Showing 27001 words to 30000 words out of 33748 words
bayanta yarigata zuwa gurin mota hakan yasashi yana isa ya buɗemata murfin motar har tayi niyyar wucewawarta taga idanun mutanen gurin gabaki ɗaya yadawo kansu hakan gefe guda kuma wata zuciyar tace mata"kishiga har yanzu kina ƙarƙashin ikonsa tunda baku tashi daka gurin aikiba".
hakan yasata jiki a sanyaye ta shiga ya mayar ya rife ya zaga yashiga mazaunin driver yaja motar suka bar gurin yana fita daka get ɗin gurin ya cilla hancin motarsa titi ya ware a.c ɗin dake motar ya kunna karatun Alqur'ani megirma ƙira'ar Sudais tashiga tashi a cikin motar suratul Muhammad ba tare daya ƙara bi takanta ba yashiga bin ƙira'ar da daddaɗar muryarsa me daɗin sauraro .
Ɓangaren Inteesar ko juyar da kanta tayi tana kallon titi hakan datayine yabashi damar ƙarewa fuskarta kallo ɗan motsawa tayi hakan yasashi saurin ɗauke kansa daga gareta cikin nutsuwa yake tuƙi ganin hankalinsa ya karkata akan tuƙin taga ya nufi hanyar cikin gari da ita saurin kallonsa tayi gani tayi ya wani make kamar besan metake nufiba sosai ranta yakai ƙololuwar ɓaci da abubuwan da yikemata ta aro jarumta cikin tsiwa tace"Malam ajeni anan".
yi yayi kamar badashi take ba hakan daya yimata baƙaramin ƙara tunzurata yayiba a harzuƙe tace"Malam ka ajeni anan".
ƙara banza da ita yayi hakan yasa takai hannu cikin ɓacin rai zata murɗa handle ɗin motar kafin taƙarasa taji ƙarar sa lock ɗinsa hakan yasa ta koma ta zauna tare da jingina da jikin kujerar ta lumshe oily eyes ɗinta cikin kwanciyar hankali ya cigaba da tafiyarsa harya isa wani tanƙamemen mall mesuna MAN OF THE WORLD SHOPPING MALL da manyan baƙi ƙarasa shiga gurin yayi tare da yin parking a tanƙamemen parking space ɗin gurin yana daidaita parking ɗinsa yaɗan saci kallonta gani yayi har bacci ya ɗauketa a haka jiyayi wani murmushin dabe shirya yinsa ba ya kuɓucemasa ganin yadda ta duƙunƙune ne yasashi gane a.c tayimata yawa yaɗan ragemata haɗe da kwantar mata da kujerar ya gyaramata kwanciyarta ya buɗe ya fita tare dasa lock ta waje ya nufi cikin gurin bejima da shiga ba yafito bayansa da masu aiki a gurin sanye da riguna da kaya niƙi-niƙi a bayansa danna key ɗin motar yayi har zasu zuba a boot ya dakatar dasu yayimusu nuni da gidan baya cikin girmamawa suka zuba yashiga motar yaja seda sukayi tafiya me nisa rasa hanyar dazebi yakaita gidane yasashi juyawa ya kalli inda take gani yayi ta tashi taɓe baki yayi haɗe da cewa"ina zankaiki".
ba tare data kalli inda yike ba tace"Suleja amma a titi zan sauka".
ba tare daya tankamata ba ya juyar da kansa ya cigaba da tuƙinsa cikin kwanciyar hankali yaƙara volume yashiga bin karatun Alqur'ani taɓe baki tayi a zuciyarta tace"ashe su wa'eeh an iya abun mutane".
jin muryarsa tayi kamar a mafarki yace"keeeh dawa kike".
