Showing 18001 words to 21000 words out of 24347 words
a gaba ba, na yi na yi ki koyi operating din waya da kanki kin ki saidai ki dameni in kira miki wannan in kira miki wancan, yanzu sai ki yi zuciya ki koya”.
Duka Inna ta kai mata ta fice da gudu tana dariyarta. A haka suka rabu yau.
Ta mike ta ci gaba da tafiya a gefen titi a hankali don yunwa take ji sosai, ledodi da hand bag dinta kamar ta watsar dasu don nauyin da su kai mata, musamman kwalin kazar Inna kaji biyu ne a ciki. A haka ta daure ta ci gaba da tafiya at the same time, faduwar gabanta na kara tsananta.
Ba wata kwalliya ba ce a jikinta, amma da ka ganta kai tsaye za ka kirata black-American. Shigar jikinta usul shiga ce ta matan Singapore (Belted-Waist-Shirt) dark blue mai dogon hannu. As a Muslim, sai ta sanya bakin dogon wando a ciki, ta kuma sanya karamin hijab na Larabawa a kanta wanda ya tsaya iya kafadunta.
Also kayan jikin nata are not expensive.....kuma basu nuna komai na jikinta ba, daka ganta kasan Musulma ce cikakkiya. Singapore is very modern but dressing very sexily will not be acceptable in certain places.... don haka matan kasar musamman musulmin can basu fiya yin shiga ta tsiraici ba balle ita Rayhanah.
Kafafunta rufe cikin bakin cover kuma flat takalmi Melissa (brand din ZALORA). Rahane ba zuwa take ta sayo kayan nan ba, Dr. Mansur ke zuwa ya sayo da kansa a shaguna duk zuwan da ya yi ya zo ya zube mata su, illa dai yana karbar size dinta har ya rike. Zamanta cikin dalibai ‘yan’uwanta musamman haifaffun Singapore shi yasa yau da gobe ta iya shigarsu.
Fuskarta ko powder (hoda) babu, haka lebbanta babu danshin mai, but they are soft and supple kamar tana basu wani extra care ne, amma babu ko daya. Babu gumi a fuskarta, fuskarta tas fresh and choculate. Ba ta da dogon hanci, gashin nan dai dan madaidaici a tsakanin idanunta. Gashin kanta a tsefe yake, baki mai karfi amma ta matse karshensa da ribbon, hakan bai hana ya yi dan tudu ba, da yake ba ta taba sanya masa relaxer ba, haka yake da karfi kamar reza na asalin Hausawan Kano jikokin barbushe da tsimbirbira.
Da wannan shiga, da wannan fuska, da wannan yanayi Rayhanah ta danna kararrawar shiga falonta.
*****
Wanda ya bude kofar wani matashi ne baki mai tsayi sambal, mai wasu irin idanu masu lumshewa da kansu, da budewa cikin nutsuwa cikin umartar kansu da yin hakan, cikin kwayar idonshi akwai wani abu mai sheki kuma ba farare ne tas ba, ga dogon hanci kamar Dacta Mansur, fatarshi ta nuna haifaffen Nigeria ne, gashi nan kamar Dr. Mansur (choculate in complexion), duk da Dr. Mansur ya fishi haske.
Ya tara suma mai dan tudu a kanshi, ba kuma nannadaddiya ba ce ta ‘yan asalin Northwest-Nigeria ce wato mai karfi, amma ta sha taza ta sha mai mai tausasa gashi (ArganaVita) da ba a samun shi sai a kasashen ketare.
Sanye yake da farar shadda kal hilton dinkin Mohammed, rigar ta kusa kasa sai wandon a ciki, kanshi babu hula, daure a damtsen hannunsa agogon ‘Calibre de Cartier’ ne da ya kwanta cikin tattausar fatar hannunsa wadda lallausar bakin gashi ya kwanta a ciki.
Babban abin jan hankali a halittarsa, wannan tsagar bakin nasa ne da bakaken lebbansa marasa kauri, sai kuma lallausar sajen da ya kwanta a gefen kunnuwansa bai iso habarsa ba, wadda dan lotsawar nan na tsakiyar haba (cleft) ya bayyana a fili ko da bai motsa bakin don cin abinci, dariya ko yin magana ba.
Kallon-kallo ake tsakanin Rayhanah Rashid Takai da matashin da ya amsa sunan Ibraheem Mansur. Kallon da bai da ma’ana at all. Kallon da kai tsaye za ka fassara shi da kallon zakuwa a tantance juna kawai, ba na so ba, na kauna, ko akasin haka ba, kawai ‘eager to see each other,’ kuma ba tare da sun bar kallon ya tsawaita ba tunda ko da kalma ba ta shiga tsakani ba kowa ya gane kowa, kuma kowa ya yi ‘quenching’eager dinsa.
