Showing 21001 words to 24000 words out of 33748 words
yi danasanin saninka a rayuwa ko ya kace Adam".
"maganarka gaskiya ce Ahmad dole musan abinyi gaskiya".
" ni ina ganin meze hana musa a yaran Namijin duniya suyi raping ɗinta ina ganin shine best solution".
tunkafin yaƙarasa maganarsa Namijin duniya ya juya garesa a fusace cikin yanayin da tun tasowarsu basu taɓa ganinsa a cikiba sukaji yace"what anya Ahmad ko kanada hankali kuwa raping ɗinta fa kace aiko wani naga yana niyyar lalatamata rayuwa se inda ƙarfina yaƙare bare nida kaina insa Allah yakyauta in ƙanwarka ce zakace ayimata hakane ".
jin yadda yaketa huci ne yasasu kafesa da ido dafashi Adam yayi yace"calm down my man irin wannan harzuƙa haka sekace wata ƙanwarka ko matarka kabari ayimata abinda harta mutu bazata manta dashi ba a ganina bekamata ace da class ɗinmu da komai ba mu tsaya ƴar wannan ƙaramar alhakin tana rainamana hankali ba duka nawa take da har zamu dinga westing time akanta kaga malam ko kanaso ko bakaso dole haka za'ai gwara ayi a wuce gurinta ni ina tinaninma ni zansa a ɗakkowa ita na mori wannan shegen jikinnata me mugun tayarwa da mutane hankali dama na daɗe ina sha'awarta".
"haba Adam kayi kaɗan kamar ba amarya za'ah kawomaka ba jibi kabarni inshana kawai sede inmu duka zamu mora domin nima na daɗe ina kwaɗaituwa da wannan karuwan jikin nata baza'ah barni a bayaba bara na kira Damisa su ɗakkomana ita yau da ita zamuyi kodumo koya kace Adam".
" hakan yayi amma kuma wani hanzari ba guduba inyana ganin wannan shawarar bata yimasa ba meze hana yabi tawa shawarar ta baya ".
Sosai ran Namijin duniya yakai ƙololuwar ɓaci lokaci ɗaya idanunsa suka sauya kala yayinda jijiyoyin kansa suka tashi ruɗu-ruɗu saboda yasan halin abokan nasa indai sukaga yarinya ko ɗiyar uban waye sesunsa anɗakkomasu ita ɗago jajayen idanunsa yayi ya zubawa aminan nasa cikin takaici yace"ya isheku haka banason irin wannan zancen banzan naku kuma wallahi duk wanda kukasa ya ɗakkota sede uwarsa ta haifi wani domin indai ina numfashi bazan taɓa bari wani ya ɓatamata rayuwa ba".
mamakin yadda ya haƙiƙance yanata zazzaga musu masifa ne yakama su Ahmad domin tunda suke a rayuwarsu basu taɓa ganin Namijin duniya a cikin irin wannan halinba dafashi Adam yayi yace"anya ko abokina baka kamuba kuwa a tinanina inkaji wannan shawarar tamu murna zakayi amma se mukaga akasin haka saboda irin abinda yarinyar nan takemaka yayi yawa dukfa abinda kaga munayi saboda farin cikinka mukeyi badon wani ba".
A matuƙar fusace yace"Wannan ba mafita bace face shawarar banza data wofi wadda zata kaini ta baroni wannan shine abu mafi muni da ƙazanta wanda zaku aikata acikin rayuwarku domin narantse da wanda raina ke hannunsa idan ɗaya daga cikinku yayi kuskuren taɓa koda tafin hannunta ne sena salwantar da rayuwarsa dan bazan nuna nasankuba wlh sena nunamuku true colour ɗina dan zanbaku mamaki a duk biye-biyen matanku bantaɓa sakamuku bakiba dan haka salin alin idanunku subar kan wannan yarinyar inba hakaba zakusan wanene Abdallah".
