Showing 9001 words to 12000 words out of 33748 words

Chapter 4 - Man Of The World Hausa Novel Complete

31 Dec 2024

195

na ɓatamasa farar kujerarsa Allah kaɗai yasan irin muzantani dazeyi Allah ka temakeni nashiga uku".
tana cikin zancen zucinnan ɗaga idonnan da zatayi caraf suka haɗa ido da Namijin duniya yana jifanta da wani
irin wulaƙantaccen kallo me cike da zallar ƙyama da ƙasƙanci Step biyu zuwa uku ya taka zuwa inda take kafin ya tsaya tare da harɗe hannuwansa aƙirji yayinda sexy eyes ɗinsa suka kaɗa sukayi jawur dasu saboda tsananin ɓacin rai se huci yike kamar wani mayunwacin zaki ya tsaya a gabanta .



Cikin lion voice ɗinsa wadda taƙara tsorata Inteesar yace"How dare You ?Waya baki izinin zama akujerata ke wacece da har kika samu damar zama akan kujerar da nike zama da wannan ƙazamun jikin naki wanda ba lallai banema yataɓa ganin ruwabama ko kina tunanin wannan wajen zama ƙasƙantattun mutanene irinkine duk ki wuce sauran chairs ɗin office ɗinnan ki rasa wadda zaki zauna se privet chair ɗina ".
yaƙarasa maganarsa cikin ɗan ɗaga murya Kasa furta komai tayi se ƙasa da tayi da kanta wani irin matsananciyar kunyarsa na shiganta dukda begani ba amma jitake kamar ƙasa ta tsage ta shige dan kunya shin taya zata iya tashi wannan mutumin ya ganta ahaka" Ya rabbi kada ka bari wannan bawa naka ya muzantani ".
tafaɗa a ƙasan ranta shiko Namijin duniya ganin tayi banza dashi yasashi ƙara hassala gani yike wani salon iskancin taƙara tsiromasa dashi hakan yasa yasaki wani guntun tsuka cikin ɓacin rai ya bugamata wata razananniyar tsawa wadda har seda ƴan cikinta suka kaɗa lokaci ɗaya jikinta yahau rawa batasan lokacin data miƙeba .



A hankali sexy eyes ɗinsa suka sauka akan kujeran data ɓatamasa Wara shu'uman idanunsa yayi yana kallon wajen wani irin baƙin cikinta ne yazo ya tokaremata maƙoshi dakyar ya iya haɗiye wani ƙullutun baƙin ciki daya tsayamasa lokaci ɗaya yaji yaƙarajin wata muguwar tsanarta na ƙara ƙaruwa a cikin zuciyarsa lokaci ɗaya kanshi yafara juyawa ga wata irin tsananin kyamarta dake damunsa ya buɗe baki da niyyar yimata magana kenan idanunsa ya sauka akanta .



Takurewa Inteesar tayi ajikin kujeran jikinta yashiga rawa saman goshinta da hancinta yafara fitar da zufa tamkar babu a.c a office ɗin kanta ta fara juyawa tana shura ƙafarta cikin tsananin azaban ciwon da cikinta ke mata a take idanunta suka shiga tsiyayar da hawaye ga jikinta dake karkarwa tamkar mazari cikin yanayin ficewar hayyaci ta janye hijabin dake jikinta tare da tasani ba ta dafe ƙasan maranta tana kuka.



Da sauri ya rintse idanunsa sakamakon ganin yanda saman breast ɗin ta suka bayyana ta saman doguwar rigar jikinta da sauri yaja baya tare da rintse sexy eyes ɗinsa dukda bawani abu dayaji a jikinsa kome ya tuna kuma yayi saurin buɗe wa yana kallon yanda hawaye ke ambaliya a idanunta kamar wani famfo dakyar ya saita kansa jiyayi a zuciyarta tabashi tausayi amma dake ya iya wanke allonsa bazaka ganeba saboda ƙara shan kunu daya ƙarayi cikin muryar zaratan maza yace"keeeeh".
tsabar firgita tafara ja baya yana binta har suka isa inda ta fara mofewa luuuu ta tafi zata faɗi hakan yasa cikin zafin nama yasa hannu ya jawota bazato ta faɗo jikinsa hakan yabawa ɗankwalinta damar saɓulewa ƙasa yalwataccen gashinta ya sauka a gadon bayanta bazato sukaji tsawa ƙara shigewa tayi jikinsa ta inda ƙirjinsu ya haɗe dana juna gam .


