Showing 18001 words to 21000 words out of 33748 words
mata mota security ɗin ya yi ta fita tare da shigewa gurin driver yaja motar suka bar gurin.
8:30Pm
Suka iso gurin dinner kallon Inteesar Hauwa'uh tayi ta ce"amma gaskiya besty kinga yadda kika yi kyau kuwa kamar bake ba kodon bakya make-up shiyasa yau da kika yi ya yi mugun yi miki kyau".
Hmm besty kenan niko kunyar fita nike yi cikin mutane da wannan kwalliyar sabo da idan naga ana kallona duk se in tsargu bakiga yadda kika yi kyau ba Wallahi besty".
"au nice banyi kyau ba kenan ko Aunty?".
Sorry my Khady nina isa in ce da wannan shagaɓaɓɓiyar ƙanwar tawa bata yi kyauba? Kinfi kowa yin kyau".
Yauwa Auntyna muje".
nan suka fita Inteesar ji take kamar tsirara take sakamakon rashin saka gyale da batayi ba kanta a ƙasa sabo da wata irin kunya da take ji haka sukabi layin da akai na shigar da amarya suka shiga tanƙanemen hall ɗin da ya gaji da haɗuwa suka fara tafiya kiɗa na tashi har suka raka amarya da ango mazauninta dafa Inteesar Hauwa'uh tayi cikin ƙasa da murya ta ce"kinsanko waye angon Asma'uh".
"a'ah waye".
"Sir Adam ne".
dammm ƙirjinta ya bayar lokaci ɗaya zuciyarta tashiga bugawa da sauri-sauri ga yawun bakinta daya ƙafe ƙaf murya na rawa ta ce"what?".
"Eyi".
Wani gumi ya shiga ketomata suka samu seat suka zau na ta ce"amma baku kyauta mun ba da kuka hanani saka gyale ko wanne tom and jerry ya gama kallemun jiki a banza".
Nan Hauwa'uh taita kwantarmata da hankali aka shiga gabatar da program.
Suna cikin hirarsu da Khadija taji muryar m.c na ce wa"muna buƙatar aminiyar amarya me suna Aishatu domin tazo ta gabatar mana da tarihin amaryar".
a gigice ta ɗago ta ce"Hauwa'uh kinga irin abin da nike gudu ko da kun barni nasa gyalena ai da duk haka bata faru ba".
"Sorry besty gani muka yi idan kika sa zaki lalata kwalliyarki kiyi haƙuri kije kiyi kin san Asma'uh bazata ji daɗi ba".
"Ba bu 'in da zani ".
Ji suka yi m.c ya ƙara kiran sunan Inteesar hakan yasa Khadija ce wa"Aunty dan Allah kiyi in baki yi ba kamar kin watsawa Aunty Asma'uh ƙasane a ido ta wuce kowa ta zaɓeki plz Aunty".
taƙarasa zancenta tare da saka hannunta alamar roƙo kamar zata yi kuka hakan yasa Inteesar ce wa"sorry my Khady karkiyi kuka bara naje".
"yauwa Auntyna maganin kukana".
nan Inteesar tafara tafiya cikin nutsuwa take tafiya kanta a ƙasa hankalin kowa kanta ya koma sakamakon m.c daketa koɗata tun daga nesa ya kafeta da shanyayyun idanunsa da sukayi kama dana me bacci gani yike kamar ita kamar ba itaba hakan yasashi tanfatsar da glass cup ɗin dake hannunsa hakan yaja hankalin mutanen dake kusa da gurin yi ke suka kalle shi ba tare daya sani ba a zuciyarsa ya ce"why zuciyata da zaki dameni da tunanin wannan kucakar yarinyar ne da kowacce nagani ganinta nike kamar ita why anyako wannan yarinyar ba mayya bace takamani".
yana wannan tunanin harta ƙarasa gurin m.c ta tsaya saurin dawowa ya yi daga tunanin daya tafi gani ya yi ba Imergination ɗinta daya saba yi bane ita ce tasha gayu tagaji da haɗuwa se ƙamshi take bazawa!!!!!!!!!