Da mugun mamaki suke Kallonsa jin furucinsa kasa furta komai sukayi se kallon dake nuni da tsantsar al'ajabi da suke binsa dashi baka jin ƙaran komai face saukar numfashinsa da yike fitarwa kamar wani mayunwacin zaki ganin irin kallon da suke binsa dashine yasa a zuciyarsa yace"ni Abdallah meke damuna ne mena faɗamusu naga suna bina da kallon mamaki na rasa meke damuna kan wannan kucakar yarinyar ne".
dake miskilin ƙarshene bazaka lura da yanayin da yike cikiba sema wani ƙara shan kunu daya ƙara ajiyar zuciya Ahmad ya sauƙe kana yakafe sa da idanu na wasu mintuna ahankali ya furta "kadde kafara sonta my man".
Wani banzan kallo ya watsa masa cikin haɗa girar sama data ƙasa yace"Banason maganan banza Meyakawo maganar so aciki wannan zancen kuma".
Adam da mamaki ya gama cikasa ne yace"Daga cikin kalamanka za'ah fahimci akwai kishin yarinyar me ƙarfi a tare dakai domin badan soyayyaba babu abinda zesa kafaɗa mana magana irin wannan wadda tun tasowarmu baka taɓa faɗamana ba ".
ajiyar zuciya ya sauƙe se yanzu ya tuna irin abinda yayiwa aminan nasa dafe kai yayi tare da cewa "Babu ɗigon soyayyarta acikin zuciyata hasalima tsanarta nakeji me tsanani ko wa'inda suka fita ajima ban kulasuba ma bare wata ita kona rasa matar aure bazan taɓa auren wannan kwailar yarinyar ba wadda ko ƙirjin kirki bata dashi wa'inda suka fita komaima basa gabana bare wata bera irinta anma ku tuna lefin data aikata be kai in ɗauki irin wannan hukuncin akantaba baya ga haka bazanso ace anyiwa ƴata ƙanwata ko matata irin wannan ba shin Mezesa Ni na ruguzawa wata rayuwarta duk abinda nayi nayisa ne domin tana ƙarƙashina banaso ta ɓatamun suna a idon duniya ".
Kai suka jinjina cike da gamsuwa da kalamansa Murmushi Ahmad yayi yace"Wallahi har nayi zaton ka faɗa tarkon ƙaunarta ".
Taɓe baki Namijin duniya yayi tare da shafa lallausar suman kansa data sha gyara yace"Allah ya kyauta wa'inda suka fita komaima basu isheni kallo ba bare ita banason haka mubar wannan zancen".
"sorry my man kawo kunnenka kaji wata hanya mafi sauƙi data kamata muyi maganinta cikin sauƙi ba tare da tashin hankali ba".
"ok".
nanya matsa Ahmad ya raɗamasa magana a kunne wadda nikaina real eeshow banji me yike cemasa ba se gani nayi Namijin duniya ya saki wani killer smile wanda shikaɗai yasan ma'anarsa bayan wani lokaci suka miƙe suka nufi gida zuciyar kowannensu cike da farin cikin samun mafita akan Inteesar.
Ɓangaren Inteesar ko tunda ta dawo gida take kuka hankalin Khadijat yayi mugun tashi ganin yadda ƴar uwarta keta kuka taƙi magana murya a raunane Khadijat tace"Auntyna wai yaushene zaki dena zubar da tsadaddun hawayenki akan abubuwan da basu taka kara sun karya bane sanadin kukannan naki yasa ƙannenki a gida sun rainaki a wajema kina niyyar kijawa kanki wani rainin ganin kinamasa kuka shiyasa yike ƙara rainaki dan Allah abinda nike so dake ko yayimiki abu dukmun ɓatamiki ran daya yi karki ƙara nunamasa ko a fuska kinji haushi idan yaga yana yimiki abu bakya damuwa haushi zekoma yanaji ki share hawayenki kinji Auntyna maganin kukana idan kina kuka ni kuma waye ze sharen nawa kukan inaso kiyimun wani alƙawari Aunty".
sosai kalaman Khadijah sukayi tasiri a zuciyar Inteesar ta share hawayenta tace"inajinki Khady".
