Showing 24001 words to 27000 words out of 37455 words
kuwa duk yana tafiyar da su ne ta yanar gizo da kwamfuta, sannan yana da mataimaka na kwarai. Amma so yake yayi nisa da Amani.
Bayan sun ci abinci Faytoory yayi musu sallama ya tafi. Mama Jalan tace bata yarda ba sai ya yi kwana uku sun gana sosai. Tasa Safwan ya kai masa kayan sa dakin marigayi dake harabar shigowa gidan bayan fajur taje ta share ta kunna turaren wuta. Fajur da Safwan suna zaune manne da Amani, sun kasa matsawa ko nan da can kada ta tafi ta bar su. Safwan zai yi shekaru sha biyar Fajur kuma goma.
Ta umarci Safwan ya raka Mukhtar ya huta, sai suka shiga daki ita da Amani da Fajur.
Ta hada mata ruwan zafi mai kamshi tayi wanka sannan suka zauna suna kara gaisawa. Sallah ce kawai ta tayar dasu a wannan ranar don kwana suka yi a zaune, Amani na baiwa Maman ta labarin rayuwar ta da mahaifin ta gabadaya tun daga sanda ta fara wayo har zuwa yanzu, da yawan matan da ya dinga aura yana saki sabida ita, da artabun su da matar shi ta karshe Haj. Rabi, da halin da yake ciki a yanzu na shanyewar barin jiki, ta bata labarin haduwar shi da Mukhy a Paris, da kawo shi gidan su da yayi, ya bashi gida daura da nasu, ya kuma sakar masa ragamar kamfanonin ta da shagunan ta, yadda ya dinga fifita alamarin sa, da irin yardar da ke tsakanin su wadda take ganin ta rage mata daraja a gun mahaifin ta, har zuwa aura mata Mukhtar da yayi ba tareda yardar ta ba wanda shine abinda ya kara sawa ta tsani Mukhtar ta kuma amince Daddy yafi son sa yanzu a kan ta.
tace Mamma wallahi bana son sa, ko kadan, ko ganin sa bana son yi, kyawun sa ko ilmi sa ko yanayin kasaitar sa dake burge Balewa bai taba ruda ta sun saka ya birge ni ba, ban taba son sa ba, kuma har gobe bazan so shi ba, sabida yaron Daddy ne a kasa na yake, kuma mara kirki mara dadin muamala ba ya girmama ni. Mara asali mara nasaba gashi nan dai shi ba tsintacce ba shi ba Da ba.
Cikin halayen sa bakidaya babu guda daya da zan iya ce miki mai kyau ne. Ga girman kai ga fadin rai, baa saka shi baa hana shi, a haka Daddy yake tunanin zan iya zaman aure da shi? A rayuwata in ba mijin da zan juya kamar waina a tanda ba, bazan taba yarda in aura ba.
Duk mazan duniya Daddy ya rasa wanda zai aura min sai wanda baida asali kuma a karkashi na yake? Ai karshen kaskantawa Daddy ya gama yi min ita, shi yasa na ce ba zan koma Katsina ba har duniya ta nade.
Ta fashe da kuka tana cewa ko sadakin su ban karba ba, don haka babu wani auren sa a kai na ni. Baba Idin ma ya san ban karba ba shi na barwa abin sa, sai dai in Baba Idin ya aura.
Jalan tayi taawizi. Tun baa je koina ba Mama Jalan ta gama karantar wacece Amani, halayen ta da dabiun ta marassa kyau na girman kai, alfahari da dukiyar uban ta, fariya da izzah na rashin sanin darajar da Allah yayi wa dan adam. Yawan alfahari da rashin kunya na rashin mafadi ko tarbiyya mai inganci.
Tausayi mai tsanani ya kamata sai ta kasa ce mata komai. Sabida ita ta koina Mukhtar yayi mata, har tsoron kwarjinin sa da ilhamar sa ta ji, don kwarjinin sa da kasaitar sa cika mata ido da falo suka yi, ta yi duba don gano makusa a tare da shi da ta sa Amani fadin abubuwan da take fada a kan sa ta rasa.
Sai kawai ta gane cewa Amani wawuya ce, doluwa, gaula kuma goyon namiji. Mai halin yan fari, kuma wadda gata da kudi ya jika har ya yiwa yawa har ya taba hankali da nutsuwar ta.
Bata samu tarbiyyar uwa da wadatar ilmin addini ba sai na zamani. Sanan bata samu religious background na musulunci sosai ba.
