Showing 12001 words to 15000 words out of 22282 words

Chapter 5 - Man Of The World Book 2 Hausa Novel Complete

31 Dec 2024

136

aiki saboda naga alamun aurenshi da wannan watsatsiyar yarinyar baze kai labari ba".
kai loma ɗaya baki Dagauta tayi tare da cewa"wayya-wayya wai amma gaskiya ƙawata kin kar kuɗi irin wannan nama haka".
"ba dole nakar kuɗi ba karfa ki manta ƴatace ta auri ɗan shugaban alƙalai na ƙasa dole na fitar da kuɗi domin nasan zan maida dubunsu".
"kwarai kuwa harmuma nasan zamu ci arziƙi".
"sosaima kuwa bara inzubamiki idan kingama ki miƙawa wa'incan sarakan baƙin halin".
"wallahi kuwa ai kinfisu mugun abinsu yakoma kansu tsinannu kawai dama wannan ɗince taɗakko halin uwarta zam ba abinda tabari na uwarta ɗayarko se tsiya".
"wlh kuwa".
suna cikin magana Aunty Badi'ah tashigo zama tayi kusa da Uwar Gwarama daketa shewa da ƙawayenta cikin yin ƙasa da murya tace"gaskiya Ummah abinda kikeyi a gidannan bakya kyautawa kin raba yarinyar nan da Zaid duk haka be ishekiba sekin ƙara da yimusu habaici gaskiya abinda kike bakyau wallahi shi rabon bawa baya taɓa tseremasa shiɗa na kowa ne".
"yanzunnan Badi'ah ni kike ƙoƙarin zagi saboda wa'incan mutanen daba ƙaunarku sukeyi ba shine har kike ƙoƙarin cin mutuncina".
"kiyi haƙuri Ummah ni karki taramun mutane".
jin Uwar Gwarama na niyyar yimata tonon silili yasata yimaza ta fita tabarsu nan sunata maida yadda akai.




Ɓangaren Inteesar ko tana shiga gidansu Hauwah tashiga tattara kayan dukda tasan na Zaid ne tana gamawa ta kalli Khadijah da Hauwah daketa maida yanda akai cikin sanyin murya tace"Khady gashi kukaiwa Jameelah kayannan wayarnanma kiciromun layina ki haɗamata da ita".
"wacce irin waya kuma aiko baza'ah mayarmasa da wayaba koda ubansa yake yawo saboda kema aikin ɓata lokutanki masu amfani gurin yin hira dashi ko biyanki yayi yayi shima ai anyi drow be isa anmayarmasa da wayarsa ba".
cewar Hauwah daketa faman huci sauke numfashi Khadijah tayi tare da cewa"wlh kuwa Aunty Hauwah ba wata waya da za'ah mayarmasa aishi yayimata kyautarta".
basu rife baki ba sega su Hafsah yayyen Jameelah sun banko ƙofa suna cewa"afitomana da lefan ƙanwarmu tunda ba gado kar ayimana barbaɗe.
a harzuƙe Khadijah ta miƙe cikin masifa tashiga cillamusu akwatuna cikin tsanani ɓacin rai tana cewa"ga tsiyarku nan kunyi kaɗan muyimuku barbaɗe dama abinda mutum yakeyi gani yakeyi kowama yi yakeyi mezamu da wa'innan wulaƙantattun kayan marasa tsarki".
"ai dole su zama marasa tsarki tunda ba yar uwarki aka kawowa ba sede a cigaba da ganta falfala a titi ".
tas Khadijah ta zagesu Hauwah na
tayata ƙarshe har wayar dayaba Inteesar seda suka basu ido kawai Inteesar ta zubawa su Hauwah har suka gama tsiyarsu fashewa da wani matsanancin kuka Inteesar tayi hankali tashe su Hauwah sukayi kanta suna haɗa baki gurin cewa"lafiya kike kuka Besty".
cikin shashekar kuka Inteesar tace"shikenan na rabu da Zaid Besty banjin zuciyata zata juri rashinsa a tare dani inawa Zaid son daban taɓa yiwa wani mahaluki son da nikewa Zaid ba meyasa ya zaɓi ya rabu dani a lokacin da rayuwata take tsananin buƙatarsa meyasa zemun alƙawarin da baze iya cikamunba shi yacemun yayimun alƙawari baze taɓa barina ba matsawar bani nabarshi ba nima kuma nayimasa segashi abin takaicin tunkafin aje ko ina shi yafara karyawa meke bibiyar rayuwata ne Besty tunda nike a rayuwata bantaɓa samun farincikiba se shigowar Zaid rayuwata yanzu kuma ya rabu dani nida farinciki munyi hannun riga".
taƙarasa zancenta tana me fashewa da matsanancin kuka sosai tabasu tausayi rungumeta Hauwah tayi tana jijjiga bayanta alamun rarrashi suna cikin haka sukaji muryar wata matashiyar budurwa na cewa"salamu Alaikum".





