Showing 15001 words to 18000 words out of 24347 words
kan mudubin, ya kuma ja shi ya kai shi toilet yana nuna masa su (Pad) har da guntun sabulu dasu maclean din da aka yi amfani da rabi. Ga jakunkuna da takalma ga su brazier, sannan ya ja shi kicin ya kai shi ya yi ta nuna masa, da gaske a rikice yake kamar yadda ya ce dinne......
“He is perplexed.....”
Sai a lokacin Daddy ya soma fahimtar me ke faruwa, me Ibraheem ke son ganar da shi? Dariya ce ta kulle masa ciki yana ta kokarin hadiyeta a cikinsa.
Ibraheem ya ce,
“Na taba tambayarka wace ce Jumah, ka nuna min wata tsohuwa. Ni kuma tabbas na yi magana da wata yarinya mai suna Juma duk da na san sunan tsofaffi ne, amma wallahi Daddy ni da (fresh girl) na yi magana. Ina jin aljana ke son aure na. I cannot live in this house anymore...... sai ranar da Allah ya bani iyali........”
Yadda yake maganar ya bala’in baiwa Dr. Mansur tausayi. Ya ji wani abu ya motsa a zuciyarsa, ya kamo Ibrahim ya jingina a jikinsa.
“Wace ce ita Juma din?”
“Nurse din ofishinka”.
“Ce maka ta yi a ofishina take? Yaushe akai hakan?”
Ibraheem ya ce, “Wayarka na kira ta dauka, bayan nan ma mun kara magana, har ta tambaye ni wai don Allah nine Ibraheem? Kafin in ba ta amsa wayarta ta mutu. Kuma wallahi da layinka Daddy”.
Sai a nan Daddy ya gano komai, ya tuna randa ya manta wayarsa a gidan. Ya gane Rayhanah ce ta amsa mishi waya ta ce sunanta Juma, kuma ya ga received calls na Ibrahim amma bai bi ta kansu ba.
Sai ya ce da Ibraheem,
“One minute...”.
Ya shigatoilet din Rayhana ya yi dariya ya koshi sannan ya fito. Ibraheem ya kulu ya kumbura, don ya gane Daddy abin dariya ya dauki abin. Ganin yanayin da yaron ke ciki sai ya zama serious.
“Kwantar da hankalinka Ibraheem...... ba wata ba ce mai suna Juman, RAYHANAH ce MATARKA!!!”
******
Ya dago fararen idanunshi da sauri ya dubi mahaifinsa. Babu alamar wasa a tare da shi. Ya ci gaba da cewa,
“Ko da yake a da ne take matarka, amma na dade da yanke shawarar raba auren zan yi, tunda baka yi na’am da zabina ba, ka mai dani ba komai ba a idanun Rayhanah da kakarta Juma”.
Wannan karon da firgici ya dubi Daddy....... “Kakar tata ce Juman?”
Daddy ya daga kai. “Wannan kuma dakin da ta zauna ne shakara guda tana dakon auren ka”.
Ya kara kallon Daddyn sosai,
“Me yasa ka yanke shawarar raba auren Daddy? Da bakina ban ce maka bana so ba”.
“Kana so ka wulakanta ni? Rimi-rimi muka yi magana, ka ce da amincewarka in aura maka wadda zuciyata ta amince da ita, baka da zabi a auren fari.
Cikin girma da mutunci da bacin ran mutane masu yawa aka yi auren nan, na dauko yarinya na kawo ta gidanka ni da Yaya Abdulkadir cikin mutunci da mutuntawa.
Tun daga ranar Ibraheem baka kara nemana ba, idan na neme ka baka amfani da layin. Yarinya na ta hakuri har kakarta ta damu, ta nemi da a raba auren.
Amma Rayhanah ta zabi ta rabu da kakarta har abada ta ci gaba da dakon aurenka har karshen rayuwarta. Koda har abada bazata ganka ba.
Ba don kai ba, ba don ta sanka ba, ba don tana sonka ba sai saboda darajata. Karewa ma da Khalipha ne zai aure ta uwarku ta wargaza lamarin.
Wai ni mai DA, wanda nake da yakinin na isa da shi, kuma shi mai share min hawaye ne a kowane lokaci na bukata, na baka auren Rayhanah don dama can kai na fi yiwa sha’awarta saboda na san za ku zauna lafiya tunda halayya da dabi’unku daya.