A yanayin da take magana ma ga kowa, gatsau ba respect ba taunawa tana gatsine baki na raini ga Mukhy ya tsorata Jalan.
Kamar Mukhtar itama nan take ta gayawa ranta cewa jan aiki ne a gaban ta jawur, don haka zata roki Mukhy ya bar mata Amani zuwa nan da watanni biyu haka. In hakan ba zai cutar da shi ba. Yo Allah ta tuba ina wani kwanciyar hankali da miji zai samu a tare da Amani mai abubuwa irin na zararru? Ai gara ma ya bar ta aga abinda zaa iya a kan ta ko kadan ne, tunda baa bari a kwashe daidai, kuma icce tun yana danye a ke tankwara shi.
A halin yanzu tana so ta karance ta ciki da bai, don ta san ta inda zata bullo mata, da yadda zata gyara gurbatattun dabiun ta da halayen ta ko da ba duka ba, kafin ta shiga dakin miji ya zama ko manner of speaking ta gyara mata. Tunda an riga an baro kari tun ran tubani.
Duk da haka zata yi iya yin ta cikin yan watannin da zasu yi tare, sauran sai ta barwa Allah mai kowa mai komaia, ta kuma hada da addua da rokon Allah ya baiwa Mukhtar zuciyar dauka da soyayyar da zata rufe masa ido daga ganin aibun munanan halaye da dabiun yar ta.
Sai bata ce mata komai a kan Mukhtar ba a wannan daren, ta barwa ran ta, don so take ta gano root causes na matsalolin sangartar Amani da rashin good upbringing din data samu, sannan ta yi tunanin hanyoyin magance su a ilmance.
Duk da ita ma din ba wai ta samu zurfin ilmin zamani bane amma tayi sakandire kuma tana da ilmin addini sosai, sannan ga shekaru ga kyakkyawan hankali.
Amani ta nemi ta bata nata labarin. Bayan rabuwar ta da mahaifin ta.
Nan ta gyara zama ta soma bata labari ta gaya mata cewa bayan Daddy ya sake ta a gadon asibiti basu taho ba sai da ta warke tas, suka dawo Saliyo tare da iyayen ta. Maman ta tayi mata jego, har ta warke. Mahaifin ta yayi fushi da ita fushi mai tsanani a kan rashin biyayyar data yi masa na kin zama da Alhaji. Ta hana shi samun makudan kudaden da yake samu a hannun Alhaji Usman. Yace yanzu gashi ta janyo ya raba ta da diyar data haifa kuma babu tabbacin yarinyar zata rayu ko aah, ko zasu sake haduwa, tunda babu wanda zai shayar da ita.
Ni kuma kullum na yi sallah sai na roki Allah ya raya abinda na haifa koda bamu sake ganawa ba, yasa rayayye ne kuma ya amfani musulunci da alumma.
Daga baya bayan wasu watanni, Luqman tsohon saurayi na dana ke so ya dawo neman aure na. Da kyar na samu mahaifi na ya yafe mini, yace Yaya ta Aisata tayi mishi biyayyar da ni ban yi mishi ba, don ita kam sayar da ita ma yayi a Nijar ga wanda bai ko sani ba, don haka kada in taba tsammanin zai barni in zauna a gidan sa, in kawo miji kawai talakan dana ke so yayi min aure ya huta.
To dama ni da Luqman mun dade tare kuma a kan sa ne naki zama da Alhaji Usman, da kuma nasa halayen wadanda na san ba sai na fada miki ba, tunda baban ki ne ya kamata ace kema kin san su.
Muka yi auren kauna da soyayya ni da Luqman, wanda shine mahaifin su Fajur, maaikacin kamfanin Tama da karafa ne (Steel Rolling Company), wannan gidan, shine gidan da muka rayu a cikin sa tsayin shekaru goma sha tara ni da Luqman, cikin rayuwar aure ta soyayya da fahimtar juna wadda mahaifin ki bai iya ko daya ba, shi dai ya yarda kudin sa ne zai samo masa duk irin matar da yake so a duniya.
Shekara na zagayowa na haifi Safwan, sai bayan shekaru biyar da haihuwar sa har mun fidda rai sannan daga baya na haifi Fajur, a shekaru ukun baya ne Allah yayi masa rasuwa bayan gajeruwar rashin lafiya.