"Wa'alaiki salam".
cewar Khadijah data leƙo matashiyar yarinyar da zasuyi sa'anin juna da Inteesar ce tace"Aunty ina yini".
a tinaninta Inteesar ce cikin sakin fuska Khadijah tace"lafiya ƙlau".
"dama Abbanku ne yace azo a faɗamiki kifito zamu tafi".
cikin rashin fahimta Khadijah tace"bangane ba".
"nice ƙanwar mijinki Abdallah".
faɗaɗa murmushi Khadijah tayi tare da cewa"au ƙanwar angon Aunty ce ke shigo muje Auntyn tana ciki".
"toh".
Rahama tafaɗa a zuciyarta tace"amma gaskiya wannan tanada kyau a tinanina naɗauka itace Auntyn tawa Allah yasa itama Aunty mekyau ce kamarta domin banaso Yayah ya rainata".
suna shiga cikin ɗakin Hauwah Khadijah tace"Aunty Inteesar ga ƙanwar mijinki nan tace kije Abbah na kiranki".
saurin share hawayen fuskarta tayi tare da ƙaƙalo murmushi tace"toh sannunki da zuwa".
a zuci Rahama tace"wow masha Allah amma gaskiya Auntynnan tahaɗu ai wannanma hartafi wadda ta rakoni kyau dole ya Abdallah ya kalleta domin ko mace taga wannan dole tabita da ido ballantana namiji".
a fili kuma murmushi Rahama tayi tare da zama kusa da Inteesar tace"yauwa sannunku ina yininku".
"lafiya ƙlau ".
cewar Hauwah Inteesar dake ƙoƙarin ɗaura ɗan kwali Rahama ta wutsiyar ido gani tayi kamar tana yimata kama da wani amma ta rasa inda tasan fuskar ganin takasa gano inda tasan fuskar ne yasata cewa"sannunki yaya sunanki".
"sunana Rahama".
"masha Allah".
"amm dama Abbanku ne yace ayomiki magana zamu tafi ".
damm ƙirjin Inteesar yabayar cikin dauriya tace"Besty ɗakkomun ankon Asma'uh nasa".
"toh".
nan tashirya cikin atamfar ankon Asma'uh me colour ɗin dark blue da light blue Hauwah tasata dole tashafa powder da lipstick se kwalli baƙaramin kyau tayiba kamar kasaceta ka gudu abinka da farar mace setayi fes da ita se ƴar ramar lokaci guda datayi hijab tasa light blue wanda yayi daidai da colour ɗin patan ɗin jikin doguwar rigarta tasa takalminta da jakarta masu sauƙin kuɗi duk light blue zuwa wannan lokacin jikinta yaƙarayin mugun sanyi dakyar Hauwah takamata suka fita falo inda su Khadijah ke zaune suna jiransu.




