Showing 33001 words to 33748 words out of 33748 words
seda sukayi kuka me isarsu sannan suka saki junansu Hauwah tace"Besty bara na koma gurin aiki".
kai kawai Inteesar ta iya ɗagamata saboda kukan datasha nan Hauwah ta tafi tabarta jiki bakwari ta koma mazauninta na sakatariya a zuciyarta tana mamakin rashin zuwan Namijin duniya.
"gaskiya Ummah kayannan kwata-kwa basu dace da wannan tsinanniyar yarinyar ba da Jameelah suka dace".
"haba Saratu ya kike irin wannan ne ke ai da Jameeha da Aishatu duk ɗaya ne meye abun baƙinciki kowa rabonsa ze samu kidena irin wannan ke babbace memakon kizama me kwantar da fitina seki zama me tayar da ita".
a harzuƙe Uwar Gwarama tayi kan Badi'ah tana huci tace"nace duk biyune karki ƙara haɗamun hafizar ƴata da wannan ƴar barikin yarinyar data gama zubar da mutuncinta a titi ai gaskiya Saratu ta faɗa ai kozan rasa zanin ɗaurawa bazan taɓa bari ɗiyar Amina tayi aure inda zata hutaba kozan rasa koda zanyi yawo tsirara senaga bayanta daka ita har shegun ƴaƴannan nata masu yawon bariki anyako nina haifi wannan salamammar kuwa ni Hajara da a asibiti na haifeki da se ince canzamun ke akayi salamammar banza wadda batasan ciwon kanta ba kika ƙara sakamana abiki wallahi akan maganarmu wallahi sena saɓamiki shegiya ƴar uwartaki kikewa baƙinciki sarkin baƙin ciki kawai me baƙin halin tsiya kawai ".
jin furucin mahaifiyarta ne yasata kama bakinta tayi shiru taji Uwar Gwarama tace"kwantar da hankalinki ƴar albarka meson ganin farincikina wannan lefe da kike gani ba makawa na Jameelah ne kedai kawai ki zuba ido kisha kallo duk wannan ɗan banzancin da sukeyi zasu koma suyi laƙwas dani suke zance ni kaina nasan bani da kyau".
cikin zumuɗi Saratu tace"Allah Ummah kice mufara shirin shiga aljannar duniya kenan".
"sosaima kuwa tawan ki kira su Hafsah ki sanarmusu suma su shirya".
"nagode Mamana takaina Allah yabarmana ke".
"Ameen dai tawan".
Uwar Gwarama tafaɗa ta wurgawa Badi'ah harara shiru tayi suna nan zaune sukaji sallamar Inteesar saurin miƙewa Badi'ah tayi ta fita tsaki Uwar Gwarama tayi haɗe da cewa "sakarai kawai wadda batason ciwon kanta ba kinga ai taji sallamar uwarta har jikinta ke ɓari dan taje gurinta karta tsinemata narasa me Aminah tayiwa Badi'ah ta liƙemusu haka ba".
"ai Ummah aikin asirine wannan kiga dan Allah yadda har jikinta ke rawa kamar mazari dakajin muryar waccan karuwar".
"aiko nafi ƙarfinta wallahi ".
nan Saratu taita zuga Uwar Gwarama.
Da fara'arta tace"nayi fishi sis shine kinsan da zuwana kikayi tafiyarki aikinki".
saurin kama kunne Inteesar tayi alamun bada haƙuri tace"tuba nike babbar yaya nina isa inyi tafiyata inbarki zuwa dai nayi saboda daka yau bazan sake zuwa ba aikuma na dawo da wuri".
"da wasa ma nike sis ɗina kinsan bazan taɓa fishi dake ba tawan naga lefe Allah yasanya Alkhairi yabaku zaman lafiya".
a zuciyarta ta amsa a fili kuma ta rife fuskarta alamun kunya dariya Badi'ah tayi tare da kama hannunta suka nufi ɗakin Ummi wani ɓangare na zuciyar Inteesar ko ba abinda take son ji se dalilin daya hana Man of the world ƙin zuwa gurin aiki ta rasa me bata amsa tambayarta hakan yasata saurin kautar da tinaninshi suka cigaba da hira da ƴar uwarta.
************* Ai Hausa Novels ****************
*************************? **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > [email protected]
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ? **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ? **************************
Cikin sauri-sauri yake sakkowa daga step!!!!!!!!
1-Meyasa Inteesar take yawan faɗuwar gaba?
2-Waye ke sakkowa daga step yana sauri?
3- Jameelah zata auri Zaid kuwa?
4-Man of the world ze tafi da Inteesar UK kuwa zata yadda tabishi kuwa?
5-Aikin boka zeci Zaid kuwa ?
6-Meye asalin maman Inteesar da ake ganin kamar bata da asali?
*Domin jin amsoshin waɗannan tambayoyin kibiya ki karanta cikin salama kuma inkinsan zaki siyane danki fitarmun dan Allah karki siya.*
_End of book one meson jin yadda zata kaya tsakanin Man of the world da Inteesar ya biya #300 Normal grp, vip # 800 , pc 1k ɗinsa ta wannan account number 2411022356 Aisha Umar Ibrahin Zenith Bank aiko da shedar biyanka ta wannan number 08108362334_
_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_rzo.*_