Showing 21001 words to 22282 words out of 22282 words
murmushin takaici Meemah tayi tare da cewa"mekuma zaki faɗamun Mummy bayan kingama dani banyi tsammanin baki damu da farincikina ba se yau kullum faɗmmun kike kinaso na ashe duk zancenki a baki ne tunda abu ɗaya common kinkasa yimun shi eyi daban santa ba na nuna nasanta ne".
"ki kwantarmun da hankalinki indai Namijin duniya ne nakine ke kaɗai matsawar ina numfashi sekin aureshi kedai kawai abunda nakeso dake ki ɗaure ki faɗamun inda kika taɓa ganin wannan ƴar iskar yarinyar".
"a offiice ɗinsa na taɓa ganinta suna rugume da juna tamkar zata shiga cikinsa".
Cikin sassauta murya da alamun rarrashi ba tare dataji haushin abinda ɗiyartata take faɗamata ba ta dafa kafaɗarta tace"kema kinyi kuskure Meemah meyesa tun a lokacin da kika gansun baki faɗamin ba na ɗauki tsa-tsauran mataki akanta ba sai yanzu aini bansan da ita ba da tini bankau da itaba itaɗin banza me akai akayita dahar zata saki kuka idan kika kwantar da hankalinki kika bani haɗin kai duk wannan me sauƙi ne a gurina yau ɗinnan base gobe ba zan sharemiki hawayenki baki da wani mijin bayan Namijin duniya matsawar ina numfashi sena cikamiki burinki koda zanyi yawo tsirara".
Cikin sauri da yanayin ɓacin rai gami da takaici Meemah ta watsa mata wani ƙasƙantaccen kallo cikin fusata tace"Enough is enough Mommy kada ki sake ruguzamin zuciya da wannan kalaman naki da kullum kike maimaita min su kamar karatu amma kin gaza cika min burina tayaya zaki ce zaki cikamun burina bayan bakin alƙalami yariga da ya bushe tunda a yanzu yanada mata abun takaicinma bani zefara kwana ba sede insamu ragowar watanma ɗiyar talakawa ƙasƙantacciya mara daraja ita zata gaji duk wani abu dayake dashi haba Mummy ina ko hankalina zekwanta banji munkwana da Namijin duniya a gado ɗaya ba Mummy dan Allah kiyi wani abu".
taƙarasa zancenta tana mai fashewa da wani matsanancin kuka jijjigata Mummy tashiga yi alamun rarrashi sannan ta sauke wani numfashi me zafi tare da cewa"hmmm Meemah kenan ki kwantar da hankalinki indai wannance matsalarki daka yau bazaki sake kuka kanta ba indai nina haifeki zaki auri Namijin duniya daga yau takau zanyimiki maganinta kedai kawai kitsaya kisha kallo kamar yadda wannan ƙasƙantacciyar yarinyar tazo gidannan da ƙafarta haka zatabar gidannan zakice na faɗamiki nasan duk wannan kutunguilar tana gurin wannan tsinanniyar tsohuwar najadun zanyi maganinsu gabaki ɗayansu kawo kunnenki kiji".
saurin kai kunnenta tayi kusa nanta faɗamata magana wadda ni kaina real eeshow bansan me tacemata ba naga dai kawai gabaki ɗayansu sun tintsire da dariya gami da tafawa Meemah tace"gaskiya Mummyna baki da kyau karo da ke ba riba haka nake sonki Mummyna maganin kukana"
Jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofa ne yasa Jameelah saurin lulluɓe fuskarta ta gyara zamanta a tsakiyar gado kamar ba ita keta kalle-kalle ba buɗe ƙofar Zaid yayi tare da lumshe ido ya saukesu akan Jameelah dake lulluɓe cikin mayafi maida ƙofar yayi ya rife tare da ɗauƙar ledojin dake hannunsa ya nufi bed side drower ya ɗora sannan ya haye kan gadon tare da zama kusa da Jameelah yasa hannu ya yaye lulluɓin dake fuskarta tare da sakarmata wani murmushin dayasa tayi suman wucin gadi yace"gimbiyata abar alfaharina wai har yau kukanne baki dena ba kinsan banason kina zubarmun da tsadaddun hawayenki da suka fi komai tsada a gurina ni banga abun kuka ba kina sona nima ina sonki a ganina farin ciki ma zamuyi tunda burinmu yagama cika munzama mata da miji".
yaƙarasa zancensa yana mai kai lallausan hannunsa kan fuskarta yana ƙoƙarin sharemata hawayen munafuncin data ƙirƙira a lokacin ƙara narke murya Jameelah tayi kamar wadda ta jima tana kuka tace"kukan farin ciki nakeyi masoyina gani nake kamar a mafarki wai yau nice a matsayin matarka tawani ɓangaren ina murna tawani ɓangaren ina baƙin ciki domin Honey naga kamar danginka basa sona koda aka kawoni ba wanda ya kulamu wata ƴar farar yarinyama har gori tayimun wai ni ban cancanta inzama matarka ni ƴar matsiyata ce wai kwaɗayin abun duniya ne yasa na aureka bakaji irin cin mutuncin datayimun ba harda dunguremun kai".
