Showing 33001 words to 36000 words out of 94091 words

Chapter 12 - Saran Boye Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

252

bata shigaba. Tasan itama Addahn bata shigo bane saboda taga baba malam ya wuni a gida jiya, yauma ya daɗe bai fitaba.     
         Kubrah kawai ta iske a falon tana  yankan ƙumba. Ta gaidata cike da girmamawa kamar yanda suka saba. Dan bayan mahaifiyarsu Umm itace mace ta biyu a gidan da suke ɗauka tamkar mahaifiya. Fuskar Umm ɗauke da murmushin itama ta amsa mata, “Ɗiyata saike kaɗai a gidan kenan?”. “Eh Wlhy Umm, daga ni sai Addah kawai. Hajarah da su Jafar sun fita aika”. “To ALLAH ya maidosu lafiya. Ina Addan?”. “Umm tana ɗaki ki shiga mana”.
     Kafinma Umm ta amsa mata Addah ta fito daga ɗaki. “Haba nifa ince kamar muryar Umm, ashe kuwa kece?”. “Ƙyaface haka mana, tun jiya rabon danaga idonki a gidannan Addah. saboda kinga ƴarki ta samu lafiya”.
               “Wacefa lafiya Umm, anason a ganmin bayanta”. Addah ta faɗa cikin ɓacin rai. Murmushi Umm tayi da kama hannunta, dan tasan Addah dama bata barin saita kwana sam. “Kinga nidai muje sarkin hawa”.
           “Bazaki ganeba Umm. Daga jiya zuwa yau naje sashenki yafi sau a ƙirga amma sai na iske Baba malam na nan. Wlhy na kwana tamkar na ciji kaina dan baƙin ciki. Gaskiya Umm wannan al'amarin bai kamata mu zuba masa idanuba a wannan karon, yanzu dan ALLAH minene na ɗaukar Number wayar likita idanba zalunci ba? Lafiyarta ne ba'ason anema kenan ko minene?”.
          “Humm Addah wlhy nama kaina wannan tambayar yafi sau dubu tsakanin jiya zuwa yau. A a daren jiya har musabbabin ciwon Nu'aymah sai da ya dawomin a rai. Bansan minene laifin yarinyar nanba akeson rayuwarta ta salwanta. Ni harma na rasa wane kalar tunani zanyi Addah, wanene? Miyasa? Mi mukai masa?......”
            “Umm nidai tsakanina da ALLAH na fara zargin jama'ar gidan nan fa, idan har mai aikata wannan abubuwan ba'a gidan nan yakeba to daga ina yake zuwa? Nifa dagama jiya na fara tantama akan barin Nu'aymah gidan nan akan maganar aurenta. Shiyyasa ni dama tun farko ban yardaba. ni dama tun jiyan wani shawarace tazomin akan yanda zamu saka ido akan motsin kowa, na tabbatar insha ALLAH a hankali zamu samo bakin zaren”.
                Kai Umm ta ɗaga mata cikin alamar nuna gamsuwa. Addah ta matso kusa da kunnen Umm ta gwargwaɗa mata hanyar daya kamata subi. Ɗari bisa ɗari Umm ta amince, suka ɗaura da addu'ar dacewa. Daga nan suka cigaba da tattauna al'amarin suna ƙarama juna haske. Umm bata bar sashenba sai da lokacin salla yayi. Ta koma sashenta tana jin daɗi a ranta, koba komai zuciyarta ta rage nauyin da tai mata. Shiyyasa akoda yaushe take sake godema ALLAH daya haɗasu aure gida ɗaya ita da aminiyarta. Su kashe su rufe matsalolinsu babu maiji sai ALLAH.
           
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
  
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________
_____________
*_DUBAI_*
________

