Showing 33001 words to 36000 words out of 37455 words
****
B
a karamin shiri Mukhtar ke yi na isowar Maman su Jalan ba. Ya sa an fente gidan gabadaya da sabon farin fenti mai feshi, an shirya mata dakuna na alfarma da furnitures yan uban su. Sannan ya sa an shirya dakin Fajur kusa dana Amani, Safwan ma yasa na fidda masa daki daga waje kusa da na Kamilu. So gida ya zama full house, family house don hatta Baba Idrisu sun bashi dakin sauka a gidan duk lokacin da ya zo. Gidan Hon. Usman babban gida ne da ya lamushe dukiya mai yawa wajen ginawa a matsayin sa na Architectural Engineer, har gobe kuma kullum kara kyawun gidan ake da gyara shi yadda zai tafi daidai da zamani da duk wani sabon abun kawata da ya shigo da shi daga waje.
Rakiya na ta hidimar dawowar uwar dakin ta, bata sama bata kasa don tabbatar da ta ajiye ma Amani komai na bukata, yadda suka saba. Ta ji labarin auren Amani da Mukhy a bakin Malam Tajudden tun kafin su dawo, tayi mamakin ta ita kadai ta bari. Yanzu kuwa Kamilu ya gaya mata har Babar Amani mahaifiya zaa dawo don haka girke-girke na musamman ta yi musu, zuwa yamma kuwa sai taji dirin motocin da suka je debo su sun shigo, wato dai sun iso gidan lafiya.
Gidan ya kaure da hayaniyar farin ciki, Mukhtar yana gidan sa yana barci bai san sun iso ba, don jiya kwana yayi da maaikatan Alhaji ana meeting na amana, kan wanda zai jagoranci kamfanin Alhaji da gaskiya a cikin su tsofaffin maaikatan Alhaji, sabida shi zai koma gida, bada jimawa ba. Bai kuma da niyyar dawowa.
Boutique din Amani ya koma karkashin kulawar Kamilu kasancewar shima kasuwanci ya karanta. A karshe Mukhtar ya zabi Alhaji Badaru Matawalle wani tsohon maaikacin kamfanin da sun fi shekara Talatin suna aiki tare da Alhaji, a shirya a bata, still dai an jure zaman tare na lokaci mai tsayi, an kuma san halin juna, Alh. Matawalle dan asalin Bindawa ne, shi Mukhtar ya baiwa kujerar sa karkashin saka hannun mutumin da Lauyoyin Alhaji, suka yi resolution kan zaa cigaba da gudanar da ayyukan kamfani yadda aka saba bisa amana da gaskiya, Mukhtar ya ce ko yaya suka fahimci wani abu ya biyo baya na rashin gaskiya a kamfani, to kuwa zasu rufe kamfanin ne kawai.
Aka yi komai a shariance, sannan ya ce gobe zai ma Matawalle handing over na ofishin sa. Ba shi ya tashi daga barcin gajiyar da yake yi ba sai ana gab da kiran sallar maghriba. Don haka a gurguje ya shiga wanka yayi alwallah ya fito yana shiryawa a gaggauce, ya san yanzu su Amani sun dade da sauka.
Ya rasa dalilin dokin da ke cin ran sa sai kace shi aka kawowa amarya ba Alhaji ba.
Murmushi ya yiwa kan sa, wani abu da ba kasafai yake faruwa da shi ba, wato bai da yawan murmushi, kuma in yayin, shi kan sa ya san ba karamin kyau yake kara masa ba.
Ya ce ma kan sa in haka ne ai shima yana da amaryar, sai dai tasa fitsararriya ce hamshakiyar shuuma mara kunya, ba irin ta Alhaji mai kirki da sanin ya kamata ba.
Sanda yake fesa turaren sa watau Azzaro Visit bayan ya fito daga wanka, sai da wani farin cikin son ganin Amani ya darsu a ran sa.
Yana duba wayar sa ya ga missed call din Alhaji dana Kamilu rututu, da sauri ya saka takalmi a kafar sa ya fita, bayan ya rufo kofar dakin da mukulli ya hau motar sa Bugatti wadda Alhaji neya bar masa ita zuwa gidan Alhajin, duk da ba nisa da nasa gidan tafiyar kafa ce kawai, ya kuma fi zuwa a kafan a yawancin lokuta, amma yau da yake cikin saurin isa gidan yake sai kawai ya hau motar.
