Showing 9001 words to 12000 words out of 24347 words
da Institute din, bai yarda Rayhanah ta zauna cikin dalibai ‘yan’uwanta ba sai bisa kulawa da sa-idon babba wato Innarta Juma. Shi a Hotel ya sauka.
A wunin ranar baki dayanta dukkansu basu tsinana komai ba sai barcin gajiya. Sai wajejen magariba Dacta ya zo a motar Hotel din da ya sauka ya kawo musu take away na Ji Hao (abincin mutanan Asia ne) da Inna Juma ta gagara hadiyewa duk dauriyarta sai da ta kwararo shi waje.
Dacta da Rayhanah suka ce me za su yiwa Inna ba dariya ba, dama tun a cikin jirgi ake dirama da ita, komai sai ta ce sun yi mata ba dai-dai ba. Haka abokan tafiyar tata da ma’aikatan jirgin mata da maza suka yi ta lallabata har Allah ya sauke su lafiya.
Yanzun ma danja ta bude ita a nemo mata ko samanbita ne ta tuka tuwo ta ci in ba so ake yunwa ta yi mata lahani ba, yini biyu kenan ba ta sa kwakkwaran abinci cikin hanjinta ba sai kayan tashin zuciya.
Cikin daren Baba Dacta sai da ya san inda ya je ya nemo mata shinkafa da kaza sannan aka zauna lafiya. Shi da suruka sai cin kayan dadinsu suke yi irin su kayanfulawar ‘McDonalds, KFC (Kentucky Fried Chicken), Cendol, Hainanese da Rojak (Asian snacks). Sai bayan isha’i ya yi musu sallama ya koma masaukinsa.
Washe gari da safe suka shiga Informatics Arena karfe takwas na safe shi da Rayhanah, a (admin office) duk wasu cike-ciken takardu da suka kama Dr. Mansur ya yi su, Rayhanah tasa hannu, kudaden da suka nema duk ya biyasu ta banki.
A take ba bata lokaci Rayhanah ta shiga aji, inda ta fara daukar lacca, ta tadda dalibai ‘yan’uwanta daga Nationality daban-daban maza da mata.
Tun a ranar ta soma kwankwadar ilimin na’ura mai kwakwalwa wanda a iya dan iliminta a Kazaure ba ta san da shi ba, kwakwalwar a wanke take, zuciyar a sake take babu damuwar komai a ciki sai godiya ga Allah da wanda ya zamo silar haskaka rayuwarta.
Don haka ta mai da hankali don bai wa mara Da kunya da fita kunyar Baba Dacta.
Kwanan Baba Dacta uku kacal a Singapore ya wuce Chicago, bayan ya tabbatar basu da matsala, ya shake musu store da kicin da duk wani nau’in kayan abinci da kayan amfani da za su bukata, da katin daukar kudi a ko’inacikin duniya (mastercard) a duk lokacin da suke bukata bayan ya koyawa Rayhanah komai.
A asibitin Illinois Baba Dacta ya doki babban gurbi na tahowar Dr. Ibraheem gida Nigeria very last week. Amma a satin suke zuba idon dawowarsa.
Kwanansa daya kacal ya juyo gida Nigeria. A nan ma gurbin ya doka, Ibraheem ya tafi wajen dan’uwansa Khalipha a Abuja da yake ta can ya sauka. Don haka ba yadda zai yi, ya zauna karbar lallashi da ban bakin Mami masu nuna nadama, da alkawarin rashin maimaitawa.
To tsakanin Mansur da Asma’u sai Allah, shi kadai ya san soyayyar dake tsakaninsu. Dole shima ya sauke nasa kan, domin ya fita jigata. Suka koma suka dinke kamar super glue, sai dai duk da haka bai kara yi mata zancen Rayhanah ba.