Ɓangaren Namijin duniya ko ba'ah cewa komai saboda ya shagala da kallon zara-zaran eye lashes ɗinta da suka kwanta sukayi luf dasu yanayin iskar da akeyine yasa yalwataccen gashinta kaɗawa ya rifemata fuska bazato taji lallausan hannunsa a fuskarta yana gyaramata dogon gashin sun daɗe suna kallon juna eyes to eyes saurin dawowa yayi daga dogon tinanin daya shiga bazato taji ya hankaɗeta ya saki wata uwar tsuka kallon farar suit ɗinsa yayi meze gani suma sun ɓaci da jini sosai cikin ƙololuwar ɓacin rai ya buɗe baki zeyi magana kenan yaji muryar Abbih ɗinsa na cewa"Son buɗe nine".
damm ƙirjinsa yabayar sakamakon ganin Inteesar dashi duk sun ɓaci da jini murya kamar ammasa dole yace"toh Abbih ganinan zuwa".
wani ƙasƙantaccen kallo ya watsawa Inteesar tare da yin tsuka bazato taji lallausan hannunsa a nata ya nufi toilet ɗinsa da ita!!!!!



*Kuyi manage da wannan saboda kwana biyunnan da banyin typing yasa na sangarce nasan insha Allahu nanda gobe zan dawo normal saboda akwai labari a bakina sosai*



_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_ar Mutanen Gwarzo.*_🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)



*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*


HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…


*BOOK 1*


*PAGES* 1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣

Ba abinda take se aikin rawar jiki domin wani sabon tsoronsa ne ya dirarmata dan gani take wata muguntar ya shiryamata domin tasan baze taɓa barinta ba tunda ta ɓatamasa guri ɓangaren Namijin duniya ko yana shiga da Inteesar toilet ya cire ƴar saman suit ɗinsa ya fita.


Dukda tana cikin firgicin abinda ya fitar dashi amma hakan be hanata bin ko ina na toilet ɗin da kallo ba a zuciyarta tace"amma gaskiya ankashe kuɗi a banɗakinnan kamar baza'ah mutu ba ace duk toilet aka tsaya ƙawatawa haka kamar mutum ya zuba abinci yaci dan kyau".
tana cikin wannan zancen zucin taji buɗe ƙofar Namijin duniya ƙara raɓewa tayi ɗan nesa dashi kamar wata munafuka ƙarasa shiga yayi ya zauna kan kujerar wanka yashiga tinanin irin rashin mutuncin da zewa Inteesar a zuciyarsa yace"haka kurum Ahmad kasa nabi shawararka kan wannan ƙasƙantacciyar yarinyar aiko dole kazo asan mafita dan seta gane kurenta bazan taɓa bari abinda takemun ya tafi a banza ba wallahi jibi yadda tasa na tsaida mahaifina a waje duk saboda iskancinta dole na gyaramata zama ".
yana cikin wannan maganar suka haɗa ido da Inteesar daketa faman zare ido kamar wadda tayiwa sarki ƙarya wani kallon tsana da ƙasƙanci da nunamata zaki gane shayi ruwane yike binta dashi tare da yin tsaki yace"kin dena kallona da wannan idanun naki kamar na mayu ko senazo nan na tattakaki mara mutunci kawai ".
yaƙarasa zancensa tare da sakin wani uban tsaki yana yamutsa fuska sakamakon zuciyarsa dake tashi saurin duƙar da kanta ƙasa tayi jiki a sanyaye zuciyarta na bugawa da sauri-sauri ga wata tsananin faɗuwar gaba dake damunta.