se lokacin tagane a fili tayi maganar tsuke bakinta tayi har suka isa bakin titi kamar yadda tace dashi yayi parking gefan titi ba tare daya kalleta ba yasa hannu ya jawo ɗaya daka cikin ledojin da yasa aka saka a baya ya buɗa ya fito da wasu rantsatsun abayas masu ɗaukar hankali ya zaro ɗaya daga ciki ya buɗa ba tare daya kalleta ba yace"daka yau wa'innan kayan zaki riƙa sawa da safarsu da niƙab ɗinsu dan bazan lamunci saka wannan banzan gyalen da kikeyi ba domin Comphany ɗina ba gurin nanaye bane da mutum zaki riƙa saka wa'innan fugaggun gyaluluwan naki masu kama da matacin koko a ciki akwai hijabs kowanne kowanne kaya da kalar niƙab ɗinsa da hijab ɗinsa su zaki riƙa sawa".
wata dariyar rainin hankali tayimasa tare da taɓe baki ta aro jarumta tace"waikai meyasa kake son takurawa rayuwata ne sekace wani mijina ina ruwanka da kayana kuma da kake cewa gyalena kamar matacin koko meye naka a ciki naga tundaka gidanmu nasawo kayana meyasa su basu yimun maganaba sekai kuma kai bakaga irin shigar da Sakatariyarka take ba se tawa saboda ni kaɗai ka tsana to bazan dena sawa ba banason kayan kakaiwa matarka tasa domin ni a ganina ita zakaiwa wannan kullen baniba".
taƙarasa zancensa tare da ture rigar daka jikinta cikin isa yace"ke wacece da zanyimiki kyauta ki mayarmu dame kike taƙama baki isa kin karyamun record ba dole ki ansa".
wani kallon tara saura kwata tayimasa cikin tsiwa tace"mutum ce kamarka kai waye da baza'ah mayarmaka ba masha Allah kaga seka aje record akaina anyi rejecting ɗin kyautarka domin ni wallahu bazan ansa ba ka adana zasu yimaka amfani gun matarka".
taƙarasa zancen tare da saurin murɗa handle ɗin ƙofar cikin sa'ah tajishi a buɗe tayi saurin fita ganin ya kawo hannunsa da niyyar cafkota tafice cikin sauri dukda tanajin zafin ciwon da ƙafarta ke mata karo na farko a rayuwarshi daya yi murmushi dukda rashin kunyar data tayimasa beja motar ba har seda yaga ta tsallaka titi tahau napep sannan ya tada motarsa yabar gurin a guje.
8:30pm
Tsaye yake a ƙofar gidansu yanata dialing number ta amma amsar ɗaya switch off sosai hankalinsa yayi mugun tashi ɗaga kannan da zeyi yaga Hauwah ta fito daka gidansu tunkaro inda yike tsaye sosai yaji wani irin sanyi ya ziyarci zuciyarsa bakinta ɗauke da sallama taƙarasa murmushin daya ƙara masa kyau yayimata cikin girmamawa Hauwah tace"Uncle Zaid anyini lafiya".
"inafa lafiya banji zuciyata ba ina zakijini naga ta lafiya".
sosai Hauwah daɗin kalamansa akan ƙawarta nanta labartamasa duk abinda yafaru a iya yadda tasani sosai hankalinsa ya tashi sosai takejin daɗin yadda yake caring ɗin ƙawarta tace "Uncle ka kwantar da hankalinka bara inshiga insanar musu seka shiga ka ga jikinta".
"aiko da kin temakeni domin bakiji yadda hankalina yayi mugun tashiba dukda kin faɗamun amma hankalina yaƙi kwanciya in naganta hankalina yafi kwanciya".
"tom bara naje".
nanta shiga .
A tsakar gida tasamu Abbah da Uwar Gwarama zaune Abbah yana cin tuwo Uwar Gwarama tana ƙuƙula magungunan mata da take siyarwa abinka dame sana'ah goma maganin me gasa ƙarasawa tayi inda suke cikin girmamawa tace"Abbah sannunku da hutawa".
"yauwa Hauwah ya mutanen gidan naku".
