Showing 3001 words to 6000 words out of 77617 words

Chapter 2 - Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel

06 Jan 2025

579

nazo da ita danta d'an ringa taimakona dawasu ayyukan saboda girma dake k'ara saukamin.
Yayi.
kaiwai hajiya tafad'a, sannan tagyara zaman Jakarta tana fad'in nawuce aiki saina dawo.
Kai gwaggo bintu ta jinjina tana mata addu'ar dawowa lfy.
Jikin Aysha yayi sanyi sosai, Dan yau taga wulak'anci irinna masu kud'i da'ake fad'a, ko kad'an batason dizgi arayuwarta, saima abinda yafi firgitata shine furicin gwaggo bintu datace wai tataho daita danta tayata aiki. Kenan aikatau aka taho da'ita tayi?, gabantane yayi mummunar fad'uwa, da sauri tace kai ALLAH ya kiyaye, nida gatana nazama 'yar aiki? Ina bahaka baneba, banji zance daidaibane.
Jan hannunta gwaggo bintu tayi suka nufi wajen dining table, wata k'ofa daked'an gefe ta Gila's suka nufa, gwaggo bintu ta danna wani green d'in Abu k'ofar tabud'e, wani k'amshi mai kwantar da hankalin mai shak'a yadoki hancinansu, mutanene ak'alla sunkai hud'u a kichin d'in.
Kusan atare sukace lale marhabin da Maman yara, baki sosai gwaggo bintu ta washe tareda musu sannu da aiki, tak'arasa gaban wata k'yak'yk'yawar mace, fara tas da'ita, itama tanada d'an jiki, amma matar d'azu tafita k'iba, ita kuma wannan kamar zatafi ta d'azun shekaru, Dan zatakai ak'alla 48year's aduniya, saidai k'yawunta da kwarjininta sun 6oye yawan shekarunta, (aganina harda jin dad'ima) tana sanye da doguwar riga bak'a wadda tak'awatu da adon fararen duwatsu, tayi rolling d'ankwalin rigar a kanta, bak'aramin k'yau tayiba kuwa, kaikace tafito daga jinsin larabawane.
Durk'usawa gwaggo bintu tayi yanzuma, cikin nuna girmamawa tace hajiya ina yini? Munsameku lfy?.
Fuskarta d'aukeda murmushi tace lfy lau Alhmdllh Maman yara, yak'arin hak'uri kuma? ALLAH yagafarta masa.
Ameen yarabbi hajiya, ya yaran?.
Duk suna lfy. Kowa yana makaranta.
Aysha dake durk'ushe itama tace inayini?.
Kallonta sosai hajiya tayi, haka kawai taji girarta tadama ta harba, hakama k'irjinta saida yad'an buga, ahankali tafirta "innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un". Sannan ta amsama Aysha gaisuwarta, har yanzu idonta nakan Ayshar, tace Maman yara wannanfa?.
d'iya tace Aunty Amarya, tawajen mai rasuwarce nataho da ita.
ALLAH sarki 'yanmata ya sunanki?.
Kan Aysha ak'asa tace, "A'ISHA!".
Masha ALLAH Ayshatu humairah, yahak'urin rashin mahaifi?.
Idon Aysha taf da kwallah tace, " Alhamdllh mama.
Aunty Amarya taji dad'in sunan da Aysha takirata dashi, tace ALLAH yagafarta masa, yabaku hak'urin rashinsa kinji.
Kowa a kichin d'in ya amsa da amin.
Bayan gwaggo bintu tagama gaisawa da sauran mutanen sukaimata gaisuwa, Aysha dai kuka yahanata gaidasu.
Kulada kukan datakeyi hajiya tace, "Maman yara kushiga cikin Ku huta kafin muk'arasa girki, yau mun makarane wlhy.
Da girmamawa gwaggo bintu ta amsa tareda Jan hannun Aysha suka fita.
Binsu da kallo hajiya tayi, wani tausayin Aysha da k'aunarta suka tsarga zuciyarta lokaci d'aya, haka kawai yarinyar tashiga ranta, (amma saita alak'anta hakan da tausayinta na maraici).


Nace humm anya kuwa Hajiya?.πŸ€”

