Showing 3001 words to 6000 words out of 22282 words
rayuwa da ita domin se yanzu nagane ba ajina bace Jameelah ce daidai da class ɗina".
A gigice Muhseen ya ɗago jin furucin abokinsa murya na rawa yace"anyako Zaid kana cikin hankalinka kuwa Jameelah fa ƙanwar Inteesar wanne irin mummunan abu kake ƙoƙarin aikatawa haka".
duƙawa Zaid yayi a gaban Muhseen kamar wanda zeyi kuka yace"niko nasan menake cewa Muhseen zancen gaskiya bazan kwari zuciyata ba na tilastata kan abunda bataso ba dan Allah ina roƙonka daka tayani neman mafita domin idan na rasa Jameelah wallahi zan iya samun babbar matsala Inteesar kuma dan Allah kazo muje nabata haƙuri domin gaskiya yanzu bana ra'ayinta……".
cikin tsananin ɓacin rai Muhseen ya bugamasa tsawa tare da dakatar dashi da hannu yace"nagaji da jin wa'innan miyagun kalaman naka marasa daɗi kuma bari kaji infaɗamaka karka indai seda sa hannuna zaka samu Jameelah wallahi bazaka taɓa samunta kuma daka ranar daka aikata wannan mummunan aikin da kake ƙoƙarinyi karka ƙara nuna kasanni domin ni bazan iya rayuwa da mutum butulu irinka ba mayaudari wanda besan abinda kemasa ciwoba mezaki da ragowar maza yarinyar daba abinda tasani sebin maza".
a zafafe Zaid yaci kwalar Muhseen yana huci idanunsa sun rine se uban huci yake yace"kai waye da zaka riƙa faɗan munanan kalamai akan farincikina to bari kaji infaɗamaka abinda bakasani ba kan Jameelah a shirye nake dana ɓata da uban kowa dan haka iname gargaɗinka da indai kanaso mushirya dakai kaso abinda nake so ".
fizge jikinsa yayi daga riƙon da Zaid yayimasa cikin ɓacin rai Muhseen yace"ni ba kowa bane face abokinka meson ganin cigabanka amma tunda kace zaka iya ɓatawa da uban kowa kasani daka yau bani bakai kowa ya kama gabansa ko a hanya kaganni karka ƙara nuna kasanni ka manta dani a babin tarihin rayuwarka banza butulu kawai".
a harzuƙe Zaid yace"seme ninamafi son haka sarkin takura kawai kai kaje ka aureta man shine zan tabbatar dakai ba butulu bane ɗan sa ido kawai rayuwarka ko tawa".
nan Muhseen yafice rai ɓace tsaki Zaid yayi yacigaba da shafarshi yana gama saka kaya wayarsa dake kan gado tashiga ringing zama yayi a gefan kan gadon tare da jawo wayar hakan yayi daidai da katsewar kiran buɗe wayar yayi yashiga cal log dan duba waye mekiran wani kiran yaƙara shigowa baƙuwar number ya gani har ze jefar da wayar yafasa ya ɗaga tare da karata a kunnensa daga ɗaya ɓangaren Jameelah naji anɗaga tasaki doguwar ajiyar zuciya tare da cewa"Yah Zaid ina yini".
jin muryarta ne yasashi lumshe idonsa haɗe da buɗe lokaci ɗaya yace"lafiya ƙlau dawa nake magana".
yaƙarasa faɗi tare dason ƙara tabbatarwa dakansa ba gizon data saba yimasa bane murmushi Jameelah tayi me sauti wanda yaƙara narkar dashi a duniyar ƙaunarta taƙara narkar da murya tace"au Yayana baka ganeni bane ƙanwarka ce Jameelah".
"a'aahhh kice Malama ce".
"eh Yayah nice ya gida dasu Ummah".
"lafiya ƙlau ƙanwata ya dalibanki".
"Alhamdulillah ai se anjuma zasu zo Yayah".
