Showing 75001 words to 78000 words out of 94091 words
Duk da ganin Aunty Kubrah ce ba Yoohan ɗinba hakan bai hana Nu'aymah sake rikicewa ba, ta shiga inda-inda jikinta na tsuma. “A..Aunty babu ko.. Komai”.
Kubrah data kafeta da ido taɗan murmusa, sai kuma ta juya bayanta tana faɗin, “Ki kwantar da hankalinki ai ba biyoki yayi ba, na tabbatar kuma babu wanda ya ganku a gidan nan”.
Wani muguwar faɗuwa gaban Nu'aymah ya sakeyi daboda jin furicin Aunty Kubrah. Cikin rawar harshe Nu'aymah tace, “Aunty Kubrah wlhy ni.......”
“Kinga kwantar da hankalinki Nu'aymah babu maiji, indai nice ko Hajarah baza taji wannan zancenba balle wani a gidan nan. Amma inason ki faɗamin gaskiya, yaushe kuka fara wannan abun ke da shi?”.
“Innalillahi! Aunty wlhy bamu taɓa yiba, yau ma na rantse shin......”
“Kinga ya isa. Share waɗan nan hawayen idan baso kike ki tonama kanki asiri ba da kanki”.
Nu'aymah duk ta sake rikicewa, tama rasa fahimtar inda maganganun Aunty Kubrah suka dosa saboda tashin hankali. Duk da ta share hawayen sun gaza tsayawa. Hannunta Kubrah ta kama har lokacin fuskarta da murmushin da Nu'aymah ta gaza fahimtar na minene. “Kinga muje sashenmu, idan ba hakaba Umm sai ta fahimci abinda ya faru, ko kinfi buƙatar hakan?”.
Da sauri Nu'aymah ta shiga girgiza mata kai, “A'a wlhy Aunty, banason Umm ta sani dan zata kasheni, dan ALLAH karki faɗa mata, wlhy kuskurene ba kuma laifina bane ba, na rantse da ALLAH Aunty ban taɓa yiba, ko hannuna Namiji bai taɓa riƙewa ba”. Ta ƙare maganar da rushewa da wani irin kuka maiban tausayi.
Komai Kubrah bata sake cewaba ta kama hannun Nu'aymah suka nufi sashensu. Ta ƙofar baya tabi da ita, dan ƙannen Addah su Aunty Basira suna falo zaune dasu Addah suna hira. Batare data bari sun gansu ba ta shige da Nu'aymah bedroom ɗinsu. Zaunar da ita tayi sannan itama ta zauna a kusa da ita. Har lokacin kuma Nu'aymah kuka takeyi, zuciyarta na ƙarajin tsanar Yoohan matuƙa........
“Ko shine Ameer ɗin Saurayinki?”.
Da sauri Nu'aymah ta ɗago tana kallon Kubrah, sai kuma ta shiga girgiza mata kai, “Aunty dan ALLAH ki yarda dani, wlhy Ameer ba saurayina bane. Wannan kuma bama musulmi bane ba, baƙone yau na fara ganinsa”.
Haɗe fusaka Kubrah tayi tamau tana kallon Nu'aymah ɗin. “Karkimin ƙarya Nu'aymah, inba hakaba wlhy na fasa rufa miki asirin, a yau da daddare zan sanarma Hajjo da Baba malam da Umm komai. Ki faɗamin tun yaushe kuke tare? Sau nawa kuma yay amfani da ke?”.
Duk sai Nu'aymah ta sake daburcewa, dan tama rasa wace amsa zata bama Aunty Kubrah, gaba ɗaya ta kasa fahimtar manufar Kubrah.......
Kamar Kubrah tasan tunanun da Nu'aymahn keyi, sai ta sassauta fuskarta tana gyara zama. Ta ɗan rage kaushin muryarta kuma ta koma magana cikin lallashi. “Nu'aymah kinsan dai yaya nake a gareki, duk abinda zan iya gani gasu Hajarah raina ya ɓaci idan nagani daga gareki dolene naji zafi, ɗiyar ƴar uwar mahaifiyata ce kuma ke, dan kuwa Umm tamkar ƴar uwar Adda take, tamafi min wasu ƴan uwan Addan. Yanzu Nu'aymah da wani ya ganki a gidannan ƙaton banza yana lalubeki mikike tunanin zai faru?, idan ma iskancin zakiyi ai gara kuyisa can a waje wani bai gankiba ko, amma a cikin gidanku? Babban gida mai daraja irin wannan? Wane kallo kikeson aima iyayenki maza damu kanmu Nu'aymah?”.
