Showing 3001 words to 6000 words out of 24347 words

Chapter 2 - Rayuwar Rayhana Book 3 Hausa Novel Complete

Takori   

28 Dec 2024

144

nuna mata tana yi mishi ba dai-dai ba, duk da ita akan sanin kanta tasan ta yi mishi ba daidai din ba, kawai ya daina yarda ya kadaice da ita, ya daina zaman gidan sam-sam.
Abinci ko ta mance yaushe rabon ya zauna su ci shi tare da ‘ya’yansu, wanda a da yake da kakkarfar akida a kan hakan.
Domin ya kan ce, hakan na kara kauna a zuciyar ‘ya’ya da iyayensu. Yana hana yaro ya zama mai kwadayi, yana kara jin kai da hadin kai tsakanin ‘ya’ya da iyayensu.
Abin da Mami ba ta sani ba shine, can a (Farm-Center) yake cin abinci in yana da bukata wajen Inna Juma da suruka, ayi hira ayi raha, ya cikasu da shopping sannan ya dawo (Lamido Crescent) ya nemi gadon barcinsa ya kulle da mukulli, duk don ya hora Asma’un, a bisa sababbin halayen da ta tsiro masa dasu wadanda ba zai dauka ba ko daya.
An ce kukan kurciya jawabi ne, in tana da hankali sai ta gane. Ba ta gane din ba, sai yanzu da dan cikinta ya ankarar da ita.
Ita kanta ta san mai laifi-kan-laifi ce a wajen Dr. Mansur, bai taba tambayarta ina Rayhanah ba, tun ranar da ta kore ta.
Wanda a yanzu take cikin fargabar ina yarinyar ta shiga babu ko duriyarta, amma Dacta bai tambaya ba, bai tambaye ta ina Khalipha ba, ina kuma zancen aurensa da ta hana ya kwana? Ina wadda ta aura masan? Me take ci? Me take bata tunda Khaliphan baya nan?
Ita kanta ta fi son kada ya tambayetan, don ba ta da amsar ba shi. Sosai yake sakar mata fuska a falo in sun hadu gaban ‘ya’yansu, sai dare ya yi ya garkame kofarsa. Wannan ya fi komi tada hankalin Dr. Asma’u wadda ke son gyara kuskurenta, amma Dacta ya ki bata dama. Babu fuska ma bashi da lokacinta.
Ba don yana kwana a gidan ba ma (if he is not on-call) da sai ta ce wata ce ta janye shi, kasancewarsa mai farin jinin mata a wajen aiki, manya da yara, masu aure da marasa aure, duk da ya manyanta saboda yadda Allah ya suranta shi, ya kuma yi masa ado da kirki da tausayi har ma da nuna kulawa ta musamman ga marasa lafiyansa da kananan likitoci da ma’aikatan dake karkashinsu.
Wadatar zuci da rikon addininsa sun shafe shekarunsa a jiki da fuska, sun ba shi shekaru arba’in da biyar na magidanci mai kananan ‘ya’ya.

Ajiyar zuciya ta sake yi ta kasa ce da Ibraheem komai, la shakka ta yi kuskure, anya ma ita ce? Ta maida kanta jahila haka? Ina zurfin tunaninta ina kwalayen iliminta? Ta maida kanta irin matan bakin- kasuwa?
Nadama ce take shigarta sosai, a kasalce ta ce da Himun.
“Komai ya canza daga yau insha Allahu, tunda na yi maganin matsalar. Kai min addu’a ka ba shi hakuri..... Himu don Allah.......”
Tausayi da kaunar Mamin suka kara kama shi. A take ya ce,
“Mami komi ya wuce, na ari bakin Daddyn na ci masa albasa, komi ya wuce, sai na iso”.
Ya kashe wayar da sauri don zuciyarsa ba za ta iya jurar sauraron kukan mahaifiyar ba. Wanda ke tada tsigar jikinsa har ya sanyawa jikinsa tsuma.
Ibraheem kenan, shi da Khalipha ban san wa ya fi kaunar Mamin nan ba (Takori).
Allah ka barmu da iyayenmu, mu rayu tare har karshen rayuwarmu. Ka bamu iko da karfin zuciyar yi musu biyayya, albarkarsu ta zama mayafinmu kuma bango abar jinginarmu. Sannan abin tinkahonmu gobe kiyama.
******


