Showing 15001 words to 18000 words out of 22282 words

Chapter 6 - Man Of The World Book 2 Hausa Novel Complete

31 Dec 2024

141

tashigo be ɗago daga aikin dayakeyi ba yace"wa'alaiki salam".
da gudu tafaɗa jikinsa tare da rungumesa tace"nayi missing ɗinka Sweetheart".
"me too My Angel ".
"Sweetheart kaje part ɗin Ammih inji Abbih yana nemanka".
jiyayi gabansa yayi mugun faɗuwa cije pinky lip ɗinsa na ƙasa yayi alamun dauriya kawai yakeyi yace"ok muje".
yaƙarasa maganarsa yana miƙewa da ita a jikinsa ajeta yayi kama hannunsa Rahama tayi cikin shagwaɓa tace"Sweetheart meke damunka naga kamar baka da lafiya kodai murar ce".
murmushin ƙarfin hali Abdallah yayi tare da cewa"ba abinda ke damuna Angel wani abun kika gani".
"eyi kawai dai naga ka rame ne".
kama mata hannu yayi suka nufi ɓangaren Granny yayinda yakejin wata muguwar faɗuwar gaba.



Jiki a sanyaye yashigs ɓangaren Granny sallama yayi suka amsa yasami guri yazauna akan carpet yayi ƙasa da kansa yace"Abbih gani".
"yauwa Abbanah Rahama bamu guri".
"toh Abbih".
nanta nufi ɗakin da Inteesar take gyaran murya Abbih yayi tare da kallon Abdallah da kansa ke duƙe yace"dama ba wani abu bane yasa na kiraka ba face inaso insanar dakai a yau na ɗauramaka aure".
a razane Abdallah yaɗago tare da cewa"what aure Abbih".
"eh nayimaka aure kamar yadda kaji na faɗamaka nayimaka aurennane badon komai ba saboda nasan bazaka taɓa watsamun ƙasa a ido ba kuma inaso kariƙe yarinyar nan amana Abdallah idan ka ƙuntatamata to tamkar ni ka ƙuntatawa nasan bazaka taɓa danasanin auren yarinyar nanba saboda yarinyace natsatsiya me hankali ga sanin yakamata duk wani uba zeso yarinyar tazamo surukarsa inaso kasa wannan abun a zuciyarka inka kyatatamata tamkar ni ka kyautatawa idan ka muzgunamata tamkar ni ka musgunawa".
wani irin abu yaji ya tokaremasa a maƙoshi dakyar ya wuce murya aɗan daƙile yace"insha Allah Abbih zan riƙeta amana".
"Allah yayimaka albarka dama nasan bazaka taɓa watsamun ƙasa a ido ba Allah yabaku zaman lafiya da zuri'ah tagari bara a kiramaka ita kaganta".
"Ameen ya Allah abarta Abbih basena ganta ba".
nan ya miƙe ya nufi ƙofa besan inda yake jefa ƙafaba saboda tsabar tashin hankalin daya shiga yana shiga part ɗinsa ya zube akan kujera tare da furta"wacce me tsautsayin ce ta yarda ta aureni kowacece senasata tayi danasanin shigarmun rayuwata datayi meyasa baza'ah barni da rashin abinda zuwata take tsananin so ba za'ah haɗani da wata gaja".
nan yayita shirya irin muguntar dazema wadda ta aureshi.