Ibraheem da me na tsira a wannan gatan da na yi maka? Sai kunya da na sha da yake da neman yadda zan yi in rage mata rayuwar kadaicin duk da bai dameta ba sai kakarta. Don haka me ya yi zafi?
Rayhanah ba rasa mijin aure ta yi ba. Ban ba ta wannan damar bane, da ka ga dama ka zo ko sau daya baka taba tambayata lafiyar matarka ba, kana jira sai na tallata maka ita. Na kasa ta a fai-fai na ce Ibraheem dauki?
To ka yi kadan, uwarku ta yi kadan. Ungo wannan.......” Ya ciro takarda a gaban kwat dinsa ya zaro biron dake makale jikinsa ya mika masa,
“Yankewa Rayhanah igiyar auren nan ko guda daya ce ta huta”.
Idanun Ibraheem suka cicciko da kwallah.
“Daddy kada mu yi haka...... kada mu yi haka...... saurareni ka ji uzirina tukunnah....”
“Zan saurare ka kadai bayan ka rubutawa Rayhanah saki ko guda daya. Wane uziri ke gareka? Ni ka ga tafiyata, kada ka sake ka zo min gida in ba takardar Rayha ka kawo min ba, babu gardin da zai zauna min a gida, ‘ya’yana sun girma kuma duk mata ne. A toh! Allah ya bamu alkhairi”.
Ya juya ya fita yana kara fadin,
“In ma aljanar ce za ta aure ka ku yi ta auren, kai ta ga ka yi mata, tunda tuzuru ne, sama da shekara talatin babu mai kiranka saurayi, ba Khalipha mai iyali abin burgewa ba”.
******
Juyi yake a matsakaicin gadon, lullube cikin zanin atamfar Rayhanah. Sai yanzu ya gane turaren ba wani bane ‘Makhmariyyah wa lamsa nectar’ ne wanda ake durawa a wani kanti a Jiddah. Shima Sapna ce ta gaya masa wata rana yana rungume da ita yake tambayarta wane irin turare ne mai sanyi da kwantar da hankali ta shafa a tufafinta haka?
Me yasa take amfani da abubuwa irin na Sapna?Is it a coincidence or what? (Arashi ne ko minene?) Ta san abubuwan da yasa yake son Sapna har da ire-iren wadannan abubuwan? Gayun Sapna cool ne and cooly ba na tashin hankali ba. She's a designer baby.
Tukunna ma, wace ce Rayhanah? Shi fa ya san wannan sunan, amma ya manta inda ya san shi. Ko Daddy zai tsire shi, ba zai taba yin sakin nan ba, ko ba don ji da ya yi ita ce Juman da ya so a murya ba, sai wannan furuci da ta yi na cewa za ta jira shi da aurensa har abada saboda Daddy. Koda har abada bazata ganshi ba. Ba don komai ba sai don cewa duk mai darajja Daddy abin so ne da girmamawa a gare shi.
Shima zai koyawa zuciyarsa bajinta, zai sota zai zauna da ita har abada saboda Daddy ko da a fili (a zahiri) ba ta yi masa ba. In yaso nan gaba sai ya je ya auro Sapna ya kara idan tana da rakin da ba za ta iya dauke shi a shimfidarta ba.
Ya tara bukata mai yawa ga duk macen da tai kasadar aurensa, shekarunsa talatin da uku bai taba sanin ‘ya mace ba. Ya killace kansa ne (insha Allahu) only ga matar aurensa, wadda yake fatan ta zama itace tubalin iyalinsa.
Ya kuma yarda ya baiwa Rayhanah da bai sani ba wannan babban matsayin tunda zabin Daddy ce. Addu’a yake har a fili Allah yasa RAYHANAH ba irin wadannan ‘yan lagwai-lagwai din bane kamar tsada irin matar Yaya Khalipha.
Bakar mace yake so ‘yar’uwarsa fully Nigerian. Ba kyale-kyalen gashi da farar fata ba. Shi kadai kuma ya koma yiwa kansa dariya duk da yana cikin tension din da Daddy ya hada masa wai ya rubuta saki. Abin da ya ba shi dariyar shine tambayar da zuciyarsa ta yi masa.
“Daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki? Tun ba a ga matar ba an ga kyau ko muninta, an ga yankan bakinta har an fara kissima yadda ake son ta a shimfida? Man! Kwanciyar aure ba ita ce kawai abin kissimawa a cikin aure ba, akwai wasu abubuwa masu muhimmanci ko da a ce basu kaita muhimmanci ba, to suma suna da nasu.