                 Tun randa Abdallah yay waya da wadda yake zaton Momynsa ce ransa ya sake dagulewa gaba ɗaya. Wani lokacin ji yake tamkar ya naɗama Adawiya mugun duka ya cillata jirgi ta koma Najeriya. Sai dai tsoron fushin iyayensa ke sakasa dannewa.
         A maimakon kwanaki bakwai ɗinma da yay niyyar suyi a kwana na huɗu yasa suka wuce Saudia. Adawiya sai jin daɗi takeyi dukda bata ganin koda murmushinsa. Ita kasancewa da shi a ƙarƙashin inuwa ɗaya kawai ya wadatar da ita a cewarta.
       Ba wannan bane karonta na farko zuwa ƙasar saudia, sai dai yanda tazo a wannan karan yanada banbanci da sauran zuwanta na baya. Shiyyasa take wani jin kanta a sama. Wanda kuma takeyi dominsan ma baisan tanayiba. Tunda suka iso gidan da zasu zauna ya nuna mata ɗakinta bata sake ganin koda ƙeyarsa ba. Tsalle ta dingayi bayan fitarsa, dan ɗakin yayi matuƙar ƙyau da tsari. Sai dai kalar komar zaɓin Nu'aymah ne, harda ma manyan frames ɗinta guda uku da aka manna a bango, sai na Abdallah guda biyu shima. Dukansu sunyi masifar ƙyau. Ta taɓe baki da jan wawan tsaki, stool ɗin mirror taja duk ta juya na Nu'aymah dan har cikin ranta ta tsani ganinta, tunda itace sanadin hana tabbatar farin cikinta, saboda Nu'aymah yah Abdallah yaƙi sake mata, saboda Nu'aymah ta gagara daraja a garesa matsayinta na matarsa. Saboda Nu'aymah saboda Nu'aymah..... Komanta yaƙi dai-daita kamar yanda tai fata, tabar na Abdallah kawai tana faman kuka kashirɓan da zagin Nu'aymah da batasanma tanayiba.

           Rayuwarsu ta saudia tana kadaran kadahan ne, baya shiga harkarta bakuma ya takura ma rayuwarta. Sai dai har yanzu ya hanata wayarta, idanma zata gaisa da Addah da Abbanta ko wani a ƴan gidan nasu saita wayarsa. Kuma yay tsaye a kanta har saita gama ya amshe abarsa. Hakanna bata haushi, amma sonsa da tsoronsa ya hanata ta nuna masa koda a fuska.
      A haka suka kwashe watanni biyu a gidan. Shirye-shiyen makarantarta ya gama kammaluwa ta fara zuwa. Da farko bata shiga harkar kowa ta maida hankalinta a karatu kamar gaske. Tana wata na biyu da fara karatunta tai ƙawa mai suna Abida, sai da ana kiranta Maman Aaida, itama matar aurece harda yaranta biyu, asalin Mamana Aaida itama ƴar Nageriya ce, amma yanzu iyayenta na nan Saudia. Ta girma Adawiya da kusan shekara uku zuwa biyar, dan itakam zatai 22years. Maman Aaida irin matan nanne masu shegen iyayi dason gayu, ga Ƙwanƙwanin tsiya kamar jikar ƙaruna, kullum cikin bama Adawiya labarin mijinta take a zatonta Adawiya budurwa ce. Adawiya dataga iyayin Maman Aaida yayi yawa saita fito ta nuna mata itama ai tanada auren. Sosai Maman Aaida tayi mamakin hakan, danta tabbatar saita shirya zuwa gidan Adawiya a wani weekend. Babu wani ja'inja Adawiya ta bata address ɗinta. A kuwa ranar Alhamis saiga Maman Aaida har gida ita da maigidanta da yaransu biyu, da yake Abdallah na gida sai har mijinma ya shiga. Abdallah dai bai wani sake musu ba, bai kuma wulaƙantasuba aka gaisa da ƴar hira suka wuce, bayan tafiyar tasu kuma bai cema Adawiya komaiba akan zuwan nasu ba duk da yasan ya dace ace yayi hakan.