A zuciyarta tace"nashiga ukuna Allah kaɗai yasan irin muzantani da wannan mara tarbiyyar mutumin zeyi haka nanma ya lafiyar kura bare antaɓota na ɓatamasa kujera yanzufa wannan mara sanin darajar ɗan adam ɗin duk wani fishinsa kaina zeriƙa hucesa".
duk wannan zancen zucin da Inteesar take batasan a fili takeyinsa ba kaf Namijin duniya yajita bazato taji ya bugamata tsawa yace"keeeh dawa kike".
saurin dawowa tayi daga zancen zucin da takeyi batasan lokacin data ce"ba magana nayiba".
hakan yayi daidai da buga ƙofar toilet ɗin kwafa yayi tare da tashi cikin tafiyarnan tasa ta isa ya nufi ƙofa rakashi tayi da uwar harara tare da yin tsaki tace"abanza man kare ko ƙarya nayimaka kanada tarbiyyarne oho stupid kawai ji da Allah wata irin tafiya da yike kamar wani wahainiya waishi isashe".
jin abinda take cewa ne yasashi sakin murmushin dabe shirya yinsa ba ya girgiza kai tare da wucewa yayi kamar bejitaba buɗe ƙofar yayi ya anshi wasu leda guda biyu na store sannan ya mayar ya rife a hankali seda yazo gabda Inteesar yace"heey you ƙasƙantacciyar cleaner ga kaya nan wa'inda ba'ah taɓa sawaba sede a gansu a t.v ko a jarida asa nasandai kan wa'innan kika ɓatamun kujera base kin nunamun kin balaga ba har kin fara period ba".
yana gama faɗin haka ya wani watsamata kayan a jikinta ya buga tsaki ya nufi can cikin toilet ɗinsa yana murmushin gefan baki domin yasa ya gama da ita.



Wasu zafafan hawayene suka zubomata saboda tinda take ba'ah taɓa cin mutuncinta kamar yadda Namijin duniya yaciba ko wanda Uwar Gwarama take musu bekai wanda yayimata ba saboda ba wanda ya taɓa kiranta da ƙasƙantacciya se Namijin duniya gashi ba yadda za'ayi tabar aikinnan Abbansu ya kyaleta a fili ta furta "wallahi bazakaci banzaba indai nice sena rama mara tarbiyya kawai inbanda tsabar jahilci meyakawo maganar wani period banda ɗan iska neshi banda kayana sun ɓaci wallahi da bazansa wa'innan ƴan iskan kayan ba da har akemun gori kansu ".
ta daɗe tana wannan maganar taji buɗe ƙofarshi dukda taji haushi cin zarafinta dayayi amma hakan besa ta ɗago ta kalleshiba sema ƙasa data ƙarayi da kanta saboda tinda yaga jinin nan taji tana masifar jin kunyarsa ko rashin kunya zata yimasa bata yadda su haɗa ido har yazo dafda ita bata ɗagoba sema wasa data riƙayi da zara-zaran ƴan yatsunta taji muryarsa cike da rashin mutunci yace"saura kuma idan kin gama ƙazantar taki kiƙi wanken toilet kinji".
yanayin yadda yayi maganar kamar yaga kashi hakan baƙaramun ƙara sosa zuciyar Inteesar yayiba ya fara tafiya abinsa bazato yaji tayi tsaki ta wuce fuuu cikin inda ya fito murmushi yayi danyasan ya ɓatamata rai ya fice.


Ɓangaren Inteesar ko tana shiga wanka taji ta tsaftace jikinta sannan ta buɗa ledar daya jefeta da ita pad tagani dozen se pant dozen da breziya dozen se kuma wata haɗaɗɗiyar abaya maroon taɓe baki tace "kome zakayimun kayimun lokacinka ne maratarbiyya kawai oh ni Aishatu wannan mutumi shiya yankewa iskanci cibi banda ƙasurgumin ɗan bariki ne meye na wani haɗowa da breziya ",.
ɗaukae pant tayi guda ɗaya da pad tasa ta da bra ɗaya ta shirya jikinta tsaf cikin haɗaɗiyar abayarta data sha adon stone se walwali take baƙaramun ansar jikinta kayan sukayiba tayi rolling da ɗan kwalin abayar sosai farar fatarta tafito tayi wani mugun kyau tamkar balarabiya kallonta a madubi tayi taga tayi kyau sosai tinowa datayi da waye ya siyo kayan yasata jin wani ɓacin rai lokaci ɗaya ta haɗe rai tayi tsaki tace"shegun kayanma da akemun gori kansu ko kyau basu dashi".
tatattara sauran ta zubamasa kayansa tashiga wanke toilet ɗin.