A FARM CENTRE
“Halan waken nan sai da aka barza shi aka fidda dusar, kafin ayi faten nan?”
Dr. Mansur kenan, ke tambayar Inna Juma. Rahane ta dau pillow na kujera ta tura bayan Daddy. Bai lura da shakiyancin da ta yi masa ba ya sake tambayar Juma.
“Kuma kifin nika shi kika yi a blander kafin ki zuba?”
Ai sai Rayha ta kwashe da dariya. Inna Juma ta zuba mata duka a cinyarta ta ce,
“Uban naki kikewa shakiyanci ko ya yi kama da Malam Hudu? (Kakanta wanda ya haifi Yalwati).
Sai a lokacin Dr. Mansur ya ankara da abinda ke faruwa, ya karashe lomarsa ta karshe ya mike ya kora da lemun safari cikin tambulan, ya dauki mukullin motarsa ya yi hanyar kofa yana murmushi ya ce,
“kyaleta Inna Juma, ta mai dani kakan nata ya fiye min da ta rikeni a matsayin siriki ta dinga nuku-nuku dani, ta kasa gaya mun damuwarta. Bayan nine uwarta, nine ubanta, nine abokinta, kuma kawarta. Ke kuma kakarta.
Bari in wuce gida yamma ta yi, yanzu zan yi tuki da kuzari tunda hanjina ya warware. Go-slow ne dai na san sai ya kai ni magariba a titin nan idan ma na yi sauri kenan, Kano is full, alhamdulillah Kanon Dabo ta yi zarrah a jihohin Nigeria gaba daya, wajen albarkar Al’ umma”.
Rayhanah ce ta bude masa kofar motar ya shiga ta rufe,
“Sleep well Daddy.....”
Ta fada tana daga masa hannu har ya bar get dinsu yana daga mata shima. Maigadi ya kulle, ita kuma ta koma cikin gida.
Nan ta ga wayar Daddyn a nan inda ya tashi santin faten waken Inna Juma ya mantar da shi. Ta ce,
“Lah! Inna kinga Daddy ya manta wayarsa”.
Inna ta ce,
“Sai ki adana gobe ya karba”.
Ta ce, “Ba lallai ya zo gobe ba, karshen wata ne zai je Takai. Bari dai na ajiye din”.
Ta yi dakinta da ita ta sanya a kan lokar gadonta, ta fada bayan gida don ta yi alwalar sallar magariba.
Kafin lokacin magariba ya cika, Rayhanah na zaune kan sallaya da carbinta a hannu cikin kyakkyawar shiga da ta ware musamman don yin ibada, doguwar Abaya ce kirar Kuwait da farin Hijab wanda ya tsaya iya gwiwoyinta, tana yiwa Ubangiji tazbihi.
Har aka kira magariba ta tada sallah, a lokacin da wayar Daddy dake kan lokar gadonta ta soma dan kida ba mai cika kunnuwa da gigita mutum ba.
Don haka a nutse ta ci gaba da sallarta har ta idar, mai kiran bai hakura ya daina kiran ba sai kira yake akai-akai-akai. Yana yi yana karawa.
Ta mike ta kwanta a gefen gadonta ta dauki wayar Daddy don ta kashe, a ranta tana kunkuni cikin fadin “these so-called AKTH emergency unit, will not leave my Dad to live in peace ........haba! Ko inji ai yana son (service) kafin ya ci gaba da aiki balle mutum dan-Adam.
Amma shi Daddyn baya gajiya, ko ya kwana da an kira shi komin dare zai tafi. Ni gara ma da ya bar wayar, yau daya dai ya huta”.
Amma ga mamakinta sai ta kasa kashewa, ta zubawa lambar ido, domin ba ta yi kama da normal lambobin da ta saba gani ba. Lambobi ne rankacau (International).
Haka nan ta samu kanta da faduwar gaba, mutuwar jiki da sanyin gwiwa, wanda suka dage da cewa lallai suna son amsa wannan wayar, ta gayawa mai su Daddy baya tare da wayar, don ganin yawan kiran mai nuna mai ita a matse yake da son magana da Daddyn daga kololuwar duniya ba kiran asibiti bane.
A dai-dai lokacin da kiran ya kara shigowa, sai ta kishingida ta amsa.

“Dacta baya tare da wayar fa! Be patient mana!!”.