Ɓangaren Jameelah koda aka kaita gidansu Zaid batawani samu karɓuwa ba saboda tunda Abbunsa ya dawo bawa ƴan uwan Zaid labarin abinda yafaru kowa yafita sabgar auren shikaɗai ke kiɗansa yana rawarsa ganin yadda ƴan uwan Zaid ke fushi ne yasa Dagauta cewa"mu wuce da ita ɓangarenta kawai domin naga alamu wa'innan mutanen basu da mutunci".
"aikuwa dai ".
cewar Uwani ƙawar Uwar Gwarama nan suka nufi ɓangaren Jameelah sosai part ɗin yayi mugun tsaruwa two bedroom ne se dining da kitchen se babban falo guda ɗaya domin Abban Zaid ya kwace gidan daya ƙerawa Zaid a cewarsa yadda yaƙimasa biyayya shima kuma baze bishi ba ɗaya daga cikin bedroom ɗin aka kai Jameelah suna ajeta kiran Uwar Gwarama na shigowa ɗagawa Jameelah tayi tare da cewa"hello Ummah".
"kice har kun isa".
"eh wallahi Ummah ammafa da matsala".
"tame fa".
nanta warwaremata yadda dangin Zaid suka ansheta zaro ido Uwar Gwarama tayi tare da ƙunduma ashar tace"buɗe kunnenki kijini dakyau bance ki ragawa duk wanda be ragamiki ba koda ko uwarshi ce karki kusa ki ragamata kinajina ko".
"kema dai Ummah kamar bakisan halina ba aikinsan ba wanda zan ragawa ko uwartashi ce ai ɗanta nake aure ba itaba a wanne dalilin zabarsu".
"yauwa tawan aida har nayi mamakin ragamusu dakikayi".
"ai Ummah ki kwantar da hankalinki ba wanda zan ragawa a cikinsu duk wanda yacemun kule sena cemasa cas kamar ba jininki ba".
"yauwa tawan jibi zanzomiki da maganin tsinannu".
"toh sekinzo".
nan sukayi sallama .





Washe gari da asuba Inteesar ta tashi tashiga toilet ta ɗaura alwala tafito gurin gado ta nufa ta tashi Rahama dake baccu buɗe ido Rahama tayi tare da yin miƙa murmushi Inteesar tasakarwa Rahama tare da cewa"Sis kitashi asuba tayi ".
"toh Aunty".
nanta miƙe ta nufi toilet itakuma ta shimfiɗa sallaya ta tada sallah bayan sun idar Inteesar ta fita falo samun Haire me aikin Granny tayi zata fara shara cikin girmamawa ta duƙa tare da cewa"Mamah ina kwana".
"lafiya ƙlau ƴata ".
"Mamah kawo na tayaki".
"a'ah kibarshi yanzu zangama".
"dan Allah ki kawo".
nanta anshi tsitsiyar hannun Haire tashiga shara tana gamawa tayi morping ɗin gurin tsaf tana gamawa tasa Iya Haire ta nunamata turarukan wuta lokaci ɗaya part ɗin yaɗauki ƙamshi tana gamawa ta tambayi Iya Haire kitchen da store nanta fito da kayan aiki tafara fere doya Iya Haire tace"ƴata dakin cire hijabinnan da kyafi jindaɗin aikin".
"to Iya ".
nanta cire miƙewa Iyah Haire tayi tace"Hajiya bara naje na cigaba da aiki".
"toh Iyah".
nanta tafi itakuma ta cigaba da aikinta tana rera karatun alqur'ani .



Yana fitowa daga masallaci ya fara tafiya ɓangarensa har ya nufi ɓangarensa yaji yanason ganin Granny ɗinsa hakan yasa ya nufi part ɗinta direct tundaga waje yake jiyo zazzaƙar muryar Inteesar na rera karatun alqur'ani megirma buɗe ƙofa yayi yashiga ba tare data sani ba yamaida ƙofa ya rife ɗaga idon nan dazeyi yayi tozali da Inteesar ta juya baya tana aikinta tana karatunta tundaga silifas ɗin ƙafarta yafara kallonta har zuwa rigar baccin dake jikinta idanunsa ne ya sauka kan dogon gashinta daya sauka har gadon bayanta a zuciyarsa yace"wannan dai ba Rahama bace bakuma wannan yarinyar Meemeeh bace to wacece".
ya tambayi kansa hakam kuma yayi daidai da juyowar Inteesar dake ƙoƙarin gyara gashi karaf sukayi ido huɗu da juna a tare suka zaro ido a tsorace suka haɗa baki gurin cewa!!!!!!!





