Showing 30001 words to 33000 words out of 33748 words
aiko garin yaƙuna abu ta sille tafaɗi batt ba aba ba labarinta dariya Bokan yaƙara yi haɗe da cewa"kinga wannan abar dana baki da kin cinyeta da shikenan kigama da wani Abdallah domin zuciyarsa gabaki ɗaya na ciro na baki kika wulaƙanta".
dafe ƙirji Feenerh tayi cikin kiɗima tace"kayi haƙuri Boka bansan zuciyarsa bace aida tini na cinyeta dukko da jinin da yike jikinta yanzu ka ƙara bani wata zan cinye yanzu yanzunnan".
"hhh ai aikin gama yarinya ya gama bakin alƙalami ya bushe sau ɗaya muke bada zuciyar ga mutum saura magani na biyu idan kinsamo aikinki zeyi kyau".
wani daɗine ya mamaye zuciyar Zuby ganin aminiyarta tayi loosing ɗin Man of the world hankali tashe Feenerh tace"yanzu Boka ba yadda za'ayi abani zuciyar yanzu kenan".
"babu zancen zuciya yanzu sede kije ki samo hantar ɓauna kuma ki tabbatar da kanki kika soketa ki yanko da ita za'ai mahaɗin maganin".
a gigice Feenerh tace"hantar ɓauna kuma Boka nashigesu ni Nafi ina zansamu wata hantar ɓauna kuma".
wani daɗine yaƙara kama Zuby a zuciyarta tanata farinciki a fili ko ta nunawa tayi kamar tana alhinin abinda ke damun Feenerh murya na rawa Feenerh tace"Boka to meze hana nabaka kuɗi a samo hantar ɓaunar ko nawa kake so a shirye nike dana kashe ko nawane matsawar nidai buƙatata zata biya ".
"hhh ke zaki samo da kanki inba haka ba maganin bazeyi aiki ba dole da kanki zaki nemo".
"toh zan gwada samowa".
"yauwa ammafa karki kuskure kisa wani ya samomiki akwai matsala gagaruma akan hakan kome yaje ya dawo ki kuka da kanki".
"bama zansa kowa ya samo ba da kaina zansamo".
"yadaifimiki idan kin samo kin kawo dashi zan haɗa miki magani ".
"toh".
nansuka miƙe Feenerh ta aje kuɗin dake hannunta suka fita suka tafi ɗan warewa gefe sukayi da Zuby tace"aiko Ummah dole nakomo gobe ni yabani zuciyar na cinye sede taji a salansa domin idan nasamu shiga gurin Namijin duniya nunawa zanyi bansanta ba wallahi zan koyawa yarinyar nan hankali seta gane shayi ruwa ne ai Ummah naji daɗi da bata ci zuciyar ba wallahi".
"kibari mukoma gida karta jimu".
"toh".
nan suka tsuke bakinsu suka cigaba da tafiya.
Washe gari tunda ta tashi da asuba bata komaba kamar yadda tasa ba kullum ta share gidan tass tayi wanke-wanke tana gamawa ta nufi gidansu Hauwah!!!!!!!
Votes and Comments
Plz share to others
_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_ƴar Mut🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
*BOOK 1*
*PAGES* 3️⃣1️⃣➡️3️⃣2️⃣
Tana cikin tafiya taji muryar Jameelah daka bayanta tana cewa"Aunty Inteesar nima zanbiki ayi aikin dani".
juyawa inda take Inteesar tayi zatayi magsna cikin tsiwa taji Khadijah tace"bama gayya a ƙara gaba ke bama kiji kunyar cewa zaki bita ba saboda ke ɓera ce karfa ki manta itace wadda kuka tsana ɗinnan kuka hanata sakat a rayuwa wadda bakwason ganin cigabanta itacefa wannan karuwar da kuke cewa wadda kuke cewa bawani karatu se yawon tazubar duk wannan be isheku ba saboda ke ɓeran masallacci ce ba kunya bare tsoron Allah kika wani yayimo wani tsumma jikinki wai zaki bita to ba inda zakije bama gayya umma tagaida Ashsha ki ƙara gaba hanyar jirgu daban ta mota daban kuma karki ƙara kiran yayata da Aunty kije can ki nemi Aunty a can badai nanba".
juyawa Jameelah tayi jiki ba kwari saurin kamo hannun ta Inteesar tayi tace"rabu da ita Jameelah kizo muje kekuma banason iskancin banza ko ke tace zatabi da zaki wani sakawa mutane baki taho mutafi bakomai sister".
"nagode Aunty Intee".
"bakomai sister".