"lafiya ƙlau Abbah dama Zaid ne yazo zamuje gidansu shine nike faɗamasa Inteesar ɗin batada lafiya ……".
bata ƙarasa abinda take son cewa ba cikin zalama Abbah ya tari numfashinta da cewa "meyasa to baki ce yashigo ciki yagaida itaba aida kince ya shigo aishima yanzu yazama ɗan gida ko Tsahare".
tsilum Uwar gwarama tace"aiko dai Malam".
jin abinda Uwar Gwarama tace sosai yabawa Hauwah mamaki tace"ai Abbah nacemasa bara inyimasa iso yashigo".
"toh! toh!! toh!!! kin kyauta ki sanar dasu suɗan gyatta seki shigo dashi".
"toh".
nanta nufi ɗakinsu Inteesar zaune tasamesu Khadijat na karantawa Inteesar wani littafin Real eeshow mesuna ZANJIRATA sosai suke jin daɗin littafin domin yana kaimusu Umman su kuma tana kan sallaya tana lazumi hararsu Hauwah tayi tace"yanzu nan saboda rashin mutunci shine kuka cigaba da karantawa koku kirani inason jin yadda zata kaya tsakanin Amatujjabar da Yayah Mahmud saboda dramar su nakaimun ".
"ya haƙuri Aunty Hauwah zan karantamiki kema seda nace tabari kizo taƙi kinsan Aunty da gauƙa yanzu ma kuma muka fara".
"toh ƴar ƙanwata takaina ".
taƙarasa zamcenta ta nufar gurin Ummah duƙawa tayi ta sanar da ita zuwan Zaid sannan tasa suka ɗan kintsa dukda ɗakinsu fes-fes yike basu da lalaci nanta fita tashigo dashi.
Uwar Gwarama na ganin fitar Hauwah ta kalli Abbah daketa sukurkuta lomar tuwo yana santi tace"Malam bara inɗanje inɗan kunna turaren wuta sirikinmu bayazo yanaɗan jin bashi -bashi ba kadai sanni da iya karramar baƙo bare kuma babban sirikinmu".
"aiko dai da kin kyauta".
wani shu'umin murmushi tayi ta wuce ɗakinta tana shiga ta iske Jameelah tana waya da saurayinta cikin azama tace"ke banza kina nan kina shashsnci Allah yakawo mana dama Zaidu yanzu ze shigo ya duba waccan tsinau ɗin ki tashi ki ɗebo rushi kizuba magain nan".
tsalle Jamilah ta buga tare da miƙewa cikin jin daɗi tace"I love you Mamah na maganin kukana".
ta fice cikin sauri murmushi Uwar Gwarama tayi ta tafi ta ɗakko maganin da boka yabata ta fito waje a tsakar gida suka haɗu da Jameelah ta ebo wuta a marfin langa nanta jiki na rawa ansa Uwar Gwarama tayi tana murmushi tace"yimaza kije kiɗan kintsa jikinki karya ganki kamar wata ƴar jaka".
"toh".
nanta wuce ita kuma ta buɗe maganin ta zuba .
Zaid na shigowa ƙamshin turarennan ya bugu hancinsa lokaci ɗaya yaji kansa yashiga saramasa dakyar yake iya ɗaga ƙafa yake tafiya har suka isa!!!!!!!!
Votes and Comments
Plz share to others
_*Daga Alƙalamun 🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
*BOOK 1*
*PAGES* 2️⃣9️⃣➡️3️⃣0️⃣
Inda Abbah ke zaune yaƙarasa tare da zama kan sallayar da aka shimfiɗamasa ya zauna cikin girmamawa yace"Abbah ina yini".
"lafiya ƙlau ya wajen iyayen naka".
"lafiya ƙlau Abbah suncema suna gaisheku".
"masha Allah Hauwah yimasa jagora zuwa gurin mejikin".