Tundaga takalminta Rahama tafara kallonta har zuwa kyakyawar fuskarta data ƙarayin fayau da ita baƙaramin kyau tayi ba saurin isa gareta Rahama tayi tare da cewa"Auntyna gaskiya kinada kyau masha Allah".
murmushin ƙarfin hali Inteesar tayi tare da cewa"ai kinfini kyau".
zaro ido Rahama tayi tare da cewa"nafiki kyau ai se a gudu".
murmushi kawai Inteesar tayi nansuka tafi suna isa cikin gida Innah Maryama matar ƙanin Abbansu Inteesar ta anshi hannun Inteesar ta nufi ɗakin Abbanta da ita zaune suka samu Abbah da ƙanin Abbansu Inteesar se karkaɗa ƙafa yakeyi alamun masifa gefansa Uwar Gwarama se Babah Mustapha wato ƙaninsa se Ummih datayi ƙasa da kanta cikin masifa Abbah yace"kaida kayi gaban kanka mekuma kasa a kawomun ita tayimun ko ƴarkace aise haka ".
"yaje yayita yin hakan aikai Malam ya ragemaka wahalar ci da ita dakakeyi".
"nasa ankawota ne dankayimata faɗa a matsayin mahaifi".
"kotabi mijinta ko karta bishi ruwanta idan taje yakorota karta sake ta nufo gidana domin wallahi kika dawomun gida sekinci ubanki ruwanki ne kiyimasa biyayya ruwanki ne kiƙi wannan matsalarki ce ba tawa ba nidai na faɗamiki ki kwana da sanin duk randa kika gwadawa mijinki baƙin halin uwarki yakoroki to badai gidana ba kinemi wani gidan uban badai nanba".
Abbah na gama faɗan haka ya miƙe yana kakkaɓe babbariga da niyyar tafiya cikin takaicin Yayansa yace"haba Yayah wacce irin nasiha kayiwa yarinyar nan kamar bakai ka haifeta ba haba Yayah kariƙa adalci a tsakanin iyalanka saboda halin rayuwa bakasan wanda ze temakekaba cikinsu kaƙi naka duniya tasoshi ne kaso naka duniya taƙishi banaso ranar lahira ka tashi da shanyayyen jiki domin abubuwan dakake sambasu kamata ba Yayah kamar yadda na saba faɗamaka bazan gaji da dena faɗamaka gaskiya ba koda za'ah a yankani sede duk abinda zakaimun kayimun kuma naji ko maganar kayan ɗaki bakayiba wanda yanzu kuma naji kana zancen na Jameelah ai wannan be daceba Ummih idan munfita zanbawa Maryam suje ayimata kuɗi dubu ɗari biyu se ayiwa Inteesar ɗin siyayya ".
"aikai ka haifeta ubana bansan adalciba sekai ni lokacin da ake rabonsa bacci nakeyi kagako ai bazan sanshiba sekai ɗan masani aljanna kuma inkai kake rabawa karka bani kuma daka yau karka ƙara takomun gidana ai nawane ni kaɗai bana gado bane bana buƙatar ganin ƙafarka a cikin gidana tunda dai kaiba zumunci ke kawoka ba munafunci ke kawoka da yimun rashin kunya to daka yau nayimaka katangar ƙarfe da gidana bani bakai kuma kuɗi kasake kabayar akayi asararsu ban yafewa yarinyar daka saiwaba indai nina haifeta to ban yarje ta anshi sisinkaba ".
