Showing 12001 words to 15000 words out of 24347 words
kuka bubbude?”
Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba a kan Himu da Khalipha. A.C din gidan ma kashe su ta yi duka kowa ya hakura, ayi jegon tare da shi. Daddy na ta yi mata dariya da zolaya.
“Ba saban ba! Ni Asma’u na zama kaka”. Ai kowa sai da ya dara.
Da Ibraheem ya ji gumi ya fara jika shi sai ya hakura da cin abincin ya yi ta kansa (ya shige dakinsu tun na kuruciya da samartaka ya kure A.C) ya yi kwanciyarshi yana hutawa, zuciyarshi babu sukuni ko kadan, ta cunkushe da tunani.
To wai ina matar da aka aura masan? So ake sai ya tsaga billensa ya tambaya? Ai da nauyi, Daddy na son ja masa rai ne kawai ya wahalar da shi. Shikuma wallahi tunda haka ne ko za’a shekara bazai tambaya ba.
Shima fa yana so ya ga irin wannan farin cikin da tarairayar a fuskar Daddy da Mami a kan nashi iyalin. Da ya ga tunanin na damunsa sai ya kira Sapna suka shiga hirarsu, tana gaya masa kewarsa da take ciki, yaushe zai dawo? Kai tsaye ya ce,
“Sapna na dawo gida kenan mahaifina ya yi min aure!”
Wannan ita ce kalma mafi muni da Sapna ta taba ji a rayuwarta. Ji ta yi kamar ya caka mata mashi a kahon zuci. Sai ta fara yi masa kuka mai girgiza zuciya, ya yi saurin kashe wayar, domin ji ya yi banda ya rungumeta ya rarrasheta ba abin da yake so ya yi.
Ya soma tambayar kansa anya Allah ba zai tuhume shi da hakkin Sapna ba? Ya riga ya mai da ita emotionally disturbed zai yi wuya ta iya fiddashi daga rayuwarta farat daya.
Shima zai dade bai mantata ba a sabuwar rayuwar da ya bude yanzu. Yana rokon Allah ya yafe masa itama ta yafe masa a kan turbar da yasa Sapna, ya gudo ya barta.
Duk da ya san bai taba keta mutuncinta ba, amma yana rage zafi da ita. Ita kuma tana ba da kai ne saboda son da take masa, da kuma tabbacin da take da shi na zai aure ta.
‘Yan’uwana mata musamman ‘yammata ku gane, ku hankaltu kusan irin sarrafawar da za ku yiwa soyayyar saurayi a zuciyoyinku, don maza, musamman yara irin Ibraheem masu tashen naira da kuruciya da zurfin ilimi, wallahi ba kowacce mace suke aura ba, sai innocent.
Za su yi soyayyar wucin-gadi dake ne kawai don amfanin kansu a dan lokacin da suke bukata, in sun gama abinda ya kusanta sure dake su tsallake su barki su nemi ‘yar mutunci mara kyale-kyalen duniya da budadden ido su aura. Yarinya danya jagab wadda ba ta kai shekaru ashirin ba ke kuma (used and dumped)Sunanki.
“Bye-Bye Sapna........!”
Ibrahim ya fada a hankali, wasu hawayen tausayi da sabo cike da idanunsa. “Ni da Illinois (Chicago) watakila sai da yawo”. Abin da yake fada cikin zuciyarsa kenan.
*****
Jego sosai Dr. Asma’u ke wa Mimtaz, tana gasa mata jiki da tawul kullum sau hudu a rana, ta sanyata a ruwan dumi sau uku. Har edcuse ta dauka a wajen aiki don an maida ta Murtala Mohammed Specialist Hospital kamar yadda ta bukata, domin raba kanta da duk wata alaka da Dr. Halima.
Tana jin yadda ake fadin irin zagin da Haliman ke mata da tonon silili daga bakin Nurses din da suka yi zaman aminci da ita, da mugun alwashin da ta dauka a kanta na sai ta rabata da Dr. Mansur ta aure shi. Wai ita tsohuwar arniyar Jos ce tubabba kuma ba a budurwa Dacta Mansur ya aure ta ba har da dan shege da ta so ta yi kuskuren lakabawa ‘yarta Allah ya cece su.
Ire-iren abubuwan da suka tsorata Dr. Asma’u kenan ta bar AKTH don ba ta iya tashin hankali a rayuwarta ba. Ta soma nemawa kanta tsarin Allah daga sharrin mutum da aljan.