Ɓangaren Namijin duniya ko yana fita ya tadda su Ahmad zaune da Abbih ɗinsa suna hira murmushin gefan baki yayi tare da cewa"sannu da zuwa Abbih".
"yauwa Son mekakeyi ne a toilet".
zeyi magana kenan Adam yace" sabuwar Cleaner ɗinsa yike nunawa yadda zata kunna kayan toilet ɗin saboda kartayi ba daidaiba".
saurin sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya yayu saboda banda Adam yayi saurin magana besan mezeceba zama yayi tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yace"Abbih anyini lafiya".
"lafiya ƙlau Son dama wucewa zanyi nace bara na shigo na kawomaka ziyarar bazata".
"aiko naji daɗi nagode Abbih Allah yaƙara girma".
"Ameen Son Allah yayimuku albarka".
haɗa baki sukayi da "Ameen".
suna cikin wannan hirar Inteesar tafito tindaka ƙafarta har zuwa kanta kwanne cikinsu yabita da kallo a hankali take tafiya ganin yadda hankalin kowa yike kanta yasa Namijin duniya yaji wani abu yazo ya tsayamishi a maƙogoro harta iso inda suke cikin girmamawa ta duƙa har ƙasa tace"Ina yini ranka shidaɗe".
"lafiya ƙlau daughter ya aiki".
"Alhamdulillah".
tana gama faɗin haka ta miƙe da niyyar tafiya Abbih yace"ɗiyata da wanne matakin karatu kike amfani".
zatayi magana kenan Namijin duniya daketa gumi yayi saurin cewa"batayi karatu ba tausayi tabani datazo neman aiki dankar inbarta haka yasa nabata cleaning ".
sosai tayi mamakin abinda Namijin duniya yace nan ta shiga tinanin itako meta tsaremishi a duniya da harya tsaneta haka wasu hawayene masu zafi suka zubomata tayi saurin sharewa taji Abbih yace"ka kyauta kuwa Son Allah yayimiki albarka ungo wannan".
ya miƙamata bandir ɗin yan dubu-dubu da farko taƙi ansa hakan yasa Abbih cewa"ki ansa ki ɗaukeni tamkar mahaifinki kinji".
"toh nagode Allah yaƙara buɗe da ɗaukaka".
"Ameen ".
nanta fita kallonsu Namijin duniya Abbih yayi tare da cewa"amma yarinyar nan tanada nutsuwa hakanan naji ta kwantamun a rai wallahi anyako ba surukata bace ba cleaner ba kuka ɓoyemu naga kwata-kwata batayi kama da masu sharaba".
kallon juna su Namijin duniya sukayi tare da cewa "wallahi Abbih cleaner ce".
murmushin manya Abbih yayi tare da cewa"to ni zan wuce".
nan suka miƙe dan yimasa rakiya seda suka fitar dashi har gurin motocinsa sannan suka juya.