"wallahi kuwa Malam haba wannan dashine gaba dakai dukanka zeriƙayi Malam dama ninasan idan Mustapha bason zamana yakeyi a gidannanba da ace yanada iko da tini yasaka Malam ka bani takardata haba wannan fitina ko ina ruwanshi dan munyi maganar kaya oho koko so yakeyi ka ɓata kuɗinka a gidan almajirin da akace azara ɗaya babu balle tushen gini".
"wallahi kuwa nima ai na daɗe da fahimtar haka ka tashi kabarmun gida baƙin munafuki dan haka yadda ban ɓata kuɗinaba gun siyamata kayan ɗaki banaso kaima ka ɓata inkuma haka kakeji kabani kuɗin inƙarawa Jameelah domin so nikeyi asaimata ƴan waje safi quality".
"ko bakace ba Yayah zanbarmaka gidanka amma kasani bazan sake tako ƙafata cikin gidanka ba Allah ya fito dakai daga duhun daka shiga ya nunamaka haske kuma danabaka kuɗina kayi rashin adalci gwara su zube wallahi nasan zubewa sukayi".
yana gama faɗin haka ya miƙe tare da taɓasu Ummih da matarshi yayimusu nuni dasu wuce nan suka fara tafiya tsaki Uwar Gwarama tayi tare da cewa"Ummah tagaida ashsha munafukai"..
nan suka fita a ƙofar gida suka tsaya cike da tausayin Ummih Baba Mustapha yace"kicigaba da haƙurinnan dana sanki dashi insha Allahu komai ze zama tarihi ba'ah taɓa dawwama a abu ɗaya kicigaba da gayawa Allah komai zezamo tarihi domin ita addu'ar wanda aka zalunta babu hijabi kuma kinsanshi bawa be isa ya kaucewa ƙaddararsa kekuma Inteesar kibi mijinki sauda ƙafa insha Allahu bazaki taɓa danasani ba a rayuwarki ki amshi ƙaddararki hannu bibiyu insha Allahu hakan ze zamemiki alkhairi insha Allahu sekinyiwa mahaifinki rana kuɗin da yake rainawa insha Allahu seya amfana daku kiyiwa mijinki biyayya kamar yadda nasankinnan karki canza insha Allahu aurenki zezamarmiki alkairi kije suna jiranki ga wannan Ummih ko sabulu kwa rage".
ansa Ummih tayi tare da cewa"angode Allah ya saka da alkhairi".
"Ameen ya Allah kiyiwa Inteesar ɗin nasiha".
"aini ba abinda zance saboda naji duk abinda zance ka faɗamata sede na ƙara da cemiki ki daɗa dagewa gurin addu'ah da azkhar".
Inteesar daketa faman kuka ce ta ɗaga kai na Matar Uncle Mustapha takamata suka fara tafiya har sunje daidai motar Ummih tabisu da sauri tace"bani hannunki".
miƙamata hannu Inteesar tayi nanta sakamata wani abu dakoni bansan meneneba kuka tashigayi sosai ta rungume Hauwah dakyar aka rabasu aka sakata a mota Hauwah kuma matar Uncle Mustapha tarriƙeta suka tafi sosai take kuka driver yaja suka fara tafiya!!!!!!!!!!





