Showing 15001 words to 18000 words out of 37455 words
a ce ita yake gayawa, ta san dai tsakanin su babu ragayya, amma bata san akwai sabo irin wannan ba ba da har zai iya furta mata wadannan maganganu masu nauyi haka, ko kuwa su maza daga ranar da aka daura musu aure shikenan kunyar su da bakunta ga diya mace ya tafi shikenan?
Amani ta tambayi kan ta, amma bata iya ta baiwa kan ta amsa ba, sabida kallon da Mukhy ke mata
A rude ta zauna ta hau jefa loma bayan loma bayan wata hararar bakin ciki da ta zabga masa, sai ta cigaba da jefa lomar tuwon dawa babu kakkautawa, bata ma bi ta kan sakwarar da ya ce ya yarda su yi musanye ba, ba don komai ba sai don yadda maganganun nasa suka kidima ta suka gigita ta, suka rikita ta duk a lokaci guda, don bata taba zaton su daga bakin mutum kamamme irin Mukhtar ba.
Duk da a yawan shekarun ta ta san cewa shaani na aure ya fi gaban nan. Sannan babu babba babu yaro when it comes to marital affair. Amma bata taba zaton Mukhtar zai iya furta mata su ba, in aka yi laakari da irin personality din sa na kamewa, fadin rai, girman kai da rike girma, da yadda ta dauka cewa kwatakwata ya tsaneta ba ya son ta. Ba ta yi tunanin zai taba wannan hasashen na samuwar yaya a tsakanin su ba, wanda ke nufin yana hasaso physical relationship (bodily contact) watarana a tsakanin su.
Gara ta cinye tuwon dawa komai yawan sa a kan dai Mukhy ya kara yi mata wannan sabon da kunnen ta ba zai iya jure ji ba, sabida nauyin da maganar ta yi mata a kwanya, don ji ta yi tamkar Mukhtar yayi babban sabo, yo sabo mana! Tana kara maimaitawa a zuciyar ta .... kada Allah ya nuna mata wannan ranar da yake hasashen zuwan ta!
Sai da ya tabbatar ta cinye tuwon sannan ya kyale ta, kuma ya yi mamakin ganin yadda ta cinye shi kamar kiftawar ido, bai san tsabar rudewar da kalaman sa suka saka ta bane yasa ta cinyewa cikin rashin sani, ya mike ya wanko hannun sa sannan ya fita zuwa reception don ya yi waya da Alhaji, yayi wayar wajen tsayin awa guda kafin ya dawo dakin, nan ya ga Amani a kan doguwar kujera tayi wata irin takurarriyar kwanciya, ta kuma kankame jikin ta cikin rawar dari sabida sanyin air condition da rashin abun rufa. Da kyar in wuyan ta bai rike ba a irin wannan kwanciyar da tayi a kan kujera.
Sai ya kasa wucewa toilet din da ya yi niyya domin ya yi wanka, ya koma uwar dakin ya dauko duvet din sa da filo guda daya, yana gayawa ran sa Amani amana ce ita a hannun sa, da mahaifin ta ya damka masa ba don ba ya so ba, ko don ya gaji da zama da ita ba, sai don aure shine cikar rayuwar diya mace, ya rabu da ita ya bashi ba don ya gaji da ita ba duk irin halin ta, ya bashi ne domin ya cikasa rayuwar ta ta diya mace. Duk abinda ya yi mata dazu yana sane, so yake ta rage masa kaifin baki amma ba shi da wata manufa a kan ta a daren yau, kai daga nan har zuwa wani lokaci mai tsahon da ba zai iya kintatawa ba bai da wata manufa ta dabam a kan ta.
Ya zo ya rufa mata abin rufar, sannan ya soma kokarin saka mata filon a kasan wuyan ta da ta dora a kan masangalin kujera, kayan da ta zo da su ne a jikin ta har zuwa lokacin bata canza su ba, duk kuwa da cewa ta yi wanka, wai don kada Mukhy ya zaci tayi kwalliya saboda shi ya kara raina ta, duk da ta yi wanka amma sai ta mayar da kayan da ta tube. Gashin kan ta baki sidik mai laushi da tsayi ya watsu a kan hannun kujerar da ta tada kan ta.