"ai gaskiya ce dole infaɗamiki maƙiyinka har abada maƙiyinka ne ko ya zo ya nuna yanasonka ƙarya yike kullum bashi da burin daya wuce yaga bayanka shine saboda ke damo ce sarkin haƙuri mutum yagama takaki yadda ransa yikeso yazo kuma ya shigemiki ki ansheshi lokaci ɗaya ba dolema mutum gobema yaji daɗin hayemiki ba ai yaci ace ki nunamata kurenta koda zaki ansheta".
wata uwar harara Inteesar ta bankawa Khadijah ta kama hannun Jameelah suka shige gidansu Hauwah suka barta nan tsaye baki buɗe ta wuce cikin gida tanata masifa.
Suna shiga suka samu su Hauwah dasu Momynta sun kammala aikin snacks ɗin har sun fara celling ɗinsu da raping sheet turus tayi haɗe da kama haɓa ta ware fararen sexy eyes ɗinta tace"badai har kun gamaba Momy".
hararta Hauwah tayi tace"da jiranki zamu tsaya yi ne alanƙosa aida mun tsaya jiranki da ƙila sede muji kunya domin ke ɗinnan yadda kike da nawa ina tinanin a gidanki Uncle Zaid zesha fama dake".
damm ƙirjin Jameelah yabayar sakamakon tinowa datayi yau za'ah kawo lefen Zaid da wata bada itaba har yau be kirata ya sanarmata da yanason ta ba tana cikin wannan tinanin taji muryar Inteesar cikin shagwaɓa tace"Momy kinji Hauwah tana cemun wai alanƙosa".
murmushi Momy tayi tace"rabu da ita ƴar albarkana itace alanƙosa domin itama yanzunnan fitowarta kenan ta zauna ba abinda takeyi se aikin ci daka ni se Hindatu mukayi aikin komai kuma ma inban dage na fitar da ɗiyata kunya ba wazan fitar rabu da ita".
gwalo Inteesar tayiwa Hauwah haɗe da cewa"muje Jameelah".
"toh Aunty".
nan suka tafi sosai su Momyn Hauwah suka yi mamakin ganin Inteesar da Jameelah amma sesuka make zama suka yi suka tayasu raping ɗin kayan suna gamawa Inteesar tace"Jameelah ki iba ki ɗanɗana".
"toh Aunty".
nanta ɗauki komai ɗaya taci itama Inteesar ta ɗauka ta ɗanɗana suka taya Hindu me aiki kai kayan cikin gida bayan sun gama kamar gaske Jameelah tace"Aunty bara naje gida na shirya tunda naga har angama aikinma".
"toh sis".
nanta fita sukuma suka nufi ɗakin Hauwah suna shiga suka zauna kan ɗan madaidaicin gadon Hauwah taɓa Inteesar Hauwah tayi tace"wai Besty ya akai naganki da wannan yarinyar ne".
"wacce yarinya fa".
"hmm gaskiya Besty rainin hankalinki yawa ne dashi wacce yarinya nike nufi bayan Jameelah naga yarinyar nan ba wadda ta tsana sama dake kika wani jawomana ita ke bakya tinanin ko turota akayi dantaga abinda mukeyi ba".
"hmm keda Khadijah kuna bani mamaki wallahi na taho zanzo nan gidan yarinya tacemun zata bini so kuke na koreta shi ɗan adam ba'ah masa haka bakasan ranar da zemaka ba shi ɗan adam rana garesa ko biki taɓa karanta littafin marubuciyar nan ba Real eeshow mesuna BAR RAINA ALLURA (Itama ƙarfe ce) labarin ya ƙayatar dani sosai saboda marubuciyar ta nuna duk yadda mutum yakai da ƙinka a rayauwa be isa ya hanaka samun rabonka ba duk ƴinshi dakai ita rayuwa haka take zakaga kaƙi mutum ƙarshe shiɗin dai daka raina gaba shize temakeka gaskiya zan turomiki da littafin ki karanta zaki faɗakantu sosai labarin Sajida duniya ne".
"eh dai naji amma kinsan wani abu idan kika cigaba da wannan haƙurin naki mutane zasuyita cutarki saboda yarinyar nan da uwarta inda za'ah basu wuƙa ace su kashe wani abu da suka tsana wallahi ke zasu kashe nifa na tsanesu wallahi".