"Aunty kiyimun alƙawarin duk inda kike zaki zama me ƙarfin zuciya bakomai zaki riƙa yiwa kuka ba koda ko ya cancanci hakan karkiyi agaban maƙiyinki".
wani murmushi ne ya suɓucewa Inteesar wanda har seda beauty point ɗinta suka bayyana tace"nayimiki my small sis insha Allah ".
"yauwa gwara da kika faɗamata Khady nima tintini nike bata wannan shawarar taƙiji".
nan sukaita hirarsu cike da nishaɗin bayan wani lokaci suka raka Hauwah har gida sannan suka dawo cikin farinciki suka nufi ɗakin Ummahnsu.
AFTER ONE WEEK
Abubuwa da yawa sun faru cikiko har da soyayya me ƙarfi dake gudana a tsakanin Zaid da Inteesar wanda a yanzu basa iya cikakken 1hr ɗaya beji ɗaya ba ɓangaren Namijin duniya ko duk abinda yasan zeyi yaɓatawa Inteesar rai shiyikeyi dan yaga fishinta bata taɓa nunamasa taji haushi koda abu yaɓatamata rai sede ta nemi wani gurin inda tasan bame ganinta tasha kukanta domin ko bata tagaleshi ba shi seya tagaleta abu kaɗan zatayi yashiga lallatsemata ƙirji yace shine purnishment ɗinta ko kuma yashiga kissing ɗinta da sunan hukunci ɓangarenta da Zaid ko shirye-shiryen biki Umminsa keyi ka'in da na'in domin Abbanshi yace bayason a wuce satinnan ba'ayi bikinba saboda yadda Zaid yabasu labarin yadda sukayi da Uwar Gwarama da alƙawarin da yayi na bayason bikin ya wuce sati ɗaya.
Zaune take a offuce ɗin Namijin duniya waya manne a kunnenta se zabga murmushi take tace"meyasa kake amsa na Hauwah ni nawa kace bakaso".
daga ɗaya ɓangaren Zaid yace"haba My 100% sure ɗina nina iya sakamiki suna se nine zakiji kunyar samamun suna ni meyasa banji kunyar canzamiki sunanba to nidai ki zaɓamun ".
yaƙarasa zancensa cike da shagwaɓa kamar wani ƙaramin yaro dariya tayi sosai sannan tace"to ɗan Ummih aikai namiji ne".
"au My 100% sure kina nufin mu maza bamu da kunya kenan".
zare sexy eyes ɗinta tayi kamar yana kallonta tace"nina isa faɗawa My Husband to be ɗina bashi da kunya".
cikin jindaɗin sunan data kirashi dashi yace"wow ɗan ƙara faɗa inji amma sunan yamun daɗi sosai".
cikin shagwaɓar data riga ta zamemata jiki tace"bazan faɗaba nidai ba ruwana".
"hmm to naji da wanne sunan kika saka a number ta nima zan faɗamiki sunan dana saka akan number ki".
cikin shagwaɓaɓɓiyar murya ta maƙe kafaɗa kamar wata ƙaramar yarinya tace"naƙi wayon baseka faɗamun kowa ya riƙe nasa ".
dariya Zaid yayi tare da cewa"to ai shikenan tunda bazaki faɗaba ammm dama Ummih tace infaɗamiki ki sanar dasu Ummah gobe za'ah kawo lefe".
"tom zan sanar dasu insha Allah".
"yauwa anjuma zan shigo da yamma zankaiki ki gaida Ammi".
"toh Allah yakawoka".
"Ameen ya Allah I love you my 100% sure".
