Showing 36001 words to 37455 words out of 37455 words

Chapter 13 - Amani Book 2 Hausa Novel Complete

Takori   

13 Dec 2024

223

Na fito daga yankin Diffa. Diffa din wani babban birni ne da ke kudu maso gabashin jamhuriyyar Nijar. Garin na da iyaka da tarayyar Najeriya daga kudu maso gabashin kasar.
Birnin Diffa ya samu asali tun a lokacin daular Borno (Kanem-Bornu Empire). Wato tun lokacin 1900. Asalin mutanen da suka yi rayuwa a cikin ta a lokacin Kanurai ne (ko kuma Barebari). Amma yanzu Diffa ta hada kabilu guda uku; Larabawan Diffa wadanda ake kira (Diffa Arabs), Buzaye da kuma Tubawa, duka suna cakuduwa suna rayuwa a cikin ta.
Diffa tana nesa da kimanin kilomita 1360 daga babban birni Niamey.
Iyayen mahaifi na sune asalin kabilar Diffa Arabs, watau Tubawa ne, yaya ga Sultan Oumarou Mai Diffa, wadanda tarihi ya nuna kakannin su, su suka kafa daular Diffa Arab. Mohammed Bazoum kan sa, wato shugaban kasar mu na yanzu dan asalin Diffa ne daga kabilar mu ta Diffa Arabs.
Sai Mukhtar yayi murmushi ya dubi Daddy, Alhaji iya labarin da zan iya baku kenan a kan inda na fito, maganar iyaye na ko abinda ya fiddo ni daga gida sai mun je gaban Ummami da mahaifi na Sultan Issoufou Massaoudou, a yanzu dana yi hankali na ga ya dace nayi exposing ciwon zuciya ta gare su, su san halin dana rayu ciki a kan su, maimakon in yi ta rike shi a kasan rai na ina fama da shi tun daga kuruciya ta har girma na.
Alhalin su basu san ina da shi a kasan rai na ba. Ko sun sani, ban taba tattauna shi da su ba.
Na dade ina fama da wani dabaibayi mai fizgata ga nesanta da gida, kullum dabaibayin nan cewa yake dani in kara nesanta kai na da Diffa, ta hakan ne kawai zan samu nutsuwa da kwanciyar hakali, idan ba haka bazan taba zama cikin nutsuwa ba.
Rana daya tun zuwan mu Saliyo na tashi na nemi wannan dabaibayin a tare da ni na rasa, na nemi fargabar da ke mamayata idan na tuna Diffa na rasa, na ji komai ya yaye daga cikin kaina duhun da ke zuciya ta ya koma haske.
Wannan alamari ya faru da ni a wannan tafiyar da muka yi zuwa Saliyo, tun daga lokacin hankali na ya koma gida da son ganin iyaye na, kuma jin zafin su da ke raina na samu yana decreasing gradually (raguwa a hankali), a halin yanzu ina iya yi musu uzurin da a baya bana iya yi musu, ina shaukin ganin su, sannan a shirye nake ga fuskantar abinda a baya nake tsoron fuskanta a gida, komai tsaurin sa.
Na shirya komawa gida a halin yanzu. Hakika Alhaji yanzu na shirya ko ba don Amani ba zan koma gida. Lokacin tafiya ta gun Ummami yayi. Ina jin kaina a zan iya fuskantar kowanne irin kalubale da zai iya tunkaro ni with a very big and brave heart, wadda a baya ban mallaka ba, na rasa farin ciki tun ina yaro, na kasance cikin kadaicin rayuwa wato solitude mai sakawa dan adam inferiority complex, a dalilin iyaye na basu yi min abinda nake so ba.
Alhaji na karbi auren da ka bani da hannu bibbiyu, banida bakin da zan godewa kyautatawar ka gare ni, da rikon da kayi min, na karbi Amani zan tafi da ita cikin ahali na duk da ikirarin ta na rashin son auren mu, ni na karba na kuma gode. Na kuma yi alkawarin rike ta da amana har karshen numfashi na.
Alhaji sai ya saki hamdalah yana fadin, na gode Mukhtar na gode Allah ya yi maka albarka, Im the one to thank you for changing my life positively, tunda ka zo gare ni rayuwa ta ta canza, albarka ta lullube rayuwa ta, dukiya ta ta rubanya ta yi albarka yadda ban taba zato ba, don haka nine da godiya na kuma yarda duk lalacewar da duniya tayi, har yanzu akwai masu mutane masu amana akwai kuma mutanen kirki, kai dai kayi wa dan kowa alkhairi ba sai naka kadai ba. Baka san wanne zaka ci amfanin sa ba. Kuma baka san wanne ne zai ji kan ka ba.
Sai ka shirya mana motocin da ya dace muyi tafiyar a ciki, wadanda basa makalewa a cikin sahara. Ya ce ai Alhaji a Land-Cruiser din ka kawai zamu tafi, tana da tsaho da fadi, a kalla zata dauke mu nida kai, Mamma da Baba Idi da Baba Sahura, da ita wannan. Ya nuna Amani da baki.
Amani ta galla masa harara ta murguda baki cikin takaici, wai ita yake cewa ita wannan, alhalin ya lissafa sunan kowa, wato ita bata kai matsayin da zai fadi sunan ta ba, irin wannan rashin darajawar da yake mata shi yake sawa take kara tsanar sa, tunda gashi ya kara fadi a gaban iyayen ta da ita kanta cewa ya gode da sadakar ta da Alhaji ya bashi.
Hawaye ya surnano daga idon Amani Faskari, yau ita ce zata koma rayuwa a kauyen Nijar! Wata alkarya da ko sunan ta bata taba ji ba, wai Diffa. Da sunan aure a inda bata da kowa. Mafarkin ta na tafiya yin masters a jamiar QUEEN MARY UNIVERSITY OF LONDON ya zama tarihi! Ya bi ruwa! Ta zama cikin Diffa Arabs, makiyayan daji da bata san ko yaya aladu da dabiun su yake ba.
Sai gani aka yi Amani tana rafzar kuka, ita ba abun tace bazata ba, ta san ba mai bin bayan ta, Mukhtar bayan saye Ubanta da mugun sumumu-kasau din sa, Uwar ta ma ya saye yanzu, sai abinda ya ce. Shi kadai ne mutum a idanun su.
Ta yi magana yanzu Mamma ta kumbura mata baki, tunda kuma a kusa da ita take zaune.
Mukhtar ya fita yasa Tajuddeen ya fido Land Cruiser din Alhaji ya ce a kai ta service a kuma yi mata full tank, gobe asubanci zasu yi zuwa kasar sa. Kuma shi da kan sa zai tuka motar.