“Dan ALLAH kiyi haƙuri Aunty Kubrah, wlhy bazan sakeba wannan ma ƙaddara ce da kuma kuskure”.
“ALLAH yasa hakane to”. Kubrah ta faɗa tana wani ɗauke fuska da ƙyaɓe baki.
Nu'aymah na kuka tace, “Wlhy da gaske nake Aunty. Dan ALLAH ki yarda dani”.
“Nu'aymah idan ban yarda da ke ba minene amfanin musawar to?, tunda idan kunbar gabanmu ALLAH kaɗai yasan mi kuke aikatawa, masu iya magana fa kance rana dubu ta barawo, ɗaya tak ta mai kaya. Yau ɗinma ai bakiyi tunanin zan ganku ba”.
Ƙasa Nu'aymah ta zube tana kuka tamkar ranta zai fita, ‘Ita mizata faɗama Aunty Kubrah ta fahimceta ne wai? Wane rantsuwa zatai mata danta yarda ba da yardarta kafirin nan ya aikata hakanba a gareta?’.
Sai da taci kuka sosai, Kubrah na zaune na kallonta kafin ta ɗagota ta rungumeta, “Kukan ya isa haka, aina yarda ba laifinki bane. Na miki hakane kawai dan kisan baki dai-dai ba”.
“Na gode da kika fahimceni Aunty, kuma namiki alƙawarin hakan bazata sake faruwa ba insha ALLAHU”.
Ɗagota Kubrah tayi ta share mata hawayen tana murmushi, “Shikenan naji, kuma na miki alƙawarin babu maijin zancen nan a gidan nan kinji, kije bayi ki wanke fuskarki kizo ki sake shafa hoda dan karma wani ya zargi wani abun kuma kinji ko. Ki kuma saki jikinki inba hakaba Umm zata gane, kuma kinsan halinta. Zatabi duk hanyar data dace dan tasan gaskiyar abinda ya sakaki kukan”.
“Insha ALLAHU bazan bari ta gane ba Aunty, bara ma na wanke”. Ta ƙare maganar tana miƙewa da sauri ta nufi bayin su dake cikin ɗakin. Tana wanke fuska tana kallon bakinta a mirror. Wasu hawayen sai sake ƙoƙarin zubowa suke tana dannesu da ƙyar. A fili tace, ‘Na tsaneka mugu ɗan iska mai suffar samudawa, bazan taɓa yafe makaba wlhy”. Ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
Taja kusan mintuna biyu tana kukan kafin ta wanke fuskar ta fito. Fitowar tata tayi dai-dai da shigowar Hajarah da wayar Kubrah a hannu. Da mamaki Hajarah take kallon Nu'aymahn, dan ita dai bataga shigowarta sashen ba.
“Nu'aymah yaushe kika shigo ne? Gashi kamar kinyi kuka?”. Da sauri Nu'aymah ta girgiza mata kai, sai kuma ta kalli Inda tabar Aunty Kubrah dan tana zaune a wajen, tana jinsu kuma amma ko kallonsu taƙi tayi balle ta nuna alamar tasan mi sukeyi ma. “Babu komai Aunty Hajarah, kaina ne kawai ke ɗan ciwo”.
Ƙarasawa inda Nu'aymahn take Hajarahn tayi, ta ɗago fuskarta cike da nazari........
“Wai miye hakane? Tace miki babu komai kanta ke mata ciwo miye na damunta ne kuma?”.
Baya Hajarahn taja kanta a ƙasa tace, “Kiyi haƙuri Aunty Kubrah, ga wayarki dama Alhaji ne ya kiraki”. Ta matsa inda take cike da girmamawa ta bata wayar.
Tana amsa ta nuna mata ƙofa da ido. Da sauri kuwa Hajarahn ta fice.
Kubrah ta maida dubanta ga Nu'aymah dake a tsaye har yanzu. “K kuma ki bada himmar tonama kanki asiri kinji ko, ki wuce ki shafa hodan, idan kuma sokike wani ya sake shigowa to”.