"love you more My husband to be".
cikin shauƙin juna sukayi sallama tana kashewa cikin zumuɗi tayi dialing no Hauwah tana ɗagawa tace"Hauwah yace gobe zasu kawo lefe".
cikin murna tace"masha Allah ,Allah yakaimu amma gaskiya basu kyauta manaba memakon yafaɗamana tun wuri musan snack ɗin da zamuyi amma se yanzu".
"wlh kuwa sannan kuma wai zezo anjuma muje mugaida Ammin su".
"toh Allah yakaimu".
"ameen ya Allah".
tana kashewa juyawar nan da zatayi sukayi ido huɗu da Namijin duniya ya zubamata narkakkun sexy eyes ɗinsa da alama ya daɗe tsaye kanta batama san yana na kallonta ba .
Cikin inda -inda tace"amm sir wani abun za'ah yimaka ne?".
saurin janye idanunsa yayi yawani basar kamar ba kallon ta yike ba jin ta anbaci lefe yasa lokaci ɗaya yaji lokaci ɗaya ransa yayi mugun ɓaci ga wani ƙullutun abu daya zo ya tsayamasa a maƙogoro ya rasa meke damunsa a zuciyarsa yaketa faman maimata kalmar"lefe badai lefanta za'ah kawo ba duka nawa take da iyayenta zasu yarda su aurar da ita amma kuma wanne shegen take faɗawa I love you".
wata zuciyar ce tace"mijin da zata aura take faɗawa tokai meye naka danta faɗawa masoyinta kalmar so ko sonta kakeyine".
wata zuciyar ce tace"Allah ya kyauta na na zauna ɓata lokaci gurin yin wata soyayya da wannan kwailar yarinyar never".
yana cikin wannan zancen zucin yaji siririyar muryarta aɗan daburce tace"amm sir kana buƙhatar wani abun ne?".
jin yadda tayi magana ne yasa tsigar jikinsa mugun tashi yayinda yaji wani irin yarrrrr tun daga ƙafarsa har tsakiyar kansa yayinda lokaci ɗaya yaji gindinsa ya miƙe saurin saka hannunwansa yayi a aljihu saboda kallo ɗaya zaka yimasa kaga yadda shatin gindinsa yadda ya jika wandon lokaci ɗaya yaji wata muguwar sha'awah ta dabaibayesa dakyar ya iya cewa"ki tafi theater hall yanzu".
"toh sir".
nanta fara tafiya tana juyamasa ɗuwawuka kamar wadda ke juyasu da gayya lokaci ɗaya yaji wandonsa yayi mugun jiƙewa dakyar ya janye ƙafafunsa da suka yimasa nauyi ya nufi gurin drower ɗin da yike aje drugs ya ɓalla ya ɗauki ruwan gora ya kora zauna kan kujera yana mai maida numfashi 30mins sannan yaji yaɗanji sauƙi ya buɗe sexy eyes ɗinsa da suka ɗan ƙanƙance a zuciyarsa yace"meyike damuna ne wai kan wannan kwailar yarinyar da ko maganarta naji senaji hankalina yayi mugun tashi konama sha magani abanza".
wata zuciyar ce tace"ƙila sabon da kukayi ne yasa kakejin haka".
sauke ajiyar zuciya yayi tare da miƙewa ya ɗauki phones ɗinsa ya fita sakatariya Feenerh tashiga takemasa baya suka nufi hall ɗin daya kira meeting ɗin.
Yana shiga yaga ya zauna akusa da aminansa su Ahmad nan Adam ya miƙe tare da ɗaukar laudspeaker yace"salamu alakum".
amsawa jama'ah gurin sukayi da "wa'alaka salam".