A hankali Mukhtar ya russuna yana kokarin saka mata filon da ya dauko a kasan wuyan ta, faffadan kirjin sa ya yi mata rumfa, sai ya ji ya kasa dagowa daga sunkuyon, sakamakon wani lallausar kamshi da ya shaka ta cikin gashin kanta, ya kara kusanta hancin sa zuwa daf da gashin kan ta, wanda ke fidda kamshin tsadadden turaren gashi na musamman, Mukhtar ya zama glued a hakan, yana ta shakar kamshin gashin Amani. Wanda hakan ya yi sanadin da wani bakon alamari ya bakunce shi, tun daga yatsar kafar sa ya tafi har zuwa cikin kwakwalwar sa.....
Kamar cikin mafarki Amani ta ji ta shaki sansanyar kamshin turaren maza na Azzaro Visit, wani masculine perfume da kamshin sa ya ratsa ya tafi har cikin ruhin ta, ya kai ziyara hancin Amani da ke barci sadidan a cikin yan dakikai, sai ta muskuta ta gyara kwanciyar, yadda zata ji dadin cigaba da shakowa sosai, don ta dauka cikin mafarki ne. Hakan ya bashi access na ganin kyakkyawar fuskar ta sosai. Mukhtar ya tsura mata ido, yana kallon wannan kyakkyawar halitta ta Ubangiji, sai ya samu zuciyar sa da cewa inama yadda ta ke da kyan nan haka halin ta ma yake da kyau! Babu shakka shi kam da ya gama morewa.
Yana dagowa don barin wurin dan yatsan sa ya sarko silin gahin kan ta, wanda hakan ya sa ta bude lumsassun idanun ta masu cike da barci da gajiya, da tabon busashshen hawayen da ya saka ta, suka sauka a hankali cikin nasa, sai Mukhy ya ji abinda bai taba ji a rayuwar sa ba. Ta mutstsike ido, ta kuma bude shi tangararau, nan ta tabbatar wa kanta da gaske Mukhtar ne sunkuye a saman kan ta tsayin lokacin da bata sani ba. She cant believe it, in aka ce kallon da ya dauki lokaci yana mata ba tareda ta sani ba na soyayya ne ko makamancin ta, to kallon me yake mata haka bayan ya gama ci mata mutunci?
Shi kuma sai kawai ya wuce toilet cikin borin kunya ba tare da yace mata komai ba, don bai so ko kadan ta kama shi cikin wannan yanayin da ya same shi ba.
Jin dumi data yi ne yasa ta duba jikin ta, sai ta ga ashe duvet din gadon ya dauko ya lulluba mata. Ta yi maza ta cire shi daga jikin ta ta ajiye a gefe, in ma wani abun ya saka mata a ciki don ya cutar da ita, to ta Allah ba tashi ba.
Ya shiga toilet ne da niyyar ya dauro alwalla ya fito amma a yanayin da ya samu kan sa ya san wanka ya gama kama shi, kunyar kan sa da haushin kan sa suka taru suka lullube shi, yana wankan a shower yana cewa Amani masifa ce, ko kallon ta mutum ya cika yi wato sai janaba ta kama shi. Da ya fito sai ya kasa hada ido da ita, tana zaune tana tufke kanta da ya warware, anan falon ya shimfida darduma zai fara sallah, sai itama ta tuna bata yi sallar ba, ta mike ta nufi toilet ta dauro alwallah.
Sai kawai ya fasa tada sallahr har sai da ta fito. Ba tare da ya dube ta ba ya ce mu yi jami, yin hakan sunnah ne, sannan ki bi ni muyi nafila za ta yi musu da harare-hararen ta data saba ya ce is an option, not compulsory. Sai kawai ya tada sallar sa ya rabu da ita.
Mukhtar da ya idar da sallah, sai ya zauna a kan kafafun sa yana lazimi, Amani ta tada tata sallahr a gefen sa ita kadai don ta ki yarda ya limance ta, har cewa take a ran ta haka kawai bata san asalin mutum ba zata yarda ya ja ta sallah? Da mayafin ta mai kama da abin tatar koko ta rufa a ka ta tada sallah, ta ki yarda suyi jamin sam, tana sallahr yana observing sallar tata, abin mamaki so many kurakurai a cikin sallar ta, ko zaman tahiya ba daidai ta yi ba.
Data idar sai ya kasa shiru, ya ce Amani haka kike sallah a gurguje? Da wannan mayafin mai kama da abin tatar ko....? Takaici ya hana shi karasawa yayi shiru. Yana so ya ce ta yi masa karatun da ta ke yi a cikin sallar ya ji, sai ya ga cewa ba wannan ne lokacin da ya dace da duk wannan ba. Lallai aiki ne jawur a gaban sa. Yana jiran ta gaida shi, irin gaisuwar kauna da girmamawa da ya san Ummami na yi wa mahaifin sa, a duk lokacin da suka idar da sallahr farillah ita da shi, amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa, sai ma komawa data yi ta kwanta a saman kujerar data tashi, ta dauki wayar ta ta soma shiga yanar gizo, ta ture duvet din da ya rufa mata gefe guda don dai ta nuna masa bata bukatar komai da kowanne taimako da ya fito daga hannun sa.