"ok masha Allah Malama Jameelah yaushe nima za'ah fara koyamun karatun nima".
dammm ƙirjinta ya buga sakamakon jin ze ƙureta dakyar ta aro jarumta tace"haba Yayah aiku manyanmu ne kune masu koyamana mukuma mu koyawa na ƙasa damu".
"a'aaah ƙanwata kice dai bazaki koyamunba dai".
"zan koyamaka man amma ba yanzu ba dama kira nayi naji ya lafiyar Yayana".
"aiko naji daɗi ƙanwata idan da kina free baki da wa'inda zaki koyawa karatu anjuma danazo kin rakani unguwa".
"kaji Yayah meze hanani rakaka aiko sunzo nabasu haƙuri na tafi raka babban Yayana inmun dawo na koyamusu kazo kawai na rakaka baka da wata matsala".
"nagode ƙanwata da kulawarki gareni idan kin shirya kiyimun flashing senazo na ɗaukeki mutafi".
"bakomai Yayah ka taho yanzu mutafi a shirye nike nanda 8pm ma dawo".
"toh gani nan zuwa".
"yauwa".
nanya kashe tare da ɗaura wayar a ƙirjinsa ya rungume yanajin ƙaunarta naƙara nunkuwa miƙawa yayi yaje bakin mirrior yaƙara turare a jikinsa tare da saka hula matching ɗin kayansa ta ɗauki wayarsa da car key ɗinsa ya nufi down stairs.
A falo yasamu Mum ɗinsa da Yasmeen zaune suna hira cikin girmamawa yaƙarasa inda suke ya langwaɓar da kansa tare da cew"Mum sannu da hutawa".
"yauwa Son ina zuwa haka naga kasha uwar kwalliya kamar wanda zashi gasar kyau kodai gurin ɗiyae tawa zaka".
sosa ƙeya yayi alamun kunya tare da cewa "eh Mum can zani".
"ok idan kaje kace ina gaisheta".
"zataji".
Yasmeen da kanta ke cinyar Mum ce tace"Yayah wai wanne event Aunty zatayine naga guri na ƙurewa har yau bamu sani ba".
dammm ƙirjinsa ya buga yawun bakinsa ya ƙafe lokaci ɗaya a zuciyarsa yace"bazan sanar daku gaskiyar al'amari ba domin nasan halin Mum zata iya yimun wani abun".
yana cikin zancen zuci yaji muryar Mum tace"kayi shiru saboda tanaso tashiga cikinsu ne ayo komai da ita".
wata dabara ce tafaɗomasa yasaki murmushi yace"Mum nima na tambayeta mezatayi tace wai ita batason ayi bidi'ah a bikinta batason komai wai idan akayi bidi'ah a biki befiye albarka ba na rasa yadda zanyi da ita dana dameta da maganarma harda yimun kuka nikuma banason abinda zeriƙa ɓatamata rai shiyasa na haƙura nima".
Murmushi Mum tayi a zuciyarta tana ƙara godewa Allah daya bata kamilar suruka a fili kuma tace"aiko daughter bata isaba dole ayi ko kamune duk salahancinta kuwa ina za'ayi biki sulungudi kamar na mutuwa".
"wlh kuwa Mum kinji Auntynnan tawani kwafsa mana data bari ansha shagali aida ba haka ba nifa harta ɓatamun rai ".
murmushi Mum tayi tace"da gaskiyarta gaskiya yarinyar nan tanada hankali shiyasa nake ƙara godewa Allah dayayimun kyautarta a matsayin suruka samun irinta a wannan zamanin se an tons kariƙa dakyau Zaid domin yarinyar bata da laifi insha Allahu zan kula da ita tamkar Yasmeen ka gaisheta kace nace dole ayi kamu".
"zataji Mum sena dawo".
"toh seka dawo Allah ya tsare".
"Ameen ".
nanya fita yabar Mum da Yasmeen sunata yabon Inteesar.