Yana parking yana fitowa da Safwan ya fara tozali, yaron ya zo da gudu ya rungume shi, bakin Mukhtar yau a bude, fararen hakoran sa a warwaje, kai ka ce shi ya mallaki kamfanin COLGATE, abinda ya baiwa su Malam Tajudden matukar mamaki, sai fara yake yana rike da hannun Safwan suka shiga gidan, yana ta bashi labarin zuwan su da abubuwan da suka gani na mamaki a hanya.
Kai tsaye falon Alhaji ya nufa inda ya tadda su su duka a can, har Mamma Jalan, sun hada kai ana cin abinci tana zubawa Alhaji ruwa a tambulan, wannan abu yayi matukar faranta ran Mukhtar. Yau rayuwar Ubangidan sa ta koma irin wadda ya dade yana masa fata, rayuwa mai kyau da maana wadda addinin musulunci yayi koyi da ita, ba irin kazantacciyar rayuwar sa ta baya ba ta babu wani jinin sa da zai rabi niimar arzikin da Allah ya yi masa. Wadda watakila ita ta jawo masa yake ta shan wahala a rayuwar sa.
Ya duba ya hanga a cikin su bai ga yar mulkin ba. Wadda tun zuwan su gidan da aka kauraye da hayaniya ta samu migraine wato ciwon kan barin kai guda wanda gajiya ta haifar mata, sai ta zame jikin ta ta haye sama dakin ta, ta shige ta kulle kan ta. Har da lika takardar data ke likawa Rakiya a jikin kofa an rubuta DO NOT DISTURB wato kada wanda ya zo ya dame ta.
A duk sanda Rakiya taga ta lika mata wannan a jikin kofa bata kara zuwa kofar dakin sai ta neme ta don kan ta.
To yau ma hakan, Rakiya ta zo don ta kawo mata nata abincin, don ta san bata cin abinci da mutane, nan ta ga abinda aka lika mata tuni ta yi ta kanta. Baba Sahura ta tambaye ta ina Uwa, ta san in ta ce UWA Amani take nufi, ta ce tana barcin gajiya ta lika kada a dame ta. Sahura ta ce Inye! Mulki sai mai shi. Wannan da basarake ta aura bansan ind zata kai mulki da iyawa ba.
Shigowar Mukhtar falon aka kauraye da yi masa barka da zuwa daga bakin kannen sa Fajur, Kamilu da sauran yayan Baba Idi dana Sahura da suka zo daga Faskari yau. Baba Sahura na fadin ango ka sha kamshi, na Uwa farin mutum mai farar aniya alherin Allah ya kaiwa iyayen da suka haife ka. Sahura ta fadi hakan ne don ta san duk wannan kokarin na gyara rayuwar su data dan uwan su, kokarin sa ne bana wani ba.
Shima yau ya kasa yin rowar murmushi, sai sakin sa yake gwanin shaawa. Ya zauna daf da Alhaji yana gaida Mammah, tace Mukhtar ya naga idanun ka sun tasa? Ina fatan lafiya dai?
barci nayi mai yawa Mamma, da yake jiya mun kusan kwana muna meeting ta ce to madallah, ga abinci ta soma serving din sa burabuskon shinkafa da miyar ganye da naman tolo-tolo, ya ce Ai Mamma ban iya cin burabusko, shake ni yake yi ta mayar ta zuba masa fried sphaghetti da romon kaza sannan ya karba ya soma ci ana ta hirar Saliyo.
Alhaji ganin kowa ya manta da Amani shi bai manta da ita ba, yar lelen sa tana like a ran sa. Yace Mukhy, ka gama cin abincin? Ya ce eh Alhaji. Alhaji yace yawwa, to maza tashi ka je ka zo min da TAFISU yau labarin rayuwar ka zaka bamu dukkan mu. Da abinda ya rabo ka da iyayen ka tun da ka ce min suna raye, da dalilin da yasa baka ko so a yi maka zancen gida ko na kasar ku.
Amma ina so ya zama an yi komai a gaban Uwa ta (Tafisu). Don haka je ka zo min da ita.
Kunya ta kama Mukhy, musamman da Jalan ta zuba masa ido, ta rasa mai yasa take jin sa kamar dan cikin ta, ta yaya zai iya tsallake Uwa da uban Amani ya je inda take a cikin gidan su?
Sai da Alhaji ya sake maimaita umarnin sa, shi ba abun yace a aika Fajur ko Safwan ba, tunda Alhaji ne da kansa yayi magana. Da kyar ya iya mikewa ya bi matattakala da sassarfa zuwa sama, wato bangaren Amani.