Don haka Rayha ta yi saurin sadda kai wani abu yammmm! Na bin ilahirin jikinta, wanda ya fi karfin tashin tsigar jiki sai circulating din jini abnormally da yadda ya saba aiki, domin bukatarsa nason ya isar da sako ta kowanne hali (by all means) daga zuciya zuwa cikin gangar jiki da kwakwalwa.
Duk wadannan mintunan da suka kwashe a tsaye, Dr. Mansur da Inna na kallon su, addu’a kowannensu ke yi cikin zuciyarsa Allah ya daidaita. Cikin Dr. Mansur ya fi na Inna Juma durar ruwa, idan Ibraheem ya ce Rayhanah ba ta yi masa ba ina zai sa kansa? Amma ga HIMUN, abin ba haka yake ba.
Kallon da ya yi mata na farko, eager look ne na neman tantancewa da kauda curiosity. Amma as his eyes enter her’s much more deeply..., (da kwayar idanunshi ta shiga cikin tata sosai), kokari kwakwalwarsa ta shiga yi wajen farfado masa da shekaru goma sha daya a baya.
Tabbas ya san fuskar, yasan wadannan idanun masu rauni da sanya kasala, ya san ‘yar yarinyar nan ce RAHANE, data shigo cikin rayuwarsu daga asibitin Malsm Aminu Kano, mai kula da ubanta a bargar dawakin Hakimi, mai yiwa ubanta wanki, yanke farce da taya shi feeding horses (baiwa dawakin Hakimi Abdulqadir abinci).
‘Yar yarinyar nan ce da Daddy ya dauko daga Takai..... wadda ta rasa jinta dungurungum, ‘yar yarinyar nan ce mai amfani da HEARING AID....... wadda ta sa shi barin gida ba don ya so ba, sai don ya ceci kansa ya ceci zuciyarsa daga fadawa soyayyah a inda bai dace ba, a kuma lokacin da bai kamata ba.
Yana ‘referring’ kowanne ‘motion’ na zuciyarsa a kanta da KARYA........ bayan kuma sau tari tsoron kar zuciyarsa ta ce ya yi karyar yake kidima shi ya yi mata KARYAR......
Ya bar gida saboda kar zuciyarshi ta wulakantashi da kauna da soyayyar kwaila ‘yar kauye mai lalurar JI, hade da wasu ‘extraordinary charismatic features’ (baiwarwaki da karama) da ake kira ‘Rahane.’ A girl with a great mind!
To yaushe ta koma RAYHANAH? (Daddy ne ya canza mata suna), zuciyarsa ta yi saurin tuno masa........
“Mene ne sunanki......?”
“Rahane”.
“Rayhanatu kenan ko?”
“A’a, Rahane.......”
“To ni ba zan iya kiranki Rahanen ba, don baida ma’ana at all sam-sam....... Rayhanah....!!!”
Ya tuno tattaunawar farko da mahaifinsa ya yi da ita a ranar da ta fara samun kanta daga hatsarin da suka yi, a kuma ranar da Baban da abokinsa Dr. Imam suka makala mata ‘hearing aid’. As soon as da suka fahimci she's hearing impaired!
Kafin Rayhanah ta ankara Ibraheem ya kai hannu gareta ya cire hijabinta yana duba kunnenta da bayan kunnen, babu komai sai dan karamin dan kunne mai barima na farin dutse. Ta saki ledodi da jakar hannunta kasa saboda razana.
“Where's your hearing aid?”.
Abin da ya tambayeta kenan da wata murya mai sanyi, harshensa da accent dinsa (American), wato na Amurka ba na Birtaniya da ya fi saukin furtawa ba.
Hannuwanta biyu ta kai kan nata tana son rufe gashinta da ya tsiraita. Sai ya russuna yana kwashe mata ledodin ta da jakarta da ta zubar ya bata hanya tareda yi mata alamar ta wuce, sai ta rabe ta gefensa ta shige ciki.
Babu kowa a falon, Inna da Baba Dacta sun shige kicin tun sanda Ibraheem ya cizge hijabin Rahane.
Ai ganin ba kowa a falon sai ta kara da gudu ta yi dakin barcinta ta rufo kofar ta jingina da ita tana numfarfashi kamar wadda ta yi gudun mita duba. Idanunta ta lumshe tana ambaton
“Yaa Wahhabu......... Yaa jamilal munzarrr (Ya mafi kyawun masu gani)!”