Iyayen mu kuwa sun jima basa raye, Aisata ya sayar da ita a kasar Nijar ko zuwa Saliyo bata kara yi ba tun karbar ta da aka yi aka tafi da ita aka bashi Rakuma masu yawa, wato shi mahaifin namu a matsayin sadakin ta, lokacin rasuwar mahaifin namu ne ban san ya akayi ta samu labari ba ta aiko min wasika ta taaziyya ta gaya min watarana zata aiko a kaini inda take aure a Nijar, kuma tun daga wannan lokacin ne ta soma yi min aiken kudi lokaci-lokaci duk da bana cikin bukatar komai, ina tare da miji na cikin kwanciyar hankali da rufin asiri lokacin, bayan rasuwar Baban su Fajur na aika mata ta hanyar dan aiken da ke kawo wasika a tsakanin mu wanda dan kasar nan ne mai kasuwancin Rakuma a Nijar, shine fa ta bude min asusu, wanda kai tsaye duk wata take turomin kudade na Saifa masu kauri, wadanda da su ne na cigaba da daukar nauyin karatun yaran nan, muke kuma cin abinci, na kuma soma sanaar kiwo, ga abinda mahaifin su ya mutu ya bar mana muna juyawa a gona, muna samun amfani daga noma da kiwon kaji da kiwon shanu. A takaice kin ji wannan itace rayuwar da muke yi a halin yanzu. Safwan yana rubuta jarrabawar kammala sakandire yanzu a nan makwabtan mu wato Gambia, ya zo hutu ne, Fajur tana karatu anan wata karamar sakandire ta kudi a bayan gidan nan, kullum da kanta take zuwa ta dawo ta huta ta wuce Islamiyya.
**** **** ****
MOTHERHOOD
Z
uwa washegarin ranar, hatta makwabtan Jalan bakidaya sun san da zuwan yar ta dake Najeriya aka shigo ana yi mata barka, wasu na aiko abinciccikan kwadayi wa Amani, kasancewar Jalan ta mutane ce mai yawan kyauta da kyautatawa ga makwabtan ta, anata mamakin kamannin su ita da Amani in ka dauke cewa Jalan mai jiki ce Amani siririya. Duk abokan arzikin iyayen su dake raye sai da ta kai Amani a washegari suka gan ta. Basu dawo gidan ba sai da yamma lis.
Shima Mukhatr baya gidan tun safe Faytoory ya zo ya dauke shi, sun shiga gari yana nuna masa wurare masu tsohon tarihi na Kenema, da inda ake Mining din Diamond. Daga can suka wuce gidan Faytoory suka ci abinci da iyalin sa sai lokacin suka dawo gidan su Amani.
Faytoory ya ajiye Mukhtar kenan suna sallama da cewa gobe in sha Allah da wuri zai zo ya tafi dashi Freetown, inda daga can zai hau jirgin Lagos.
Mama Jalan ta aiko Safwan ya kira shi su ci abincin dare yadda suke yi kullum, a lokacin yana hada kayan sa a jaka yana tunanin tunda su ka zo rabon sa da kebewa da Amani ko da da sunan su gaisa, wato ya gama mata amfanin da zai mata, tunda ta dafe uwar ta a gefen ta shikenan. Sai ya shiga tambayar kan sa na me zai yi wannan tunanin ma? Amani ce fa! Wadda ya sani ba tun yanzu ba. Ai ya dade da sanin Amani ba yar goyo bace shakiyya ce ya sani dama, kuma ta fada ta kara haduwar su ta kan hanya ce da zarar ta ga uwar ta babu ita babu shi.
Ya tuna cin mutuncin data yi masa sa Freetown da zagin fitar hankali na sheganta shi, sai ya ji zuciyar sa na kara tafarfasa, Amani na kara fita a ran sa. Amma mutuncin iyayen ta a zuciyar sa na kara ninkuwa.
A ladabce Safwan ya shigo ya gaida shi, sannan ya gaya masa sakon Mamma na ya fito su ci dinner tare.
Ba tare da ya dago ya dubi yaron ba don baya so ya ga idanun sa, a dai yanayin da suke ciki yanzu na tsananin bacin ran Amani. Ya ce ya je ya gayawa Mamma cewa a koshe yake, ya ci abinci a gidan Faytoory kuma yana so zai shigo yayi mata sallama don gobe in sha Allah zai koma Katsina.
Safwan ya je ya dawo ya ce Mamma ta ce ya shigo, a gaskiya a lokacin baya son shiga cikin gidan a yanayin da fuskar sa ta koma yanzu, wato boyayyen yanayin nan nasa da ba kowa ya san yana da shi ba ya bayyana, domin baya so Hajiya Jalan ta ga hidden side din sa na rashin walwalar nan. Gashi idan ya zo baya iya controlling din sa har sai ya bace don kan sa.