Shakuwa da juna, kusancin zuciya da zuciya, soyayya, tausayi da jin kai a tsakanin ma’aurata, fahimtar juna, nuna kulawa da bakin cikin ko farin cikin juna, planning a kan tarbiyyar ‘ya’ya da yanayin yadda ta dauki addininta da yadda take gudanar da ibadarta.
Idan ta dauki nauyinka yadda kake so a shimfida, ta kuma rasa wadannan qualities din she’s not enough wallahi auren ba zai dore ba.
Ga kuma kasancewar dan adam tara yake bai cika goma ba, da wuya a samu wadda ta hada dukkan wadannan din, a wurin Ibraheem idan irin haka ta faru to saki ba shine solution ba.
Dubo wata wadda ba ta da wancan take da wannan ka hadasu, sai rayuwa ta fahimta da soyayya ta dore. Tunanin Himu kenan har barci mai karfi ya dauke shi, mafarkin yadda zai ga Rayhanah yake, saboda yasa abin a ransa.
*******
Da asubah bayan ya yi sallah a masallacin dake kusa da gidansa wajejen karfe shida na safe, ya zauna ya shiryawa Daddy (text msg) na ban hakuri da neman afuwa. A ciki yace da Daddyn
“Aurensa da Rayhanah na har ranar busa kaho ne. Ya yi hakuri ya yafe masa ba zai iya ko da kwatanta abin da ya umarce shi ba, ya ba shi RAYHANAH....... akwai uzurin da ya janyo bai neme shi a waya ba shima ya kasa samunsa.
Ya rufe wayar ne kwata-kwata a dalilin jinya mai tsaho da ya yi a SanFrancisco, ya tambayi Mami ita ai ya gaya mata. Ya kare da cewa,
“Daddy I’m sorry........ Luv u Dad!”
Shima fitowar shi kenan daga masallacin asibitin wayar dake aljihunsa ta sanar da shi shigowar sakon. Ya dauko ya karanta, sai jikinsa ya yi sanyi. Amma bai ba shi amsa ba.
Mota ya dauka ya nufo gida da yake aikin kwana ya yi. A farfajiyar gidan ya cimma motar Ibraheem, jikinsa ya kara yin sanyi da ya shigo falo ya ganshi zaune cikin kujera yatsunshi goma cikin sumar kanshi kansa a sunkuye. Kayan jikinsa na barci ne.
Duk sallamar da Daddyn ya yi bai ji ba, ya yi nisa cikin tunani mai zurfi, kawai so yake ya ga wannan Rayhanah da ta tokare masa a kahon zuci. Yasa hannu ya mikar da dansa tsaye, sannan ya rungume shi.
“Jeka dauko passport ayi biza in sadaka ga Rayhaanah, amma don Allah Ibraheem ka rike min Rayhana amana, domin amanar Allah ce a hannuna. Idan ba ta yi maka ba, ka bani ‘yata kar ka wulakanta min ita yadda uwarku ta wulakantata......!!!”
Hannu ya kai ya toshe bakin Daddyn don ganin yana so ya tuno tsohon bacin ran da Mami ta dasa mishi.
“Past is past Daddy........ just the present!”
Dacta Mansur ya girgiza kai, wato ya yarda da shi. Ibraheem a dan nauyaye da nauyin harshe ya ce,
“A ina Rayhanah take?”
Daddy ya ce,
“Informatics - Singapore”.
Fiddo idon da Ibrahim ya yi ya baiwa Dr. Mansur dariya.
“Ita da wa Daddy? Da aurena?”
Daddy ya ce,
“Ita da budurwarka Juma, da kuke soyayya a waya”.
“Kasa tsage in shige!”.
In ji Ibraheem........ sai ya rufe fuskarsa da tafukansa. Wai ya ji kunya kenan. Dacta ya wuce ciki yana dariyar Ibraheem.
Idan yana tare da Dr. Mansur (mahaifinsa) bai san sanda yake mai da kansa kamar yaron goye ba. And the Dad likes it..... shi har gobe Ibrahim da Khalipha hangosu yake suna ‘yan digwui-digwui a Al-Muntada da Al-Falah (Children Islamic Schools) a Birtaniya.
Sanda yake kama hannun daya, Asma’u ta kama daya su tsallaka titi. Su shigar dasu makaranta.