Ta rage barci kullum sai tsayuwar dare duk da dai hidimar baby Mansur ba ta barinsu suyi barcin kirki daga ita har Mimtaz din, ga shi da kukan dare, ya wuni sur lafiya lau yana barci dare na yi ya bude musu murya ya gigitasu, nonon ma ya ki sha sai kuka, har su Jawahir kwana suke a kansa suna miko wannan suna miko wancan.
Dr. Asma’u ta soma bincikensa da kyau, inda ta gano kashi ne baya iya yi da daren saboda tsutsar ciki, sai ta fara treating dinsa da antibiotics masu sa cin abinci, don ko nono da ruwa in dare ya yi baya amsa da sauran magunguna masu kashe tsutsar ciki da narkar da abinci da taimakawa digestive system. Sati bai zagayo ba yaro ya yi ras, cikin koshin lafiya.
Tuni Khalipha ya koma bakin aiki ya barsu a gidan karkashin kulawar likitoci har uku, uwa da uba da brother. Ai kuwa cikin wata daya baby Mansur ya zama garjeje dagawa da kyar, goyawa da dan banzan nishi, domin Azizah da ta zo hutu daga Turkish kasa daga shi ta yi.
Ita ma mai jegon ta zama sambaleliya mul-mul da ita, sai ka ganta cikin su Jawahir ta takarkare wai tana koyon Hausa za ka ci dariya, sun saba sosai, ta soma koyon amma namiji shine mace, mace ita ce namiji a bakin Mimtaz. Sai ta cewa Jawahir “Dauko Mohd Mansur ki canza mata audugar nan (Pampas).....” Sai su kwashe mata da dariya sai da Mami ta tsawatar.
Ibraheem a nashi bangaren, ya zubawa Daddy ido kamar yadda Mami ta zuba masa a kan aurensa. Tunda ya zo ko da subutar baki Daddy bai yi masa zancen matarsa ba, amma fa yana ta janshi a jiki cikin kauna da kulawa.
Ya kuma dauke shi a yau ya sada shi da gidan da ya mallaka masa shi da Khalipha a Farm Center, ya bar dakinsu na gidansu ya koma gidansa, shi Daddyn bai zauna ba har yau ya kwashi takardun Ibrahim ne ya mikasu federal.
Abin da bai sani ba, kuma miskilin dan nasa bai gaya masa ba, shine cewa ‘nephrology associates’ da sauran ‘medical associations’ da yake ciki suna ko’ina a duniya za kuma su ba shi aiki dai-dai da matsayinshi a (Illinois Teaching Hospital) Chicago sai inda ya zaba.
To zaben ne har yanzu bai yi ba, saboda basu zauna da Daddy ba har yau ko ko ya ce Daddy bai ba shi fuskar ya furta masa damuwar tashi ba.
Babu zancen da yake masa sai na aiki kamar wani inji babu hutu babu mata babu budurwa saboda shi karfe ne, kullum ya yi ta hada shi da voluntary jobs wato aikin sa kai na neman lada ga marasa karfi masu cutar koda a Najeriya da basu da karfin fita waje kamar wani inji.
To ya daina zuwa AKTH, Abdullahi Wase, Murtala Mohammed daga yau zai yi kwanciyarsa a gida ya huta, Daddy ya yi ta boye matar zai koma ya auro Sapna. Wani abin dariya Ibrahim ya tambayi Daddy rannan suna kan hanyar zuwa Abuja.
“Plz Daddy wace ce Juma da ta amsa wayata lokacin da ka bar wayarka a office ta amsa kirana?”
Daddy ya ce, “Au Juma? Ai ba a ofis bane na bar wayar a gidanka ne. Ita ta amsa ma wayar?”
Ya ce, “Eh”. Cikin fargaba ya ce da Daddy, “Don Allah Daddy zan iya ganin hoton ta?”
Fuska a sake Dacta Mansur ya ce, “Why not?”
Ya yi parking a gefen titi ya fiddo dalleliyar wayarsa yabude gallery ya fiddo hoton Inna Juma da ya taba daukanta ita kadai lokacin da za a yi mata passport din tafiya Singapore ya nuna masa.
Ibrahim hannu na kyarma jiki na tsuma ya karbi wayar ya duba. Me Ibrahim zai gani? Wata bakar tsohuwa ce da a kalla ta ba saba’in baya, ta sha dauri da Adiko ta kawata idonta da farin kwalli ta yi ras!.
Haba! Ai ba shiri Ibrahim ya jefa wayar Daddy a kan titi yana haki kamar wanda ya tiki gudun cetar rai. Ya ja bakinsa ya yi shiru kirjinsa na ta bugawa..