meson shiga group ɗin wannan novel ɗin tayimun magana ta wannan number 08108362334
Votes and Comments
Plz share
_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_r Mutanen Gwarzo.*_🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
*BOOK 1*
*PAGES* 1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣
Cikin amsa kuwwa m.c yace "masha Allah ga babbar aminiyar amarya amma gaskiya tahaɗu kwarai dagaske bara muji taƙaitaccen tarihin babbar aminiyartata".
yaƙarasa zancensa tare da miƙawa Inteesar laudspeaker amsa tayi tare da ɗago da kyakyawar fuskarta wadda tayi mugun kyau domin inba farin sani kayimataba ba lallai bane ka ganetaba saboda kwalliyar tayi mugun amsar jikinta kamar ka saceta ka gudu jin abinda m.c yafaɗane yasashi ƙara tabbatarwa da kansa tabbas ba gizo tayimasa ba itance dai zuciyarsa ce tacemasa"to a ina tasamu kuɗinda harta iya saka wannan tsadadden material ɗin domin nidai a iya sanina bamasu hali bane".
wata zuciyarce tace"wataƙila saurayinnan natane ya siyamata".
tsaki yayi saboda lokaci ɗaya yaji wani mugun ɓacin rai yadirarmasa lokaci ɗaya yaji duniyar tayimasa zafi Mimah dake zaune kusa dashi ce tace"wow Hubbi ammafa ƙawar amaryarnan kyakyawace ajin farko".
taɓe baki Namijin duniya yayi kamar wanda yaga kashi ya waigar da kansa gefe yadda bama zaka ɗauka yaga Inteesar ba.
Cikin zazzaƙar muryarta me tafiya da zuciyar duk wani ɗa namiji me lafiya tashiga zazzaga speach kamar wata baturiya yadda take ba kowacce kalma haƙƙintane yasa taƙara burge mutanen gurin uwa uba kuma a natse take komai nata bayan ta gama da yaren turanci ta juya larabci yadda take fitar da harufa bazaka taɓa ɗauka ba balarabiya bace tana gamawa gabaki ɗaya gurin ya kaure da tafi saboda baƙaramun tafiya da hankalin mutane tayiba ta juya zata tafi m.c yace"ranki shidaɗe kitsaya babban abokin ango yazo yabada biography ɗin ango sannan ku zauna a seat ɗin da aka tanaza dominku munason ganin babban abokin ango ɗaya tamkar da dubu uban gayya Sir Abdallah Namijin duniya ".
damm ƙirjin Inteesar yabayar jin sunan wanda aka kira lokaci ɗaya hankalinta yayi mugun tashi amma dayike miskilace bazaka taɓa fuskanta ba tafi gurin ya ɗauka alamun Namijin duniya ya miƙe a hankali ta ɗago lulu eyes ɗinta da suka cika da tsoronsa ta saukesu akansa ɓangaren Namijin duniya ko yanajin abinda m.c yafaɗa yaƙara shan kunu ya ɗauki glass cup ɗin dake kusa dashi kenan yaji wasu abokan kasuwancinsu ɗaya na cewa ɗaya"wow amma gaskiya wannan babe ɗin ƙarshe ce anyako bazan raɓa ba kuwa".
"gaskiya dai Muhseen kayi maza ka raɓa domin tahaɗu yarinyar tunkafin wani ya rigaka domin irin wa'innan sune irin matan da ake layi gurin neman aurensu se me tsananin rabo kesamun aurensu kagafa ga kyau ilimin addini da boko ga nutsuwa uwa uba hankali kai Muhseen inka sameta kagama morewa wlh ga dirin jiki".