"dan Allah mubar wannan zancen batashi nike ba tin jiya narasa gane kan Zaid tunda yabar gidanmu na kirashi ya ɗaga ko magana be bari nayi ba yacemun wai aiki yikeyi idan yagama ze kirani shiru-shiru inata jira ya kirani be kirani ba dana daɗa kiranshi be ɗauka ba har zuwa yau idan na kirashi baya ɗauka na biki yadda nikejin zuciyata ba na riga na saba da waya dashi wallahi jiya se wajen huɗu bacci ya ɗaukeni hankalina har yanzu yaƙi kwanciya wallahi".
dariya Hauwah tayi ta kama baki tace"oh su Besty anyi nisa ba'ah jin kira wannan irin ƙauna haka harda ƙinyin bacci lallai Uncle ɗina ya iya love irin wannan mutuwa haka da kikayi kansa haka sefa kina mishi uzuri tunda kinsansu masu kuɗinnan sunada sabgogi a gabansu bare kuma satin biki yakama dole sekinmasa uzuri romeo".
"eh najin inban damu da mijin dazan aura ba wa kikeso na damu dashi amma aida baya iya bacci har seya yimun addu'ah na kwanta sannan muke sallama a waya shiyasa jiya nakasa bacci".
"hhh dole Besty ki kasa bacci tunda yariga yagama shagwaɓaki dole kice kinkasa bacci niko Allah muntuba aini gani nike ba'ah yo mutumin dazan kasa bacci ba dominsa ba gaskiya".
"hmm haka dai kikace dandai har yau baki haɗu da wanda kike so bane shiyasa wayasanma ke me zaki gwarama ni anga nawa".
"hhhh".
nan suka cigaba da hirasu da ƴan tsare-tsaren ansar kaya.
Kwance yake akan tamfatsetsen italian bed ɗinsa idanunsa a lumshe kamar me bacci tsaki yayi haɗe da buɗe sexy eyes ɗinsa yace"anya ko wannan yarinyar ba mayya bace ba kuwa meyasa dana rife ido ba abinda nike gani se ita gaskiya inko ba mayya bace ƙila ta haɗa iri dasu take ƙoƙarin cinyeni koma dai menene Allah yafiki stupid kawai".
ƙara sakin wani tsakin yayi yaƙara lumshe idanunsa nanma still ba abinda yike gani se ita tsaki yaƙara yi yaji an turo ƙofa anshigo wasu english wears ne jikinta wando da riga wandon iyakarsa guiwarta jeans baƙi se rigar sky blue me ratsin net daka gurin ƙirjin baƙaramin kama jikinta kayan sukayi ba tasha uban kitson atarch har ɗuwawu tana tafiya ko ina na jikinta na motsawa hannunta ɗauke da cup ɗin coffe jikin drawer ta nufa da niyyar aje coffeen dake hannunta caraf idanunta ya sauka kan faffaɗan ƙirjin Abdallah dake cike da gashi irin na jaruman maza masu ji da class se ɗaukar ido gashin keyi shedar yana shan gyara tana ajewa ta juya idanunta ya rife ta kai hannu da niyyar taɓawa taji ya dakamata tsawa haɗe da cewa"ke wacece irin tinkiya ce mara tarbiyya waya baki izinin shigomin part da har kika wuce falo kika shigomin bedroom with out my permission dakin bari wannan ƙazamun hannun naki ya taɓamun jiki da sekin raina kanki domin wallahi da sena nunamiki true colour ɗina ".
sosai yayimata kwarjini lokaci ɗaya ta diririce murya na rawa tace"dama Yah Abdallah coffee na haɗomaka".
batare daya buɗe sexy eyes ɗinsa ba yace"nacemiki ina buƙata ne da zaki shigowa mutane bedroom bako sallama saboda rashin hankali ko da ke kike bani coffee ɗin ko ancemiki ni inashan coffee ɗin kowanne tom and jerry ne irinki kinfice da tsiyarki kinbani guri ko sena tashi stupid kawai mara aji".
saurin ɗaukar coffen ta tayi jiki na rawa ta fice tana fita yayi tsaki ya miƙe tare ɗaura towel ya nufi toilet.
4:00pm
Hauwah na shirin shiga gidansu Inteesar wasu haɗaɗun motoci guda huɗu suka yi parking biyu hilux biyu Parado baƙaƙe se ɗaukar ido suke parking suka yi daidai ƙofar gidansu Inteesar wasu haɗaɗun matane dattijai wanda bazasu gaza shekaru 50 ba suka fito daka mota ɗaya su biyu amma inkagansu seka ɗauka ƴan shekaru talatin da biyar ne saboda yadda jikinsu ya nuna kana ganinsu kasan sun jiƙu da naira ɗaya motar kuma wasu matane su huɗu matasa masu jini a jika suka fito masu tsananin kama da Zaid musamman ma ƙaramar cikinsu sauran hilux ɗin biyu kuma shaƙe suke da akwatuna wani daɗine yakama Hauwah ta nufi inda suke cikin girmamawa tace"Ina yininku".