Direct unguwar su Inteesar ya nufa ya tsaya daka ɗan nesa da gidansu yayi parking yayi hakan yayi daidai da fitowar Hauwah zata shiga gidansu Inteesar daga nesa ta hangi kamar motar Zaid mamakine yakamata ganin ya tsaya nesa da gida shiga gida tayi cikin sauri Jameelah dake raɓe a zaure tana ganin wucewar Hauwah cikin sauru ta fice ta nufi inda yayi parking tashiga yaja suka ɗauki hanyar oasis.
Samun Inteesar tayi ta fito daga wanka se ƙamshi ketashi sakamakon anfara yimata gyara cikin girmamawa tace"Ummih sannu da hutawa".
"yauwa Hauwah".
"Inteesar kunyi waya da Uncle Zaid ne naga motarsa a ɗan nesa da gidannan".
"a'ah mekika gani ".
"motarsa nagani aɗan nesa da gidannan ".
"ko ɗaya wataƙila gurin Abbah yazo zasuyi wata maganar".
"ƙila kuwa".
nan suka cigaba da hirarsu batare da zargin komai ba.
Suna isa Oasis yana gama parking cikin shaukin so yace"ƙanwata bara na buɗemiki saboda banaso kina aikin wahala".
"kaji Yayah daka barshi ma na buɗe aiki ni nake aikin abincin gidanmu gabaki ɗaya".
"eh dai kidaibari na buɗemiki".
"toh".
nan ya fita ya zaga ya buɗemata suka fito suka nufi cikin gurin ɓangaren Namijin duniya ma baƙaramin siyayya yayiwa su Rahama ba shikuma yasamu seat ya zauna yasa sukayi oder duk abinda sukeso aka kawomusu bayan sun gama cine yabawa Rahama atm card ɗinsa aka ciri kuɗin abubuwan da suka siya yayi gaba suna binsa a baya necklace ɗin dake hannunsa ce ta faɗi ya duƙa da niyyar ɗakkowa kafin yakai ƙasa Zaid ya rigasa!!!!!!!!!
*Kuyi haƙuri Sisters bani da lafiya se yau na samu sauƙi dan Allah ku sakani a addu'o'inku .*
Votes and Comments
_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow
_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_
Book 2
4️⃣1️⃣➡️4️⃣2️⃣
Yana ɗagowa da niyyar basa sukayi ido huɗu da Namijin duniya kallon-kallo suka shiga yi yayinda Namijin duniya ke jifansa da kallon tuguma cikin inda-inda Zaid yace"Ina yini Yah Abdallah".
"lafiya ".
yana gama faɗin haka ya miƙa hannu ya anshi necklace ɗin hannun Zaid ta gefan ido ya kalli wadda ke gefan Zaid a zuciyarsa yace"kenan yaudarata yakeyi".
rasa me basa amsa ne yasashi fara tafiya yana mamakin abinda idanunsa suka ganemasa lokaci ɗaya yaji wani abu na tasomasa daga zuciyarsa se huci yakeyi yayinda yakejin haushin kowa direct gurin da yayi parking ɗin motarsa yashiga tare da jingina da jikin seat yanajin zuciyarsa na mugun tafarfasa a zuciyarsa yace"meyasa zeyimata haka seda yarinya ta aminta dashi shine ze zage yariƙa cin amanarta aiko yazama dole na ɗauki babban mataki akansa ".
wata zuciyarce tace"tokai meye naka na damuwa da yarinyar da bata ganin darajarka yaje yayita yaudararta matsalarsu".
wata zuciyar ce tace"yazama dole ka kula da rayuwarta tunda a ƙarƙashinka take kaje kawai ka faɗamata koda zata gwasaleka shine kawai mafita".
jin shigowar su Rahama ne yasashi buɗe rinannun idanunsa da yaketa ƙoƙarin ɓoye damuwarsa yashiga yiwa motar key dafa kafaɗarsa Rahama tayi tare da cewa"Yayah meyasa naga gabaki ɗays mood ɗinka ya canza daka haɗuwa da Yah Zaid lafiya".
ba tare daya kalleta ba yace"bakomai sweetheart muje nakaiku gida inada wani mahimmin aiki a office ".
"toh mutafi tare man Yayah".