Sannan haka kawai yake jin muryar Mamma Jalan da accent din ta kamar yadda yake jin tashin muryar Ummami, wanda hakan ke kara tono bacin ran dake kasan zuciyar sa na kewar Ummami da jin zafin ta (as well), yana kara bayyana a kan fuskar sa.
Ba yadda ya iya dole bayan yayi wanka ya canza kayan jikin sa zuwa farar jallabiyya kal kirar Dammam, ya yi sallah a masallacin kofar gidan sannan ya shiga cikin gidan da karamar tazbaha mai kyau a hannun sa. Nan ya gan su complete family a kan teburin cin abinci abin gwanin ban shaawa. Amani ta sha ado da laffaya koriya sharr da irin matsatsiyar rigar nan ta roba mai dogon hannu daga cikin laffayar light green itama. An yi mata wai irin setting din gashi wanda ya zubo a saman goshin ta ya zarce har bayan kunnen ta. Bakin nan sai shining yake da Elizabeth Arden Lip gloss kamar ka sace ta ka gudu (looking takeaway), idon nan nata mai kama da kwan zabo ya sha mascara gashin idon ya fito gazar-gazar.
Rabon ta da yin ado irin wannnan bazata iya tunawa ba. Sai ko yanzu da take jin kanta a daidai wato bata da damuwar komai, tunda rayuwa ta koma mata daidai, ga ta ga uwar ta a duniya, ga kanne, sosai take cikin nishadi, barin ma data ji Safwan ya zo ya fadi sakon Mukhy na cewa gobe zai koma Katsina.
Ai kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, yi ta yi kamar ta tashi ta ka rawa, murnar tata har kasa boyuwa ta yi sai da Mamma ta gane bakin ta ya ki rufuwa don Mukhy ya ce gobe zai koma ya bar ta a nan. A cikin zuciyar ta Jalan tana mamaki, ko meye aibun Mukhtar haka da matar sa ta kasa son sa? Mutum son kowa da shi a halitta da dabia, abun alfaharin kowacce mace wajen kamun kai da kamewa da girmama iyayen ta, amma Amani na neman maraba da shi irin haka bata ko jin zata yi kewar sa don ko a waya bata ga sun gaisa ba balle text din soyayya. Kwata-kwata ta gama lura Mukhy baya ran ta, kamar kishin sa take akan Baban ta kamar kuma zuciyar ta bata taba kimsa mata soyayya a kan sa ba.
Ta riga ta dauke shi rival a zuciyar ta, ko kuwa wani wanda ya tare mata gaba ya hanata rawar gaban hantsi. Sai Jalan ta shiga tambayar kan ta ko yar tata bata da lafiya ne irin ta yaya mata ko kuma tana da shafar jinnu. Ta lura bayan dolonci, rashin kunya, rashin ilmin addini, rashin cikakkiyar tarbiyya har da rashin sanin muhimmancin da Allah ya baiwa miji a kan ta, da rashin sanin hakkin aure.
Kada dai tarihi ne yake maimaita kan sa, tunda itama abunda ta yiwa Uban ta Alh. Usman kenan, kusan tsayin shekaru biyu tana wahalar da shi a dalilin bata son sa.
Tunda ya aure ta sau daya ya taba samun saar ta, shima ta karfi, wanda daga baya ta gane rabon Amani ne ya rantse.
Tana kuma lura da cewa tunda suka zo Amani bata je inda yake ba, bata kara bi ta kan sa ba, bata kara yin zancen sa ko kula da alamarin sa ba a matsayin su na sabon aure, balle ta damu da sanin halin da yake ciki a masaukin nasa, ko ta tambaya an kai masa abinci ko aah? Don in an kira shi ya ci ma baya zuwa.
Sai ta ji tausayin Mukhy mai tsanani da kaunar sa kamar dan cikin ta ya kamata, bata san dalili ba amma jin sa tayi ya kwanta a ranta kamar dan ta Safwan, ba banbanci, don in ba kuskure idanun ta suka yi mata ba ita ta hango kwantacciyar soyayyar Amani maras misaltuwa a can kasan kasaitattun idanun sa masu sheki da sparkling a duk sanda ya juya su a kan Amani. Ita a wurin ta Alhaji Usman ya kware shi, da ya hada shi da auren Amani, hakika ya so kan sa, domin Mukhy data ke faman kira yaron Baban ta ita sai taga ajin sa da kasaitar sa sun dame na Amani.
Gashi ya san irin tarbiyyar da yayi