Gaban Mirror Nu'aymah ta ƙarasa. Ta shafa mai da hoda harda kwalli, duk da dai hakan fuskar dai babu walwala.
Amma sai Kubrah batace mata komaiba suka fito falo inda su Hajarah ke hira tare. Zama tayi kamar yanda Addah dake kallonta ta Umarceta. Su Aunty Basira nata tsokanarta da faɗin ina tsarabarsu ne?.
Tun tana noƙewa dai harta ɗan ringa amsasu, amma ta gaza sakin jikinta yanda ya kamata sosai. Duk motsinta Hajarah da Addah na lura da shi, sai dai babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu.
___________________________
A ɓangaren Yoohan kuwa duk yanda su Hajjo sukaso ya zauna jiran dawowar baba malam ya gaza hakan. Yace musu zai dawo da safe yanzu yanada wani uziri.
Badan hajjo taso ba ta barshi. har ƙofar gida su Yah Ahmad sukai masu rakiyya shi da Manager. Inda su Solomon ke jiransa a mota. Kasancewar basu iske baba malam ba yasa bai shiga dasu cikiba. Yace su jirashi a waje. Dan da ƙyarma Su Ahmad suka lallaɓashi ya shiga cikin gidan. Da farko ya ce zai koma tunda baba malam ya fita. Dan dama yaso yin surprise ɗinsa ne shiyyasa bai sanar masa shigowarsa kanon ba ma.
Har drivern sa ya tada mota ya tsaidashi. Kuɗi ya ciro a cikin jakarsa rafa guda na ɗari biyar sabbi ƙal ya miƙama malam ƙarami yana faɗin, “Please a bama yarinyar nan barka da salla. Na manta ban bata ba”.
Malam ƙarami da ya fahimci Nu'aymah yake nufi sai yay murmushi. bai musa ba ya amsa yay masa godiya, dan suma daya basu sukaƙi amsa a ciki ɓata rai yayi, wai basu ɗaukesa ɗan uwansu ba. Hakanne ya sakasu amsa tunda yace barka da salla ce.
Duk abinda ke faruwa Solomon na saurarensu. Dama cike yake da haushin sake zuwa wannan gidan. Ya kuma ɗauki alwashin suna komawa wannan karon sai ya sanarma madam Chioma. Dan tsaf ya fahimci waɗan nan mutanen zasu iya jan hankalin Ogan nasu tsaf, musamman yanda suke masa hidima kamar wani sarki. Yanzu haka a gabansa aka saka babbar leda a booth wai kayan barka da salla ne aka bama Yoohan ɗin a cikin gida. Ya cije bakinsa yana satar kallon Yoohan daya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanu kamar mai barci ta mirror.
Babu abinda kema Yoohan kai kawo a zuciya da ruhi sai kalaman Nu'aymah. Kalaman sunyi masifar tasiri a ransa fiye da zaton mai karatu. Sai faman tisasu yake dalla-dalla kamar mai bitar karatu. Duk da ac dake aiki a motar bai hana zufa tsatstsafo masa a goshi ba. Mafarkin da yayi shekaran jiya da baba malam ya kuma sake maimaita shi yau da safe ya shiga tariyowa shima.