"a'ah bari na kira Salisu driver yazo yamaidaku gida".
"toh".
nan yayi dialing number Salis yayimasa kwatancen ta hanyar da zasu haɗu yabada su ya nufi office ɗinsa cike da zaƙuwar son yaganta.
Ɓangaren Muhseen ko yana isa gida ya nufi part ɗin Abbansa zaune ya sameshi yana karanta jaridah Amminsa na haɗamasa tea ƙarasawa yayi cikin falon ya zauna kusa Abbansa yayi ƙasa da kansa kamar me neman wani abu yace"Ammih sannunku da hutawa".
"yauwa Auta waya taɓamunkaine ".
cewar Abbah yana aje jaridar dake hannunsa yajawo Muhseen jikinsa kwantar da kansa yayi a cinyar Abbansa tare da cewa"ba Zaid bane".
"me aminin naka yayimaka".
cewar Amminsa tana miƙawa Abbansa tea turo baki yayi kamar wani ƙaramin yaro yashiga zayyanewa su Amminsa duk abinda yafaru har abinda Zaid yayimasa be rage komai ba seda ya faɗamusu murya a raunane yace"Abbih dan Allah inaso kuyimun wata alfarma".
"faɗi Auta kota mecece indai munada halin yimaka zamuyimaka".
sauke numfashi Muhseen yayi tare da cewa"Abbih batama fi ƙarfinku ba dan Allah ku temakeni kuyimun ".
"faɗi munajinka".
cewar Amminsa dake maida hankalinta garesa ƙasa yayi da kansa yana wasa da ƴan yatsunsa tare da cewa"dan Allah Abbih inaso indai Zaid ya fasa auren Inteesar ku ɗauramun aure da ita a ranar kuma misalin lokacin ɗaurin aurensa da ita banaso a fasa komai".
shiru gurin gabaki ɗaya ya ɗauka zuciyar Muhseen se bugawa takeyi da sauri-sauri gani yakeyi dakyar idan iyayensa zasu yadda gyaran muryar da Abbansa yayine yasa jikinsa ƙarayin sanyi a zuciyarsa yanata addu'ah muryar Abbah ce ta katseshi daga dogon tinanin daya shiga yaji yace"indai wannanne Auta ka kwantar da hankalinka indai yadda ka faɗamana zancennan haka yake insha Allah zan nemamaka aurenta".
cikin farinciki Muhseen ya rungume Abbansa tare da cewa"nagode Abbana maganin kukana ina alfahari da samunka a matsayi mahaifina I love you Abbah".
murmushi Ammih tayiwa tilon ɗan nata ganin yadda yaketa farinciki tace"wato ni baka alfahari dani ko".
saurin sakin Abbah Muhseen yayi tare da rungume Ammih yace"niko nake alfahari da uwata datafi ta kowa a duniya amma Abbah karka faɗawa kowa wannan zancen a gurin ɗaurin aure idan yafasa sena aureta domin banaso duniya tayimuj kallon maci amanar abokinsa".
"toh Allah ya nunamana".
"Ameen".
nsnsuka cigsba da hirarsu daka bisani Muhseen ya nufi part ɗinsa ya kwanta a makeken gadonsa tare da kara wayarsa a kunne tare da cewa"ƙawar amarya se yanzu naga miss call ɗinki".
"eh dama kira nayi naji ya zancen schedule ɗin biki najiku shiru kuma abu se matsowa yakeyi ko ƙunshi bamuyiba".
murmushin takaicin abubuwan da abokinsa keyi yayi tare da cewa"turomun da account number ki nasakamuku kuɗin ƙunshi shaf na manta ne muna cikin hidima munata tsara event ne".
"okay toh bara na turomaka ".
"tom".
nan sukayi sallama yanamaijin tausayin Inteesar.
