Showing 6001 words to 9000 words out of 37455 words

Chapter 3 - Amani Book 2 Hausa Novel Complete

Takori   

13 Dec 2024

214

da kamfani. Kamilu ne kawai zai zauna da su saboda kula da Alhaji da tafiyar da Mukhy zai yi wadda shi kan sa bai san tsayin kwanaki nawa zata dauke su ba shi da Amani, idan har ta yarda sun tafi taren kenan. Sai ko Baba Sahura da dake dakin Haj. Rabi. Su kenan a gidan sai Rakiya mai girki. Da maigadi Malam Tajuddeen da sauran maaikatan waje
Sai dai Mukhtar ya san mawuyaci ne duk bacin ran da Amani take ciki, da halin kuncin da ta saka kan ta a ciki na babu gaira babu dalili sai kiyayyar auren sa a ce mata ga ido tace doyi yake. Wato bazata iya tankwabe zuwa gun Innar ta ba, iyakaci in aka je din ta ce ba zata dawo ba, ya riga ya san hakan ce zata faru, kuma ya shiryawa hakan.
Karfe sha biyu na ranar washegari Mukhtar Diffa ya sauka a filin jirgin saman Sir Abubakar Tafawa Balewa. Sanye yake da farar shadda kal Wagambari babbar, ya aza hula zanna bukar a kan sa mai ruwan kasa-kasa ta zauna daram a cikin tarin sumar kan sa, kamar yadda takalmin kafar sa na fata kirar Italy shima ruwan kasar ne, haka fatar agogon rolex da ke daure a damtsen hannun sa na hagu wanda bakin lallausar gashi ya kwanta a hannun itama brown ce. Yana takun sa cikin nutsuwa da haiba yadda ya saba yana tura matsakaiciyar jakar matafiya. Hamidah da kan ta ta tuko motar ta ta zo daukar sa, ta baro Amani ta shiga wanka bayan ta tashi barci ta more ta sau nutsuwa. Ba yadda Hamida bata yi da ita kan ta karya kumallo ba amma Amani ta ki, ta ce daga ranar yau ta daina cin komai, ta daina shan komai, ta fi son yunwa ta yi mata illar da har har sai ta mutu, in ya so Hamidah ta kai wa Mukhtar da Alhaji gawar ta, tunda Hamidan ta ce abinda suka yi mata din ba laifi bane, kauna ce.
Hamida sai ta kada kai ta fita tana dan murmushi.
Har falon Haj. Muna Hamida ta yi wa Mukhtar iso, ta gaya mata angon Amani kenan. Jiya aka daura auren, shine Amani ta taho basu sani ba. Yanzu Daddy ya ce Mukhtar ya zo ya tafi da ita zasu wuce wajen Maman ta a Freetown.
Haj. Muna tace ikon Allah, masha Allah tabarakarrahman, dalilin tahowar ta a motar haya babu sanin ku ranar daurin auren ta nake son sani, ko bata son auren ne da wannan miji sardidi haka son kowa?
Kunya ta kama Mukhtar ya kara dukar da kai kasa. Shi kansa yasan Allah ya kyautata halittar sa ko mutane basu fad aba, amma baya so ana fada sai yaji wani iri, Hajiya ta cigaba da fada tana cewa.
Da sabon aure haka a kan ta tayi wannan kasassabar, tahowa har Bauchi babu iznin mijin ko na Baban ta? Maza kirawo min Amanin, in wanke ta tatas, haka ta zo tana langabe min jiya kamar mutuniyar kirkin da ke cikin matsala, ashe ashe gudun nata na aure ne.
Hamida da Mukhtar babu wanda ya tanka, amma sun ji dadi da Hajiya zata wanke musu Amani wankin babban bargo, illa yayi kasa da kan sa da ke duke yana danna wayar hannun sa. Zaune yake bisa kilishi kafafun sa a tankwashe, yana fuskantar Haj. Muna, wadda ke kan kujera tana masa nasihar yayi hakuri da Amani irin hakurin da zai yi da kanwar sa, kasancewar bata tashi tare da mahaifiya ba wani abun sai ana mata uzurin sa. Don dabiun ta ba irin na wadanda suka tashi da uwa da dangi bane. Goyon namiji ce.
Shi kam Mukhtar har ya gaji da cewa da ake yayi hakuri da Amani, wai wane irin hakuri? Ita tafi kowa shafuwa da mai ko yaya ne? A wurin sa ai saidai duk su yi hakuri da juna don shima ba kanwar lasa bane, in ta so a zauna lafiya a zauna, in ta zabi tsiya a tsiyace, shi duk wanda ta zaba daidai ne a gun sa. Babu diya macen da zata daga masa hankali, don in dubu yake so a rana zai samu, bai yi raayi bane. Koko ya ce lokaci bai zo ba.