Daddy ya bude murfin motar ya dauko wayarsa har ta tsage tawargajeakan titi, ya kuwa ce da wa Allah ya hada shi ba da Ibrahim ba. Fadi yake,
“Wane irin wulakanci da iskanci ne wannan? Ba kai ka ce in nuna maka hotonta ba? Don ka ganta talaka sai ka wulakanta hotonta har ka fasa min waya? Ka ci gidanku, ka ci kaniyarka.Wannan tsohuwar mai daraja ce a wajena.....”
Shi dai ya yi gum da bakinsa ya rasa inda zai sa kansa da mamaki da takaici. Tsohuwa ce da muryar danyar yarinya har da Turanci? Saboda bakin ciki har suka zo Abuja bai kara yin magana ba.
A lokacin Khalipha da iyalinsa sun tafi Hurghada har da Azizah da Jawahir da Abida za a kai wa dangi Muhd Mansur su ganshi. Ya iya zama har da kokarin mikewa bul-bul da shi a lokacin watanninsa hudu. Kamanninsa da Mami da duhun fatarsa basu canza ba da ka ganshi ka ga half caste, very cute da shi.
Yau kwanan Ibrahim Mansur goma a gidansa na ( Farm Center ) wanda ya yi dai-dai da cikar sa watanni na hudu a Nigeria, bai taba damuwa da wai ya shiga daki-dakin dake a kulle ya ga yadda suke ba, iyakancinsa ya shigo ya wuce bed room dinsa ko ya zauna a falo ya kalli labaran tara ko CNN.
Amma a yau Asabar kulle wayarsa ya yi ya kuma kulle kansa a gidan kada Daddy ya neme shi ya hadashi da aikin dashen kodar nan. Shima tashi ba ta da lafiya it's now weak and delicate to such an extent that it fails to perform its normal functions properly, in zasu dasa mishi mai kwari shima yana so. Daddy yana wujijjiga shi, ba don ubanshi ne ma ba cewa zai yi rainin hankalin ya isa.
“I need a life partner, ina sha’awar rayuwar Khalipha, ina bukatar mace, I’m at the Zenith of my thirty (30)”.
Abin da yake fada kenan cikin zuciyarsa, yana daga kwance ciki sofa din dake gefe guda a mayalwacin dakin barcinsa, pjamas ne kawai a jikinsa ruwan toka, wadanda basu rufe faffadan kirjinsa ba. Lallausan gashi ne baki sidik kwance luf a kirjinsa.
A wannan lokacin Ibrahim rufe idonsa ya yi, muryar yarinyar da ta kira kanta da (Jumah) ta soma amsa kuwwa a kwanyarsa.
“Dacta ba ya tare da wayar fah..... Dacta is not yet at office.......”
Ya Allah! Wannan wane irin bala’i ne ya same ni? Dana sani da ban yi maka waya ba....... watakila aljana ce ta yi min magana ta dasa min wannan bala’in. Bari kawai na mai da kaina busy na yi sanitary ko na samu sa’eedah.
Da nashi dakin ya soma, ya canza bedsheet ya hada kayan wankinsa cikin kwando ya turasu laundary ya goge ko ina ya fesa insecticide ya kullo dakin. Yasa injin shara yana zuke kurar (center carpet) dake tsakiyar wawakeken falon.
Yasa duster ya karkade kujerun da plasma da sauran tarkacen kayan lantarkin dake dakin. Sai ya koma daya dakin dake bude wani bedroom din ne shake da kayan wasan yara da gadajensu da study table na yara da katifu, kekuna, babur, toys, teddies da ‘yan tsanoni masu aiki da batir.
Sai ya samu kansa da yin dariya, dariya mai yawa da ya dade bai yi ba, ya kara kaunar mahaifinsa. Komai ma sabo ne ba a fiddashi daga kwalinsa da ledarsa ba, don haka dakin baya bukatar wani gyara amma duk da haka sai da ya sharo yana ya fesa Rambo.
Daki na karshe wanda shine a kulle da mukulli sai da ya yi ta gwada bounch of keys sannan ya samu guda ya bude. A nan ne Ibraheem ya daskare cikin mamaki.
Ibrahim na da masaniyar cewa, wannan gidan da Dacta ya mallaka musu, gina shi ya yi ba sayen shi ya yi a gine ba, don kafin a fara ginin ma sai da ya nemi Ibraheem din da ya turo sample na irin ginin da yake so.
Shi ya turo samfur daga San Francisco da Daddyn ya yi amfani da shi, don haka bai sa ‘yan haya ba. Zai rantse shine mutum na farko da ya fara kwana a gidan, amma wannan dakin ya karyata haka.