ya sauke wani irin nannauyan numfashi yana sake tariyo mafarkin nasa da yayi a karo na biyu kenan,
*Ya kanga kansa a mafarkin a gaban wani kogo ƙaton gaske, cikinsa akwai wani irin wuta dake ci mai ban tsoro, dan duk iya hasashensa ya kasa kamanta ƙarfin wutar da zafinta a zahiri. Aduk lokacin da yake a gaban wannan kogon dake zuwa masa a mafarki, ya kan tsinci kansa cikin matsanancin mawuyacin hali da ruɗu, sai dai kuma abin mamaki sai ya ga baba malam acan gefensa cikin shiga ta kamala, a wasu irin korayen ciyayi masu bada ni'imtaccen yanayi yana masa murmushi da miƙa masa littafin nan na musulmai (Al-Qur'ani), yakan ringa ce masa_______*
*_“Yoohan wannan shine zancen ALLAH, littafi dake ƙunshe da kowane irin sirri, littafin da aka aiko MANZONMU ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) da shi. kanada sauran daman riƙo dashi domin ka samu tsira daga wannan narkon azabar dake gabanka. Kazo gareni, zan nuna maka hanyar sanin UBANGIJINA kamar yanda ya aiko MANZONMU ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) a garemu ya nuna mana muma, ya kuma koyar damu. Ni Sooraj bin Hashim, na rantse maka da ALLAH, babu wani addini na gaskiya sai musulinci, babu wata hanya ƙyaƙyƙyawa sai ta bin UBANGIJI, babu wani abin taƙama da riƙo sai MANZON ALLAH. Inhar kabi ALLAH, kai koyi da koyarwar MANZON ALLAH, ka riƙe gaskiya da amana, ka tsare gangar jikinka daga saɓama ALLAH, ka nema dukiyarka ta hanyar halak, kaji tsoron zalintar mutane, ka kiyaye jinka da ganinka daga haramun, ALLAH bazai jarabceka da shiga wannan taskar azabar dake a gabanka ba. Domin UBANGIJI ya tanadi gidaje guda biyu, WUTA DA ALJANNAH, ya kumayi alƙawarin cikasu da mutane. Dan haka Yayha kazo gareni, kazo ka karɓi kalmar LA'ILAHA ILLAH, MUHAMMADURRASULULLAH (S.A.W)._*
A wancan ranar da yay wannan mafarki ya wayi garine a yanayin sanyin jiki, da tunane tunane kala-kala. Ya kuma yini zuciyarsa na rinjayarsa da amsa wannan kira. Sai dai daya tuna wani gagarumin al'amari sai yay azamar ƙwaɓar kansa harma da alƙawarin nisanta kansa da su baba malam ɗin. Dan yau ɗin nanma da ƙyar manager ya lallaɓa shi sukazo nan ɗin. duk da kuwa yana a cikin kanon yau kwanansa biyu kenan ma.
Kafin su ƙarasa hotel ɗin daya sauka sosai ya tsinta kansa cikin ruɗanin kalaman Nu'aymah da mafarkinsa. Sai ɗunbin takaici da dana sanin abinda ya aikata ma yarinyar yakeyi, wanda sam ba halinsa bane yin hakan, amma yasan ita da duk wanda zai iya ji ko ganinsu a lokacin bazai taɓa yarda da shi ba. Ya ɗan ciza leɓensa na ƙasa da ƙarfin tsiya, ƙirjinsa na sake masa zafi.
Motocin na tsayawa baiko jira an buɗe masa ba ya buɗe da kansa ya fice. Daga Solomon har sauran guards ɗinsa tsaye kawai sukai suna kallonsa cike da mamaki da tsoron yanayin nasa. Da sauri Solomon yabi bayansa shima dan yasan ba lafiya ba dai. Gashi key ɗin ɗakin Yoohan ɗin yanama a hannunsa ne.
Ɗan gudun da yayine ya sakashi cimmasa. Dan haka suka ƙarasa ƙofar ɗakin tare. Solomon ya buɗe masa tare da matsawa ya bashi hanya dan ya shiga.
Batare da yace masa komaiba ya shige, shi ma Solomon ɗin sai ya bisa yana faɗin, “Sir lafiya kuwa?”.
Cak Yoohan ya tsaya da ga yunƙurin shiga Bedroom ɗin da ya keyi, batare da ya juyoba ya ɗagama Solomon ɗin hannu da masa alamar ya barsa.
Da baya-baya Solomon ya rinƙa tafiya harya fice da ga ɗakin, yaja masa ƙofar a hankali gabansa na faɗuwa da yanayin ogan nasu.............✍
🤔🤔🚶🏻Tofa, Dr Yoohan yaya dai?🚶🏻
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/18, 12:14 PM] Amina Mama: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 29
.............“Na faɗaɗa maka muhimmanci kalmar shahada ne domin kasan addinin musilinci ba abin wasa bane, sannan bautama UBANGIJI shi kaɗai bashi da abokin tarayya shine cikakken imani. Gujema shirka babba da shirka ƙarama domin dawwama da tsira wajen bautama ALLAH shi kaɗai da tabbatar da soyayyar MANZONMU a zukatanmu wajibine. Zaka karɓi kalmar shaha yanzun nan Yahya, da ga haka ka tabbatar kabar kafircema ALLAH har abada, ka tsarkake ranka da zuciyarka cewa babu wani sarki sai ALLAH, ANNABI MUHAMMADU kuma MANZON ALLAH ne”.