Amani yana jin ta da matsayi na dabam ne saboda karamcin mahaifin ta gareshi da irin kauna da yardar da ya yi masa, da tausayin halin da yake ciki na rashin lafiya, sannan kuma yana da son rama alkhairi da alkhairi.
Ba don haka ba Amani ta yi kadan ta wahalar da shi irin haka, ko ta saka shi yawon da bai shirya ba irin haka, yana bin ta gari-gari kamar wani jelan ta.
Yana cikin wannan mitar a ran sa ya ji kamshin turaren Amani a falon.
Ko kusa bata kawo a ran ta wanda ke duke gaban Haj. Muna Mukhtar ne ba, ta ina ma zata yi tunanin ya san inda take? Ko ya sani tunanin ta bai taba bata zai iya ajiye girman kan sa ya biyo ta har nan ba, balle kuma tayi tunanin Balewa zata iya tona mata asiri ta fadawa Mukhy tana gidan su a Bauchi.
Har ta zauna a kujerar da ke fuskantar Hajiya bata gane Mukhtar ba, sabida keyar sa ce kawai a duke, duk da hasken fatar sa daban ne dana mutane da ke saurin fallasa shi hankalin ta bai kai kan sa ba, watakila kuma don bata taba kawowa ran ta ganin nasa anan bane.
Mukhtar ya dago fusatattun idanun sa ya dubi Amani da su a lokacin da take zama a kujerar kusa da shi, bayan ga Hajiyar ma na kan kujera, wato rashin tarbiyyar nata a koina ma yin sa take yi har a bakon wuri, tunda dai gashi tana ganin daga shi har Hamida sun zauna a kan carpet Haj. Ce kadai a kan kujera amma ta dare kan kujera tana fuskantar Haj. Muna.
Haj. Gani, Balewa tace kina kira na.
Haj. Muna ta jefa mata harara sannan ta dunkule hannu ta mika mata ta ce ungo naki (dakuwa) sannan ta nuna mata Mukhy da ke zaune yana hararar ta shima wata irin sassanyar harara.
Ga mai kiran naki nan, ba ni bace, dauko mayafin ki kafin in kyafta ido na, sawun ki a likkafa ki bi shi duk inda ya sanya kafa bisa umarnin mahaifin ki, ina maki kallon mai wayo ashe Amani sakarai ce ke? Ki sa kafa ki taho ke kadai tun daga Faskari ba da iznin mijin ki da sanin mahaifin ki ba? Shin kina son albarka Amani ko kuwa kin fi mahaifin ki sanin abinda yake daidai a gare ki?
Sai a lokacin Amani ta gane Mukhtar ne, da kuma ainahin fadan da Hajiya ke yi. A firgice ta juya ta kalle shi suka kuma hada ido, saura kadan fitsari ya kwace mata da irin zazzafan kallon da Mukhtar ke mata. Hankalin ta in ya yi dubu to ya tashi tsaye, nan take ta hau yi wa Haj. Kuka mara sauti tana fadin Hajiya ki yi hakuri ni ba zan koma Katsina ba, idan kin kore ni ma gaba zan nausa Hajiya tace ki wuce birnin Sin, amma tare da mijin ki ba da ni ba, maza Hamidah dauko mata kayan ta kisa a bude musu guest house yanzu, su kwana gobe sai su yi sammako tunda dare ya riga yayi yanzu.
Amani ta wuce dakin Hamida tana kuka wiwi tana tattara kayan ta. Hamidah ta shigo dakin tana fadin da gaske Sahibah ba wanda ya isa ya gaya miki ki ji? Na dauka Hajiya ta matsayin uwa take a gare ki, ta dauka zata yi miki fada ki ji ko ba kya so, tunda tace ki bi shi sai ki bi shi, baki san alherin da ya zo miki da shi ba.
Nan ta gaya mata cewa Mukhtar ya zo ne don ya kai ta Sierra Leone.
Amani tayi tsit! Kamar ruwa ya cinye ta, jikin ta yayi dan sanyi, da gaske yake ko kuwa yaudara ce don ta yarda ta bi shin? Me ya hana tun lokacin da yayi mata alkawarin ya cika? Sai yanzu da ta zama matar sa da bata da iko da kan ta?
Hamida ta shiga lallashin ta, tana cewa ki bashi dama Sahibah, hes a very serious person babu batun wasa a abinda ya gayawa Mama, da gaske Sierra Leone zai kai ki.