Yana shiga Comphanynsa ko parking beyi mekyauba ya buɗe ya fita ko takan masu gaidashi bebiba ya nufi gurin elevator yashiga ya nufi office ɗinsa mutane se gaidashi sukeyi bemasan sunayi ba ya tura ƙofar office ɗinsa da ƙarfi kalloj kujerar Sakatariya yayi yaga ba kowa hakan yasashi cikin sassarfa ya buɗe ƙofar da zata sadashi da office ɗinsa yana buɗewa sansanyan ƙamshin room freshner daya haɗe da sanyin ac ya bugi hancinsa lumshe sexy eyes ɗinsa yayi yana shaƙar daddaɗan ƙamshin tare dabin ko ina na office ɗin da kallo gani yayi ko ina fes dube-dube yashigayi koze ganta ganin beganta anan bane yasashi nufar toilet direct ya buɗe nanma beganta ba jiki ba kwari yakoma kan ɗaya daka cikin kujerar office ɗin yazauna tare da tinanin ta inda zefara nemanta yabata shawara kan karta yarda ta auri Zaid ba mutumin kirki bane ganin bashi da wata mafita yasashi fita ya shiga motarsa nufi unguwar daya taɓa ajeta yana tinanin koze ganta ya daɗe a cikin mota ya dube-dube ko Allah zesa yahanta amma bega kome kama da ita lokaci ɗays yaji kansa na mugun ciwo tsintar kansa yayi da jin haushin kansa na nemanta da dayayi yaja motarsa yanata tsaki ya nufi gida.
Washe gari suna tashi da sassafe suka shiga aikace-aikacen gida ita da Khadija sunkusa gama wanke -wanke Jameelah ta fito tana miƙa alamun tashinta bacci kenan kama baki tayi cikin iya bariki tace"Aunty meyasa baki tasheni nazo munyi ba kuketa gumurzun aiki ku kaɗai".
hararta Khadijah tayi a zuciyarta tace"tsinanniya sekace yin aikin dama takeyi ".
murmushi Inteesar tayi cike da soyayyar ƴar uwarta tace"ai aikinma ba yawa harma munkusa gamawa kije ki shirya idan muka gama semu tafi gurin ƙunshi".
"toh Aunty".
nanta koma ɗaki tana yiwa Inteesar dariyar tagama da ita a zuciyarta tace"toh a ina tasamu kuɗi bayan Yayah Zaid yacemun ko biyar be bataba ". ƙumƙunai Khadijah tashiga yi harara Inteesar ta watsamata haɗe cewa"kinga Khadija inbaki fita idonaba wallahi zakiga yadda zanyi dake koke zaki biyamat".
nan taitayiwa Khadijah faɗa har suka gama wanke -wanken suka shirya gabaki ɗayansu suka tafi gidan ƙunshi.
Ɓangaren Namijin duniya ko kobaccin kirki besamu yayiba Allah,Allah yakeyi gari ya waye ya nufi comphany ɗinsa ana kiran asuba yana fitowa daga masallaci yana komawa bedroom ɗinsa ya faɗa wanke yana fitowa a gaggauce yashiga shafa mai yana gamawa yasaka wasu haɗaɗun ƴan kanti sunyi matuƙar amsar jikinsa ya ɗauki phones ɗinsa ya shiga sauka daga bene cikin hanzari kaciɓus sukayi da Abbih ɗinsa daya dawo daga masallaci kallonsa yayi cike da mamaki yace "ina zaka haka da sanyin safiyar nan ".
cikin girmamawa yace"Abbih ina kwana dama office zani inada wani aiki me mahimmanci ne shiyasa zantafi da wuri".
"lafiya ƙlau amma dai ka tsaya ko tea ne kaɗansha kafijin kwarin yin aikin".
"ai da wuri zan dawo idan na dawo nayi breakfast".
"ok seka dawo ina fatan dai ka tuna yaune ranar da alƙawarinmu ze cika".
"eh Abbih idan na dawo zan falamaka".
yaƙarasa zancensa yana ficewa dankar Abbih ɗinsa yaƙara tayo da wata maganar murmushi Abbih yayi ya wuce .