"ba wani abu bane yasa muka taru ananba face daka yau munƙarawa duk wani ma'akaici dake ƙarƙashinmu albashi saboda yanayi da ake fama dashi na tsadar rayuwa wanda takai takawo ƙaramun ma'aikaci nauyi yayimasa yawa kuɗaɗen albashin da ake basu basu isa suyi hidimar iyalansu wannan dalilin yasa muka yanke hukuncin ƙarawa duk wani ma'aikaci albashi".
tafi hall ɗin ya ɗauka gabaki ɗaya da hayaniyar jin daɗi ta kauraye hall ɗin hakan yasa seda aka ɗauki 3mins kafin gurin yayi tsit Adam ya cigaba da cewa"sekuma abu na biyu kuma muna me farincikin sanar daku an kammala komai na babban branch ɗin pharmacy na Namijin duniya wanda za'ah cigaba da haɗa magunguna ranar asabar za'ah buɗesa in Allah yakaimu akwai a cikinku akwai wasu tsiraren mutane da muka ɗaukesu wanda matakin karatunsu ne yakaisu ba zaɓenmu ba zasu koma can da aiki ga sunayensu kamar haka zamu fara faɗowa tundaka sabbin canje-canje da aka samu ciki kuwa harda sakatarorinmu da aka canza su zamu fara kira".
tafi gurin yaƙara ɗauka da hayaniya.
Daɗa gyarawa Sakatariya Feenerh tayi ta kalli ƙawarta Zaby daketa ƙara shafa powder danta siye zuciyar Namijin duniya cikin kishi tace"mezan gani haka Zuby kike wani shafa powder sekace me ƙoƙarin yimun snatching".
cikin muryar riƙaƙun ƴan bariki Zuby tayi dariyar da iya kacinta fatar baki tace"haba ƙawata inani ina yiwa babbar aminiyata snatching ai Namijin duniya ni yafi ƙarfina wane ni dashi ai seku manyanmu inadai gyarawa ne domin ba'ah ga ƙawar Mrs Namijin duniya ba kamar wata mahaukaciya ba saboda banaso a rainamun ke ".
cikin jin daɗin kalaman Zuby tace"da wasa nike miki dama ƙawata nasan bazaki taɓa cin amanata ba aiko gwara ki gyara dakyau kinyi tinani mekyau kodon waccan berar da tin ɗazu suke kallonmu inkin gama ki bani nayi na gyara domin nasan ni za'ah fara kira da alama Oga fa kamar yafara kamuwa da soyayyata domin a sati biyunnan ni yike sawa inyimasa komai na office".
sosai ran Zuby yaɓaci da aminiyartata amma dake ƴar duniya ce seta dake kamar bataji komai ba tace"masha Allah kice aiki dai yafara kyau ".
"sosaima kuwa".
nanta cigaba da abinda take tana gamawa ta miƙawa Feenerh powder tashiga shafawa .
Tin fara shafa powdernsu Feenerh Hauwah ta lura dariya shiga yi hakan yasa Inteesar kallonta cikin ƙasa da murya tace"lafiya kiketa dariya".
"wani abu ne yabani dariya mutanenki nagani anata aikin wahalar da aka saba kallasu can ita da aminiyar nan tata".
taƙarasa zancenta tare da nunawa Inteesar su Feenerh dakyar tayi control ɗin dariyar data kusa suɓucemata taita dariya ƙasa-ƙasa seda tayi me isarta ɗaga idonnan da zatayi sukayi 4 eyes da Namijin duniya yana kallonta saurin janye lulu eyes ɗinta tayi domin gabanta dataji ya buga da ƙarfi tashiga karanto duk addu'o'in da suka zo bakinta tace da Hauwah gaskiya iska na wahalar dame kayan kara mutum yayita abu a inda ba'ah san yanayiba".
"wallahi kuwa ni yanzu dariyama suke bani".
"nima haka dukkansu fa yadda na fahimta sonsa sukeyi amma da alamu ɗaya ke ha'intar ɗaya inda zasu dena saka wa'innan kayan da suke fitomusu da shegen ƙirjinnan nasu me kama da lawashin albasa daya fimusu alheri ƙila ya kulasu ni banga abun so a wannan mutumi ba da mata suke zubar da ajinsu da darajarsu ta ɗiya mace suke cemasa suna sonsa yana ɗisgasu amma dukda haka suyita liƙemasa yana yabasu ba".