Amani ta rage kukan ta ce Hamida, idan da amana bazaki gaya masa inda nake ba, daga yau na san ajin da zan ajiye ki, ya kamata tuntuni in fahimci kema kina yin mutumin nan, in ba ke ba babu wanda zai gaya masa inda nake.
Hamida ta soma kokarin kare kan ta da cewa wallahi tausayi Daddyn ki ke bani Amani..bashi da lafiya kuma yana cikin damuwar inda kika shiga ni bana baki tausayi ko? Ni da a ka yi wa auren dole da wannan green snake din? Hamida ta ce wato sunayen nasa kala-kala ne har haka, shine Dirty Human Being yanzu kuma shi ne Green Snake, sannan Sumumu-kasau, duk shi kadai bawan Allah!
Tsaki Amani tayi tace in dai Bauchi ce yau zan bar miki kayan ku, zan shiga duniya tunda hakan kike so, ba zaki bani refuge daga auren dole ba. Hamida ta yi murmushi tace don Allah Mama ta ce in kin tashi shiga duniyar ki wuce har bangon ta (birnin Sin).
Suna wannan cece-kuce din Hajiya Muna ta shigo dakin, don ta ga Amani ta bi umarnin ta ko aah, mai aikin ta biye da ita dauke da fakadeden tray da ake jera abinci da abin sha a kai, ta ce,
Amani ga nan abinci dauki ki kai masa da kan ki, Hamida ki raka ta masaukin bakin, na sa Ali ya raka shi tun dazu.
Hamida ta ce da mai aikin ta wuce gaba ta kai masa abincin zasu zo yanzu. Ta dauka Amani zata bi umarnin Hajiyar ta, amma ga mamakin ta Hajiya na bada baya Amani ta yi rantsuwa ba inda zata je, in kuma Hamida ta takura mata sai ta fita to kuwa ta fita kenan har abada itada sake zuwa inda Hamida take.
Hamida ta dauka wasa take yi, amma sai ta ga ta rantse ta kara rantsewa kan cewa bazata kwana inda Mukhtar yake ba, har ta ce saboda daurewa karya gindi sai ki sauke shi a gidan nan? Koda yake dama ai ke kika gayyato shi, don haka sai ki karasa ladan ki ki kai masa abinci. Ki kuma kwana kina taya shi hira.
Hamida ta rasa yadda zata yi da Amani, ta tabbata wajen taurin kai da kafiya babu na biyun ta duk fadin garin su Faskari tabbas ta Faskari kowa, sannan a tarbiyyar da aka yi mata baa koya mata bin umarnin na gaba ba, sai dai ita tayi wa wani umarnin.
Hamida zata soma yi mata waazi ta mike ta hau hada kayan ta ta soma kuka a haukace, fadi take in dai don na zabi yin mafaka a wajen ki ne kika tona min asiri haka bari in tafi gidan karuwai cikin daren nan, in kika takura sai na je inda yake.
Hamida ta rike jakar kayan nata ta ce na kyale ki Amani, ba zan kara takura ki zuwa guest house ba, amma kin manta ya ce wajen Maman ki ya zo ya kai ki? Ta ce don wannan na yarda zan bi shi, ai zaman jirgi ne kuma babu transit, daga nan Bauchi kai tsaye a hau jirgin da zai je Freetown, inba haka ba na hakura, wallahi bana ko son ganinsa Hamida. Hamida ta hadiye dariya, ta soma mayar mata da kayan da take kwasowa cikin jakar ta, tace kada ki manta hausawa dai sun ce komai wayon amarya.?!.
Hararar da Amani tayi mata kamar idanunta zasu fado kasa tasa ta ficewa daga dakin da sauri tana cigaba da tillika dariya. Masaukin Mukhtar din ta nufa, so take ta ji yaya tafiyar tasu zata kasance goben, tunda ta gane transit ne Amani bata so a yi a koina, bata kuma jin akwai jirgin Freetown daga Bauchi dole sai daga manyan birane wato Abuja ko Lagos.
Hamidah tayi sallama a kofar guest room, daga ciki Mukhy ya amsa, bai kuma taso ya bude ba amma don ya ji muryar Hamida ne, a hankali ta ce Hamida ce, zan iya shigowa? Sannan ne ya taso ya bude, kallo daya Hamida tayi masa cikin kayan barci na DKNY ta ji zuciyar ta ta tsinke, sannnan ta doka da karfi, a zuciyar ta ta shiga neman tsari daga sharrin zuciya dana shaidan masu gaya mata tace da shi, ya kyale Amanin da ta tabbatar bata kaunar sa ita ya zo gare ta. Ta yi maza ta yi taawizi ta nemi tsarin Allah daga sharrin zuciya dana cin amana, ta bi bayan Mukhtar zuwa cikin falo, suka zauna a kujerun da ke fuskantar juna a falon, har ya yi wanka ya canza shaddar jikin sa zuwa shirt da wando marasa kauri blue samfurin DKNY. Yana shirin taje sumar nan tasa da ta jike jagab da ruwa ta mammanne a saman fatar wuyan sa, da alama bai kai ga taje ta ba, fitowar sa kenan daga wanka Hamida ta kwankwasa masa kofar.