taƙarasa zancenta tana mai fashewa da kukan munafunci jiki na rawa Zaid ya miƙe har huci yake yace"ya haƙuri Sweetheart zanyiwa tufkar hanci zanyi maganinta dan uwarta sena karyata naga ubanda ya tsayamata da har zata ci muki mutunci sukuma dangina karki damu dan basa sonki aiba dasu zaki zauna ba dani zaki zauna".
yakai zancensa yana mai yin hanyar ƙofa da niyyar fita saurin riƙo hannunshi Jameelah tayi cikin ƙissa tace"haba Honey so kake ka ƙara jamun wani baƙin jinin a gurin daginka ace daka zuwana nafara haɗaka da ƴan uwanka kuma ma bekamata mu ɓata wannan daren me albarka ba kamata yayi ace ina nan ina farantamaka ranka ta hanyar baka kulawa ta musamman tsakanin miji da mata kumama ita yarinyar data yimun ai yarinya ce bata da hankali bama taru muzama ɗaya ba wataran idan akace tayima bazata yarda tayiba".
rungumeta a ƙirjinsa yayi yayinda yakejin wata sabuwar ƙaunarta naƙara ratsa ko ina na jikinsa yace "gaskiya ne Mar'atussaliha meson farin cikin mijinta a koda yaushe".
nan ya kama hannunta kamar ze haɗiyeta danso ya zaunar da ita ya ɗakko ledar daya shigo da ita ya aje akan stool sannan ya rakwafo ya sakarmata wani kiss da seda wutar ta ɗauke na wani lokaci yace"Baby wait for some minutes".
ɗaga kai kawai Jameelah tayi domin batasan me Zaid yace ba nanya wuce ya nufi kitchen yana fita ta ɗaga waya ta kira Uwar Gwarama bugu ɗaya ta ɗauka tare da cewa"alo ƴar albarka tasamu ne".
"wallahi kuwa Ummah tasamu domin bakiga dakwa-dakwan gasassun kajin daya shigo dasu ba guda biyu da lemuka".
washe baki Uwar Gwarama tayi tare da cewa"kice Allah toki ajemun nawa kason don gobe zaki ganni da sassafe ya batun ƴan ɗauke-ɗauken ne wai ina fatandai kinfara domin kinsan da hakafa zamu samu mu biya ƙarashen kuɗin katakwaye muɗan tara abinda muka tara ".
"Ummah bakiga yadda idan nayi magana jikinsa ke rawa ba kamar ba wannan Zaid ɗinba me shegen girman kan tsiyaba gaskiya Ummah kina shege".
"yoto ni ta wasa ce ai duk wanda yace ze kara dani sede uwarsa tahaifi wani da yanzu wannan ƴar iskar yarinyar kejin daɗi da kikeji kinga se tsinanne girman kannan ya ƙara ƙaruwa yanzu ko sede ayi wannan iskancin a gidan almajiri shima ɗin idan ansamu abun sawa a bakin salati wai da itace a jindaɗin dakike da anga iskanci ai kozan rasa zanin ɗaurawa bazan taɓa barin ƴaƴan Khadijah suyi aure gidan hutu ba sede su kalla anayi".
"gaskiya ne Ummah wadda tafi takowa sekinzo bara inkashe karyazo ya sameni".
"toh senazo karfa kiyi maganin nan a gaban kowa".
"bazanyi ba ai zan kula sosai".
"yauwa dan kinsan boka yace kar asamu matsala wani yagani inba haka ba gabaki ɗaya zata kwaɓemana ayi bawan ba ƙanin karatun ɗan kama mushiga bala'ih".
"toh".
nanta kashe tana aje wayar Zaid na shigowa.
Tun daka nesa ya kafeta da sexy eyes ɗinsa dake cikin baƙin glass a zuciyarsa yace"lallai ma wannan futsararriyar yarinyar waya bata damar fita da wannan shigar da igiyar aurena akanta".
yana wannan maganar harta ƙaraso gurin motar tana niyyar buɗe owners corner taji muryar Namijin duniya yace"wakika tambaya zaki unguwa dahar kika samu damar shigomun mota".
yaƙarasa zancensa tare da ɗauke kansa daka gareta yawani ƙara shan kunu kamar ba daka bakinsa wannan maganar ta fito ba kallonsa Inteesar tayi sama da ƙasa a hassale tace "Ammih ce tasa nashirya banda haka meze sani na yarda ajina nashiga wannan gwangwanin naka"!!!!!!!!!!!!!
Votes and Comments
_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_