Yana fita ta anshi makullin ɗaya daga cikin sababbin motocinsa yashiga yaja ya nufi comphany ɗinsa lokacin daya isa tsirarin mutane ne suka isa ya nufi office ɗinsa yana shiga ya zauna tare kunna syatem ɗinsa yashiga duba abubuwa yanayi yana duba lokaci wasa-wasa har 11am ba Inteesar ba alamunta ɓangaren Namijin duniya ko yarasa meke damunsa se tsaki yakeyi yana duba cctv camera koda zega ɓullowarta amma shiru bata bs labarinta har ƙarfe huɗu jiki ba kwari haka ya nufi gida yanata tinanin meya hanata zuwa!!!!
Votes and Comments
_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow
_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_
Book 2
4️⃣3️⃣➡️4️⃣4️⃣
Yana isa gida direct y part ɗinsa ya nufa a ya zube akan haɗaɗen gadonsa ya lumshe sexy eyes ɗinsa ya lula duniyar tinani dakyar ya iya tashi yashiga toilet yayi wanka yafito yana fitowa ya shirya cikin ƙanan kaya marasa nauyi ya nufi hanyar fita domin samawa cikinsa abu mara nauyi a falonaa yayi kaciɓus da Rahama datazo kiransa tana ganinshi tayi saurin juyamasa tana kukan shagwaɓa murmushin daya ƙarasamasa kyau yayi tare da kawota jikinsa cikin tausasa murya yace"sorry Sweetheart nasan nayi laifi na fita da wuri ".
yaƙarasa zancensa yana kama kunnensa alamun bada haƙuri murmushi Rahama tayi tare da yin hugging ɗinsa cikin shagwaɓa tace"indai kanaso in haƙura seka faɗamun sunanta".
"wakenan".
"wadda ta zautarmana dakai kaketa zabga smiling jiya wadda ka siyawa necklace".
murmushin dabe shirya yi bane ya suɓucemasa ya lakacemata hanci tare da cewa"zaki santa amma ba yanzu ba".
bubbuga ƙafa tashigayi alamun bata yardaba kama hannunta yayi yace"muje yunwa nakeji idan nagama cin abinci zan faɗamiki kinji amma sekin dena kuka".
"yauwa Bro na Abbih na nemanka a part ɗin Granny".
damm ƙirjinsa yabayar domin yasan kwanan zancen jiki ba kwari yace"muje".
"toh".
nan suka nufi ɓangaren Granny yayinda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri.
Suna isa falon Granny suka tadda Abbih da Granny suna hira cikin girmamawa suka samu guri kan carpet suka zauna ƙasa da kansa yayi cikin girmamawa yace"sannunku da hutawa".
"yauwa sannu mesunan Manya ".
cewar Granny tana kallon Abdallah kallon Rahama Abbih yayi cikin nuna alamun rashin wasa a fuskarsa yace"ki shiga ɗaki zamuyi magana".
"toh Abbih".
nanta miƙe tashige bedroom ɗin Granny shiru ne ya biyo baya naɗan lokaci kafin daga bisani Abbih yayi gyaran murya tare da tattara hankalinsa ga Abdallah dake wasa da zara-zaran ƴan yatsunsa yace"kai muke saurare inafata dai yanzu kasamu daidai da ra'ayinka ko?".
cikin dakiya tare da basarwa kamar besan me Abbih yake nufi ba yace"bangane ba Abbih".
murmushi manya Abbih yayi domin yasan halin ɗannasa yace"kasan dai yaune ranar ƙarshe dana ɗibamaka akan ka fito da matar aure shine zaka nuna kamar bakasan inda zancena ya dosa ba to yanzu na tunamaka kasamu ko kuwa haryau bakasamu daidai da ra'ayin naka ba".
jiɓine yashiga ketomasa dukda sanyin ac dake falon abinka da Namijin duniya seya make ya sosa ƙeya yace"eh to gaskiya har yanzu bansamu wadda ta kwantamunba amma aɗan ƙaramun lokaci zuwa lokacin dazan samu wadda tayi daidai da ra'ayina".
"aiko kayi kaɗan yaro kayi ƙarya ka kwana da yunwa jiƙaka kakeso muyi musha yau ni Indo naga