"toh Abbah".
taƙarasa faɗa tana kallon Zaid da bashi da niyyar miƙewa ɓangaren Zaid ko ji yayi duk bayako son ganinta daurewa yayi ya miƙe da nufin bin bayasan sukaji muryar Uwar Gwarama dake fitowa daka ɗaki cikin shiga ta alfarma jiki na rawa Zaid yayi saurin duƙawa yace"Ummah ina yini".
ganin yadda jikinsa yaketa faman tsuma baƙaramun daɗi taji ba a zuciyarta tace"kai gaskiya Boka Tsula aikinka na kyau jibi yadda jikin wannan shu'umin yaron daya wulaƙantani yaketa faman karkarwa kamar mazari kaɗanma kagani ɗan shegiya zaka kwashi kashinka a hannu domin seka gane shayi ruwa ne seka zama tamkar raƙumi da akala domin Jameelah se yanda tayi dakai badai kai ƙaramin tsageraba hadda wani cewa dani ni Inteesar nike itakuma har wani gwalli takeyi wai ita zatayi aure gidan jindaɗi maga yadda za'ayi ayi auren matsawar ina numfashi bazan taɓa barin ɗiyar Aminah taji daɗin duniya ba kamar yadda na hanasu jin daɗin gidannan haka bazan taɓa barinku kuji daɗin gidan mijiba sede ku ƙare a bauta matsawar ina numfashi ".
katsemata zancen zucin da takeyi Zaid yayi murya na rawa yakuma cewa"Ummah ina yini".
wani gauron numfashi ta sauke haɗe da dawowa daga duniyar tinanin data lula tace"lafiya ƙlau yaron kirki ya wajen magabatan naka".
baki har ɓari yikeyi yace"lafiya ƙlau Ummah sunama gaisheku",.
a wani yatsune Uwar Gwarama tace"muna amsawa ɗiyar kirki ƴan makaranta kifito ga yayanku yazo ku gaisa ko duk hadda ce har yanzu kiriƙa barin kwakwalwarki ta huta dan Allah darenma ace mutum baze hutaba sekace al'huda-al'huda aikya fito ku gaisa inyaso seki koma kicigaba da karatun".
Jameelah dake ɗaki tana chart ɗinta da saurayinta ce tayi gyaran murya alamun bata kai ayaba ta cigaba da danna wayarta bayan 5mins cikin fi'ili tayi kabbara sannan ta miƙe taƙara feshe ko ina na jikinta da turare sannan ta gyara zaman hijab ɗinta tashiga tafiya cikin yanayin ɗaukat hankali.
Ganin yadda jikin Zaid keta faman ɓari baƙaramun mamaki hakan yaba Hauwah ganin yadda bakinsa har rawa yike gurin gaida Uwar Gwarama tinani tashiga yi a zuciyarta tashiga tinanin ita a iya saninta Zaid baya shiri da Uwar Gwarama to kuma meyasa taga jikinsa har ɓari yikeyi kanta rasa wanda zebaa amsa ne yasata tsuke bakinta tana mamakin iyayi irin na Uwar Gwaramaa zuciyarta tace"hmmm iska na wahal dame kayam kara ko a ina Jameelah ta taɓa shiga class oho Allah dai yasa ba wata kitumurmurar suka haɗa ba".
tana cikin wannan zancen zucin taji ƙamshin turaren Jameelah ya bigi hancinta saurin ɗagowa tayi caraf sukayi ido huɗu da Jameelah daketa faman zuba ƙamshi tasha kwalliya kamar wadda zata gasar kyau baƙaramun ɗaurewa kanta yaƙara yiba da mamakin abinda take gani ganin abun take kamar almara wata uwar harara Jameelah ta bankamata suna haɗa ido da Zaid tasakarmasa da wani narkakken murmushi wanda yasashi suman wucin gadi lokaci ɗaya yaji wani mugun sonta na fisgarsa jiyike duk duniya bashida wani abu da yikeso kamarta martanin murmushin data yimasa ya mayarmata wani sanyine ya ratsa zuciyarta inda takejin wata muguwar ƙaunarshi na ƙara ninkuwa a cikin zuciyarta jitake kamar taje ta rungumesa haka takeji .
