Kima sake mana, mara wayau kawai”. Umm ta faɗa tana hararta da barin wajen. Harta kusa ƙofar sashen baba malam ta juyo. “Kiyi ki tashi a wajen nan kuma kafin na fito, ga man-shanu can a kitchen ki ɗauka ki kaima Addah, kuma idan kinje ki zauna shiririta karki dawo ki ƙarasa aikin dana sakaki kinji ko”.
Sake ɓata fuska Nu'aymah tayi hawaye na zirara mata. Sai dai batace komaiba har Umm ta shige ciki. Dan zuciyar gadon tazo mata wuya.
Duk yanda Umm tace tayi haka tayi, sai dai data shiga kitchen Rabi tasha harara, dan a ganinta saboda itane Umm ta Mammangare ta. oho ita batama san tanaiba, dan aikinta takeyi koda ta shigo bama ta kalli inda Nu'aymahn takeba tunda tasan basa doguwar magana lafiya sai sunyi faɗa.
Manshanun ta ɗauka zuwa sashen Addah. Sai da tai sallama kusan sau uku kafin a amsa mata ciki-ciki. Bata damuba ta shige tana ɗaure fuska dan har yanzu akwai haushin faɗan Umm tare da ita. Kubrah kawai ta iske zaune a falon, tunkan ta ƙaraso ciki take jefo mata harara.
Jitai kamar ta juya dan haushi, amma sai ta daure ta ƙarasa da faɗin, “Aunty Kubrah Umm ce ta aikoni wajen Addah?”.
Banza tai mata tamkar bata jitaba, har Nu'aymah ta fara yanke shawarar juyawa sai ga Hajarah ta fito daga ɗakinsu hannunta ɗauke da Al-qur'ani.
“A'a Aymah ce a wajen namu?”.
Ajiyar zuciya Nu'aymah tayi da maida kallonta gareta. Fuskarta da ɗan damuwa tace, “Aunty Hajarah Umm ce ta aikoni wajen Addah. Amma ina tambayar Aunty Kubrah tamin banz.....”
Kafin ta ƙarasa taji saukar duka a bakinta, Kubrah da tai dukan ta nunata da yatsa cikin magana ƙasa-ƙasa tace, “K dan uwarki ni sa'arki ce ko?”.
“Kai haba Aunty Kubrah daga tambaya, yanzu dan ALLAH mita miki zaki dakar mata baki? Minene abin laifi anan to?”. Hajarah ce mai maganar dai-dai tana ƙarasowa inda suke ta kama hannun Nu'aymah dake hawaye, dama bakin bai gama mata zafiba akan dukan da Umm tai masa yanzu. Ga kuma Kubrah ta ƙara mata wani.
Cikin masifa Kubrah ta kalli Hajarah, “Kozaki rama mata ne?”.
“Bazan rama mata ba, amma ALLAH zai saka mata. Tunda duk wanda ya zalinci wani ALLAH na kallonsa. Nu'aymah jeki Addahn na ɗakinta kinji ko”.
Kai Nu'aymah ta ɗagama Hajarah tana share hawayenta. Batare datace komaiba ta nufi ɗakin Addah zuciyarta na mamakin yanda Aunty Kubrah kejin zafinta a ƴan kwanakin nan, duk da dai dama ita babu wani shaƙuwa sosai tsakaninta da ita tun da can. Sai dai bata taɓa nuna mata banzan hali irin na wannan karonba. Tana gab da shiga ta tsinkayo muryar Kubrah na faɗin, “Ƴar iskar yarinya ki taka a sannu dan a tafin hannuna kike wlhy, inba hakaba saina tona asirin iskancinki a gaban kowa yasani a gidan nan”.
Sosai gaban Nu'aymah yay bala'in faɗuwa, dan tasan inhar Kubrah ta faɗi abinda ta gani tsakaninta da Yoohan ranar tata ta ƙare. Da ƙyar ta iya haɗiye kukan daya taho mata.
Da mamaki Hajarah ta kalli Kubrah, “Haba Aunty Kubrah wace irin maganace haka? Wai nikam minene ya haɗaki da Nu'aymah mai zafi a kwanakin nan dan ALLAH?”.
“Ki shaƙeni in faɗa miki mana”. Kubrahn ta faɗa a harzuƙe.
“ALLAH ya baki haƙuri”. Hajarah ta faɗa tana barmata wajen ranta fal tunane-tunane kala-kala akan ƴar tsamar yayar tata da Nu'aymah data gaza fahimtar tushenta a kwanakin nan sam.
Sai da Nu'aymah tai sallama Addah ta bata izinin shiga sannan ta shiga ɗakin. Tsaye ta isketa tana ninke abin salla alamar sallar ta idar. Ganin Nu'aymah na sharar hawaye yasa fara'ar fuskar Addah gushewa lokaci guda. “Lafiya Nu'aymah? mi akai miki?”.
“Babu komai Addah, Umm ce tace na kawo miki wannan”.
Sam Addah bata yarda da maganar Nu'aymah ba, dan haka tai shiru tana cigaba da kallonta kawai batare data amshi man-shanun ba. “Nu'aymah bana son shirme, faɗamin gaskiya mi akai miki?”.
“Addah wlhy aunty Kubrah ce ta dakar mata baki dan hawai tacemin ta tambayeta kina ina ta mata banza”. Hajarah dake shigowa ɗakin ta bama Addah amsa.
Cikin ɓacin rai Addah tace, “Kubrah?!”.
“Eh wlhy Addah, ni bama dukan ya ɓatan rai ba, bakiji yanda take faɗama Nu'aymahr maganar banza ba. A kwanakin nan dama na kula tana matsama yarinyar nan a gidan nan, haka ɗazun a islamiyyar asuba dan kawai Nu'aymah ta fiddo Fahad ɗin maman Sadiya daga aji saboda suna faɗa da wani yaro wlhy bakiga abinda tai mataba. Alhalin baikamata taima Nu'aymahn maganaba tunda yaran duk ƴan ajintane, ta fita sanin halin kowa a cikinsu”.
Kama hannun Nu'aymah Addah tayi suka fito ranta a ɓace. Hakan yasa Hajarah biyo bayansu da sauri itama.
“Kubrah!!”. Addah ta ƙwala mata kira ganin bata a falon.
Da sauri ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da plate ɗin abinci.
“Ubanmi Nu'aymah tai miki kika daketa?!”.
Sake tsuke fuska Kubrah tayi, ta kalli Nu'aymah data duƙar da kai tana hawaye har yanzun. Wani ɗan murmushin mugunta tayi kafin ta kalli Addahn. “Addah catai na daketa?”.
“Ni na faɗa ba ita ta faɗaba, tunda a gabana akai komai”. Hajarah ta bata amsa kafin Addah tai magana.
“Mtsooow!! Munafuka kawai. Addah ni ban daketa haka kawaiba, rashin kunya zataimin shiyyasa........”
“To amma shine zaki ce mata ƴar iska, kuma sirrinta a tafin hannunki yake. Idan kinso zaki tona mata asiri agaban kowa”.
“Wlhy Hajarah zan sauya miki kamanni, wai ni sa'ar wasanki ce?”.
“Kai!! Ya isheni haka, banason rashin mutunci. Bazan ɗauki wannan wawancinba kunji na faɗa muku. Shin kuɗin yaran goye ne da kullum baku da wani buri sai na samin ciwon kai? Kusani daga