Wata irin sassanyar murya ce mara amo da karsashi, sannan kuma mai taushi, yarinyar ta yi amfani da ita wajen yi masa wannan kalamin, wadda ta tsirga har cikin kwakwalwarsa, ta haifar masa da macewar jiki, at the same time, ta tada tsigogin jikinsa.
Da ta ji anyi shiru kawai sai ta katse wayar ta ajiye. Ta dau remote ta kunna A.C ta soma addu’ar kwanciya barci.
Ibraheem ya yi shiru yana kallon wayar hannunsa, tsaye yake a balcony din gidansa (terrace) a saman bene yana kallon yadda ruwa ke tsiri, yana zuba cikin furanninsa korra sharr.
Akwai wani abu extraordinary cikin muryar yarinyar da bai taba ji a muryar wata diya mace ba, mai sanya sanyin jiki da kasala.
Me ya hada Daddy da budurwa har wayarsa ta je hannunta? Yana da kyakkyawan zato a kan mahaifinsa, amma wannan ba Abida ba ce ba Jawahir ba, ba kuma Azizah ba.
Idan ma sune ba yadda za ai wayar Daddy ta zo hannunsu. Don haka ya ji yana so ya tambayeta ita wace ce? Me ya hadata da wayar mahaifinsa?
Don haka ya sake kira, ta kuwa sake amsawa don yau cikin nishadi take, don Daddy ya ce za ta tafi Singapore jibi in Allah ya kaimu ta dora karatunta kafin Ibraheem ya nemi gida.....
“Wace ce ke?”
Abinda ya tambaya kenan a gintse, da makalalliyar hausarsa mai fita a doron harshe, cikin tsananin takaitawa.
Ita ma a takaicen ta samu kanta da amsawa.
“Sunana Juma”.
“Juma? What kind of name is this?”
Ta amsa da cewa, “Sunan da iyayena suka rada min kenan”.
A muryarta kamar ta ji zafin tambayar da ya yi mata, shi kuma a rayuwarsa bai iya muzanta dan adam ba. Sai ya yi saurin cewa,
“Ki gafarce ni plz, ina so in san yadda akai wayar Dr. Mansur ta zo hannunki ne?”
“Am the Nurse on duty, and he left it at the ward”.
Ibraheem ya gamsu da bayaninta har ga Allah, ita kuma kawai cikin nishadi take kan wannan albishir mai dadi da Daddy yayi mata na tafiya Singapore (Informatics-Singapore) ta rasa da wanda za ta yi sharing nishadin nata, sai ya fada a kan Ibraheem.
Ya ce, “Alright, zan kira zuwa gobe. Thank you”
“Don’t mind”. In ji ta.