Tajudden tun a lokacin ya soma kewar Mukhy, wani kwayan mutum guda daya wanda ya zame masa tamkar dan uwa a gidan Alh. Usman Faskari, ba irin alkhairin da baya yi masa. Ya yi wa Mukhtar fatan alkhairi, yana hawaye, tare da rokon sa ya dinga zuwa suna ganin sa lokaci-lokaci. Ko albarkacin Amani da zai dinga kawowa ganin gida.
Haka yai ta sallama da duk maaikatan gidan. A daren kowa ya hada kayan da zai tafi da su banda Amani, sai Mamma ce ta zo ta hada mata da kan ta. Kwana ta yi akan kujera tana kuka, kafin asubah bayan ta ya rike, wuyanta ya kage, kuma a haka suka ce bazasu jira ta ta yi wanka ba ta yi sallah kawai su kama hanya, don already Mukhy (wanda yau wata irin shiga yayi, ta asalin ainahin larabawan Diffa), in ba har ka yi masa farin sani ba bazaka gane shi ba, ya shirya tsaf cikin kayan kasar shi a jikin shi wato traditional attire na Diffa Arabs ya fito a ainahin kamannin sa na Tubawa ko kuwa larabawan Diffa). Kasancewar duku-duku ne cikin su babu wanda ya ga irin shigar da Mukhy yayi, musamman da yana cikin mota ne a zaune, ya tada mota ya bata wuta a waje, su kawai yake jira su fito.
Mamma duk zafin ta sai da tausayin Amani ya kamata ta hada da lallashi, ta kuma yi mata alkawarin zata kawo mata Fajur daga baya in ta gama makaranta, kuma zata bar Baba Sahura ta zauna da ita har sai ta saba da mutanen data tarar, kuma zata nemi Yayar ta dake Nijar ta hada su. Wannan ne ya dan sanyayawa Amani, amma in ta tuna ta bar comfort zone din ta kenan zuwa wani kololuwar kauyen Nijar bata sanin sanda take sake rushewa da kuka, tana laantar Mukhtar da kaddarar data yi sanadin zuwan sa gidan su.
**** **** ****

MU BIYO JARUMAR TAMU AMINA-AMANI, UWAR BABA IDI, SANNAN TAFISU YAR GIDAN BABAN TA… ZUWA YANKIN DIFFA A LITTAFI NA UKU DON GANIN YADDA ZATA KAYA TSAKANIN TA DA MIJIN TA MUKHY’ DAN KABILAR LARABAWAN DIFFA.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login