"lafiya ƙlau badai kishiyar tawa bace daiko data kwacen miji na bace ko" .
cewar ɗaya daga cikin dattijan dariya Hauwah tayi tace"Babah ba ita bace ƴar uwarta ce ita tana can gidan".
tafaɗa ta me nuni da gidansu sosai taji daɗin jin wannan kalaman daka bakin wannan matar hakan ne yaƙara tabbatarmata da dangin Zaid suna son aminiyartata nan tayimusu jagora zuwa cikin gidan ɗaya daga cikin matasan matannan ce tace"amma dai sister zaki kaimu inda amaryar tamu take ko".
"insha Allah zankaiku".
"yauwa Jabeer ku shishigo da kayan ".
"toh ranki shidaɗe".
cewar Jabeer nan suka shige gidansu Inteesar .
Bayan sun gama gaisawa ne su Jabeer suka fara shigo da haɗaɗun akwatuna seda suka shigo da akwati sha biyu nan aka shiga buɗa akwatunan dake shaƙe da kaya tsadaddun kayane ƴan ubansu a ciki kowanne da takalminsa da mayafinsa da jakarsa sosai murna gurinsu Khadijah da Hauwah ba'ah cewa komai tun suna ƙirga kaya har suka dena domin Zaid yayi ƙoƙari sosai nan Momynsu Hauwah tasa su Hauwah su fito da snacks ɗin da sukayi aka aje a gabansu da kuɗin tukuicin da Abban Hauwah ya bayar dubu goma aka basu har an aje akasa aka kaisu mota Hauwah tayiwa wannan budurwar rakiya zuwa gidansu suga Inteesar .
Kwance take tana karatu littafi taji shigowarsu Hauwah ba tare data tashi daka inda take ba ta amsa sallamar su Hauwah shiga sukayi suna shiga ƙanwar Zaid a zuciyarta tace"wow gaskiya dole bro ya gigice amma gaskiya ta haɗu ko ni mace nasan ta haɗu balleshi da yike namiji kalli gashinta dan Allah har gadon baya".
tana cikin zancen zucin taji Hauwah tace"Besty ga ƙanwarki tace tana son taga wadda ta susutamata Yayanta".
rife fuska Amna tayi tana dariya tace"Aunty ina yini".
murmushi Inteesar tayi tace"lafiya ƙlau Amna ko".
ɗagamata kai tayi bayan sun gaisa suka kawomata ruwa tasha suka ta miƙe nan suka mata rakiya a bakin get ɗin gidansu Hauwah Inteesar ta tsaya tare da ɗagamata hannu alamun bye-bye sannan ta juya.
Ɓangaren Uwar gwarama ko tunda taga irin dukiyar da Zaid ya kashe a lefen Inteesar hankalinta yaƙara tashi takasa zaune takasa tsaye ko gurin lefan bataje ba saboda tsananin baƙin cikin dake damunta ga Jameelah ta tasata a gaba se kuka takemata kan ita har yau bataga alamun Zaid baze auri Inteesar ba hankalinta inyayi dubu ya ɓaci ta rasa inda zata saka kanta taji daɗi.
Washe gari suna tashi suka tafi gurin aiki da wurwuri suna isa Comphanyn kowacce ta nufi gurin aikinta a hankali take tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki yayinda zuciyarta ke dukan uku-uku sakamakon tayi fashi bata sanarmasa ba a hankali ta tura ƙofar office ɗinsa yayinda zuciyarta tashiga bugawa da sauri -sauri kanta a ƙasa tashiga!!!!!!
_*Ga meson karanta book two ɗin MAN OF THE WORLD nafara post ɗinsa a paid group ɗina domin book two na kuɗine akan farashi mafi sauƙi naira #300 domin neman ƙarin bayani ki tuntuɓi wannan number koda kuɗinka seda rabonka 08108362334.*_
Votes and Comments
Plz share to others
_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_anen Gwa🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
*BOOK 1*
*PAGES* 3️⃣3️⃣➡️3️⃣4️⃣
Samun office ɗinsa tayi bakowa a ciki se ƙarar a.c dake ta faman aiki da mayataccen ƙanshin turarensa daya kama office ɗin waige-waige tashiga yi gani tayi bataga alamar yazo ba sosai tayi mamakin rashin zuwansa da wuri domin tasan yana rigata zuwa duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta tayi taga har goma tayi zuciyarta ce tacemata"ke meye naki na damuwa dan wannan mara mutuncin bezo ba aikyama fi sakewa da binki da yikeyi da wa'innan mayun idanun nasa masu firgita mutum".