Kamshin kakkarfan turaren sa na Azzaro Visit da ya fesa yanzu-yanzu, ya mamaye dakin, ya cakude da sanyin air conditioner ya bada wani atmosphere mai dadi a falon da sanyaya zuciyar duk wanda ya shake shi.
Hamida ta russuna ta gaida Mukhy with much respect, kwarjinin sa na kara rikita nutsuwar da ta shigo da ita. Shikuwa ya kara daure fuskar nan tamau kamar yadda take as usual. Duk sai ta kara firgicewa, ga kwarjinin sa ya mamaye dakin. Yarinyar bata yi kama da masu kawo shirme ba amma me zata gaya masa da zata biyo shi har inda suka sauke shi a irin wannan lokacin?
Da karfin sunan Allah a bakin ta Hamida ta samu nutsuwa ta ture duk abubuwan da shaidan ke kissima mata, ta ce.
By the way, ni ce Hamidah Balewa, ni kawar ta ce tun muna secondary school.
Mukhtar yace I can relate, tunda har zata iya gudowa wajen ki har nan tun daga Faskari ba da izni na ko na Alhaji ba. Ya fada da dan fusata a muryar sa, na ganin ta ita kadai ba tare da Amani ba, wanda kai tsaye ba sai an gaya masa ba ya gane bazata zo su yi magana akan tafiyar su ta gobe ba.
Hamidah ta karya murya tana fadin, ka yi hakuri Mr. Mukhtar, Amani sai a hankali, ina so in san tsarin tafiyar taku ne ta goben in mata bayani, don nayi kokari mu taho tare yanzu ta ki.
Da fusata sosai ya ce then bani da say da ita, in har bazata zo da kan ta ba, in baza ta je bama ni zan koma Katsina gobe, amma ki tabbatar mata kafata kafar ta, bisa umarnnin Alhaji.
Hamida ta ce in sha Allahu ma zata je, ai tafi kowa son ganin Maman nata. Mukhtar yace matsalar ku ce wannan, zuwan ko rashin sa, bani da asara a ciki, ki dai gaya mata in bazata je Sierra Leone din ba ta sanar da ni a daren yau ta waya, don in saki booking din, in kuma zata je shima ina son sani don in san ina muka nufa goben daga nan. Ta bani amsa ta waya ya wadatar.
Zan jirata har karfe tara na safe, don booking din mu zuwa Lagos 12 na rana ne, daga can ne zamu hau jirgin Freetown, babu jirgi mai zuwa Sierra Leone anan Bauchi.
Hamida ta ce a ranta transit dole Sahibah! Allah ya fishsheki daga fushin wannan Zakin.

Ta dawo dakin su shi kuma ya rufe masaukin nasa ya kwanta. Ya dauki wayar sa ya kira Alhaji, Kamilu ne ya dauka suka gaisa ya tambaye shi ya hanya, ya gaya masa ya isa lafiya, sannan ya hada shi da Alhajin, ya gaya masa ya sauka a Bauchi lafiya, kawar tata Hamidah da iyayen ta mutanen kirki ne, don a gidan su ma suka bashi masauki, sun roke shi kada ya sauka a hotel.
Alhaji ya ce ai tuntuni na san Hamida mutuniyar kirki ce ba irin Tafisu ba, shi yasa na ke son abotar tasu, da mutum yana shirya mutum da tuni Hamida ta gyara min halin Amani, to abotar tasu ba irin wadda ake kira ta abokin barawo- barawo bace.
Sun dade suna tattaunawa, Mukhtar ya gayawa Alhaji dole sai sun kwana a Lagos kafin washegari da asubah su bi jirgin Freetown. Alhaji yace ta dai yarda zata je din ko? Mukhtar ya nisa, kafin a hankali ya ce Alhaji maganar yarda ta je ko rashin yardar ta duk basu taso ba, abu ne dana sani ba abinda take so kuma take buri a yanzu sama da ganin Innar tata, don haka zata bi ni ne ko bata so, donmai binciken nata dan damfara ne kawai, alkawari ne na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login