"ai da wuri zanyi sauri inje ana tashi zanje insanarmata da kudirin zuciyata ko Allah zesa insamu shiga da aduniya zanga nafi kowa sa'ah".
lokaci ɗaya yaji wani ɓacin rai ya lulluɓesa idanunsa sun canza kala saboda tsananin ɓacin ransu yayi saurin ɗaukar glass cup ɗin ya shanye ruwan tas kozeji sauƙin zugin da zuciyarsa kemasa amma wani canji ga wani abu daya tsayamasa a zuciya na ganin irin shigar dake jikinta .
Sanye yake da white arman suite wanda sukayi matuƙar amsar jikinsa se necktiet ɗinsa data kasance baƙa sumar kansa kamar kullum se sheki takeyi anyimata irin askinnan na zamani wanda an aske gefe da gefe anbar tulun suma a tskiya wadda taketa ɗaukar ido da sajensa tamkar wani balarabe kunnensa sanye yike da ɗan kunne me matuƙar ɗaukar hankali ga wasu shegun sarƙoƙi daya saka suka zubomasa har ciki cike da isa da izza yike tafiya yayinda hankalin ƴammatan gurin gabaki ɗaya yayi kansa saboda a ƙasarma gurin ƴammata haka suke cemasa burin kowacce ɗiya mace ƙarasawa yayi inda Inteesar ke tsaye a hankali ta ɗago fararen sexy eyes ɗinta da niyyar satar kallonsa caraf idanunsu ya sargafe cikin na juna saurin janye idanunta tayi a nasa tare da yin ƙasa da kanta ta ƙarasa inda yike cikin ladabi ta miƙamasa laudspeaker ɗin hannunta bazato taji lallausan hannunsa ya haɗa da hannunta wani irin shock ne ya ziyarci gabaki ɗayansu hakan yasa tayi saurin janye lallausan hannunta a nasa cike da izza gami da taƙama yashiga bada biography ɗin ango yana gamawa gurin ya ɗauki tafi jin yagama sanya Inteesar fara tafiya ba zato taji hil ɗin takalminta ya tafi luuu zata faɗi saurin rife zara-zaran eye lashes ɗinta tayi saboda tarigada tagama sadaƙar da zatajita a ƙasa bazato tajita a jikin mutum wata wawuyar ajiyar zuciya suka sauke a tare sexy eyes ɗinsa da suke kamar na me bacci ya sauke akan zara-zaran eye lashes ɗinta da suka kwanta kamar na kanti sunsha lining da baƙin kwalli ga eye shadow da suka sha lokaci ɗaya yaji tsigar jikinsa ta tashi yarrrr idanunsa sun wani ƙanƙance irin na wa'inda suka kai ƙololuwar buƙatuwa a hankali yashiga yawo da sexy eyes ɗinsa kan kyakyawar fuskarta ya shagaltu da kallonta ɓangaren Inteesar ko jin bata faɗi a ƙasa bane yasa tashiga buɗe oily eyes ɗinta ta saukesu kan kyakyawar fuskar Namijin duniya lokaci ɗaya gurin yaɗauki tafi domin baƙaramun bada style sukayi ba idan kagansu seka ɗauka couples ne saboda matching ɗin da sukayi kallon-kallo suka shigayi hakan yayi daidai da ɗauke wutar gurin bazato taji ya manneta da faffaɗan ƙirjinsa da kowacce ɗiya mace ke burin jinta a gurin saurin haɗe fuskarsu yayi gurin ɗaya yayinda dogayen hancinansu suka haɗe guri ɗaya a tare suka saki wata nannauyar ajiyar zuciya jikinta ne yashiga rawa saƙala kansa yayi ta jikin wuyanta yashiga shinshina wuyanta da kamar anyimasa ɓarin turare akaikai yashiga sauke ajiyar zuciya wadda daga ita seshine kawai sukeji bazato taji saukar numfashinsa daidai kunnenta cikin narkakkiyar muryar dabata taɓajin yayi magana da irinta ba kamar yana yimata raɗa yace"waya baki izinin saka irin wa'innan banzayen kayan keko kunyar fitowa a haka bakijiba jibi wata kwalliya kamar wata aljana kewai a tinaninki kinyi kyau dama zuwa kikayi kika wanke dayafimiki alheri domin mutane dariya suke tayimiki a hakan kike cewa wani bashi da tarbiyya ke ai itan gareki domin dai duk mace me aji datasan darajar kanta bazata saka irin wannan kayan ta fito cikin taron jama'ah ba jibeki kamar wata one ko lankwasa babu".
