Showing 6001 words to 9000 words out of 22282 words

Chapter 3 - Man Of The World Book 2 Hausa Novel Complete

31 Dec 2024

137

abinda ya isheni anyako wannan katon ba aljana ce ta aureshi ba kuwa yaza'ai ace duk irin zuƙa-zuƙan matan dake sonsa yace duk basuyi daidai da ra'ayinshi ya yaro da anyi maganar aure seyace a ƙaramasa lokaci inbaka da lafiya ka faɗamun in nemamaka magani domin so nike naga masu yimun addu'ah gaskiyar Meramu tacemun jifan jikana akayi shiyasa yaƙi aure naƙi yadda aiko kowaye senayi maganinshi ungo kiramun Meramu mutafi Malam na bayan tsauni ya bincikamun domin banga ta zamaba za'ah kassaramun jika".
taƙarasa faɗa tana miƙawa Abbih waya yakiramata aminiyartata ansar wayar Abbih yayi tare da cewa"Innah ki kwantar da hankalinki ba wanda yayimasa wani abun basekin tafi wani gurinba".
"yo ina hankalina ze kwanta anjefi jikana bakaga yadda idonsa yakoma kamar gautaba daka yin maganar aure oh ni Indo ka tashi ka miƙani gidan Meramu mutafi gurin wannan mutumin na bayan tsauni".
"naji Innah amma inda kike ƙoƙarin tafiya ba gurine mekyauba Malami baze zauna a bayan tsauni ba sede boka kuma babu kyau zuwa gurin boka".
matsar kwalla Innah tashiga yi tana jan majina tana cewa"yanzunan Iro ni kake ciwa zarafi kan zanje samowa ɗanka lafiya shine zakayimun sharri a ina nafaɗamaka gurin boka zani to nabarka da ɗannaka magautan su kasheshi insuna iyawanz zame hannuna akan ɗanka kuma ku barmu sashina tunkafin nima naci zarafinku".
murmushi Abbih yayi ganin yadda Innah ta haƙiƙance wai ita ala dole an nunamata iyakarta lallashinta Abbih yashiga yi dakyar ta sakko tabarsu su zauna a falonta kallonsa Abbih yayi naɗan lokaci sannan yace"tunda kace har yau bakasamu wadda ta kwantamaka ba to ni dakaina zan lalubomaka".
damm ƙirjinsa ya buga yayinda yaji yawun bakinsa ya ƙafe lokaci ɗaya kai kawai ya ɗagawa Abbih nan Abbih ya miƙe yayiwa Granny sallama ya tafi .




Yana ganin fitar Abbih yasaki wata nannauyar ajiyar zuciya miƙewa yayi tare da zama kan kujera ya lumshe idonsa kamar koda wannan lokaci tinanin kyakyawar fuskarta yashiga yi wani ɓangarena zuciyarsa se tsukulinsa yakeyi daya kira Ahmad daya turomasa da numberta yaji ko lafiya batazo ba jin muryar Innah yayi tana cewa"mesunan Manya ka rabu da wancan sakaran uban naka bawani boka wallahi Malami ne gobe da safe zanje gidan Meramu ta rakani in ansomaka kasha abunka ba tare daya sani ba duniya ba gaskiya kai baka damu da mutumba shiya damu dakai kodai baka da lafiya mesunan Manya".
jin abinda tacene yasa Namijin duniya yin wata dariyar dabe shirya yinta ba jin waiko bashi da lafiya a zuciyarsa yace"Granny dakinsan yadda lafiya tayimun yawa da bikice haka ba domin ina tausayawa yaran mutane domin nikaina nasan nakama ɗiyar mutane nasan bazataji da daɗiba".
a filikuma ɗagamata kai yayi alamar eh bashi da lafiya riƙe hannunshi tayi tare da cewa"aikoda naji aiko gobe zansa Barirah ta tafi ƙauyensu tasamomin magunguna kafara sha shiyasa kenan naga kamar kana tsoron mata ashe ga inda matsalar take doleko kaji tsoron mata ashe ba kayan aiki aiko ba zance yanzu dai ka kwantar da hankalinka insha Allahu zaka samu lafiya kaima kamar sauran maza".
dariya Namijin duniya yaƙarayi jin wai shike tsoron mata yace"Granny ya mutum yake gane yafara soyayya".
washe baki Granny tayi tare da cewa"Mesunan Manya wata ka kamu da sonta ne".
"a'ah abokina ne yakamu dason wata shine ya tambayeni".
"ayo aina ɗauka kai ka fara soyayya ".
"a'ah".
"zakaji kana son ganinta akowanne lokaci baka da buri sena ganinta komai nata ze riƙa burgeka kodako rashin kunya tayimaka bazakaji haushi ba zaka kasance mejin tausayinta akowanne lokaci".
ƙirjinsa ne yabada damm jin abinda tace a zuciyarsa yace"kenan sonta nike".
wata zuciyarce tace"Allah ya kyauta inrasa wadda zanso se ƙasƙantacciyar cleaner tausayinta kawai nakeyi ".
a fili ya furta "no tausayinta nakeji domin ni bani da lokacin ɓatawa".
kallonsa su Granny sukayi Rahama tace"intayi wari maji".
hararta yayi tare da miƙewa ya fice yabarsu.