Daga nana fita suka kumayi daga falon gaba d'aya zuwa wani gini madaidaici dake can baya, shima yanada k'yansa, amma k'aramine sosai, suntadda matsakaicin falo mai d'aukeda kujeru set 1, sai d'akuna ak'allah hud'u, gwaggo bintu tabud'e d'aya da makulli suka Shiga, d'akine madaidaici mai k'atuwar katifa, sai wardrop d'in bango da abinda ba'a rasaba.
Kaya kawai suka ajiye gwaggo bintu tashige wata k'ofa, inaga band'akine awajen.
Wannan yatabbatarma Aysha shine 6angaren dazasu zauna kenan.
Ba'a wani d'au lokaciba gwaggo bintu tafito, da'alama alwala tayi, tace Aysha taje itama tayi.
Bayan sun gabatar da sallah cikin wad'anda suka Tarar a kicin takawo musu abinci, zama tayi suka k'ara gaisawa da gwaggo bintu.
Daganan surutu ya 6alle a tsakaninsu Wanda yawanci duk gulmar 'yan gidance da labarin abinda yafaru bayan tafiyar gwaggo bintu wajen rasuwar abbasu Aysha.
Itadai Aysha taci abincinta, tana kuma saurarensu daki-daki.
Zuwa can iya Hama ta mik'e, tana fad'in bara naje Na huta kafin uwar saka aikincan takiramu, kinsan duk ranar aikin Hajiya Bilkeesu babu mai Hutu agidannan, itabata hutaba batabar wani yahutaba, barema yau Alhaji Na gari.
Ha6a gwaggo bintu tarik'e tana fad'in ke Dan ALLAH?.
wlhy kuwa yana nan, yau kwanansa uku da zuwa, jiya hajiya babba ta ajiye aiki, yau hajiya Bilkeesu takar6a.
Cikin magana irinta gulma gwaggo bintu tace, haba nifa ko ince, nayi mamakin tadda hajiya Saudah agida irin lokacinnan.
Ina hama ta ta6e baki tana fad'in hummm, kemadai k'yafad'a aii. Daganan tafice abinta.
Aysha tace, "ALLAH ya k'yauta azuciyarta, dankuwa su gwaggo bintu sun bata mamaki sosai, suna k'ark'ashin arzik'in mutane amma suna gulmarsu da saka musu ido alamarin gidamsu...............πŸ–Š








*I love you all my fan's*😍
[8/7, 7:36 AM] Aisha Galadima: *_Typing_*πŸ“²



🀰
*_CIKI DA GASKIYA.......!!_*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_



*_Bilyn Abdul ceπŸ€™πŸ»_*


*_NIKA'DAI WRITER ASSO......._*😜


*Sadaukarwa*
_My sweet dady_
(ALLAH ya gafarta maka)🀲🏻



*_part 1_*
(littafi na d'ayaπŸ“•)


_Godiya gareki billy s fari, luv you so much_
.
,´¯`,
,´¯`:,..../
/Β―/.../..../ β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’
/../.../..../..,----,
/../.../....//Β΄...........`. Happy
/../.../..../......../´¯\....\ β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’
('.('..('....('.........|. πŸ’™πŸπŸ’™
\.....................`\.../Β΄...)
\.......πŸ’™...../ New book
\.... πŸ’™.../ β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’
\......................./
|......................|Billyn abdul
πŸ’™β–ˆβš€βšƒβš„βš…βšƒβš€β–ˆπŸ’™
.πŸ‡―πŸ‡΅.ΒΈγ€€ΒΈ.πŸ‡―πŸ‡΅
γ€€ (✺`β€œβ€’.\\ . // ΒΈ. β€’"´✺)
γ€€ β€œβ€’ΒΈ.. πŸ’™πŸπŸ’™ .β€’β€œ
γ€€ (✺¸.β€’β€œ// \\`β€œβ€’.¸✺)
γ€€ πŸ’™ciki da gaskiyaπŸ’™
πŸ’™β–ˆβš€βš„βš…βšƒβš„βš€β–ˆ πŸ’™



0⃣3⃣


Gwaggo bintu ta kalli Aysha dake zaune a gefen katifa ta rabga uban tagumi, gaba d'aya kewar iyayenta da 'yan uwanta sun addabeta, jitake kamar tayi tsuntsuwa taganta a Kano....
Ta6atan da gwaggo bintu tayine yakatse mata tunaninta, tajuyo tana kallonta, harara gwaggo bintu tasakar mata tareda fad'in waike wannan dogon tunanin namiyene? Kosukike mutanen gidan sud'auka satoki nayine?.
Aysha tagoge kwallan dasuka cika mata idanu, kanta tashiga girgizawa alamar a'a, Dan tana magana zata iya 6arkewa da kuka.
Baki gwaggo bintu ta ta6e, murya adak'ile tace saiki mik'e mushiga gaida mutan gidan.
Aysha tamik'e jiki a sanyaye, afalo suka iske su iya hama suna kallon film d'in kalan dangi, sai k'yalk'yala dariya suke zubawa, gwaggo bintu tace musu bara mugaida Ammah da Alhaji da hajiya babba.
To afito lfy cewar karime tana dariya, ammafa AMMAH bata dawoba.
Gwaggo bintu tace, "to bara mugaida uwargidan.
Dariya su iya hama suka farayi, itama gwaggo bintu dariyar takeyi.