Mukhtar bai damu ba, jikin ta ko nasa? Amma ya riga ya sanyawa ran sa kin hakuri da rashin gaisuwar nan tata, a zuciyar sa ya ji takaicin wannan rashin tarbiyya nata, ya kuma gane ba karamin aiki ne jawur a gaban sa ba, in ya bar ta a haka me zata koyawa yayan sa?
Murya shake, ya ce ba ki iya gaisuwar bayan idar da sallah ba ko AMINA? Baki san gaida na gaba da ke ba? Baki san muhimmancin yin jami tsakanin mace da miji ba? Baki san yawan ladan da ke cikin hakan ba? Gaisuwa ga miji in an idar da sallah alada ce mai kyau ta iyayen mu da kannin mu.
Amani ta murguda baki ta kauda kai, ta ce a ran ta in Ustazu ya koma sai ya nemo duro, zata bashi kyautar lasifika. Bata san cewa a fili maganar ta fito ba.
Mukhtar ya fusata ya ce haka kika ce? Fine. Abinda ya fi ustazu ma ki kira ni, amma dole ki gyara dabiu da tarbiyyar ki muddin muna tare, ba zan dauki ko dayan su ba, don ba haka na taso na ga ana yi a gidan mu ba. Oya! Ki gaishe ni ko a zuciyar ki ne, in ba haka ba mu koma gida kawai a fasa zuwa Saliyon.
Juya kai tayi tana kunkunin fadin in dai sai ta gaida shi ne, to kuwa saidai a koma gida din. Ya tabbatar ba zata gaishe shi din ba, takaicin ta kamar ya kashe shi, sai aka kira shi a waya shi yasa ya rabu da ita da zancen gaisuwa ya amsa wayar.
Tana jin sa yana waya da wani mutum, wanda ta ji ya kira Abdussalam Faytoory, Alhaji ne ya hada su, cewa da sun sauka a Sierra Leone su kira shi, shi zai kai su har gidan su Jalan a Kenema. Shi Abdussalam din tsohon abokin harkar sa ne a Saliyo lokacin da yana harkar fitar da Iron ore, da Aluminium ore. Da turanci suke magana shi da Mukhtar, ya gaya masa suna Lagos, zasu tafi Airport da asubahin washegari daga nan su taso Sierra Leone.
Ya dubi Amani bayan ya gama waya da Faytoory, ya na so ya ce ta tashi ta yi wankan kwanciya barci ta canza kayan jikin ta zuwa na barci su koma ciki, in ya so ya bar mata gadon, don ya ga zaman ta a kan kujerar ya takura ta, sai ya ga cewa wani daddadan barci irin na gajiya yayi awon gaba da ita.
Ba da sanin Amani ba, Mukhtar ya ware ido tsab yana kallon ta, kallo sosai, irin wanda bai taba yi mata kwatankwacin sa ba. Kamar mai karewa halittar ta kallo, koda yake hakan ne, kallon kyautar da Alhaji yayi masa yake yi a nutse, a zaune, a tsanake, kallon da ya san a yanzu yana da hurumin yin sa ba tare da shamaki ba ko daukar zunibi ba.
Ji yayi wani abu mai kama da shaawa na sake darsuwa a cikin ran sa, sauri ya yi mike ya bar wurin zuwa uwar dakin, ya haye gadon ya yi light off, ya kwanta, rokon Allah ya ke kada ya baiwa zuciyar sa ikon abinda take son darsa masa a daren yau, don bai shirya ba, itama kuma ya tabbata bazata taba yarda ba, bai san yana da lafiyar mazantaka ba sai yau da ya kebe da Amani, amma ya gwammace har abada ya dawwama cikin samartakar sa, da dai ace wani abu makamancin hakan ya hada shi da Amani.
Wani irin wahalallen barci Mukhy ya yi, da bai taba yin irin sa a wahala da tsayi a rayuwar sa ba, shi kadai ya san yadda zai fassara shi, da izayar da ya sha a cikin sa a dalilin yana daki daya da Amani. Da irin tsayin da daren ya yi masa, kafin a kira assalatu. Da asubahi tunda assalatun fari ya tashi yayi wankan da ya tabbatar ya dada kama shi karo na biyu, ba tare da ya amfana da komai daga yar mutanen Faskari ba.