Ita ce dai abin ke cin ranta tana kuma tsoron tambaya, idan ta tuna korar karen da ta yi mata. Cike take da fargabar ina yarinyar ta fada? Har Khalipha ta tambaya ya ce wallahi Allah bai sani ba, Daddy bai kara yi masa zancenta ba.
Cikin Mami ya kara durar ruwaa lokacin.Cike da alhininzuwan ranar da Baba Dacta zai gama miskilancinsa ya tsuye ta ta fito masa da Rayhanahr da ya bata amana, me zata ce masa? Shi Khalipha yanzu shirin taren Babynsu suke yi Mimtaz haihuwa yau ko gobe.
Zuwan Ibraheem Abuja unexpected haka ya gigita Khalipha, wata irin runguma suka yiwa juna har saida suka kai kasa, dukkanninsu babu wanda bai zubar da hawaye ba, inda Mimtaz ta cika da mamakin to kukan me suke yi? Na farin ciki ne ko na mene ne? Su kansu basu sani ba
Shi dai Ibraheem kewar da ya yi ta shekara goma ta Khalipha ita tasa shi kukan, duk da cewa Khaliphan ya sha kai wa Ibraheem din ziyara wajen sau hudu, sai kuma farin cikin ganin kyakkyawar rayuwar da Khalipha ke ciki da matarsa ‘yar’uwarsa Mimtaz har ga albarkar aure na shirin fara zuwa.
Duk yawancin hirarsu a kan dangin Khalipha ne na Hurghada da yadda ta kwaranye tsakaninsu da yake Ibrahim ya san Khalipha step-brother dinsa ne tuntuni.
Shima ba Mami ce ta gaya masa ba Uncle Yohan ne, amma bai taba nunawa Khaliphan ya sani ba, don ya san Khalipha bai sani ba. Sun hana shi kwana a otel yana dakin saukar bakin gidan Khaliphan.
Mimtaz duk da nauyin da ta yi ba ta kwanta ba, girke-girken Egyptians kala-kala take shiryawa Ibrahim, irin su Kushari, Mulukhiyah, Ful-Medames, Fatta, Feseekh da Tarokolacasia Soup da sauransu.
Kuma Ibrahim din is appreciating ya samu canjin yanayi, canjin abinci da canjin atmosphere. Ya rabo da kankara da dusar ta. Haka kawai cikin ransa ya ji ba zai iya komawa Chicago ba, weather din kasar Nigeria ta yi mishi dadi.
Sanyin is not too much da an sa rigar sanyi ko an rufa da bargo shi kenan, zafin idan kana da A.C a gidanka da motarka da ofishinka, to ba za ka san ana yin shi ba ma.
Rayuwar Khalipha da iyalinshi ta burge shi, ta kuma kara kwadaitar da shi son aure. Goyo ne kawai Khalipha baya yiwa Mimtaz, ko abu zai bata sai ya russuna, ko faranti ta dauko sai ya mike da sauri ya amsheta ya hau fada kamar zai ari baki shi meye amfaninsa?
Girkin ma da take yi kusan shine ginshikin aikin, illa tana instructing din sa tana zaune daga kujerar da ya kafa mata a kicin..... zuba kaza adadi kaza yanka kaza..... fere kaza ka zuba....... to motsa shi sosai ya hade jikinsa...... cakuda shi da wannan, markada wannan ka juye a ciki..... haka dai har a gama.
Ibraheem na jiyowa daga falo yana ta dariya, duk da bai fiya yinta da tsayi ba. Lallai soyayya ta yi, don dai shi bai taba ganin kafar Khalipha a kicin ba tun tasowarsu, don Mami ba ta saka su.
Amma yau ga Khalipha ya zama kwararren Egyptian-chef (kukun-Masar) saboda iyalinsa, ya sha Apron da zungureriyar hular Larabawa ta girki, Apron din ma fari ne tas irin nasu suka taho da abinsu daga Hurghada.
Ko ofis Khalipha ya tafi baya barin kunnuwan Ibraheem su huta da waya, wai ya leka ya gano Mimtaz kada nakuda ta zo basu sani ba.