Votes and Comments




_*Daga Alƙalamun ƴar mutanen Gwarzo.*_




# Real eeshow



_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_


Book 2


5️⃣3️⃣➡️5️⃣4️⃣



Sosai take kukan rabuwa da gida dukko da irin rashin daɗin gidan datakeji jitayi dama abarta a gida ta dawwama cikin girmamawa da muryarta data dishe tace"ina yini".
"lafiya ƙlau kishiyata kin kwacemun miji sannan kuma kinbini da kuka aini yakamata danayi kuka tunda kin kwacemun miji me yomun cefane ba dare ba rana".
dariya Inteesar tayi tare da ƙara yin ƙasa da kanta kamar yadda tayi da zata gaida Granny batare data ɗago ta kalli Abbih ba tace"ina yini Abbah".
murmushi Abbih yayi a zuciyarsa yana ƙara godewa Allah daya bashi suruka me hankali yace"lafiya ƙlau daughter yasu Mamanki".
"duk lafiya ƙlau suke".
"masha Allah".i
nan ta gaida Salisu driver shima cikin gurmamawa sundaɗe suna tafiya duk tsawon wannan lokacin kan Inteesar na duƙe batasan ina sukebiba yayinda gabanta ke ƙara tsananta faɗuwa har suka isa gaban wani tanƙamemen mension horn taji driver nayi hakan yasata ɗagowa mamakine yakamata ganin sunayin horn a gaban wani jibgegen gida wanda tunda uwarta tahaifeta bata taɓa ganin irinsa ba addu'o'ih tashiga karantowa duk wanda yazo bakinta domin tunda uwarta tahaifeta bata taɓa ganin gida mekyau da tsaruwa kamar wannan gidanba wasu kitika-kitikan garadane majiya ƙarfine suka wangale tanƙamemen get ɗin cilla hancin motar Salisu driver yayi gani tayi haɗaɗɗen fili ya bayyana me shuke-shuke masu matuƙar ɗaukar hankali baƙaramin kyau gurin yayimata ba se mamaki take a zuciyarta na haɗuwar gurin tafiya kaɗan suka ƙara suka isa gaban wani katafaren get wanda yafi na farko da suka wuto kyau da haɗuwa ga matakan tsaro nan duk tsaitsaye da bindiga wani mugun tsoro ne ya dira a zuciyar Inteesar tace"anya ko Babah Mustapha yayi bincike kan wa'innan mutanen kuwa kafin ya aurawa ɗansu aure dani da Abbanane dasena ce saidani yayi to ni Aishatu meke shirin faruwa danine haka".
wasu hawayene masu zafi suka silalomata na takaicin Abbanta bata ƙara tsinkewa da al'amarin ba seda taga anbuɗemusu sun wuce wannan get ɗinma gani tayi filin gurin yafi na farko tsaruwa komai da komai tafiya sukayi meɗan nisa kafin su wuce wani round about su nufi wani tamfatsetsen get golden se ɗaukar ido yakeyi wani kantamemen mutumi tagani tsaye a jikin get ɗin ya buɗemusu get tare da risinawa cikin girmamawa yace"barkanku da dawowa".
zuge glass Salisu driver yayi tare da cewa"yauwa Emeker".
nan suka wuce zuwa wannan lokacin cikin Inteesar yagama tsurewa ba abinda takeyi se gumi dukda ac motar dake ta faman aiki se zare ido sakamakon tozalin datayi da wasu tanƙama-tanƙaman mension guda uku a jere farare tas dasu ko wanne yana wane wannan ga shuke-shuke masu matuƙar ɗaukar ido gefe guda kuma swiming pool ne cikinsa gabaki ɗaya farin tiles ne se ruwan daya kasance colourless da wasu resting chairs ne a kusa da swiming ɗin se table a tsakiya akan tables ɗin kuma wata flower ce red a aje masu matuƙar ɗaukar hankali gurin wani tanƙamemen tamfal dayake shaƙe da motoci ƴan ubansu sukayi parking ɗin motarsu suna gama parking securities suka buɗemusu ƙofofi Abbih ne yafara sauka se Granny zungurar Inteesar Rahama tayi tare da cewa"barkanki da zuwa gidanki matar Yayah".
saurin dawowa tayi daga duniyar tinanin data shiga taɗan ƙaƙalo murmushin da iyakarsa leɓanta tace"nagode sis".
taƙarasa zancenta tana mai tattaro ɗan ƙarfin daya ragemata ta sakko biyo bayanta Rahama tayi wata fresh air taji tana kaɗawa bin bayan Granny sukayi data nufi building ɗin dake tsakiya.



Suna isa gaban ƙofar building ɗin Granny ta kwance zaninta tazaro makulli daga haɓar zaninta ta buɗe ƙofar tashiga bin bayanta sukayi yayinda Inteesar keta faman kalle-kalle tana shiga falon taga ashe da bataga komaiba saboda baƙaramin haɗuwa falon yayiba komai na falon black and red ne hattana carpet ɗin dake falon zama Granny tayi akan kujera tare da cewa"wash Allah na".
zama Rahama tayi kusa da Granny rakuɓewa Inteesar tayi ɗan nesa dasu tazauna akan carpet ganin yadda ta takurene yasa Granny cewa"haba kishiyata yaza'ai ki raɓe keda gidanki tashi ki zauna kan kujera man kamar wadda tazo baƙon guri haba takwarata".
murmushi Inteesar tayi tare da cewa"nanma ya isa".
"ki saki jikinki sosai kidena wani jin kunya gidam baki sake a gidanki ba a ina zaki sake tunda naganki naji kin kwantamun naɗaukeki tamkar ɗiyar dana haifa ta cikina inaso kema ki ɗaukeni tamkar mahaifiyar data haifeki duk wani abu daya shigemiki duhu karki tsaya jin kinya kifaɗamun kanki tsaye kinji shima kuma me sunan manya zanjamasa kunne sosai yakulamun dake banaso naji wata ɓaraka ta bayyana".
"insha Allahu Hajiya nagode".
"yauwa Inteesar ki riƙa kirana da sunan dasu Mesunan Manya ke kirana wato Ammi".
"toh Ammi".
"yauwa ɗiyar albarka sarkin lalaci tashi kishigar da ita ciki tayi wanka tayi sallah sekuci abinci".
"toh Ammi Aunty tashi muje ciki".
"toh".
nan Rahama tayi gaba Inteesar tabi bayanta.