Ya Himu ne, tabbas shine....Daddy ya kinkimo ya kawo mata tana zaman-zamanta lafiya, ita ina ruwanta da wani Ibraheem. Tun can bai son ta, kyankyaminta yake, kalma wannan ba ta taba shiga tsakaninsu ba tun saninta da shi a gidan Dacta Mansur, kawo barinsa gidan don ba ta ishe shi ko da kallo ba.
Ita fa wannan auren kawai ta dauke shi suna ne, biyan bukatar ran Daddy bata taba tunanin zai zama reality ba.
Ta yi zaton haka za ta kare rayuwarta cikin kwanciyar hankali da neman ilmi da taimakon Babanta Mansur da Innarta Juma. Ba ta taba kawowa ranta Ibraheem din zai shigo cikin rayuwarta ba.......
Ta shiga uku....... wannan gundamemen Ba-amurken ne mijin nata da har Inna da Baba Dacta za su fita su barta da shi a gida akan saninsu? To tace masa me? Ko tayi masa me? Tayi yaya da shi?
Watakila ma dubawa ya yi in da hearing aid ya ce baya son ta. Duk Khalipha shi ya janyo mata....... da sunyi aurensu na so da kauna da ganin mutunci da kimar juna ai da Daddy bai yi mata AUREN HUCE HAUSHI da Ibrahim ba.
Sai ji ta yi hawaye na bin fuskarta. Bokon nashi har ya zarta misali, tsoro yake bata, kwarjinin shi razanata yake, ba ta san inda Daddy ke nufi ta kai shi a matsayin life-partner ba. Wannan gandamemen baqin bature haka wanda zai iya hadiyeta baki dayanta?
Ya yi biyun Yaya Khalipha a girma da tsayi, ba wai kiba ce da shi ba (physique).
Kuma ita bata taba yiwa kanta sha’awar rayuwa da wani Da namiji ba bayan Khalipha, shine dai-dai ita, domin ta kowanne bangare bai tsaurara ba...... ga boko ga addini, ga simplicity bai dauki kansa a bakin komai ba.
Rana daya wannan iftila’i ya ratsa, ta karbi zabin Daddy don biyayya da yakinin da take da shi na cewa a haka za su kare rayuwar tasu ita da Innarta da Daddy Ibrahim ba zai zo ba. Yau gata ga IBRAHIM MANSUR TAKAI.
Kokarin bude kofar ake, kofar da take jingine a jikinta. Ai da ta yi wata zabura guda daya sai ganinta ta yi a toilet dinta na bedroom ta kulle kanta.
Inna ta shigo tana cewa,
“Yau na ga abin da ya isheni ni Juma, mijin kike gudu haka? Lallai kin hada kanki da aiki.
Fito ki ci abincin da kika siyo shi Ibraheemu ma ya dade da fita a gidan nan.......”
Ai kuwa ta bude kofar ta fito idanunta sun ci kuka sunyi jawur. Haka Inna ta yi ta lallamin ta don ta ci abincin, amma ta kasa cin abin kirki duk soyayyarta da ‘wontonmee’ da ‘chili crab’. Ga Inna ba ta iya cin wannan cakudedeniyar ba, barta dai a KFC (Kentucky Fried Chicken).
Sai ta tattara ta zuba mata a firij tana ta mita.......
[12/27/2019, 11:51] Takori: “Kuma shi kenan don Allah ya amsa addu’armu Ibraheem ya zo, sai ki kuntatawa kanki?
Tun safe baki yi karin kumallon kirki ba kika fita, na kuma tabbata a can baki ci ba, kin sayo abin dadin ki rimi-rimi sai ki ki ci Rahane?
Haba Rahane, an Rahane na! ‘yar gidan BABANTA!! Kina son Uba kina gudun Dan sa, anya an taba yin haka?!!!”
Hawaye suka fitowa Rahane surrrrr...! Har daga cikin hanci, cikin dakushewar murya mai cike da kuka ta ce,
“Inna ni dai na fi son Yaya Khalipha.......”
Sai bammm! Inna ta buge bakinta da hannun ta,
“Kina auren wani kina cewa wani kike so? Maza-maza ki yi istigfari. Wanene Yaya Khalipha kuma? Shashashar banza, irin wannan zabgegen miji haka na likawa a goshi?
To ni ina son sa ki bar mini, ki ga yadda zan killace abina a daki kada wata ta tayi min kwace...... idan baki godewa Allah kin godewa Baba Likita ba, to za ki ga ba dai-dai ba a rayuwarki wallahi Allah ki dawo cikin nutsuwarki.
Haba an Rahane na? Ibraheem mai kyau da shi? Mai tarin ilmi. Daga yi min allura ya bani kwayoyi na sha na nemi ciwon bayan dake damuna na rasa.
Ubangiji ya ce idan bamu godewa rahamarsa ba, la-shakka zamu godewa azabarsa.