sosai ranta yakai ƙololuwar ɓaci dashi ta matsar da bakinta daidai kunnensa zatayi magana taji yayi saurin haɗe bakinsa da nata seda ya shanye jambakin bakinta tas sannan ya zame bakinsa a nata cikin muryar raɗa yace"da kinwani saka jambaki kamar wata buranya ke dan bakiga irin munin da kikayi bane temakonkifa nayi domin banaso ina ganin mutane suna miki dariya keko bikiyardaba se wani yanga kikeyi ala dole gani kike kinyi kyau".
a zuciyarta tace"kodai banyi kyau bane dagaske shiyasa naga mutane nata kallona ne bara zan tambayi Khady naji".
a filiko sosai ranta yakai ƙololuwar ɓaci dashi ganin yadda yaketa tattaɓamata jiki bako sisi a sanga hakan yasa tasa hannuwanta da iya ƙarfinta ta tureshi ta sassauta murya yadda iya shikaɗaine zejita tace"to ina ruwanka idanma banyi kyanba kokai ka biyamun" .
"wayema zeyi ɓarnar kuɗinsa kan wannan mummunar fuskar taki dako taushi bata dashi ƙabe-ƙabe take kamar bayan kada ayimiki kwalliya sede wannan ɗan asaran saurayin naki dayaga ze iya".
sosai ran Inteesar yakai ƙololuwar ɓaci idanunta suka fara kyallin fito da ruwa zatayimasa magana kenan wani diff haske me circle yafito a inda suke yayinda wani cool music yashiga tashi bazato taji hannunsa a waist ɗinta yashiga yin rawar nan ta turawa ya wurnata can yayi can da ita kamar wata ƴar baby ganin mutane na kallonsu ne yasa ba yanda ta iya tabishi sukayi rawar bayan sun gama aka dawo da haske ɗaukar tafi gurin yayi lokaci ɗaya suka nufi high table suka zauna yayinda Inteesar tazauna nesa da Namijin duniya.
"Feenerh wai wannan wacce tsinanniyar yarinyarce dahar ta haɗa jiki da Namijin duniya kina zaune Feenerh".
" hmm Zuby kenan to itace sabuwar cleaner ɗinnan danake baki labari kike ganin kamar bata da abinda zata siyi zuciyar Namijin duniya to gadaishi kingani da idanunki har rawa yayi abinda nike burin inyi da Namijin duniya shi wannan kwailar tayi to kindai gani da idanunki keda dabiki ɗauki zancennan serious ba ni dama tunda tazo gurinnan naji na tsaneta wallahi".
sosai ran Zuby yaɓaci a zuciyarta tace"dole inyi maganin duk wanda ze kawomun cikas a rayuwata dakai Abdallah domin kai nawane ni kaɗai ba wata ɗiya mace data isa inyi sharing ɗinka da ita ban kauda itaba".
a filiko sosai ta nuna ɓacin ranta ta dafa kafaɗar Feenerh cikin nuna alhini tace"aiko ƙawata dole muɗauki babban mataki akanta bata isa tazo da rana tsaka ta rabaki da abu mafi soyuwa a garekiba ko itaɗin banza kinkoyi amfani da maganin dana kawomiki kuwa".
"sosaima kuwa amma kinga shiru anyako maganin bokannan kuwa yanayi Zuby domin ni banganin wani canji ko ɗaya".
damm ƙirjin Zuby yabayar amma dake ƴar duniya ce seta make tace"yikai domin bokannan kaf inda su Ummanmu suke zuwa ba wanda yakaishi aikinsan irin wannan aikin ba'ah yimasa garaje kibari mugani nanda sati uku".