Uwar Gwarama ce ta kalli Zaid cikin iyayi tace"kaganta nan Zaidu kullum aikin kenan daka hadda se zuwa makaranta koda yike tafi masu rataya jaka kullum kamar wanzamai aje can aje nan duk wani lungu na garinnan inkabi seka gansu kamar wa'inda akaimusu hakika da kare shiyasa ƙilama shiyasa aka rasa mashinshini".
murmushi Zaid yayi yace"masha Allah sister yanzu izunki nawa".
farr Jameelah tayi da mitsi-mitsin idanunta da suka ƙara narkar da Zaid cikin ƙaunarta zatayi magana kenan caraf Uwar Gwarama tace"hmm ai dake tayi sauka Hafizah ce bakaga yadda ƴan unguwa suke zuwa ɗaukar karatu gurinta ba".
"wow masha Allah ashe ƙanwar tawa Malama ce kenan a daɗa bada himma watarana zakiga amfanin abun ".
"insha Allah Yayah".
Hauwah dake gefensu dakyar ta tare dariyar data kusa kuɓucemata tace"muje Uncle Zaid kaga me jikin".
taƙarasa maganarta tana niyyar yin dariya sauke numfashi Zaid yayi danshi har yama manta da abinda ya kawosa lokaci ɗaya yaji wani irin abu yazo ya tsayamasa a zuciyarsa jiyike kamar ya zura da gudu saboda yadda kansa ke mugun saramasa dakyar ya yaƙi zuciyarsa gurin cewa"ok muje".
nan tayi gaba yabi bayanta ɓangaren Hauwah ko baƙaramun mamakin su Uwar Gwarama take ba tana wannan tinanin har suka isa ɗakinsu Inteesar.
Suna shiga yaji kansa ya daɗa juyewa yanajin wata irin muguwar tsanarta na shigarsa a zuciyarsa yanajin inda za'ah bashi wuƙa a lokacin ace ya kashe maƙiyinsa to ba makawa Inteesar ze kashe dakyar ya yaƙi zuciyarsa ya duƙa yagaida Umminsu Inteesar ba yabo ba fallasa ya gaidata Khadijah tagaidashi a ciki-ciki ya amsa cike da mamakin yadda taji ya amsa gaisuwar Khadijat ta ɗago idanunta ta kalleshi gani tayi yana bin ko ina na ɗakin da kallon ƙasƙanci da zallar tsana gami da kyama sosai abun yashiga bata mamaki tana cikin mamakin abinda idonta ke ganemata taji muryar Umminsu tace"Khadijah kawomasa ruwa".
cikin yatsuna yace"a'ah nagode Ummih".
murmushin manya Ummih tayi suka fice suka barsu ragewa gurin yayi daka Inteesar seshi a hankali ta miƙe tana tunkaro inda yike abun mamaki setaga ya miƙe zumbur kamar wanda aka tsireshi da allura ya miƙe yana toshe hanci ya fice waje da sauri dube-dube tashiga yi taga ko ina tsaf yike na ɗakin ba abinda ɗakinsu yike se ƙamshin turare a zuciyarta ta tambayi kanta"to meyasa yake toshe hanci kamar wanda yakejin wari".
rasa me bata amsa ne yasa wata zuciyar cemata "ƙila ƙamshin turaren ne bemasa ba to amma kuma meyasa yake binmu da irin kallon danaga yana binmu dashi ".
rasa me bata amsa ne yasata saurin bin bayansa.
Ɓangaren Zaid ko yana fita ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya lokaci ɗaya yaji wata fresh air na shigarsa ya nufi gurin dasu Abbah ke zaune cikin girmamawa ya duƙa a gaban Abbah yace"Abbah ga wannan a siyawa me jiki magani".
washe haƙora Abbah yayi irin na zalamammun iyaye masu tsananin son abun duniya yace"toh!toh!! toh!!! angode Malam Zaidu kaidai baka gajiya da abun arziƙi angode Allah ya saka da Alkhairi".
"Ameen Abbah ni zan wuce sauri nike".