Ɓangaren Inteesar ko tana fita ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya tare da dafe ƙirji waigawar nan da zatayi sukayi ido huɗu da sakatariya nata bankamata harara tsaki Inteesar tayi tare da cewa"andaiyi asara zuwa duniya mutum yayita ɓata lokacinsa kan wanda bemasan yanayiba dama hijabinki kika fara sawa kina rifawa wannan kwantaccen ƙirjin naki da yike kamar farantin fawa asiri ƙila yasan kinayi".
"oho dai a haka ake ganin ake sha'awa kuma ba'ah kula na masu miƙaƙƙen se inzonan in zauna kanki da ubanki inga ƙaryar fitsara ".
dafa kwankwaso Inteesar tayi a zuciyarta tace"wai wannan me ɓaka-ɓakan duwawun tazauna kaina aina shigesu".
a fili kuma taɓe baki tayi tace"waya gayamiki dama ni inaso asoni ai abu me tsada binsa ake yana wulaƙanci abu me arha ko kullum buɗesa ake ana tallarsa kamar dai wannan ɗan silifas ɗin ƙirjin naki me kama da takalmi ɗan madina saboda taushi".
taƙarasa zancenta tare da niyyar fita Sakatariya Feenerh ko cikin jin ɓacin ran maganganun Inteesar tace"inkin isa ki tsaya inbaga tsoro ba dasekin gane ke ƙaramar mara kunyace wallahi".
gabda zata fita ta juya tace"Allah ya kyautamun na tsaya ina goga jiki da wannan ƙazamun jikin naki dayasha taɓawar ƴan bariki".
taƙarasa zancenta tare da saurin ficewa da gudu dankarta cimmata tasan duka zatayimata sosai abinnan yaƙara ɓatawa Sakatariya rai taji taƙara tsanarta.


Zaune suke suna hira Ahmad ya kalli Adam tare da cewa"ammafa yarinyar nan ɗazu baƙaramun kyau tayiba kasan Allah seda ta matso nagane wacece Allah yayi halitta anan gurin".
"gaskiya tayi kyau sosai wannanfa da a gidan hutu take zatayi yaya wallahi".
cikin ɓacin rai Namijin duniya yace"ban kiraku nan dan kuzauna kuyita yimun surutan banza ba".
yaƙarasa zancensa cike da ɓacin rai kallonsa Adam yayi yace"abokina lafiya naga duk ranka yaɓaci kamar wata girlfriend ɗinka abinda kakeyifa like kishifa anya abokinmu ko be zurma ba kuwa Ahmad ".
"nima tinanin da nikeyi kenan".
cikin tsananin ɓacin rai Namijin duniya ya miƙe ya fice a fusace binsa sukayi da kallo gabaki ɗayansu sannan suka tafi suma.



4:00pm
Zaid na tsaye jikin motarsa suka fito daga cikin comphany ɗin bakinsu ɗauke da sallama suka ƙarasa inda yike murmushi yayi tare da cewa"wa'alakumus salam sannunku da aiki".
"yauwa ina yini Uncle Zaid".
"lafiya ƙlau Hauwa'uh".
"ina yini".
"lafiya ƙlau My heart ya aiki".
"Alhamdulillah ya naka".
"lafiya ƙlau".
nan suka shiga motar yajasu suka nufi Suleja.