Ki nutsu, ki manta da wani Khalipha Rahane ki karbi mijin da Allah ya baki.
Shi bai ce baya son ki ba, bai kamata ke ki fadi hakan ba. SO na Allah ne, shi ke sanya shi a tsakanin bayinSa.
Je ki ki yi wanka Rahane, ki yi kwalliya ki tarbi mijinki, ki yi kwalliyarki ta ‘ya’yan Hausawa ya san cewa tushensa ya aura. Tashi maza ki cire shirmen nan na jikinki ki yi wanka.....”
Rahane ta katseta cikin kuka,
“Ni wallahi babu wankan da zan yi, da can bana wanka sai don ya zo? Kuma ai gidan nan babu dakin da zai sauka in ba naki za a ba shi ba ina zai je?”
Inna dai lallami take don haka ta gintse dariyar da ta cika mata ciki, ta ce,
“Na ji na ba shi nawan ni zan kwana a falo, ai ko wadannan lausasan kujerun sun isheni in yi barcina har da saleba. To canza kayan tunda ba za ki yi wankan ba.......”
Ai kuwa ta rantse ba abin da za ta yi a ciki. Ran Inna ya soma baci, ta tashi ta rabu da ita ta shiga kicin don yin abincin da Daddy ya ce ta yi musu kafin su dawo, ta barta nan ta sanya kai cikin kafafu tana ta kuka.
Ta gama kular da Inna, don haka ta fita sha’anin ta har ta gama girkinta ta jera a dining dan karami na mutum biyu (mai kujeru biyu kacal) dake can gefe a falon. Duk shiga da ficen da take sai ta ganta yadda ta barta, zuwa lokacin kuma ta gaji da kukan ta yi shiru, sai ajiyar rai take.
Kararrawar kofa ta soma kara, ai kuwa ta yi fit, ta yi dakinta kamar filfilwa. Inna ta bude kofa, Ibaheem ne a gaba Daddy na bayansa, dukkansu rike da manyan ledojin cefanen da suka yiwowa Inna na African-Food.
Da hanzari Inna ta amshe su tana musu sannu da dawowa. Sai a lokacin Ibraheem ya dube ta sosai, sai ya gane ita ce Juman da Daddy ya nuna mishi hotonta. Sai ya yi murmushi. Ya ce a ransa,
“Lallai yarinyar nan ja’ira ce, wato ita ce Juman”.
Da yake sun yi sallar isha’i kan su shigo a wani masallaci, dining suka hau suka soma cin funkason Inna da miyar ganye da aka yi da manja da kaji zuku-zuku a ciki. Loma biyar Baba Dacta ya kai ya dakata ya soma kwalawa Rayhanah kira.
Ai ji ta yi hanjin cikinta ya nannade waje guda ta kara kudundunewa a cikin bargon ta. Kira har sau uku ta ki amsawa. Sai ya ce,
“Ibraheem je ka zo min da amaryar nan taka. Na lura yau surukuta take yi dani, ko gaisheni ba ta yi ba”.
Ya fada yana nuna masa dakin. Kamar ba zai je ba, ko tunanin me yayi sai kuma ya tsame hannunsa daga plate dinsa ya ciri tissue ya goge, ya sha ruwa sosai sannan ya mike ya nufi dakin.
Murda kofar ya yi ya shiga dakin, tana can karshen gadon ta kudundune cikin blanket mai bala’in taushi kamar curin alkaki, dariya ta kama Ibrahim, gata a Singapore amma ashe bagidajiya ce. Abin da bai sani ba, Rayhanah ko a ina ta tsinci kanta ba abin da zai canza mata akida ko dabi’a, ko al’ada ta kasar haihuwarta.
Ita Rayhanah ba ta yarda da wani abu wai shi wayewa ba, abin da ta sani shine ita musulma ce kuma Bahaushiya, amma tana karatun boko don fita daga duhun jahilci, ba abinda zai canza mata wannan perception (belief). Ba za ta aro wata dabi’a ba wai don ta burge ko a ce mata wayayya, masu yin hakan ma a Informatics Institute mahaukata take kallon su.
Bargon ya kama ya zare shi ta karfin tsiya tana rikewa yana fizgewa ya cillar. Ya zauna a gefen gado ya ce,
“Toh ke Rayhanah kuma haka zamu yi dake? Haka ake tarbar miji? Ko gaisheni baki yi ba Rayhanaah, ga dukkan alamu ma bakin ciki kike da zuwana zan takura miki......”
Shiru kake ji, ta juya bayanta ta cure jikinta.
“Juyo nan, Allah-wallahi kada ki sa in kai hannu jikinki da sunan duka, ko in dauke ki a hannu in kai