Vote and Comments



_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_


# Real eeshow



_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_


Book 2


5️⃣5️⃣➡️5️⃣6️⃣



Nuna juna sukayi a tare suka haɗa baki gurin cewa"kece? kaine?".
suka nuna juna lalubar hijab ɗinta tashigayi bazato taji ya fisgota tafaɗa faffaɗan ƙirjinsa numfashinsu na sarƙewa cikin na juna a harzuƙe yace"ke wacce irin mayyace tace da duk inda nayi sekinbini".
"kai zancewa ma mekakeyi a gidanmu Allah ya kyauta inrasa mayyar wanda zanzama setaka kaima zancewa mayena da duk inda nayi seka bini goto-goto ko kunya bakaji".
binta yashigayi da kallon mamaki gani yayi babu alamun zuwa tayi lokacin sema lura dayayi kamar anan ta kwana kallon tamfatsetsen agogon dake falon yayi yaga a lokacin seven daidai ƙuramata sexy eyes ɗinsa yayi yanamata kallon mamaki karaf idanunsu ya sargafe cikin na juna kallon kallo suka shigayi na wani lokaci bazato sejin muryar Rahama sukayi akusa dasu tace"Sweetheart barka da asuba My Aunt barka da asuba".
saurin sakinta yayi yana sosa ƙeya alamun kunya ya wani ƙara haɗe rai kamar bashine ke rungume da itaba yawani ɗauke idanunsa akanta a zuciyarsa yace"tome wannan futsarariyar yarinyar kuma takeyi a gidannan bayan anɗauramata aure jiya anyako ita nagani kuwa ba gizon data saba yimun bane kuwa to kuma meyasa Rahama takirata da Aunty har kuma take gaisheta".
ɓangaren Inteesar ko a zuciyarta tace"me wannan mara mutuncin yakeyi a gidannan iwannan lokacin kuma da jallabiya tomeyasa Rahama takirashi da Sweetheart kuma".
wata zuciyarce tabata amsa da"kika sani ko saurayinta ne".
sauke ajiyar zuciya tayi tana tinanin yadda zasu ƙare da Namijin duniya
sakejin muryar Rahama yayi tana cewa Inteesar data lula duniyar tinani"Aunty memakon nima ki tasheni infara course ɗin girki gurinki shine kikaƙi tashina ko".
taƙarasa zancenta cikin shagwaɓa saurin danne tsananin mamakin ganinsa a wannam lokacin Inteesar tayi tare da yin sansanyan murmushi cikin zazzaƙar muryata meƙara tafiya da zuwar duk wani ɗa namiji tace"sorry My Sis gani nayi bekamata na tadaki kina bacci ba saboda wasu in antadasu suna bacci suna iya tashi da ciwon kai shiyasa ban tasheki ba amma gobe insha Allahu zan tasheki kinga nima seki riƙa koyamun girkin dama nima karan bani nakeyi
"kinji wai Aunty wai na riƙa koyamiki kefa nikeson ki koyamun domin ba abinda na iya".
"toh zan koyamiki".
sosai Abdallah ke mamakin yadda Rahama take magana da Inteesar abinka da miskilin mutum seya make abunsa kamar ba mamaki yskeyi ba ya wuce ya nufi bedroom ɗin Granny da kallon mamaki Inteesar tabishi har ya ɓacewa ganinsu sauke nannauyar ajiyar zuciya tayi suka cigaba da aikinsu ita da Rahama.