5:00pm
Zaune kowa yake a ɗakin taro kowa yasha kwalliya ta alfarma ba abinda ke tashi a gurin se kiɗa zaune take akan kujerar higher table ita kaɗai tasha make-up harta gaji inba farin sani kayimata ba bazaka ganeta ba domin tayi kyau sanye take da wata rantsatsiyar gown white me adon stone red se net ɗin da aka rifemata fuska daya kasance red komai na jikinta red ne shiru-shiru ba ango ba alamarsa se amarya tsu kan step ɗin Hauwah tahau ta nufi gurin Inteesar da idanunta sunfara tara ruwa ta sunkuya daidai kunnenta tace"Besty ki kwantar da hankalinki insha Allahu ba abinda yafaru dashi".
maida hawayen dake ƙoƙarin fitowa tayi tare da yin murmushin yaƙe tace"Allah yasa Besty kinga irin abinda nake faɗamiki kinƙi yadda kikayo uwar gayya gashi ba lallai yazo ni bikinnan wallahi duk yaficemun daka rai domin jikina duk sanyi yakeyi".
"dan Allah kiriƙa haƙuri wataƙila wani abun yatsayayi bakiga abokansa duk sunzo ba shima yana hanya".
"Allah yasa".
nan Hauwah takoma seat ɗinta na babbar ƙawar amarya.



Dariya Jameelah tayi ganin Inteesar kaɗai akan kujera tare da kallon ƙawarta Hindatu tace!!!!!!!!