"hmm wallahi kina bani dariya da ƙirjinnan nasu me kama da silifas da kike cewa mutuniyas ƙila fa harda ke a cikin wa'inda zasu koma pharmacy ɗin Namijin duniya ".
"hmm kema kinsan yadda mutuminnan ya tsaneni baze taɓa sakawa dani ba wallahi kima dena wannan tinanin ƙila dai kiga masu goga powder a gaba-gaba".
Hauwah zatayi magana kenan sukaji muryar Adam a laudspeaker yana cewa"zamu fara da sakatariyar Namijin duniya mesuna Aisha Muhammad Ahmad ".
dammm gaban Inreesar yabayar sakamakon jin full name ɗinta dataji Adam ya anbata basu ƙara tabbatar da abinda sukaji taji muryar Adam a laudspeaker yace"Malama Inteesar idan tana kusa zamu so ganinta a step tazo ta gabatar da kanta".
ƙululu taji cikinta yabayar cikin yanayin damuwa tace"Hauwah anyako ba wata kitumurmurar suka shiryamunba kuwa saboda mutanen nan basu da mutunci".
"ki kwantar da hankalinki Besty insha Allahh bakomai kedai kiyi addu'ar duk data zo bakinki kinji insha Allahu ba abinda zefaru se alkhairi basu isa suyimiki abinda Allah bemiki ba".
jiki a sanyaye tace "toh".
jiki a sanyaye ta miƙe tafara tafiya yayinda zuciyarta tashiga bugawa da sauri-sauri!!!!!!!!!
Votes and comments
Plz share to others
_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_ ƴar Mutanen Gwarzo.*_🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
_Wannan shafin kyauta ne ga masoyan MAN OF THE WORLD a duk inda kuke Real eeshow na alfahari daku._
*BOOK 1*
*PAGES* 2️⃣3️⃣➡️2️⃣4️⃣
Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka take tafiya domin idanun mutanen gurin gabaki ɗaya na kanta jiki a sanyaye taƙarasa step ɗin kanta a ƙasa ɓangaren Namijin duniya ko tunda ta fito ya kafeta da mayun idanunsa dake mugun bata tsoro harta tsaya a step ganin yadda tayi ƙasa da kanta ne yasa Namijin duniya taɓe baki a zuciyarsa yace"wai ita ala dole ace tanada kunya da tarbiyya".
a hankali ta ɗaga golden eyes ɗinta dake masifar tafiya da zukatan mutane taɗan saci kallon inda yike caraf suka haɗa ido gani tayi ya taɓe baki saurin janye idanunta tayi daga garesa zungurarsa Ahmad yayi yace"bakaga yadda mutuniyarka tayi bane dubeta a haka kamar mutuniyar kirki se rashin tarbiyya kala-kala a cikinta kamar kuɗin cizo batasan munkusa zuwa ƙarshen game ɗinba".
wani killer smile ya saki nan Adam ya cigaba da kiran sauran mutane ba sunan Feenerh ko ɗaya sede canzamata muƙami da akayi takoma sakatariyar Adam .
Ɓangaren Sakatariya Feenerh da Zuby ko mutuwar zaune sukayi ganin abubuwan da suke faruwa sosai ran Feenerh yakai ƙololuwar ɓaci tana huci ta zunguri Zuby da kamar zatayi kuka tace"nidai na rasa mena tsarewa wannan tsinanniyar yarinyar ne da bata da wani burin daya wuce taga bayana ƴar kujerar da nike taƙama da itama seda ta rabani da ita a tinanina da wannan kujerar yakamata nayi amfani gurin shawo kansa shine saboda ita tambaɗaɗɗiya ce tayimun haka dole wannan karon ta ɗanɗana kuɗarta domin sena nunamata na rigata zuwa duniya ko ta halin ƙaƙa senaga bayanta tsinanniya ƴar gidan masu dattin