Don haka shi har gobe yaran goye ne a idanunsa baya sakar musu ragamar rayuwarsu sai a bisa hanya madaidaiciya, ba kuma takura musu yake ba, tsaka-tsaki. Ayi raha lokacin raha, ayi discipline in sun karkace, sannan ayi musu abin da suke so
[12/26/2019, 21:08] Takori: *****
HADUWAR AMARYAR DA ANGON!
Cikin jirgin ‘Turkish Airlines’ da sukeciki, bairin tunanin da Ibraheem Mansur Takai bai yi ba, ya gaza ko da kurbar dan jusin dake cike da kananan kankara da suka mishi a dan kofin su dan kankani dake hannunshi.
Wace ce wannan Rayhanan? Ya take? Wace irin tarba za ta yi masa? Shima wace iri ya dace ya yi mata? Zai so ta? Zai iya ba ta matsayin mata a gare shi? Zai iya hada rayuwarsa har abada da yarinyar da bai sani ba bai taba gani ba? Bai taba yin wata mu’amala da ita ba balle ya san kamanninta ko halayenta?
Tunaninnikan da suka addabi kwakwalwar Ibraheem kenan, yayin da a bangaren mahaifinsa Dr. Mansur Takai, babu abin da ya dame shi, daga ya sha jus sai ya bude shafukan jaridar ‘Daily Tribune’ dake hannunsa, in yaso ya yafito ma’aikatan jirgin su zo su ba shi abinda yake bukata da yake a first class seats suke.
Lokaci-lokaci ya kan saci kallon Ibrahim ta gefen idonsa, sarai ya san tunaninnikan da ke damunsa, amma bai ce masa komai ba, bai ma nuna ya san halin da yake ciki ba.
A lokacin da aka ba da order a daura belt jirgi zai sauka a ‘Changi-Airport’, Ibrahim bai ji ba. Sai ji ya yi Baban yana makala masa, bayan ya makala nasa. A lokacin ne Ibrahim ya gane ‘he is lost...... (ya yi nisa a tunani).
Ya kalli uban, shima ya kalle shi, sai suka yi ‘yar dariya a tare.
Bayan sun sauka motar hotel din da Daddy ya yi booking tun kafin su taho (Mandarin Orchard Singapore) already tana jiransu, ta kwashesu da ‘yan jakunkunansu marasa nauyi zuwa otel din.
Tun a hanya Daddy ke kiran wayar Rayhanah ana gaya masa a kashe take. A lokacin ita Rayhanah tana aji suna wata jarrabawar gwaji (test) domin gab suke da fara jarrabawar karshen shekara. Kuma dama karatun na shekaru biyu ne kacal, da yake tana da diploma tare dasu.
Karfe shidda na yamma ta baro cikin institute din nasu ta kamo hanyar gida, ta tsaya ta sayawa Inna roasted KFC, ita kuma ta sayawa kanta ‘wantanmee’ ko ‘wonton’ (yadda suka fi kiransa), ‘chili crab’ da ‘fried hokkien mee,’ duka suna daga cikin (40 Singapore foods Singaporeans cannot live without) abincin mutanen kasar Singapore guda arba’in da baza su iya rayuwa basu ba, saboda ta ce da Innar yau kada ta yi musu girki za ta yo take away don ta wayi gari ba ta jin dadi, sauri ma take ta isa gida don ta kaita clinic a duba ta.
Haka nan ta tsinci kanta da faduwar gaba a lokacin da ta doso gida. Sai da ta tsaya a kan wani dan tudu ta zauna ta zube ledodin hannunta a kasa tana dan hutawa tana hango kofar gidan nasu da bakuwar motar otel din (Mandarin Orchard) fara sol. Ta san hotel din da Daddy ke sauka kenan, don haka jikinta ya ba ta Daddy ne ya zo.
To amma wannan faduwar gaban da ta samu kanta a ciki ta mece ce? Ta so ta kunna wayarta, sai ta tuna a gidan ta barota.
Sai kawai ta mike da dan kuzari tana cewa a ranta bari in karasa gidan, daman dai kuma ta kwan biyu basu yi waya da Daddyn ba, har Inna kan tambayeta kwana biyu Baba Likita bai kira ba, lafiya?
Ta kan ce lafiya sumul insha Allahu, kin manta Baban nawa busy doctor ne?’
Inna ta ce, “Allah yasa buzu ne ba busy ba, ki kira min shi kawai”.
Ta yi dariya ta ce,
“To ai ni yanzu bani da lokacin kunna waya idan ban gama tsarge tests din nan da suka sako ni