Votes and Comments




_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow



_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_


Book 2


4️⃣5️⃣➡️4️⃣6️⃣



"Hmmm kalli tsinanniyar se zare kurma-kurman ido take a kujera ita kaɗai kamar kazar da aka tsoma cikin ruwan zafi ai wallahi tunda tace zata jadani tana tare da wahala domin muddum Ummanmu na numfashi bazata taɓa barinsu suyi aure gidan jindaɗi ba sede suganmu muna hutawa suko sede su ƙare dayin aikatau da wanke-wanken gidan mutane da shara domin ni idan na auri Zaid ko kwancen kaya bazan temakesu dashi ba".
"gaskiyane Mrs Zaid Cheif judge aikinki na kyau mudai idan abunnan ya tabbatu Allah yasa kar a manta damu domin nasan halinki dakinsamu duniya kike shafawa idanunki toka ki babbake komai".
"haba ƙawata kisha kuruminki wannan karon zanbaki mamaki domin so nike kema kiyi ramm da zuciyar babban amininsa Muhseen kinga shikenan amincinmu yaƙara ɗinkewa".
"Allah ƙawata ammafa kinaja sosai amma kina ganin ze kulani kuwa domin gayennan naga alamu kamar yanada girman kaifa".
"ke da Allah jacan girman kanshin banza munada Umma fa faɗuwar gaba asarar namiji ai ba'ah shiga dawa dan ƙarya kedai kawai ki kwantar da hankalinki zakiga yadda jikinsa ze riƙa tsuma akanki ai ina tinanin duk girman kansa bekai ɗan gogana ba amma dayasha aiki idan yaganni kamar ze lasheni haka yakemun shima zakiga yadda ze koma kai gaskiya nagaji so nike naɗan fita shan ice cream bara na kira Sweetheart yakaimu gurinnan yacika zafi".
dariya Hindatu tayi tare da tafawa da Jameelah daketa faman yatsuna tace"lallai ƙawata gaskiya kin ƙaro wulaƙanci wato angon da amaryarsa ke jirama keshi zakisa ya kaiki shan ice cream baki da case kina cin duniyarki da tsinke wallahi".
"sosaima kuwa idan banci lokacina ba yanzu yaushe kikeso naci koko so kike nayi ƙara'ih shekaran jiya da muka fita yasiyamana layin me &u dan yariƙa jina a waya suko wa'incan gaulayen da kikaga sunata faman kiranshi aikin banza sukeyi domin nina sakashi ya kashe wayarsa bazasu taɓa samunsa ba sa ƙaraci nacinsu su haƙura inbada abin namiji mezeyi da ɗiyar marasa asali bayan ga ƴar dangi gaba da baya itakuwa fa waya taɓa sanin dagin wannan me farar ƙafar".
"gaskiya ne tawajena kici lokacinki".
"yauwa tawajena".
nan ta ɗakko wayarta daka jaka murmushi tayi tare da cewa"oh kinga ɗan halak yanzu muke maganarsa sega kiranshi ai bara naɗauka".
"yadai kamata tawan".




Ɗagawa tayi tare da yin ƙasa da murya tace"hello Dear yakake".
"lafiya ba lafiya ba tunda banji lafiyar sarauniyar birnin zuciyata ba tunɗazu naketa kiranki kinyi bakiyi picking ba lafiya".
murmushin daya ƙara narkar dashi a duniyar soyayyarta tayimasa tare da cewa"tuba nake My King ina gurin shagalin aurenku ne".
"kingaki ko zaki farako kinsandai na faɗamiki banaso kina haɗani da wannan me warin jaɓar shine kike ƙara lanƙayamun itako ko sokike na fara miki kuka to ".
wani daɗine yaƙara kamata zuciyarta tace"sorry My nadena karkamun kuka wasa nake maka idan ba wani abun kakeyi ba inason muje shan ice cream inba damuwa".
"kinji sweetheart ai koda aikin da nikeyi na bari nakaiki kisha kina ina nazo na ɗaukeki mutafi".
jinjina Hindatu tayimata alamun aikinta na kyau kashemata ido ɗaya Jameelah tayi tare da cewa"Sweetheart ina gurin kamu ".
"ok gani nan zuwa amma sede ki fito waje domin banason aganni a zata gurin abun nazo".
"tom shikenan inka iso ka kirani sena fito mu wuce".
"toh gani nan zuwa".
yaƙarasa zancensa jikinsa na tsuma kashewa tayi tare da cewa "bara inje inɗan nuna alhinin rashin zuwan ango dankar a zargeni".
"aiko dai".
nanta miƙe ta nufi step tashiga nuna alhininta .