Daki ne yalwatacce mai dauke da fararen Italian furnitures, ga bargo ba a ninke ba, ga kayan kwalliya da turarukan mace da su deo-spray a jere a kan mudubi, a gefe ma wasu jakunkuna ne shake da kayan ado na mata sababbi da alama ko sa su ba ayi ba, ga braziya da pantis farare kal an wanke an shanya a bayi (toilet) ba’a kwashe ba, ga su brush da maclean da turarukan wanka har da audugar mata (pad), da alama an cira ne an aje ragowa ba sabuwa ba ce.
Ibraheem kidimewa ya yi da tsoro, firgici da mamaki don ya tabbatar kam ba shi kadai yake kwana cikin gidan nan ba, duk da bai taba jin motsin dan adam a cikin gidan ba. Tabbas akwai aljana a tare da shi, amma fa yana son kamshin dakin aljanar nan idan ma aljanar ce.
Sai ya zauna a bakin kyakkyawan gadon ya dauki bargon yana sunsunawa, kamshin is cool..... sai ka sunsuna za ka ji. Ji ya yi tsoron ya fice daga zuciyarsa, ya samu kansa da kwanciya sosai a gadon ya ci gaba da shakar kamshin yana kara nazarin dakin.
Kaya baja-baja a warwatse ga takalma flat da masu tsini masu kyau da jakunkunansu ‘yan gidan Micheal Kors, Nordstrom, Replica, Cloe da Harrods cikin wata jaka ko sa su ba a yi ba. Ya ce a ransa,
“Cikin aljanun ita wannan ‘yar gaye ce, tunda har irin kayan Sapna take amfani dasu”.
Nan Ibraheem ya lalace a dakin ya kwana, a dakin ya wuni, sallah ke ta da shi da shaye-shayen lemuna da madarar dake dankare cikin firjin dake gefen gadon. Sai da suka nemi karewa yaje store da zummar karo wasu.
Tunda ya zo gidan ma bai leka kicin ba, don a koshe yake shigowa barci kawai ke kawo shi sai ruwa da jus da madara yake sha a nashi dakin. A kicin din ma ya kara tsinkewa da lamarin aljanar gidansa. Tukwane a wanke kal-kal an kife su komi tsaf, amma fa ga potatoe ya rube har ya yi tsutsotsi yana ta wari har ya soma busar da kansa.
Da ya bude firij sai ya ja da baya cikin dan tsoro yana fadin “Subhanallahi.....!” Kifi ne, nama ne, markade ne, kaji ne duk gasu nan sunyi kankara sun kankare kamar duwatsu.
Ai da azama ya fito ya bude kofofin da ya kukkule ya zari mukullin mota ya yi asibitin da yake gudu don ya gayawa Daddy ba zai zauna gida daya da mutanen boye ba. In ba zai barshi ya zauna kusa da uwarsa ba to zai koma inda ya fito.
Daddy yana seminar-room da likitocin bangarensa gaba daya wadanda suke karkashinsa, meeting suke yi mai muhimmanci a kan sabuwar cutar da ta iso Nigeria ‘Ebola’.
Ibraheem ya fado dakin tattaunawar babu ko sallama, kwarai a firgice yake kira yake
“Daddy-Daddy.....”
Gaba daya likitocin sama da talatin suka maida hankalinsu da idanunsu gare shi. Ba ta tasu yake ba sai da ya isa jikin mahaifinsa ya rungumeshi jikinsa yana kyarma yana fadin
“Wallahi ba zan koma gidan nan ba, in ba auren za ka bani ba to zan koma Chicago, I’m exetremely perplexed.......”
[12/26/2019, 13:19] Takori: Hannunsa Dr. Mansur ya kama sannan ya manna shi a jikinsa ya dauki excuse suka fito yana jaye da hannunsa yana yi masa magana cikin lallashi.
“Kwantar da hankalinka gaya min me ya faru?Ka ji Ibrahimu?”
Ya rungume shi sosai a jikinsa don ya samu nutsuwa, yana jin yadda yake sauke numfashi da sauri. Sai da ya nutsu ya ce, “Muje kawai Daddy ka gani da idonka”.
Daddy ya ce, “Ba zai yiwu ba, baka ganin meeting muke yi”.
Ya ce, “To bari in jiraka a ofis dinka ka je ku gama”.
Ya ce, “Alright”.
Mintuna arba’in Dr. Mansur ya yi kamin ya dawo. Shi ya karbi tukin suka nufo Farm Center, Ibraheem ya kame bakinsa ya yi shiru. Daddy ne ya bude gidan da kansa don Ibraheem baya-baya yake yi.
Ya kama hannun Daddy zuwa bedroom din ya shiga nuna masa.
“Ka gani, ka gani....... akwai spirit a cikin gidan nan”.
Yana nuna masa