8:30pm
Motoci ne masu tsada jere a ƙofar gidansu Inteesar sunzo ɗaukar Jameelah cikin gida nashiga domin ɗakkomuku rahoto Dagauta nagani ta riƙo hannun Jameelah daketa faman zare idanu bsko lulluɓe fuska ta nufi ɗakin Abbah da ita Abbah naganinta ya washe baki Dagauta ce tace"gatanan ayimata faɗa".
taƙarasa zancenta tana Uwar Gwarama dake kusa da Abbah washe baki Abbah yayi tare da cewa"sannu kinji Jameelatu Allah yayimiki albarka yabaki kema masu yimiki biyayya kamar yadda nima kikayimun nasan nayimiki karan tsaye batare danaji tabakinki ba kan Zaidu na ɗauramuku aure nayi hakane badon komai ba saboda nasan keɗin me biyayya ce inaso idan kinje gidan mijinki ki gwadamasa halayennan naki na kwarai kiyimasa biyayya yinayi bari na bari shi aure dakike gani ɗan haƙuri ne kowa kika gani a gidansa to zaman haƙuri yakeyi haƙuri shine babban jigo".
"Abbah ai bakomai insha Allahu bazan kasance me baka kunya ba zanyi iya yina".
"yauwa ƴar albarka Allah yayimiki albarka".
"Ameen Abbah".
"yauwa Saratu ga Jameelatu nan".
gyara zama Uwar Gwarama tayi tare da cewa"aini duk abinda zan faɗa ka faɗamata shi sede wasu ƴan abubuwa da baka faɗamata ba idan munfita zan faɗamata".
washe baki Abbah yayi tare da cewa"toh madallah".
nan suka tashi suka fita har suka isa bakin mota sannan Uwar Gwarama taja hannun Jameela suka keɓe ta kwance haɓar zaninta ta danƙawa Jameelah wani ƙulli a hannunta tace"wannan dakike gani shine mallaka na ansomiki a gurin boka yace Zaid zeriƙa yimiki kyauta kamar ba gobe sannan zezamarmiki tamkar raƙumi da akala se yanda kikayi dashi ammafa yanada hatsarin gaske daddare ake ki shafashi koda safe saboda ba'ah so kowa yagani inkikayi sake wani yaga lokaci dakike shafawa shikenan aikin dukda mukayi kan Zaid ze lalace dan haka seki kula sosai zamu riƙa kewayowa nida Dagauta muna ansar abinda kika tatsa gurinsa domin Allah ne yakawomu lokacin dazamu huta ki kula sosai karki lalatamana shiri".
"ai Ummah ki kwantar da hankalinki bawani abu dazan lalata".
"yauwa tawan domin so nike abinda kika ɗan tatsa a gurinsa jibi nazo na ansa afara biyan masu kayan gado da aka ɗakko bashi koɗan agogo yaɗan aje kiyi wuf dashi ki ɓoye saboda kinsan irinsu waɗanda kuɗi suka yimusu yawa ba ganewa suke ba".
"toh Ummana karkiji komai yadda kika tsara haka za'ai ga wannan wayar da waccan tsinanniyar ta aiko da ita".
"bani ita nan mariƙa waya dake".
"toh Ummah".
nan sukayi sallama tahau mota su Dagauta suka shishiga suka nufi Garki.






Zaune yake akan sofa yana aiki da system ɗinsa yaji ana ƙoƙarin buɗe ƙofa be ɗago daga aikin da yakeyiba sakamakon yasan bame shigomasa bedroom direct se Rahama bakinta ɗauke da Sallama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login