Zaune yake a falonsa ya zubawa tv ido kamar wanda yake gane abinda akeyi ba abinda kemasa yawo se kalaman Granny na tambayar daya yimata hannunsa ɗauke da glass cup yana shan coffee turo ƙofar da akayine yasashi dawowa daga duniyar tinanin daya lula kallo ɗaya yayiwa aminan nasa tare da amsamusu sallama yacigaba da shan coffeensa hankali kwance zama sukayi akan kujerar dake facing ɗin tashi tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya murmushi Ahmad yayi tare da yaɓa Adam dake gefansa suka saki murmushi taɓe baki Abdallah yayi tare da cewa"kwagama munafuncinki a gidanma mutum be tsiraba se anbi mutum da gulma".
dariya Adam yayi tare da cewa"ai gwara mu munafunafunci mukeyi da wanda yakeson abu yana hana zuciyarsa abunfa yariƙa basarwa waishi ala dole bayason raini fa".
"mekake nufi".
dariya Ahmad yayi tare da cewa"abinda kunnenka yajiyemaka saura kwana biyar afara tafiya gurin seminer nan kaikuma kaƙi motsawa wallahi mudai tafiyarmu zamuyi tunda muba gwauraye bane irin wataƙil baka da rabo idan mundawo maɗan sanmaka riba".
"bangane saura kwana biyar ba har abun yazo".
"eyi badai munbaka shawara kaƙi ɗauka ba da yanzu seka tafi da ita inmundawo ka saketa kaga riba biyu ga sauro ga revenge ga ribar seminer".
shiru yayi secan yace"to yanzu meye abunyi kasanfa banason rasa wannan seminer ".
"bara nakira Hauwah naji yadda za'ayi tabamu number Aishatun".
"ok ".
dialing number Hauwah yayi tare dasata a hansfree yadda kowa zeji bugu ɗaya ta ɗauka tare da komawa gefe saboda hayaniyar kiɗa tace"salamu Alaikum Sir".
"wa'alaiki salam".
"ina yini?".
"lafiya ƙlau Hauwah dama number Inteesar mukeso inba damuwa".
shiru gabaki ɗaya sukayi danjin mezatace daga ɗaya ɓangaren Hauwah tace"Sir yanzu haka muna gurin kamun Inteesar gobe ake ɗauramata aure".




Lokaci ɗaya hankalinshi yayi mugun tashi ya rasa mekemasa daɗi amma dake namijin duniya ne seya dake kamar beji komai ba har suka gama wayar bayan sungama Ahmad yace"tokaji irin abinda muke gujemaka tunfarko da yanzu ba wannan zancen akeyi ba yanzu sede a nemi wata".
ɓangaren Man of the world ko kasa magana yayi sakamakon wani kullutun abu dayazo ya tsayamasa a maƙoshi lokaci ɗaya sexy eyes ɗinsa suka rine zuwa ja yayinda jijiyoyin kansa suka tashi sukayi ruɗu-ruɗu ba abinda ke ketowa a jikinsa se zufa yayinda kansa ke mugun saramasa ganin zasu ɗago jirginsa ne yasashi lumshe idanunsa ganin halin daya shiga ne yasa Adam zungurar Ahmad ya raɗamasa"mutuminmu fa ya auka ba tare daya sani ba".
"hhh aini tun kwanakin baya na lura yanzu dai yakamata muyi wani abu akan aurennan nata".
"hakane kam".
nan suka miƙe suka yimasa sallama kai kawai ya ɗaga musu sakamakon wani ciwon kan dake barazanar tarwatsamasa kai ba abinda ke kai komo a ciki zuciyarsa se kalmar Hauwah na cewa"gobe za'ah ɗaura mata aure ".
a zuciyarsa yace"ashe zata iya aure batare data sanarmun ba".
wata zuciyarce tace"to waikai meye naka naseta sanarmaka ".
rasa me bashi amsa ne yasashi miƙewa yana haɗa hanya kamar wani ɗan maye ya nufi bedroom ɗinsa ya zube kan tanƙamemen gadonsa wani zazzaɓine me zafi ya rifeshi har kyarma yakeyi dakyar ya miƙe ya kashe ac ɗin dake aiki ya kashe hasken ɗakin ya kwanta yanata rawar sanyi.