Abdallah na zama akan sofa Granny tafito daga toilet tana ganinshi tayi murmushi tare da zama gefan gado suna fuskantar juna tace"Mesunan Manya ba haƙuri wato amaryar taka kabiyo da sassafenan saboda rashin haƙuri irin naka yaushe rabon danaganka da sassafe se yau kamar mejiran kaɗan".
ƙara haɗe rai yayi tare da cewa"Ammih ina kwana".
"lafiya ƙlau ".
miƙewa yayi da niyyar tafiya yayinda a zuciyarsa yaketa tinanin ta yadda ze fara tambayarta kan Inteesar ƙara haɗe girar sama data ƙasa yayi tare da cewa"Ammih sabuwar ƴar aiki kikayine?".
"meka gani ".
"wata yarinya nagani a kitchen ɗinki".
"ƙila takwarata ce Aishatu matarka ce ai wannan yarinya akwai tarbiyya jiya daddare muna gama cin abinci ita ta kwashe kayan ta gyara gurin gaskiya anyi sa'ar samunta komai na yarinyar nan abun birgewa ne anyako ba shuwa arab bace kuwa kai kaga kyau ko a gurin yarinyar nan kamar ita tayi kanta".
a zuciyarsa ya maimaita cewa"matata kuma".
ashe a fili yafaɗa ba'ah zuciba yana cikin maimaitawa yaji Granny tace"kwarai kuwa ɗan iya nasan yanzu zakace batayimaka ba uban sanabe todai kaji abinda mahaifinka yafaɗamaka atoh nasan yanzu zaka kusheta inkyau kake nema Aishatu kyakyawa ce ajin farko ga tarbiyya ga nutsuwa da hankali ga girmama nagaba da ita mekuma kake nema inama laifi data rufamaka asiri ta yadda kamar yadda bakasan da aurennanba haka itama batasan dashi ba dahar kake wani taɓe baki".
jin tahowar Inteesar ne yasashi taɓe baki yace"ina wani kyau yake anan gurin aba single bawani diri kamar one yazanyi tunda anliƙamun alaƙaƙai dole na haƙura na ansheta ammafa sede intemakamata amma ba ajina bace".
yaƙarasa zancensa yana sakin murmushin mugunta.




Jitayi wani iri luu jiri na ɗibarta sakamakon jin abinda Namijin duniya ke cewa dafa bango tayi sakamakon jindatayi tana niyyar yanke jiki zata faɗi lokaci ɗaya zufa tashiga ketomata a zuciyarta tace"Innalillahi wa'innah ilaihi raji'un nashiga ukuna ni Aishatu idan naji daidai ana nufin wannan mugunne mijina meke shirin faruwa dani ne daka wannan masifar se wannan wannan wacce irin rayuwa ce ya Allah kabani ikon cinye duk jarabawar dake bibiyar rayuwata".
taƙarasa zancenta wasu hawaye ne masu zafi suka zubomata saurin sharewa tayi sakamakon jin sautin tahowar Rahama ta ƙaƙali murmushi a fuskarta jiki sanyaye tashiga cikin sanyin murya tace"salamu alaikum".
washe baki Granny tayi tare da cewa"wa'alaiki salam takwarata ashe kitchen kika shiga dasassafennan aida baki wahalar da kanki ba ga Haire ai duk zatayi komai aida kin huta".
ƙarasa zama tayi tare da yin ƙasa da kanta tayi kamar batasan dashi a gurinba taɗanyi dariya tace"ai bakomai Ammih bawata wahala sema lada dazan samu na farantawa Ammih na rai danayi".
"aikuwa dai ɗiyata Allah yayimiki albarka".
"Ameen ya Allah Ammih na".
a wutsiyar ido tasaci kallonsa karaf suka haɗa ido saurin ɗauke ido tayi daga kallonsa turo ɗan ƙaramin pinky lips ɗinta tana ƙunƙunai ta juyar da fuskarta tace"ina kwana Yayah Abdallah".
shiru yayi kamar bejita ba harta fidda ran ze amsa sannan ya taɓe baki tare da cewa"lafiya ".
aninda kawai ya ce da ita kenan shigowa Rahama tayi tare da cewa"Ammih bakiji ƙanshin da falonki keyiba harna ƙagu danaci abincinnan da Aunty ta girka dakajin yadda yake ƙamshi nasan zehaɗu wallahi".
dariya Ammih tayi tare da cewa"kema hakanan zaki dena wannan banzan baccin naki na ƙaddara ki fara koya".
"ai yau ma Ammih seda nace meyasa bata tasheni ba aida munyi tare nima na koya Auntyna dan Allah gobe ki tasheni muyi tare".
taƙarasa zancenta a shagwaɓe ɗaga idonnan da Inteesar taga Namijin duniya ya taɓe baki tare da cewa"amma dai Rahama kinji kunya wallahi kirasa wadda zakiyiwa shagwaɓa se wannan ƴar abar wadda a girme kin girmeta ".
murmushi Inteesar tayi dantasan danya ƙularda ita yayi wannan maganar tace"ki kwantar da hankalinki Sis insha Allah gobe zan tasheki".
"yauwa Auntyna nagode".
fakaitar idanun mutane tayi ganin bame kallonta tayiwa Namijin duniya gwalo aiko sukayi ido huɗu dashi jinjina kai kawai yayi alamun zekamata ya miƙe yana duba agogon wayarsa yace"Granny nizan wuce Sweetheart anjuma kije ki wanken toilet".
turo baki Rahama tayi tare da yin ƙasa da murya tana ƙunƙunai tana cewa"waikai Yayah koda yaushe bazaka bari masu yima aiki suyima aikin bedroom ɗinka ba sede kasa mutum to daban dawo ba kumafa yanzu aiga matarka nan setayimaka".
ƙara haɗe rai Namijin duniya yayi kamar betaɓa dariya ba yadakamata tsawa tare cewa"kee yaushe nafara wasa dake dahar kika rainani haka to bazansa masu aikinba kenaga damar sawa".
"a'ah Malam dakata bazakazo har ɗakin kace zaka takurawa ɗiyata ba ai gaskiya tafaɗa ko ƙarya tayimaka meyasa bazakasa masu yima aiki suyima ba kokuma matarka tunda sune yazama dole suyima da dabatanan yaya kakeyi ".
"Ammih ke kikeja yara suna rainani wallahi".
yaƙarasa zancensa yana yin kwafa yafice fuuu yana fita ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya dariya Rahama tayi tare da cewa"tofa munfa kinsawa Sweetheart baƙin ciki se Allah ya zuciya".
murmushi yaƙe kawai Inteesar ta yiwa Rahama domin hamkalinta duk baya jikinta tanacan tana tunanin rayuwar dazatayi da Abdallahnta ɗan zafin kai hira kawai sukeyi amma ita hankalinta kaf baya kan hirar tasu dariya Ammih tayi sosai tace"ai gwara daya fusata haka kurum yaro se baƙin miskilancin tsiya da faɗin ran tsiya ga matarka seka dami yarinya da mugun sa aiki idan matarshi batasan cikinsa ba wa yakeso yasani anjuma Aishatu ki shirya kije ɓangarensa ki gyaramasa".
gaban Inteesar ne yabada dammm sakamakon jin zataje gurinsa lokaci ɗaya yanayinta ya canza zuwa kalar tausayi tace"Ammih da anbarshi tunda yafison na Rahama".