           Sanadin haɗuwa da Maman Aaida fa idanun Adawiya ya ƙara buɗewa. Dan tunda Maman Aaida ta bigi cikinta taji yanda akai aurenta da Abdallah sai ta shiga ɗorata bisa wasu hanyoyi da zata ringa jan hankalin Abdallah, ciki harda abubuwan irinsu turaren jan hankali da sauransu. Tun Adawiya najin tsoron yin hakan harta fara hawa kan network da sha'awar fara gwadawa ko zata dace Abdallah ya manta da Nu'aymah.
      A ranar farko da ta fara buɗe jikinta da turare Abdallah bai kwana gidanba, yamayi tafiya bata saniba. Da yake sai ya gadama take ganinsa sai bata fahimci baya nanba, washe gari ta wuce makaranta. Data dawoma bata gansaba bata kawo komai a ranta ba har dare, lokacin kwanciya ta sake shanana turare ta nufi ɗakinsa. Sai dai kuma wayam. saida ta leƙa har toilet sannan ta lurama ba'ai amfani da toilet ɗinba ma kwata-kwata. A take kuma sai tsoro ya kamata duk ta tsure, leƙe-leƙe ta shigayi cikin gidan kamar wata zararriya. Data ga dai lallai babushi a gidan saita fara kuka, ta koma ɗakinsa ta ƙulle ƙofa ta ƙudundune a bargo. Ta kusa awa guda a haka sannan ta fara jin motsin za'a buɗe ƙofa. Sake rikicewa tayi da kuka catake wanine ya shigi. Cike da mamaki Abdallah daya shigo yake sauraren kukan nata dan baiyi zaton ganinta a ɗakin nasa ba. Ƙarasawa yay gaban gadon ya yaye bargon. Tako dage zata kwarara masa ihu dan ruɗewa ya hanata nutsuwa taga wanene. Saurin hayewa gadon yayi ya rufe mata baki ruf da hannunsa yana kallon yanda jikinta ke rawa.
        A take yanayin nata ya juye masa tamkar na Nu'aymah, dan duk lokacin da abu ya tsoratata haka zakaga jikinta na rawa duk ta fita hayyacinta, daga haka kuma saita suma. Yanda zuciyarsa ke ƙawata masa Nu'aymah sai tunaninsa ya gushe zuwa gareta harya rungume Adawiya batare daya fargaba. “K malama ki nutsu nine?”.
         Sosai Adawiya ta sake maƙanƙale masa dan a rikice take sosai, amma taji daɗi da taji shine.
            Tun Abdallah na shaƙar ƙamshin turaren data saka matsayin ƙamshi kawai harya fara canja masa yanayi. Hancinsa ya ɗaura bisa wuyanta yana shinshina da lumshe idanu, kafin a ɗauki tsahon lokaci jikinsa ya fara tsuma, sai ya sauya salon riƙon da yay mata. Anan nefa Adawiya ta dawo hankalinta da ƙyau. Da farko nishaɗin abinda yake matan ta farayi. Sai dafa taji al-amarin bawai wasan yara bane sannan ta fara kuka da roƙo da magiya. Da al-amari yay zurfi saiga hajiya malama mandiya ƴar ƙwalisar soyayya Adawiya na tsinema Maman  da jamata ALLAH ya isa🤣😂🤣.
     Oho, Abdallah baisan tanayiba, morewarsa yakeyi dai-dai gwargwado, yama manta dawa yake tare. Iya wahala ya bama Adawiya batare da tausayawaba, kafin ya koma gefe ya barta ko numfashin kirki bata iya yi.