Haka zai yi ta zarya daga dakin baki zuwa falon Mimtaz don cika umarnin babban yaya, ya ganta tana waya da carkwadeden Larabcinta ko tana cin abinci ko tana kallo ya koma ya gaya masa.
Ranar da zai koma Kano wato ranar da ya cika sati guda a Abuja, ko da yake zaman shi a Abuja da dadewarsa cikin ta, ba wai kawai saboda Khalipha bane, transferring komai nashi yake yi daga Chicago zuwa Nigeria.
A ranar da ya samu wayar Mami wato ranar da ya cika sati guda inda take sanar da shi Daddy ya dawo, a ranar ne Mimtaz ta haihu, yaro namiji kamar Mami ta yi kaki ta tofar ko farin iyayen bai debo ba, lafiyayye katoto sai suma mai yawa da ta cika kansa.
Ibraheem ne ya karbi haihuwar har dinki shi ya yi mata. Ko asibiti sai daga baya suka je aka duba lafiyarsu itada jaririn komi normal, suka sallamo su gida bayan an yiwa yaro takardar haihuwa. A daren ranar su Khaliphan ma tareda su gaba daya suka kamo hanyar Kano duk da magariba ta yi.
Gudu yake shararawa dasu a kan titin da zai kawo su Kano daga Abuja cikin lafiyayyar motar Khalipha‘Ferrari has come....., shi ya zama direba domin Khalipha na kankame da jaririnshi a baya ya hana Mimtaz da jaririn sakat wai lallai sai ta yarda jininsa ya fi nata karfi, da kamar Mami ce ta haife shi
Ita dai Mimtaz murmushi take saboda tana kunyar Ibraheem,saboda bata saba da shi ba, har rokon Khaliphan take yicikin Larabci don Allah ya matsa gefe Uncle Ibrahim na jinsa.
Ya ce, “An ki a matsa din”. Da turanci yadda Ibrahim din zai ji sosai.
“Idan ya yi zuciya ya kwato matarsa daga duk inda Daddy ya boye ta shekara mai zuwa su haifi nasu babyn, in yaso ya matsa gefen daga jikin matarsa”.
Shi dai Ibraheem murmushi yake yana jinsu yana tukinsa cikin nutsuwa, cikin ransa yana cewa, “Au boye matar tasa Daddy ya yi?
To shi ina ruwansa in ya ga dama ya ba shi in ya ga dama ya hana baya cikin matsuwa a kan wannan auren da Daddy ya yi masa da bai san da sunan da zai fassara shi da shi ba, left or right (hagu ko dama) duk ta inda Daddy ya bullo dashi ta nan zai karbe shi.
Sai dai Allah yasa ba mai ragunta bace irin Mimtaz, ihu da kururuwar da ta rika yi lokacin haihuwa ya rika tunawa. Da ya dauko allura ya zarga zaren dinki ta tabbatar dinketa zai yi kamar kwarya, ai sai ta gyagije ta daka tsalle ta fado daga gadon kamar ba ita ce katoton Da ya fado daga jikinta ba yanzunnan.
Tayi bayan Khalipha tana kururuwa sai da suka hadu shi da Khaliphansuka sa mata karfi tukunna.
Tunnin da yake ta yi kenan yana murmushi shikadai yana jin shakiyancin da Khalipha ke masa.
“Ya daina cika miki ido kina daukar shi maigida sama dani, duk wannan tsare gidan nasa za ki yi mamaki ranar da za ki je gidansa ki ganshi yana wanke-wanke da canzawa baby diaper. Hura hancinsa ya daina razanaki irin su in sun tashi tasu soyayyar Alkur’an mata suke komawa”.
Mimtaz ta rufe baki cikin kidima ta toshe masa baki da lallausar tafin hannunta,
“Ka yiwa Allah ka yi shiru Yaya Khalipha, akwai girma da kimar Dacta Ibraheem da yawa a idaniyata”.