Yana zuwa kofar dakin ya ci karo da sakon ta na Do Not Disturb. A jikin marikin kofa. Dariya ce ta kama shi, sai kace a Hotel! Ai kuwa zata ga disturbance yanzun nan. Kofar ya hau kwankwasawa da karfin sa kuwa. Amani na tsakiyar barcin wahala barcin da migraine ya sabbaba mata, ta ji ana mata wannan bugun na rashin tsanaki. Ta mike cikin rangaji da sarawar kai ko kayan jikin ta da suka zo dasu a jikin ta bata cire ba balle dogon hill shoe dake kafar ta, haka ta afka gadon duka, tana tafe zuwa kofar a fusace, tana fadin mai raba ta da Rakiya yau sai Allah.....sai tayi kasa-kasa da ita, sai ta ci abu kaza-kazan ta.
Tana budewa dogon baabzinen yana sako kai cikin dakin har yana kusan ture ta, saura kadan ta fadi don dama jikin ta ba kwari. Ta yi maza ta rike marikin kofar.
Farin gilashin dake idon sa ya zare, yadda zai ji dadin kallon matar tasa rigimammiya Amani Faskari, ta yi yar kiba kib-kib ta yi jawur ta murje abinta. Mai nuna ta samu kwanciyar hankalin da bata taba samu ba a zaman ta a Saliyo. Ga wani uban su kunshi mai ja da baki da Mamma tasa aka yi mata a sawayen ta da zara-zaran tafukan hannayen ta. Ta fito a amaryar ta sosai sai rashin mutunci fal a idanun ta. Tace a fusace.
Shin baka ga an saka do not disturb bane? Da zaka zo ka tada ni daga barci bayan bani da lafiya?
Mukhtar ya ce do not disturb, a dakin hotel kike? Ko wata tsiya kike kullawa a dakin banda barcin asara? Kuma na dauka a gidan mutane kike ba a gidan ki ba, da zaki kwanta kina zuba iko?
Kallon mamaki Amani tayi masa, ta ce gidan namu ne gidan mutane? Ni da gidan uba na? Ya ce aikin kenan! Alfahari da Uba, ko anan aka binne cibiyar ki baki da ikon cewa kada a dame ki a gidan nan, tunda ba gidan mijin ki bane gidan Mama Jalan ne yanzu.
Amani tayi kwafa, ta koma gefen gado ta zauna tana fadin har akwai wani gida da ya fiyewa mace gidan uban ta? Mukhy ya ce sosai ma kuwa, gidan uban nata na wucin gadi ne, gidan da zata je ta haifi yaya shine comfort zone din ta, shine inda duk mulkin data zuba babu mai kalubalantar ta. Amani ta zo iya wuya, idan nace maka ni kuma babu wani comfort zone da ya fiye min gidan uba na muhimmanci zaka yarda?
Idan nace maka baka da gidan da ya isa ka ajiye babbar yarinya iri na zaka yarda?
Idan nace maka Alhaji ya cuce ni iya cuta da ya bada aure na gare ka kaskantaccen bawan sa zaka yarda?
Idan nace maka kyan ka da ake fadi bai taba bugar da ni ya sa na ji ka da wani matsayi a rai na ba saboda baka kai matsayin da zan aure ka ba zaka yarda?
Ina bakin cikin abinda ya shiga tsakanin mu ranar nan a Saliyo, saboda kai ba aji na bane, ka yarda?
Mukhy ya juyar da idanun sa da suka canza launi, yana kokarin hadiye bacin ran da ya taso masa, ya ce me kuwa zai hana ni yarda tunda na kwana da sanin yar Qaruna ce, Tafisu wadda tafi sauran mata, kuma a hakan aka bani sadaqar ta, ana roko na Allah Annabi in karba da hakuri, saboda Alhaji kan sa ya san ba yar kwarai ya haifa ba; ballagaza ce, banza ce, mahaukaciya ce kuma jahila, wadda ta rako mata duniya!.
Amani sai ta fashe da kukan da baya mata wuya na shagwaba da sakalci, amma na yau iya gaskiyar ta take yin sa bilhaqqi, domin Mukhy yayi mata cin mutunci da wani dan adam bai taba yi mata ba, tun baa je koina ba, ai ga irin ta nan, Daddy ya sayo mata gori da rashin daraja a wajen wanda bai isa komai ba, sai ta kara tsinkewa da kuka.
Mukhy yayi kwafa, yace yarinyar nan ina tausaya miki domin baki san rayuwa ba ko kadan, baki san Annabi ya faku ba, baki san dukkan mu darajar sa muke ci ba, duk wani rawanin tsiya ya kare a kan ki, Ubangiji ya laanci shaidan ya kuma fitar da shi daga Aljannah ne sabida girman kan sa da jin cewa yafi kowa.