Ɓangaren Inteesar ko har ƙarfe tara ba ango ba alamunsa sunyi kiran number Zaid har sun gaji amma amsar ɗayace switch off ƴan uwansa se mamakin rashin zuwansa sukeyi har aka tashi taro bezoba komai dayakamata ango yayi Muhseen ne yayi a makwafinsa har aka tashi taron yayinda ran Ummin Zaid yayi mugun ɓaci akan abunda ya aikata haka kowa ya tashi yayinda jikin Inteesar yaƙara yin mugun sanyi akan aure.





Washe gari da safe yana tashi ya nufi ɓangaren Abbansa zaune ya samesa akan sallaya yana lazumi gefansa ya zauna tare da jiran ya idar yana gamawa ya shafa tare da yin murmushi yace"Abbah na lafiya kamar da magana a bakinka".
murmushi Zaid yayi tare da sosa keya alamun kunya yace"eh Abbah".
"ok faɗi damuwarka Abbanah kanka tsaye".
ƙasa dakai Zaid yayi tare da cewa!!!!!!!!




Votes and comments




_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo*_# Real eeshow



_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_


Book 2


4️⃣7️⃣➡️4️⃣8️⃣



"Amm Abbah dama! dama!! dama!!!".
murmushin manya Abbah yayi tare da cewa"dama me kafaɗi maganarka straight forward meye abun wani inda-inda dukka wani ruɗe kamar wanda baida gaskiya haba Abbanah kayi maganarka inajinka".
sake yin ƙasa yayi da kansa tare da cewa"Abbah dama akan zancen auren daza'ah ɗaurane".
"meyafaru ko Aishatun ce tace batasonka naga duk hankalinka ya tashi Abbanah".
girgiza kai yayi alamun a'ah murmushi Abbah yayi tare da cewa"to menene".
"Abbah gaskiya yanzu nafasa auren Inteesar ƙanwarta Jameelah nake so".
sosai ran Abbah yakai ƙololuwar ɓaci yace"anyako Zaid kana cikin hankalinka kuwa koka fara shan wani abunnne bansaniba to bari kaji baka isa ka maidamu ƙananan mutane ba ya agama komai da sunan yarinya se yanzu da rana tsaka kazomun da wani zancenka na banza mara makama tashi kabani guri tunkafin na saɓamaka mutumin banza kawai ashe ina ganinka a me hankali ashe ba haka bane bari infaɗamaka baka isa ka zubarmun da mutunci a idon duniya ba ni kaifi ɗayane idan na zartar da magana bana canzata".
murya kamar ze kuka yace"dan Allah Abbah kabarni na auri Jameelah idan ban aureta ba mutuwa zanyi itace farincikina rayuwata ce gabaki ɗaya idan na rasata tamkar an raba ruhina ne da gangar jikina domin na tabbata lokacina yayi tawa ta ƙare Jameelah yarinya ce me tarbiyya sanin yakamata uwa uba kuma sanin darajar ɗan adam a unguwarsu ma Malama saboda tsananin ilimin addinin da take dashi tako ina bata da makusa itako Aishatu wallahi Abbah rashin sanin halinta ne yasa na nuna inasonta dana tambaya a unguwarsu kwata-kwata batasamu shedaba ba abinda takeyi se aikin yawon tazubar wasuma a unguwar cewa suke karuwanci takeyi batayi karatuba se yawon bariki datasa a gaba dan Allah Abbanah kayimun adalci irin wanda nasanka dashi kabarni na auri muradin zuciyata Jameelah".
yaƙarasa zancensa tare da fashewa Abbansa da kuka a zafafe Abbansa ya tari numfashinsa da cewa"tashi kabani gurin tunkafin na saɓamaka kuma bari kaji infaɗamaka wallahi baka isa ka maidani ƙaramun mutum ba ko kullum Aishatu kwana takeyi a titi tana zubar da mutuncinta seka aureta sakarai mutumin banza baka isa ka ɓatamun suna ba kamaidani ƙaramin mutum ba ka tashi kaje ka shirya domin lokaci na ƙaratowa danasan wannan banzan zancen zakazomun dashi da tini ban koreka ba karfa ka manta nine Cheif Judge a ƙasarnan idan ban aikata adalci a gidanaba a ina kakeso na aikata ka ɓacemun da gani ko kuwa".
miƙewa yayi jiki ba kwari yana haɗa hanya kamar wani ɗan maye ya nufi part ɗinsa.