Salati Ammih tayi ta sanar da ubangiji gami da tafa hannayenta duka biyub tace"yau ninaga ja'irar yarinya ni Indo ana ƙoƙarin kwatarmata ƴanci tanaiwa mutane shashanci amma gaskiya albasa batayi halin ruwa ba anyako sunanki Aisha ba Sarai ba kuwa ƴar nan domin nidai a iya sanina dame suna Aisha jaruma ce batada tsoro keko daka cewa kije ɓangaren mijinki duk kinbi kintashi hankalinki kamar wadda akace taje gurin mutuwarta hadda wani marairaice murya Ammih kibarshi tunda yafison na Rahama".
taƙarasa zancenta tana kwaikwayon muryar Inteesar ganin yadda taƙara ruɗewa ne yasa Ammih kamo hannunta Granny tayi ta zaunar da ita gefanta ta kama hannunta tace"karki bani kunyaman takwara ta kizama jaruma kidena jin tsoronsa mijinkine a tafin hannunki yake duk wani hura hanci dakikaga yanayi yadena baki tsoro ki tsaya ki natsu ki gyara mijinki aida ba haka yakeba kinada damar da zaki canzashi daga wannan murɗaɗen halin nasa yadawo normal kefa macece kiyi amfani da kisisinarmu ta ƴaƴa mata ki canzamanashi kinji ɗiyata nasan abu ne me matuƙar wahala amma ki daure nasan zaki iya kinji ɗiyata watarana se labari kiyimun alƙawarin zakiyimun wannan aikin danasaki Aishatu domin rabonda muga haƙuri Abdallah a waje da sunan dariya tun kafin mahaifiyarshi ta rasu dan Allah ki temakeni ki dawomasa da walwalarsa kamar da yazama mutum kamar kowa dan Allah ƴata".
jiki a sanyaye Inteesar tace"insha Allah Ammih zanyi iya bakin ƙoƙarina".
murmushi Ammih tayi tare da cewa"nagode ɗiyata Allah yayimiki albarka yabaku zaman lafiya da zuri'ah tagari kuje ku shirya saboda Abbih ɗinku yace idan angama cin abinci akwai meeting.
ƙasa Inteesar tayi alamun jin kunya a zuciyarta ta amsa da Ameen dukan wasa Ammih takaiwa Inteesar saurin gocewa Inteesar tayi tana dariya .