"toh mujira amma yanzuma semunje munyiwa wannan kwailar kashedi".
"toh kibari a tashi".
nan sukaita tsinewa Inteesar.
Ɓangaren Mimah ko sosai rawar dayayi da Inteesar ta ƙonamata rai hakan yasa takira Mum a waya kamar zatayi kuka ta zayyanemata abinda yike faruwa daga ɗaya ɓangaren Mum tace"ki kwantar da hankalinki duk duniya Abdallah bashi da wata mata data wuceki ko ubansa be isaba bareshi me akai akayisa dazaki tsaya kina zubarmun da tsadaddun hawayenki ki kwantar da hankalinki karki nunamasa kinji haushin abinda yafaru kinjini ninasan yadda zanyi dashi".
"to Mum".
nanta kashe ta goge hawayenta tayi kamar ba abinda ke damunta.
Sosai aka shiga gabatar da program yayinda gawurtattun masu kuɗi sukaita ɓarin naira kamar basaso har akazo yanka cake ango ya gutsura yabawa amaryarsa a baki itama amarya ta gutsura tabawa ango matsawa Inteesar tayi ta yanko cake ɗin da niyyar bawa Asma'uh yazuba akan tsadadden takalmin Namijin duniya jikinta ne yashiga rawa sakamakon ganin kan takalmin wanda cake ɗin ya zuba lokaci ɗaya oily eyes ɗinta suka tara ruwa murya na rawa tace"sorry Sir".
ɓangaren Namijin duniya ko sosai ranshi yakai ƙololuwar ɓaci a tinaninsa dagangan tayimasa haka saboda ta tozartashi ne gaban abokansa hakan yasa zuciyarsa ta hassala ba abinda yike se huci hakan yasashi zama kan wata resting chair ya ɗaga idanunsa da suka rine saboda tsananin ɓacin rai yazubawa Inteesar da zuwa wannan lokacin hawaye yagama wankemata fuska saboda tsabar tsoron hukuncin dazemata murya na rawa taƙara cewa"sorry sir wallahi bansan yazubarmaka akan takalmiba".
Saurin ɗagamata hannu yayi cikin ɓacin rai gamida isa da izza a gadarance yace"kima bar ɓata bakinki gurin bani haƙuri domin bazan taɓa haƙuri ba sena hukuntaki daidai da abinda kikayimun saboda bakisan darajar kuɗiba shiyasa kika samun wannan ƙazamun hannun naki mara tsarki kika lalatamun takalmi kee wacece".
wasu zafafan hawayene suka shiga sinturi akan kumatunta jin irin rashin mutuncin da yikemata dakyar ta yaƙi zuciyarta dan batason ta biyemasa su raba hali cikin muryar kuka tace"kayi haƙuri sir wallahi bansaniba".
taɓe baki Namijin duniya yayi a gadarance yace"kisa harshenki ki lasheshi na jikin takalmina inkinaso in haƙuri kafin na irga uku ki lashe".
yaƙarasa zancensa tare da ƙara haɗe fuska jin abinda yace baƙaramun girgiza mutanen hall ɗin yayiba a hankali ta duƙa da niyyar lashe cake ɗin kowa yabada attention ɗin lashewa zatayi wasu daka cikin mutanen hall ɗin sun rirrife idanunsu saboda tausayin data basu se buɗe ido sukayi sukaga bata tabar hall ɗin gabaki ɗaya sosai ran Namijin duniya yakai ƙololuwar ɓaci ɗaga idannan dazeyi yaga wata me kama da Inteesar tasa hanky tana sharemasa cake ɗin cikin sanyin murya tace"kayi haƙuri sir".
tana gama faɗin haka tabi bayan ƴar uwarta hakan yasa Namijin duniya ya fice a hall ɗin rai ɓace.