Khalipha da Ibraheem basu san sanda suka sa dariya ba saboda yadda ta yi maganar tsakaninta da Allah da darajjawa mai yawa cikin murya da idanunta.
Sun shigo Zaria take tambayar Khalipha cikin rada,
“Matarsa baka ce ko fara?”
Allah ya yiwa Ibraheem ji mai karfi, saboda cin gasasshen nama, don haka Mimtaz ba ta san ya jita ba.
[12/25/2019, 19:13] Takori: Khalipha da ba a sirri da shi ya kara rungume wankan tarwadan jaririnsa ya ce da karfi yadda Ibraheem zai ji,
“Yadda yake baki, haka take baka sidik. Aradun Allah nawa jaririn zai washe kwana biyu idan ya fara shan nonon farar mace, amma ‘ya’yan IBRAHEEM da RAYHANAH sai an rufe ido don muni. Ni wannan yaron ma ba don ina son mai da shi little Mansur ba, ai Ibrahim zan sa masa tunda ya nuna min da shi yake uban ba dani ba”.
Ibraheem bai tofa musu ba.......ya yi nisa a cikin tunanin kalmar da Khalifa ya ambata......
RAYHANAH! RAYHANAH!! RAYHANAH!!! A ina ya taba jin wannan sunan????????
So Khalipha na nufin sunan matarsa Rayhanah.... kamar ya san sunan..... tabbas ya taba jinsa.....amma a ina? Ba zai iya tunawa ba.
Shekaru masu yawa sun shude, abubuwa da yawa sun shude, wasu kuma da yawa sun shigo in one’s life journey of struggle toward achievements........ ya takurawa kwakwalwarsa da umarnin ta tuno din, amman ga dukkan alamu ta kasa! Sabida yawan sababbin abubuwa da al’amuran da aka dura mata cikin shekarun da suka gabata din.
A dai-dai garin Tiga sitiyari ya kwace masa motar ta yi jeji....... cikin wani mugun zafin nama ya kama akalarta ya maida ta kan titi. Dukkanninsu sai da suka jirkito don ma Allah yasa da belt a jikinsu. Sannan yadda Khalipha ya kankame jaririnsa bai kankame Mimtaz haka ba.
Wuta ta daukewa Khalipha da matarsa, tabbas yau sun ga mutuwa kusa. Sai Khalipha ya sassauta murya ya ce “Man! Am not ready to die now. Life began at fourty....”
Murmushi ya yi, wani irin murmushi mai nufin amsoshi da dama ga statement din Yayansa Khalipha. Shi kansa ai bai son mutuwar yanzu, gara Khalipha tunda shi har ya ajiye mai yi masa addu’a. Shi me ya cimma a rayuwar? Just his proffession......
Akwai sauran bukatun sa masu muhimmanci bayan wannan..... SOYAYYA..... AURE.... ‘YA’YA.... TARBIYYAR ‘YA’YA..... son binciko hakikanin ko wace ce JUMAH!. A kalla ko ya karbi auren da Daddy ya ke ikirarin yayi masa, yayi alfarmacikin dimbin alfarmominsa da basa karewa agareshi, ya kara masa da ita.
Muryarta kawai ya ji.... amma ta tabo wani al’amari mai girma a can tsakiyar zuciyarsa. Zai iya hakura da son bakin Sapna, ya kara da JUMAH NURSE.
Wata bakuwar halittar da bai taba gani ba data shigo cikin rayuwarsa in an era of global communication...... (waya), ga auren iyaye mai albarka, ga kuma na son rai, wanda zai karairaya akidar nasara ta zama da mace daya dake zuciyarsa zuwa karbar na sunnah (polygamy) na Musulmi, musamman Bahaushe.
“To an taba son mace ba a ganta ba Ibraheem?”
Zuciyarsa ta jefo tambaya. “Eh.....”