      Tun daga wannan ranar Abdallah ya maida Adawiya abar hutawarsa. Daya samu biyan buƙatarsa kuma ya watsar da ita tamkar bai taɓa sanin daga inda ta fitoba. Sam ta gagara gane kansa balle inda ya dosa. Komai nasa yana yinsane da kulawa da lura. Abincinta dama kam bai taɓa ci ba, zai dai ajiye mata duk abinda ta buƙata ya kuma bata kuɗi. Amma babu wani farin ciki da kulawa kamar yanda Maman Aaida ke faɗa mata. Duk iya dabarun Maman Aaida cikin gwadasu take ga Abdallah amma saiya yi kamarma baisan tanayiba. ba shiga ɗakinta yakeba, ko abu zai bata sai dai yay knocking ta fito ta amsa. Idan yana buƙatar moranta ma zai mata knocking ne idan tana ɗaki yace ta samesa nasa ɗakin.
     A haka rayuwar auren nasu ke tafiya tare da karatun Adawiya da ta fara saka shiririta saboda damuwarta kawai itace Abdallah ya sota a yanzu.

*_NAJERIYA_*

            Rayuwa ta shuɗa, kwanaki nata gangarawa, inda ake neman watanni na takwas kenan da lalacewar auren Nu'aymah da Abdallah. Tana cikin tsananin damuwa da begensa, kullum dare sai tayi kuka, tana sonsa matuƙa, dan ta rayune da son nasa. Yawan damuwar da take a cikine ya haifar mata da yawan yin ciwo, saboda ciwonta bayason damuwa sam. A duk sanda ta takura kanta da tunani da damuwa yakan yawaita motsa mata akai akai, tana kuma matuƙar shan wahala.
        Gaba ɗaya a awatannin nan lafiya taƙi wadatarta, haka taketa fama yau fari gobe tsumma. Gashi baba malam kullum cikin mata jan ido yake akan ta kawo Ameer yay musu aure. Tayi kuka tayi rantsuwar akan Ameer ba saurayinta bane amma sam yaƙi ya saurareta. Umm kanta wannan al'amari na tada mata hankali. Amma babu yanda ta iya ta zuba musu ido kawai taga iya gudun ruwan mijin nata.
   
      Burin Nu'aymah cigaba da karatu a yanzun, amma Baba malam yay banza da maganar karatun nata, bayan kuma kowa a gidan yasan burinta a rayuwa shine ta zama likita ko Nurse tun tana yarinya. Addu'arta kullum itace Baba malam ya haƙura a sake nema mata makaranta kafin ALLAH ya dawo da hankalin Abdallahnta gareta, dan ita duk ɗaukarta Abdallah fushi yake da ita akan ta gudu ran aurensu, shiyyasa yaƙi nemanta koda a wayama. Ta dage da azumin litinin da alhamis da sallar dare tanata gayama UBANGIJI kukanta.
      Ana cikin wannan yanayin su Baba malam suka gama shirya gagarumar walima na saukar Al-Qur'anin yaransu na gidan marayu, tare da aurar da waɗanda suka samu mazan aure. Wasunsu anan cikin gidan suka dai-daita kansu. Wasu kuma a waje suka samu mazajen aure da mata.
    Shirye-shirye ake babu kaman hannun yaro, dan shinema ya ɗauki Baba malam Busy sosai ya samawa Nu'aymah lafiya daga takurar zancen fiddo mijin aure. Duk da dama dai yana matane kawai dan hukuntata ta cikin ruwan sanyi akan abinda ya faru. amma ta ƙarƙashin ƙasa neman hanyar ganin likitan nan kawai yakeyi da nema mata makaranta batare da ko Umm ta san da hakan ba. 
      Ana saura sati ɗaya su Yusrah suka iso, washe gari kuma su Amal. Hakan ba ƙaramin daɗi yayma Nu'aymah ba, koba komai ta rage kaɗaicin da ta tsinci kanta a cikin a waɗannan watanin ai. Abinda ya ƙara faɗaɗa farin cikin natama shine Amal da Yusrah bazasu komaba, dan zasu zaunan zana jarabawar ssce anan. Cikin kwana biyu kacal da dawowar tasu ta fara komawa cikin walwalarta.
       Tuni suka fara addabar gidan da ƙiriniyarsu da bata ƙarewa, sauƙinma babu Adawiya, amma hakan baisa sun fasa abinda suka saba yiba. tun ana saura kwana uku suka saka Hajjo ta roƙa musu baba malam komawa cikin gidan marayu har sai an kammala komai. Dan yawancin ƴammatan da za'aima auren duk ƙawayensu ne, duk da dai a shekaru gaskiya zasu girmesu da kusan shekara bibbiyu ko ɗai-ɗai.
     Bai hanasu ba, dan gidan marayun nan nada matuƙar muhimmanci a garesa dama family ɗin gaba ɗaya. Yanda suke ƙoƙarin dagewa akan tarbiya da karatun yaransu haka suke dagema yaran gidan marayun nan suma. Shiyasa suma yaran suna tsananin ƙaunar wannan family, su suke ɗauka danginsu da komai a rayuwa.

★★★★★

             “Wai wannan akwatin da kika lodama kaya duk na miye Nu'aymah?”. Umm data shigo ɗakin Nu'aymah ta faɗa tanabin Nu'aymahr daketa shirin kaya da kallo.
     Ɗagowa tai ta kalli Umm cike da ɗoki, “Umm yo na bikine mana, sati guda zamuyi a can”.  “To lallai, ashema kune iyayen bikin kenan?”. Dariya Nu'aymah tayi dajin zancen Umm, Umm kam daga haka bata sake cewa komaiba ta ajiye mata magungunan ta tana faɗin, “Gasu nan, saura kije kita wasa da shansu Nu'aymah, dan ALLAH ki kula da kanki, duk abinda kikasan zai zame miki matsala ki kujesa, ku kuma riƙe mutuncin kanku, na kira Baba Habi a sashenta zaku zauna kafin Hajjo ta iso gobe idan ALLAH ya kaimu, saura naji wani abu mara ƙyau na shegen tsiwanki, ALLAH saina ɓata miki rai”.
        “Umm insha ALLAH bazakiji komaiba ma”. “ALLAH yasa”. Umm ta faɗa tana juyawa ta fice daga ɗakin..