Dariya gabaki ɗaya sukayi Ammih tace"kinibabba kinason mijinki kina kaiwa kasuwa Allah ya shiryamunku kutashi kuje ku shirya muci abinci".
"Ameen dai Amminmu toh".
cewar Rahama daketa dariya nansuka tafi suna shiga bedroom Rahama tayi sauri ta shige toilet tanaiwa Inteesar dariya tayimata wayo taɓe baki Inteesar tayi haɗe da cewa"kedai kika sani yarinya tunda dai bakwana zakiyi a toilet ɗinba aida sauƙi bawani haushi dazanji".
nan tashiga tazar dogon gashinta Rahama batawani jima tafito nan Inteesar itama tashiga batawani daɗe ba tafito ɗaure da towel kama haɓa tayi alamun mamaki ganin yadda Rahama tasha uwar kwalliya kamar wadda zata gasar kyau tasha abaya ƴar ubansu se walwali takeyi tasha stone tace"Sis irin wannan kyau haka kamar wadda zata gasar kyau ai wannan inkika fita waje seki haddass accident ɗin motoci a gari".
murmushin daya ƙaramata kyau tayi tare da cewa"kai Aunty banda sharri duk kyauna aiban kaiki ba kefa ko bakiyi kwalliyaba kyau gareki bare kinyi".
"Allah ba sharri bane gaskiya na faɗamiki idan nayi kyauwunki ai a kalleni".
"bawani nan kawaidai tsokanata kikeyi dan kinga kinfini shiyasa kawai kike ƙoƙarin zagina".
"wlh ba zaginki nake ba gaskiyata nake faɗamiki ƙaraso kiyi ki shirya nasan ƙila yanzu kowa ya hallara a dining mukaɗai ƙila ake jira ".
"toh ai yanzu zan shirya ni ai shirina bashi da wuya mai kawai zan shafa".
"wanne irin mai Aunty aiko dai kwalliya zan tsaramiki saboda so nike ki gigita Yayah ta yadda zeƙara faɗawa a kogin sonki ".
murmushi tayi kawai tare da cewa"Allah shiryeki Sis".
"ameen dai matar babban Yayah".
murmushin yaƙe kawai tayi domin baƙaramin faɗuwa gabanta yakeyi ba idanta tino da wai wannan mutumin me girman kan tsiyar ne mijinta tana wannan tinanin har Rahama tagama tsaramata kwalliya tana gamawa ta tsaya ƙaremata kallo tas sannan tace"amma Aunty kin haɗu tsarki ya tabbata ga Allah subhanahu wata'ala gaskiya bazaki kalli kanki a mirrior ba sekin saka kaya nayimiki rolling kinga muna gama cin abinci semu wuce shopping ɗinda Ammih tace basemun dawo ɗaki ba".
"toh nagode Sis dan Allah idan mundawo ki aramun wayarki nakirasu Besty".
"toh ai se a haɗo da wayarma ".
"toh".
nanta saka inner wears ɗinda ta fitomata dasu sababbi masu colour ɗin coffee sannan ta ɗora wata haɗaɗiyar abaya coffee wadda tasha adon stone se walwali takeyi da ɗaukar ido ɗauremata dogon gashinta dayasha gyara Rahama tayi da coffee ɗin rebom sannan tayi rolling ɗin kanta da ɗankwalin abayar lokaci ɗaya ta rikiɗe tazama tamkar balarabiya kama hannunta Rahama tayi takaita gaban mirrior

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login