tana gama faɗin haka a zuciyarta ta taɓe ɗan ƙaramin pinky lips ɗinta ta wuce toilet tashiga aikinta tana gama wankin toilet tashiga goge chairs and tables ɗin dake cikin office tana gamawa ta share ko ina fes ta gyara ko ina yazama neat ta nufi gurin zaman sakatariya ta zauna ta shiga duduba takardun dake kan tables ɗin kamar an tsikareta ta miƙe tare da kallon tamfatsetsen agogon dake manne a office ɗin ta nufi cikin office ɗinsa tana shiga ta nufi drower dataga room freshners ta ɗauki ɗaya daga cikinsu tashiga fesawa ko ina na gurin ta wani toshe hanci tana cikin mitarta Hauwah ta shigo bakinta ɗauke da sallama amsamata tayi ta cigaba da fesa room freshner ɗinta ƙarasawa inda take Hauwah tayi tare da cewa"Besty wai yanaga kinata faman toshe hanci sekace wadda taji wari bakiji yadda kika cika room freshnern nanba har hawa ka yikeyi ".
"ai warinne domin turaren wannan mutumin har hawa kai yikeyi sabo da rashin daɗin ƙamshinsa har tasarmun da zuciya yikeyi wallahi inji kamar zanyi amai ".
"hhh Besty banda dai sharri dandai kuna faɗa dashine shiyasa kika tsaneshi amma ai Sir Abdallah komai nasa na daban ne ni tunda nike bantaɓa jin irin ƙamshin turarensa jikin wani kinsanfa shiɗin duniya ne ".
taɓe baki Inteesar tayi haɗe da cewa "Besty Allah bazancen sharri bakuma tsanarsa nayi ba kawai halinsa na tsana na girman kai da ɗagawa da nuna shi wanine uwa uba rashin tarbiyya da rashin ganin girman nagaba dashi ko kunya bayaji mutanen da suka girmesa suyita duƙawa suna gaishesa sekiga seya ɗauki lokaci saboda isa da izza sannan ze amsa wa'innan halayen nan nasa na mugun ɓatamun rai wallahi shi ko kunya bayaji isa kamar wani basarake".
"hhh ni banga wata izzaba kedai kawai dan bakwa shiri dashine shiyasa kike ganin kamar bashi da kirki amma Sir Abdallah yanada kirki sosai ga sanin yakamata".
zaro sexy eyes ɗinta tayi haɗe da cewa"wannan mutumin ne yasan yakamata tabɗi a rashin samun wa'inda suka san yakamata ƙila a ɗaukeshi domin wannan mara tarbiyyar mutumin ko hanyar inda yakamata tayi bebi ba".
"to maida wuƙar bani nakar zomon ba rataya aka bani Besty ba wannan yakawoni ba gani nayi har 12pm tayi so nike yau mutafi da wuri saboda mufara tsare-tsarenmu ina tinanij daka yau ba lallai bane muƙara zuwa office ba inaso a gyarawa Uncle Zaid ke sosai dan karya rainamun ke ".
"dama nima yanzu nagama tinanin hakan yau tunda na tashi gabana keta faɗuwa na rasa dalili kome yake faruwa oho jinike kamar wani abu ze faru dani".
" insha Allahu Besty ba abinda ze faru dake se Alkhairi kinji Bestyna kedai kawai idan kinji haka ki riƙa Innalillahi wa'innah ilaihi raji'un ki yawaita addu'ah wajan biyu zamu tafi kisan dabarar da zakiyiwa Sir Abdallah".
sauke numfashi Inteesar tayi cikin sanyin murya tace"nagode Bestyna Allah yabarmu tare keɗin mahaɗin rayuwata ce Besty kinmun komai na rayuwa kullum baki da burin daya wuce kisani farinciki Besty nagode da kulawarki gareni Allah nima kabani ikon temakon wannan baiwa taka ".
taƙarasa zancenta hawaye na niyyar zubowa daga lulu eyes ɗinta girzgizamata kai Hauwah tayi alamun kar tayi kuka tace"Besty banason godiyar nan da kikemun domin nasan inke kike da damar da nike da ita da ba abinda bazakimunba toni meyasa bazan mikiba bayan inada halin yi domin keɗin kin wuce ƙawa a gareni ƴar uwata ce dan Allah duk abinda zanmiki kidenamun godiya".
saurin rungumeta Inteesar tayi haɗe da fashewa da kuka