Karfe biyar na Asubahi tana tsaka da barci sai ga kira again, ta yi dan tsaki ta mika hannu ta dauko wayar tana ganin laifin kanta da ba ta kashe wayar ba tun jiya, ga shi an katse mata barci mai dadi da take yi bilhakki.
Sai dai ita kanta ta san ba laifinta bane, laifin yatsunta ne, sun kasa kashe wayar kada mai Turanci mai dadi ya bugo bata dauka ta sake gillara masa karya ba.
Ai tana ganin lambar ce sai ta nemi barcin da ya cika mata ido ta rasa. Ta amsa da sallama cikin muryar barci, wannan karon tasirin da muryar ta yi a jikin Ibrahim Mansur, Allah ya yi yawa da shi, ta yadda biro na bazai iya rubutawa ba.
Har ta kai ga Ibraheem ya fada cikin wani yanayi na daban. Muryarshi can kasan makoshinsa ya ce,
“Ki yi hakuri na tashe ki daga barci”.
“Don’t mind”. Ta sake cewa.
“Jumah!”
Ya kira sunanta da murya (which is deeply suffering).... Sai ta ji jikinta ya kama rawa, ta yi magana cikin sarkewar harshe.
“Doctor is not yet at office!”.
Ta kashe wayar hannunta yana rawa, gangar jikinta ma gabadayana yi. Irin wadannan mazan sune masu yin zinar murya, me yasa zai rika yi mata magana da irin wannan sauti mai kassara gabban jiki kamar wata matarsa ko budurwarsa? Ba za ta kuma amsa wayarsa ba. Batasan cewa murya ce da Ubangiji Subhana ya halicce shi da ita ba.
Sai kuma ta baiwa kanta dariya, sanda wani bari na zuciyarta ya tambayeta,
“Wa ya gaya miki haka miji ko saurayi ke yin magana da budurwarsa ko matarsa Rayhah?Tunda ke baki da saurayin ko mijin? Babu kuma wanda ya taba yi miki magana hakan including Yaya Khalipha?”
Oho!”
Ta fada tana kyabe baki tareda shigewa cikin lallausan bargonta tana cewa,
“A to, haka dai na ga Daddy na yiwa Mami magana, ita ma in ya yi tafiya tana waya da shi ai haka take yi mishi magana”.
Barci ne mai karfi ya dauke ta. Hasken rana da ya hudo ta farin labulen da ya zagaye dakin barcin nata shi ya ratso ya dallare mata fuska. Ba shiri ta tashi tana mittsike ido ta fada toilet ta yi wanka ta yi brush da yake ta yi sallar Asubahi ta fito falo.
A kicin ta jiyo motsin Inna, don haka ta tasarma kicindin. Can ta iske Inna Juma tana kwabin Alkubus, ta ce,
“Allah ya ja da ran Inna ta, yau Alkubus zamu ci haka?”
Tana buga fulawar ba tare da ta juyo ba ta ce,
“Ni ba ke nake yiwa ba, Baba Likita nake yiwa don jiya ya gaya min yana son shi”.
“Ba kya jin magana Jumah.......! (ta fada da sauti irin na Ibraheem) wanda ita kanta ba ta san sanda muryarta ta karye ta canza ta koma haka ba. Na gaya miki yau ba zai zo ba zai je Takai Asabar din karshen wata ce”.
Inna ta yi dan jim, sannan ta juyo ta dubeta. Abubuwa biyu ne suka sa Innar yin shirun da juyowar.
Na farko kiran sunanta da Rayhanah ta yi da wani irin amo (tune) da ba nata ba, na biyu kuma ba ta ce mata Inna ba kamar yadda ta saba.
Gani ta yi Rayhanah na rawar dari, ta kankame hannunta a kirjinta, murya na rawa idanunta na lumshewa, suna budewa ta ce,
“Inna sanyi nake ji”.
Sai ta tsame hannunta daga cikin fulawar ta rufe ta don ta tashi, ta wanke hannunta ta kama Raihanan, ta soma tofa mata duk addu’ar da ta zo bakinta, domin a tsammanin Inna aljanu ne suka shiga jikin jikar tata yanzu-yanzun nan.
Tabbas muryar da ta yi mata magana da ita, ba tata ba ce.
Daki ta maida ita ta ce ta kwanta, bari ta je asibiti ta kira Dacta (da yake ta san ofishinsa ya taba kaisu).
Rahane ta ce, “Wai Jumah........! (ta kara yin magana da irin sautin dazu) sau nawa zan gaya miki Daddy baya nan ne?”
Inna ta ci gaba da tofa mata addu’a. Haushi ya kama Rahane, don ta ga Inna ta mai da ita mai aljanu kawai don ta ce da ita tana jin sanyi.
“Kinga Jumah..... (ta kara fada da sautin Ibrahim da tune dinsa na yin magana) jeki ki yi Alkubus dinki, ki rabu dani don Allah bana son wannan tofe-tofen da kike mini, fever ne kawai ke son shiga na, rufa min bargo, jeki don Allah”.
Inna ta ce,
“Ba zan tafi din ba, aljani ke son auren ki. Bari Baba Likita ya zo a daddale magana, idan dan American nan baya sonki, to ya sahale miki ki yi rayuwar ‘yanci ki samu wani mai sonki ki aura.
Wannan ba aure bane, watanni goma fa! Ana shirin shiga na sha daya. Babu miji ba dalilin sa”.
Inna babatu take ba ta san cewa Rayhanah ba jinta take ba. Zazzabi mai zafi ya rufeta ruf. Ina ma ba ta kashe wayar nan dazun ba, da watakila ta ji sunan mai wannan poisonous murya wadda ta dura mata virus ta cikin kunnuwanta ta haifar mata da zazzabi mai zafi.
Ita dai fatanta Inna ta fita ta ji da abinda ya sameta, amma Innar ta ki. Sai da ta hada da magiya sannan Inna ta fita tana ta mita, ita wannan aure ya isheta, ba ta san irinsa ba. Bata taba gani ba!
Bayan fitar Inna kira ya sake shigowa, Rayhanah ta daga, duk da ta ce ba za ta kara dagawa ba, zuciyar da gangar jikin sun ki amincewa, cewa suke;

“........ ba zamu samu sauki ba in bamu ji shi ba, ba zamu barki ki zauna lafiya ba sai mun ji ko shine IBRAHEEM!!!
[12/25/2019, 15:42] Takori: Ya tabbata ta amsa kiran, amma ba ta yi magana ba.
Ya dade shima bai ce komin ba, sai da ya saisaita kansa ta hanyar yin ajiyar zuciya akai-akai, sannan a sanyaye ya ce,
“Am now not to ask for Doctor, (yanzun ba Dr. Zan tambaya ba) don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login