Shima ya ba ta amsa.
Akwai wani abu “Soyayyar zuciya” da ba ido ne yake gani ba. Ita wannan soyayyar Allah ne yake yin dalilinta ba ido ba, wanda ke gina tashi soyayyar akan kyawu ko (personality). Wato kyan mace da yadda Allah ya suranta ta ko halinta da dabi’unta.
Shi soyayyar zuciya kuma, zuciya ce take so da gangar jiki gaba daya. Wasu daga cikin physical parts (bangarorin jikin dan adam wadanda Allah ya halicceshi dasu) su suke so ba ido ba........ sune.....
- ZUCIYA (tana son kullum ta yi ta tunanin wannan mace).
- KUNNE (yana so kullum ya ji muryarta).
- HANNAYE (suna so su kai kansu gareta).
- BAKI (yana so ya sumbace ta)
- KWIBI (pelvic girdle) zuwa kafafu (suna so suyi exceptional tarayya ta har abada da ita (sexual need).
-Dr. Norman Vincent Peale
(American Psychologist)
-SegmundFreud (Sociologist/Psycho-Sexual Analyst....)
Wannan shine tunanin Ibraheem, tunanin da ya kusa shekawa dasu jeji su karairaye da dan kyakkyawan jaririn da Allah ya basu.
Suka dauki buri mai yawa suka dora a kansa, musamman hope din ya gaji suna da halin mutum mai daraja da martaba a garesu (Muhd. Mansur).
Karfe tara na dare suka shigo Kano suka doshi Lamido Crescent. Malam Dahiru ya wangale musu kofa suka shiga.
Daddy, Mami, Jawahir, Abida (babu Azizah) suke cin abincin dare tare bisa tebir cikin raha da annashuwa mai yawa wadda su kansu sun mance tun yaushe rabonsu da hakan, a kalla za su iya cewa, tun kafin Khalipha ya ce yana son Rayhanah, soyayyar da ta wargaza musu gida da duk wani farin cikin dake cikinsa.
Ibrahim Mansur da Khalipha Abdullahi Mansur Takai, Matasan Maza masu wata irin baiwa ta zati da kamala da wani kwarjini na daban daga Indallahi, suka yi sallama cikin muryoyinsu na kasaita, Balarabiyar surukar na biye dasu, Ibraheem rungume da jariri.
Gabadaya daga ‘ya’yan har iyayen mikewa tsaye suka yi, suka gigice suka rikice da murna. Yau ga Yaya Khalipha ga Ya Himu......... ga baby da rabon da su same shi cikin gidansu shekara a kalla goma.
Rige-rigen karbar baby ake tsakanin ‘ya’yan da iyayen, ba wanda ya bi ta kan bakuwar fuskar sai Jawahir, ita ta nemota ta rungume, ta yi mata jagora zuwa tebir dinsu tana zuba mata lemo.
Sai da kowa ya dau baby sannan hankali ya dawo kanta. Daddy da Mami “Sannu Mimtaz”. Suke jera mata ba kakkautawa, kanta a sunkuye tana dan murmushi. Ai a take Mami ta mike ta soma shirin jego, abincin da ba ta ci ba kenan.
Su gidansu basu gina shi da safayan daki ba, don basu bukatar bakin kwana. Don haka Mami a dakinta ta sauki Mimtaz. Nan da nan ta yiwa kuku waya ya zo, ta lissafo abubuwa masu yawa na fannin kayan abincin da mai haihuwa take bukata.
Ta hada mata ruwan dumi da dettol ta sanyata a ciki, ta dauki baby ta soma wanke shi sai da ta yi sabi uku tana canza ruwa. Ta shafe shi da olive oil ta sunke shi cikin kayan sanyi farare kal masu kamshin turaren baby mara karfi.
A sannan ne bawan Allah ya soma atishawa. Mami ta hau fada,
“Hala A.C kuka kunna a motar ko tagogi