He sighed! In the toilet, saying to himself this lady is dilemma to him.
Ya fito ya tada sallah, bayan ya idar ya soma hada kayan sa da ya fidda daga jaka. Saida ya kammala tattare kayan sa da ya zo dasu ya fahimci Amani ta tashi ta shiga wanka itama, don yana jiyo karar saukar ruwa a shower, ya fito falon ya zauna a kujerar da ta tashi da jakar kayan sa a gaban sa yana hada mata nata shirgin kafin ta fito, yanzun an yi saa ta canza kayan jikin ta, ta sanya wasu wankakkun zani da riga na atampa super holland a jikin ta, wadanda da su ta shiga toilet din a hannun ta, fuskar nan tayi fresh da santsin sabulu mai kamshi sai daukar ido take.
Mukhtar ya juyar da kan sa wani gefen daban, ji da yayi wani ignition irin wanda ya kwana cikin sa na tsunkulin sa, fatar bakin ta ta yi pink shar, tayi wani irin sumul kamar kasa hannu ka latsa don kaji irin sulbin ta, tasirin kebantuwar mace da miji a ranar farko ya cigaba da aiki a jikin sa yana waskewa da karfin hali irin nasa..., wadannan pinky lips din nata kawai ya ji ya ke son sumbata, musamman da ta sunkuya don daukar gyalen ta, ya hango abinda ya firgita shi ta cikin rigar ta, tsaye suke kyam cikin brazier, wadanda ake kira masu gindin tasa, da sauri ya kauda kan sa ya mike tsaye, saboda gabadaya ji yayi jikin sa na vibrating, yana amsar sakon da kwakwalwar sa ke darsawa, at the same time, ya shiga neman agajin Ubangiji a cikin ran sa, wani bakon alamari ne ya same shi again irin wanda ya kwana cikin sa jiya, shine ya sake ya dawo masa sabo, alamari ne mai wuyar fassaruwa a gare shi wanda bai taba kwana cikin irin sa ba sai jiyan, dukkan ilahirin jikin sa ke vibrating yana karbar sabon yanayin da ke sauka masa yana kashe kuzarin sa, ta hanyar sanya masa unbearable feelings na matukar son hada jiki da Amani. A rayuwar sa bai taba yi wa wata mace irin kallon da ya yi wa Amani jiya da yau ba, watakila hakan ne ya janyo masa fadawa wannan masifar. Bai taba saka idanun sa sosai a kan kowacce mace ba, don kiyaye dokar Ubangiji, sai yau a kan Amani Usman Faskari, da yake da tabbacin a yanzu ta zama matar sa, wato halalin sa.
Mukhtar ya fahimci cigaba da zaman su wuri guda shi da Amani hatsari ne babba a gare shi, mai barazana ga mutuncin sa da kimar sa da girman sa a idanun ta, don Amani ba irin matan da lafiyayyen miji zai gani ya iya kauda kai bace. Sai kawai ya mike ido jajir ba tare da ya dube ta ba ya ce,
Hajjaju, zamu wuce idan kin gama.
Amani ta dauki dan yalolon mayafin ta na raka ni gantali (cantitly) ta yafa, sannan ta zuge jakar kayan ta, bata amsa masa ba don duk ta bi ta tsargu da kallon da yake yi mata tun jiya kamar sabon maye, tafiyar tasu daga dakin nan zai fi bata ventilation da sassanyar iska, domin dai tun jiya bata shakar numfashi daidai yadda ya kamata idan ta tuna akwai Mukhtar da mayatattun idanun nan nasa a cikin dakin, abu daya ya kwantar mata da hankali jiyan, tayi barcin ta har da munshari, da ta fahimci ya bar mata falon ita kadai, ya shige cikin daki har ya rufo kofa da key ta ciki, bai kuma kara fitowa ba sai dazun da ya fito don yayi sallah. Sai kawai ta yi gaba zuwa kofa, ya janyo jakar sa ya fito shima ya rufa mata baya.
Ya bada mukullin a reception sannan mai taxi ya dauke su zuwa filin jirgin Murtala Mohammed. Zuwan su ba jimawa suka tarar jirgin da zasu hau ya sauka. Ethiopian Airlines ne ya daga da su birnin Freetown, wato babban birnin kasar ta Sierra Leone.
**** ****