Yana fita Abdushakur na shigowa ɗakin Abbah da kallon mamaki yabi Zaid tare da cewa"salamu Alaikum".
"wa'alaika salam".
Abbah yafaɗa murmushi kwance a fuskarsa ganin Abdushakur yasha wankan farar gizner malun-malun da ƴar ciki zama yayi kusa da Abbah tare da cewa"Abbah ina kwana".
"lafiya ƙlau Abdul wannan irin wanka haka kamar kaine angon".
dariya Abdul yayi tare da cewa"eyi Abbah ai nine angon dama baƙinkane suka fara zuwa".
"okay bara nima naje na shirya".
"yauwa Abbah yanaga ango yafita kamar bashida lafiya".
"rabu dashi lafiyarshi kawai sakarcinsa ne ya motsa ".
"ok Abbah idan mundawo daga gurin ɗaurin aure zanje gidansu Abdallah nakirashi naji kamar bashi da lafiya kasan halin miskilancinsa dana tambayesa se yacemun ba abinda ke damunsa inaso inje inga jikinsa".
"ok ba damuwa nima bara na shirya".
"tom".
nan Abbah ya shiga wanka dake ɗaurin auren na sha ɗayane shikuma ya nufi cikin gida.




10:am
Wata baƙar jeep ce tafito daga wani tanƙamemen block me matuƙar kyau da tsari ɗaga kaina nayi sama dan ɗakkomuku rahoto daga saman ginin naga anrubuta *MY HEART ORPHANAGE* aka rubuta da manyan rubutu dark blue me matuƙar ɗaukar ido Salis driver kejan motar gefan me zaman banza Abbih ne ke zaune ya amsa call baya kuma Granny ce se Rahama dake kusa da ita taɓa Granny Rahama tayi tare da cewa"tsohuwa meran ƙarfe wai ya akai mijinki yasakawa new orphanage ɗinsa suna zuciyarsa besa sunanki ba ko nasa".
"kekuma meran roba ni banson gulma besaɗinba aishi aikin Allah ba aikin riya bane koko sokike ya rubuta sunansa ko nawa sekace wani bankaɗaɗɗe".
dariya Abbih yayi dake jinsu yace"Ammih ki rabu da wannan kishiyar taki ".
"aifa dole na rabu da ita naga alamu angwaji ƴar kwata a kanta oh ni Aishatu yau banga mijina ya leƙoni ba yau anya lafiya".
"nima yau gaskiya bangansa ba ƙila yanada wani mahimmin aiki a office ɗinsa shiyasa ya tafi da wuri".
"ƙila".
dafa kai Abbah yayi alamun mantuwa tare da cewa"kash nakusa yin wata babbar mantuwa Ammi se yanzu na tina da yau ake ɗaurin auren ɗan Abubakar gashi naga lokaci yaƙure".
"aiko dai idan bakaje ɗaurin aurennanba baka kyautawa yaronnan ba muma se yamma zamu tafi muyimusu Allah yasanya alkhairi yanzu abinda za'ai mu wuce gidan kwandon sukarin seku aje motar daga ɗan nesa kaikuma seka ƙarasa domin Kwandon sukari bazeji daɗin rashin zuwanka ba ".
"kona kira Shu'aibu driver mu haɗu a hanya ya ɗaukeku saboda gurin nasan zeyi mutane".
"mu wuce tare kawai seku ajemu daga ɗan nesa kuyi ɗaurin aurenku inkungama kazo mutafi".
"toh Ammih".
nan Abbih ya kira yaronsa wato baban Zaid yayimusu kwatancen gidansu Inteesar bayan sungama waya ya umarci Salisu driver dasu nufi suleja.





Zaune Hauwah tashigo tasamu Inteesar baki ta buɗe da alamun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login