Zaune suke a gaban boka Tsula Uwar gwarama na zayyanemasa labarin Zaid wata uwar dariya Boka Tsula yayi tare da gintseta lokaci ɗaya yace"base kin ƙarasa ba ki kwantar da hankalinki indai kan wannan ƙaramun alhakine indai zaku cika sharaɗan dazan gindaya muku auren Jamilah da Zaidu kamar an ɗaura ne ammafa sede muci galaba akan Zaidu amma wannan sheɗaniyar yarinyar kullum setayi addu'ah shiko yanada sake da ita".
tsaki Uwar Gwarama tayi haɗe da cewa"ai wannan munafukar uwartata kullum seta sasu a ɗaki inajinsu sunyi ai so nike boka duk yadda za'ayi ayi banaso yaronnan ya auri yarinyar nan saboda naci alwashin indai ina numfashi kozan rasa zanin ɗaurawa bazan taɓa barin jinin Aminah yaji daɗin duniya ba seda su gani a wajen wani badai su ba boka kayi koma menene zan aikata nidai buƙata tabiya".
wata uwar dariya boka Tsula yaƙara fashewa da ita lokaci ɗaya ya ɗaure fuska cikin muryasa mara daɗin sauraro yace"sharaɗi na farko shine yau dole in sadu da Jamilah domin akwai wani magani dazan zubamata a jikinta se abu na biyu kuma zan baku wani turare da zatayi hayaƙi dashi zakusha mamaki domin Zaidu zezama tamkar raƙumi da akala tsakaninsa da Jamila se yanda ta juyashi abinda nikeso daku dole inkunyi turaren ya shaƙa inba hakaba akwai gagarumar matsala matsawar be shaƙaba".
wani daɗine ya mamaye zuciyar Uwar gwarama tace"ai boka indai wa'innan ne sharuɗan ba wata matsala bara nabaku guri kaji daɗin zubamata maganin dakyau sannan zamuyi turare dolensa ma ya shaƙeshi dan ubanshi be isa ya lalstamun shiriba Jamilah ki saki jikinki da boka Tsula sosai saboda ya zubamiki maganin sosai yadda lokaci ɗaya mejan kunne ze manta da wannan sakaran yarinyar".
"Toh Ummah kinsandai zan iya bada komai nawa matsawar burina zecika na auren mejan kunne".
"yauwa tawan".
nanta miƙe ta fita baki bukkar boka Tsula ta barsu acan suna sheƙe ayarsu bayan 1hr sega Jamilah ta fito daka bukkar tana gyara zani taƙarasa gurin Uwar gwarama tace"ga na turarenma yabani da kuma wannan wai a barbaɗa a ƙofar ɗakinsu Inteesar ta tsallaks Ummah ".
"yauwa ƴar albarka ki kwantar da hankalinki zakisha mamaki yanda lamari ze canza lokaci ɗaya".
"yauwa Ummah na ina alfahari dake".
"nima haka muyi mutafi dare nayi ".
"toh".
nansuka tafi kowannensu zuciyarsa cike da farincikin samun nasara da suke fata.
10:30pm
Tunda yakoma guest house ɗinsa ba abinda yike ss faman safa da marwa yike yana tinanin irin mummunan matakin daya kamata ya ɗauka kan Inteesar katse shirun da sukayi Ahmad yayi ta hanyar cewa!!!!!!
Votes and Comments
Plz share to others
*Soyayya ɗaya da zaki nunamun sister idan kin gama karantawa kiyi sharing zuwa group goma da kike dashi shine kawai zansan kinayi na over kamar yadda nike yinku over.*
_*Daga Alƙalamun🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
*BOOK 1*
*PAGES* 2️⃣1️⃣➡️2️⃣2️⃣
"Wai yanzu meye abunyi ne yarinyar nan takai maƙura gurin rainaka fa ace tana ƙasanka saboda rainin hankali kasata tayi abu taƙiyi a gaban bainar jama'ah saboda ta nunawa duniya irin rainin data yimaka dole wannan karon mu ɗauki mumman mataki akanta seta