"toh madallah ka gaida magabatan naka".
"toh zasuji".
yaƙarasa faɗa yana duben ta inda zeganta caraf suka haɗa ido da Jameelah dake ɗauke da tray a hannunta cikin karairaya take tafiya harta isa gabansa ta aje tray ɗin dake hannunta haɗe da waro mitsi-mitsin idanunta tace"badai Yayah har zaka tafi ba".
"eh Sis sauri nikeyi meeting ɗin gaggawa ne ya tasomun".
"okay to amma dai ko jus ɗin kasha dai".
"anya Sis sauri nike kibari watarana nasha".
kukan shagwaɓa Jameelah tashigayi harta buga ƙafa hakan baƙaramun ƙara burge Zaid yayiba yaƙara lula cikin duniyar ƙaunarta yace"sorry Sis bani insha".
"yauwa Yayana".
nanta zubamasa yasha baƙaramun ɗaurewa kan kowa na gurin yayi Uwar Gwarama tana haɗa ido da Jameelah ta ɗagamata hannu alamun aikinta na kyau nan yayimusu sallama kota kan Inteesar dayaga tana tahowa bebiba ya fice da sauri saurin bin bayansa tayi amma me tana zuwa yana barin gurin a guje ko kulata beyiba zubewa tayi a gurin tare da fashewa da wani marayan kuka jitayi an dafata tabaya hakan yasata saurin goge hawayenta tayi saurin ɓoye damuwarta tayi ta juya haɗe da cewa"Besty tinanin yadda za'ayi gobe nike narasa meza'ah tarbi ƴan kawo kayannan dashi".
"shine kuma zaki duƙa kamar wadda wani abun ke damunta kodai ƙafar ce ta motsa muje nagama tsara abubuwan da zamu siyo semuyi snacks da drinks se chickens ina ganin ya isa".
"eh ya isa ammafa ni a hannuna befi 6k ba ina tinanin har su sai lemo susai chicken ga uwa uba snacks".
"muje inada kuɗi a account ɗina semuyi amfani dashi".
"toh ke bakida amfanin da zakiyi dasu da zaki ce ga wasu a gurinki".
"ai Besty ko inada amfanin da zanyi dashi na fasa meye ranar inada shi ban temakekiba ai abun bemun rana ba haba Besty a tinanina in inada abu tamkar kema kinada shine muje dan Allah musan abunyi".
"hakane kam Besty nagode Allah ya saka da Alkhairi yabarmu tare".
harar wasa Hauwah tayimata haɗe da cewa"ameen Bestyna Allah ya shiryeki Bestyna inban miki ba wazan yiwa".
"Ameen dai Besty".
nansuka shiga dan tsara abubuwan da zasuyi domin tarbar ƴan kawo kaya.
Zaune suke a gaban Boka sun gama zayyanemasa duk abinda ke faruwa tsakanin Inteesar da Man of the world wata uwar dariya Boka Kutsugu yayi lokaci ɗaya ya haɗe rai tare da cewa"tunkafin kuzo nan nasan da zuwanku wannan yarinyar da kuke gani ba'ah zaune take haka kawai ba domin yarinyar nan da kuke gani ba ƙaramar hatsabibiya bace dole sekinyi da gaske sannan zaki kamota".
"kinji ko dama na faɗamiki yarinyar nan baƙaramar hatsabibiya bace dama ni ina ganinta nasan ba haka nan take zaune ba ".
"Boka yanzu ayi duk yadda za'ayi a cire yarinyar nan ta fita daka zuciyarsa asamasa soyayyata a zuciyarsa".
wata uwar dariya Boka kutsugu yaƙara kecewa a karo na biyu yaƙara haɗe rai ya ɗaga hannu sega wani abu ya bayyana duk jini a jikinsa me kama da zuciya yana hurawa ya miƙawa Feenerh irin ɗari-ɗarinnan ta riƙa yi da kyankyami ta ansa a yaƙune wai ita me kyankyami