Yana gama daidaita parking suka fito gabaki ɗayansu kallon Inteesar Hauwa'uh tayi tare da cewa"sena shigo Uncle Zaid ka gaida gida mungode".
"toh Hauwa'uh se Allah yakaimu".
"Ameen".
taƙarasa faɗa tanaiwa Inteesar inkiya da ido ta wuce ƙasa Inteesar tayi da idonta tana tinanin ta inda zata fara faɗawa Zaid maganar mahaifinta taji muryar mahaifinta na tunkarosu batace ƙalaba harya ƙaraso inda suke Zaid ya duƙa cikin girmamawa yace"Babah ina yini ".
"lafiya ƙlau ɗannan ya magabatanka".
"lafiya ƙlau Babah".
"masha Allah Inteesar ta faɗamaka saƙona kuwa?".
"a'ah Babah".
"aidama nasan bazata faɗamaka ba tunda ita ba auren bane a gabanta haka nace da ita indai da gaske kake ka turo iyayenka a tsaida ranar biki domin nina gaji da gulmammakin jama'ar unguwa duk inda na shiga ana nunani ".
Inteesar da kanta ke ƙasace ta share hawayenta taji Zaid yace"Babah dagaske nike son Inteesar insha Allahu gobe zan turo iyayena domin banaso na rasata".
"to toh madallah ".
nan Abbah ya juya ze tafi Zaid yace"Babah ga wannan ayi cefane".
ya miƙamasa bandir ɗin ƴan ɗari bibiyu saurin miƙe hannu yayi tare da cewa"angode ".
nanya shige gida cikin murna kasa ɗaga idonta tayi ta kalli Zaid ganin haka yasa Zaid be takurataba suka ɗan taɓa hira kaɗan tashiga gida tana shiga Zaid yabita da kallon tausayi lokaci ɗaya yaji soyayyarta taƙara nunkuwa fiye da da a zuciyarsa yashiga tinanin anyako wannan dagaske shine mahaifin zuciyarsa ba riƙonta yikeba ya juya zetafi kenan yaji muryar Uwar Gwarama a bayansa tace"ɗannan tsaya ".
saurin juyawa yayi jin muryar babbar mace saurin duƙawa yayi a tinaninsa itace mahaifiyar Inteesar yace"Ina yini Ummah".
"lafiya ƙlau ɗannan miƙe kaji dama magana nazo muyi dakai bakaine me neman auren Inteesar ba?".
cikin girmamawa Zaid yace"eh nine Ummah insha Allahu gobe zan turo ".
"yaro aiba wannan ya kawoni ba temakonka nazo inyi yaro karka sake ka auri wannan yarinyar data daɗe tana bin maza da sunan wai karatu take".
saurin ɗagowa Zaid yayi da mamakin jin kalamanta yace"bangane bin mazaba Ummah".
"karuwanci daka sani shi wannan yarinya takeyi itada wannan Hauwa kullum basu gun wancan ƙaton yau gobe basu gun wancan ninan shedace saboda ƴar kishiyata ce shiyasa ko kare be taɓa zuwa ƙofar gidannan da sunan yana sonta ba sekai kowa a unguwarnan yasan abinda suke aikatawa shiyasa bata da mashinshini ko ɗaya shine danaji abinda Malam yike cewa nace bari inzo insanar dakai komai amma akwai ƙanwarta Jamilah yarinyar kirkice in kana sonta nabaka ita duniya da lahira ƴatace gama tanan tana fitowa daka gida Jamilah zoku gaisa man".
saurin ɗaga ido Zaid yayi dan yaga wacece Jamilah cikin yauƙi taƙaraso inda yike ana karairaya kamar wata riƙaƙƙar ƴar bariki tana fari tace"ina yini".
murmushi Zaid yayi tare da cewa"lafiya ƙlau Jamilah sannunki".
"yauwa Ummah ni zan wuce makaranta".
" to ƴar albarka ayi karatu sosai".
"toh Ummah se anjuma babban Yayah se anjuma".
ta wuce tanata karairaya binta yayi da ido yana kallon ikon Allah yaji Uwar Gwarama tace"Jamilah kenan ƴan makaranta kullum aikin kenan ba dare ba rana karatu ni har cemata nike ta riƙa barin kwakwalwarta tana hutawa sede tayi murmushi ya kagani ɗana tayimaka?".
murmushi Zaid yayi tare da ƙara bin Jamilah da kallo yace!!!!!!!!!



_Bansamu nayi editing ba koda kunga typing errior aiki nike_



*Rashin comments ɗinku da votes shike sani ƙinyin typing saboda banajin daɗin irin abinda kukemun koba komai na tsaya dogon lokaci ina typing danna farantamuku amma ku comments and votes ya gagareku na ƙone a hannuna kullum se an wanke hannun amma haka na daure inayi amma ku comments dabe wuce layi biyarba shi kuke kyashin yi.*



Votes and Comments
Plz share to others



_*Daga Alƙalamun ƴ🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)


*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*


HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…


*BOOK 1*


*PAGES* 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣



"Hmmm banyi mamakin jin irin abubuwan da suke fitowa daka bakinba domin kincemun ke kishiyar maman Inteesar ce jin kalamanki akan Inteesar yaƙara tabbatarmun dakece babbar mara tarbiyya da har kika iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login