          Bayan sallar azhar su Nu'aymah sukai sallama da kowa suka wuce, Yah Abubakar ne ya kaisu. Da yake shima irinsu ne ɗan taraliya saida ya kaisu sukai shopping sannan ya wuce dasu gidan marayun.
     Ƙaton gaske ne, sannan an ƙawatashi ta ko ina babu makusa. Akwai makaranta da asibiti da duk ma abinda masu rayuwa da iyayensu suke samu. Makarantarsu ta fara tun daga noziri har zuwa sakandire. Ana koyar da boko da arabic, idan kaji yanda yaran ke larabci da turanci sai kasha mamaki da al'ajabi. Rayuwarsu suke cike da farin ciki da jin daɗi wadda ko wasu masu iyayenma basa samu. Gasu da tarbiyya abin birgewa.
     Ɓata lokacine zama bayyana muku yanda gidan marayun nan ya ginu da tsari mai ƙyau, kusa a ranku kawai ya haɗu. Dan sosai su baba malam ke samu taimakon manyan mutane dama masu mulki game da riƙe gidan. Ga kuma suma kansu masu nemane basu zauna jiran na sadakaba. Kaso mafi yawa na ɗunbin dukiyarsu yana tafiyane wajen tattalin rayuwar marayun nan da kulawa da su. Shiyyasa Alhmdllh da wahala ace sun nema abu sun rasa. Sai dai ace yau da gobe sai ALLAH, komai arziƙinka dama wani abun sai ya gagareka.
       A yanda su Nu'aymah suka sami tarba zai tabbatar maka da sanannune a gidan, kuma ba wannanne farkon zuwansu su kwanaba. Dan rigima aka shigayi musamman ga sa'anninsu, kowa na faɗin sashinsu su Nu'ayma zasu sauka. Bayan ansha taƙaddama dai kowa ya haƙura zasu zauna a sashen da amare suke, wato sashen baba habi da Umm ta faɗama Nu'aymah tun a gida.
        A yau kowa ya kalli Nu'aymah yasan tana cikin farin ciki sosai, haƙoranta sun kasa rufuwa. Tsiyarsu sukaita tsulawa uwa ba kwaɓa uba babu tsanani, dan suna son suga sunzo gidan nan, shiyyasa wani lokacin baba malam da kansa yake cewa suzo suyi weekend ɗinsu anan, dama anan duk yaran gidansu ke karatunsu tun daga noziri har zuwa sakandire, shiyyasa sukeda shaƙuwa sosai da yaran gidan marayun fiye da zaton mai tunani.

     Washe gari Nanah tace suma gasunan zuwa ita dasu Suhailat, hakan yasa bayan sallar la'asar ana tsaka da musu ƙunshi dan ranar itace suka saka ranar ƙunshin, Nanah ta kira wayar Yusrah ta sanar musu gasu a bakin titi suzo su shiga dasu dan baza'a barsu su shigaba kai tsaye.
        Nu'aymah da Yusrah da biyu cikin ƴammatan gidan suka fita shigowa da su Nanah dansu ƙunshinsu harya bushe sun wanke, Nu'aymah ce kawai bata wanke nata ba amma ya bushe. da ƴar tafiya tsakanin gate da gidajen yaran, amma haka suka taka a ƙasa suna hira har suka iso. suna a gab da fitane suka haɗu da yaran gidan maza da bazasu gaza shekaru sha biyu ba kusan su bakwai wai wajen ball suka tilla ƙwallon waje ta katanga shine zasu zagaya ɗakkowa. Security ɗaya ne tare dasu zai rakasu. A tare suka fita dasu Nu'aymah da zasuje tarbar su Nanah.
       Gidan marayun yana akan babban titine, shiyyasa sam ba'a barin yaran fitowa ko ina su kaɗai koda hakan ta kama sai da security.
     
        Dariya Nu'aymah tai ganin su Nanah acan ɗayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login