Kai Yoohan ya jinjina a hankali, zuciyarsa na wani irin tsitstsinkewa, tsigar jikinsa na tashi batare da yasan dalili ba. Hakama jininsa gudu yake a cikin jijiyoyinsa da sauri-sauri. Wannan yanayin sai ya saukarma jikinsa da kasala da wani rauni da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba.
Baba malam na faɗar kalmar shahada yana maimaitawa, suna kai ƙarshe sai kawai hawaye suka ɓalle masa tamkar an buɗe fanfo. Ya sakko a kujerar da yake zaune a hankali ya durƙushe ƙasa jikinsa na wani irin rawa. A matuƙar mamakin su baba malam sai gani kawai sukai ya kai goshinsa ƙasa yayi sujda.
Ɗan yatsa baba malam ya saka ya ɗauke hawayen da suka sakko masa gefen ido kaɗan. Hakama Abban Abdallah sai da hawaye suka cika masa idanu, sai jin wata irin ƙauna da soyayyar Yoohan ɗin suke tana nunkuwa a zukatansu. Kamar yanda shima ƙaunarsu ke sake masa ninƙaya a zuciya.
Koda ya ɗago da ga sujudar da yayi kamar yanda yaga baba malam yayi ɗazun sai kawai ya matsa ya rungume baba malam ɗin yana cigaba da hawaye. Sunja tsahon lokaci a haka kafin baba malam ya ɗagosa yana murmushi, yace,
“Yahya ina tayaka murna. akwai ayyuka sosai a gabanka. Amma kafin su yanzu zakayi wankan shiga musulinci”.
Cikin lunshe idanu dajin wata nutsuwa ta musamman Yoohan ya gyaɗa masa kai.
Bisa jagorancin baba malam Yoohan ya gabatar da wankan shiga musilinci, tare da tsaftace wasu najasosi dake jikinsa, kamar tarin gashin kansa, an ragesa, amma ba sosai ba, dan baba malam ya shaida masa barin gashi ado ne, sannan koyine da MANZON ALLAH (S.A.W), bama ason ayi aski tas-tas ɗin nan kai na ƙyalli. Yanke masa ƙunba. Duk da shi bama mutum bane mai tarata, tare da sauran abubuwan da suka dace su kasance a tsaftace ga ƙa'idar musilinci.
Bayan ya shirya tsaf cikin sabuwar suturarsa farar ɗanyar shadda tas, da taji ɗinkin da yay masa ɗas a jiki baba malam suka rungumesa suna sake masa marhaban da shigowa addinin gaskiya, sannan suka sake zama da shi a karo na biyu domin masa bayani akan SALLAH.
yanzu kam harda su Abba Musbahu suma sun shigo tawagar. Bayan an kawo musu breakfast sunci tare su biyar abin sha'awa. Bayyana muku irin farin cikin da nutsuwa da Yoohan ke ciki a wannan lokaci ɓata lokaci ne.
Shiru falon ya ɗauka duk suna sauraren baba malam dake zuba bayani cike da nutsuwa da ƙwarewar ilimi da sanin da ALLAH ya azurtashi da shi.
Yoohan! Sallah na nufin addu'a.
Amma a shari'ance ibada ce ma'abociyar karatu da ayyuka Keɓaɓɓu, da ake fara ta da kabbara a kuma rufe ta da sallama, sallah ita ce rukuni na biyu a cikin Addinin Musulunci bayan kalmar shahada, wato *_(ASH'HADU AN LA ILAHA ILALLAHU WA ASH'HADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH)_* sai ita. kuma ita ce kashin bayan addini, saboda girmanta da matsayinta ALLAH bai aiko mala’ika da ita ba sai ALLAH Madaukakin Sarki Ya kirawo ANNABI (SAW) a daren Isra’i da Mi’iraji ya bashi ita. Yana daga girman sallah ambatonta da ALLAH Madaukakin Sarki Yayi sau hamsin da takwas (58) a cikin Alkur’ani, kamar inda yake cewa:
{وَأَقِيمُوا الصَّلَوةَ} [البقرة: 43]
Ma'ana: "Ku tsaida sallah"
{قُلْ لِعِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا يُقِيمُوا الصَّلَوةَ}[إبراهيم: 31]
Ma'ana: "Ka fada (Ya Muhammad S.A.W) ga