Baki san Allah ya ce Inna akramakum indallahi Atqakum. Ubangiji yayi alkawarin dankafar da maabota girman kai dagawa da alfahari, masu girman kai iyalen shaidan ne, ni ina tausaya miki, ina kuma tausayawa kaina, sannan ina tausayawa yaya na idan kika haife su baki yi hankali ba.
Ke kam ai dadi ne ya yi miki yawa, shi yasa kika kasance mara godiyar Ubangiji; Uwa da Uban ki na son ki, suna tarairayar ki da ririta ki da son ganin kin zama matar aure ta kwarai, wani kama na iri na bai samu wannan gatan da kika samu ba.
Don haka in kin gama ki zo suna kiran ki a kasa.
Daga haka ya juya ya fice ya koma wajen su Alhaji. Yana kokarin maida walwalar sa ta dazu, amma hakan ya faskara, domin kullum Amani ta ci mutuncin sa fita take kara yi a ran sa, baa jimawa kuma in ya huce zata dawo ta yi masa kaka-gida a rai, ya manta duk wani aibun ta.
Ba jimawa sai gata ta sauko cikin shiga ta kasaita, ta ci hill shoe din ta kamar mai shirin tafiya dinar babbar aminiya, ta kafe dauri a gaban goshi tana tana taunar cingam rakakas-rakakas. Ita a lallai ga wadda tafi sauran mata.
Da dane, da tuni Alhaji ya fara yi mata kirarin TAFISU! Amma yanzu da yake yayi hankali sai cewa ya yi Uwa yaya kika sakko babu mayafi? Maza koma ki yi lullubi ta zumburo baki sannan ta koma, Jalan tayi fatan a kusa da ita take ta kaiwa bakin da ya sha purple din jambakin Elizabeth Arden lipstick kalar material lace din dake jikin ta kyakkyawar mahangurba. Sai Allah ya ceci Amani daga can nesa da ita kafar bene ta tsaya.
Ta dauko mayafin wanda dashi da babu duk daya dai ta dawo. Baba Idrisu yayi sallama ya dawo dakin don ya dan zaga toilet ne. Alhaji ya nuna mata gefen Mukhy ya ce nan ne wajen zaman ta family meeting zasu yi.
Kallon da Mamma Jalan ke mata ne yasa ta yarda ta zauna a gefen Mukhy din, ba tareda ta yi musu ba. Jalan ji tayi kamar ta fashe da kuka a kan irin taunar cingam din da take yi a gaban kowa. Ta na Allah-Allah a tashi meeting din ta ci uban ta. A Saliyo ta dan samu saiti, wato yanzu an dawo gaban Alhaji da ke daure mata gindi shine zata koma halin ta? Ita kuwa Amani tana sane duk abinda take yi don ta kular da Mukhy ne, wato ta rama cin mutuncin da yayi mata, ta san baya son ta da cin uwar kwalliya irin haka. Balle daurin gaban goshi. Har taunar cingam din ma baya so ya taba ce mata ba tarbiyya bane.
Alhaji bai san tana yi ba. Haka Mukhy bai bata hankalin sa ba balle ta kular da shi din data ke so, ya ce Mukhtar yau ina son in san tarihin ka, abinda ya fiddo ka daga gida, da kuma abinda yasa baka so ka koma kusan shekaru tara kenan. Lokaci yayi da zaka je gida tunda ka fara aje iyali. Ba fata ake ba, amma akwai mutuwa akwai kuma ciwo. Ba damuwa muka yi mu san cewa kana da asali ko baka da shi ba, amma lallai zamu kai Amani ga iyaye da yan uwan ka don su san da zaman ta, tunda auren sunna ne muka kulla, wanda muke fatan a samu zurria a mai albarka a cikin sa.
Mukhtar ya nutsu sosai yana sauraron ubangidan sa kuma surukin sa a halin yanzu, ya san gaskiya ya fada, amma sabanin lokutan baya da in yayi masa maganar gida ransa ke baci yau shi da kansa cikin nostalgia (begen gida) yake domin ya fara gajiya da gorin Amani. Kuma ya saka a rana sa cikin satin nan in Allah ya yarda zai koma gida ko da Amani bazata yarda ta bi shi kasar su ba.
Mukhtar ya ce.
Labari na mai tsaho ne Alhaji, and very complicated, tragic story. Wanda nafi so in yi revealing din shi tare da ku da iyaye na a zaune gabadaya.
Abinda zan iya cewa a yanzu shine iyaye na suna raye (as far as I know), ina kuma da labarin duk halin da suke ciki ta hanyar wani abokina na kuruciya mai suna Ari.