Tsakar gidan kwanyar yake da haske tamkar rana, ko'ina kwayayen wutane masu k'yau, da sallama suka Shiga k'aton falon d'azun.
Bakajin komai sai hayaniyar yaran gidan Dana TV's, dan duk tvn uku akunne take, kuma kowanne rukunin kujeru akwai yaran.
Aysha tuni tsoro yakamata, Dan haka take bata cikason Shiga jama'aba.
Yaran suna ganin gwaggo bintu suka fara fad'in oyoyo Maman Yara, k'ananunma zuwa sukayi suka rungumeta,, wannan ya tabbatarma Aysha da kowa yasan gwaggo bintu agidan. Aysha takai dubanta ga set d'in fararen kujerun inda matasan samarin gidan suke zazzaune, wasu a kujeru wasu ak'asan center rug, su kusan 7 ne awajen, sai surutu suke zubawa suna dariya, kallonta yatsaya akan Wanda ke a tsaye yanata zabga surutu, fira sukeyi akan Ball, wannan yasa suka rud'e da gaddama, kowa Na k'ok'arin kare Team d'insa.
Sun birge Aysha sosai, Dan duk suna kama da juna, d'ayan gefen kuma 'yammatane su hud'u, Wanda zasu iya zama sa'annin juna, saikuma biyu dasuma Kansu d'aya, amma basukai Girman Na farkoba, sai kuma k'ananun yara biyar suma bidabi.
Cikin ladabi Aysha tagaida matasan samarin kamar yanda gwaggo bintu ta umarceta.
Duk suka amsa idonsu akanta, ganin bak'uwar fuska, Na tsaye mai surutu yace uhhm INA Maman yara tasamo mana pretty girl d'innan?.
Wanda ke kusadashine ya shuri k'afafunsa, cikin wasa yace kai Musleem kaga takanka, anya kuwa bakai za'a farama aure agidannanba?.
Da sauri musleem yadafe inda Ramadan ya shureshi, yace, " kutt kai ya Ramadan rufamin asiri mana, ga ya khaleel can mai shekaru 32 baya maganar aure saini daban wuce 25 ba, gasu ya Sultan & ya mujaheed nanma.
Hararsa ya Sultan tayi, yace, " mukad'ai ka raina ko? Kafad'a agaban ya khaleel mana in ba tsoroba.
Dariya suka kece da'ita gaba d'aya, cikin dariya Muhseen yace, "wlhy yafad'a inbaici k'aniyarsaba, kwanaki naje falon Baffah gaidashi lokacin ya khaleel nagida, saina tadda ana MASA fad'a, bammajifa akan abinda ake MASA fad'an ba, saidai nafahimci akan aurene amma wlhy tun agabam Baffah yake antayamin harara har muka fito......
Ananma dariya suka kumayi, yanzu harda 'yanmatanma, dan sunajiyo hirar yayun Nasu.
Aysha dai da firar tatashi domin ita kanta Na 'ak'asa, saida gwaggo bintu tace tatashi suje sannan tamik'e da k'yar saboda kunyar matasan samarin, masu matuk'ar birgeta, ganin kansu ahad'e family's abin sha'awa, ga zallar k'aunar junansu dasukeyi daga gani.
Harsun fara tafiya Hafeez yace, "Maman yara 'yarkice?.
Dariya Maman yara tayi, tace, " 'yatace Hafeez, d'iyar yayanace daya rasu naje gida.
Kusan atare sukace Maman yara rasuwa akayimiki? ALLAH bamu saniba, munzata kinje gidane ziyara.
Nan suka shiga mata gaisuwa, dayawansu tausayin Aysha yashigesu, Zunnurain sarkin tausayi har idonsa yacika da kwallah.
Godiya gwaggo bintu tamusu takama hannun Aysha suka nufi 6angaren hajiya babba.

Tana zaune hakimce a falonta, tana karatun jarida, babbar macece hamshak'iya, kallo d'aya zaka mata Kasan tagama jik'uwa da 'yan canji, gawata tak'ama da Isa irinta manyan mata 'yan boko, itamadai tanada k'ibarta babu laifi, saidai bak'ace, amma akwai k'yawu sosai, sanye take cikin doguwar Riga mai sul6i, zamu iya dangantata da rigar barci, Tamata k'au, dukda fuskarta babu alamun annuri, sai tsabagen mulki da tink'aho, gefenta 'yammatane su uku, biyu Kansu d'aya, d'aya kuma dagani tagirme musu, da kyar 'yan matan suka amsa sallamar tasu.
Gwaggo bintu tazube ak'asa tana gaida hajiya babba, saida taja wasu mintuna sannan ta ajiye jaridar hannunta tana amsawa da lfy cikin isa.
Cikin rawar murya Aysha ma ta gaisheta, ita saima yanzu takula da ayshar, tsuramata idanu tayi kurr batareda ta amsaba.
Aysha tayi k'asa da kanta, Dan ganin kallon kurillar da hajiya babba kemata, ita kanta gwaggo bintu talura, Dan haka gabanta yashiga fad'uwa, Dan batasan manufar kallonba, takuma kwana da Sanin rashin mutunci da k'yamar talaka irinna hajiya babba, wannan yasa Sam 'yan aikin gidan basuda kwarjini agareta da 'ya'yanta.
Hajiya babba tayi gyaran murya, cikin isarta tace bintu! Wannan yarinyarfa?.
Muryar gwaggo bintu narawa tace am... Am.... Hajiya d'iyar yayanace mai rasuwa aka bani.
d'an yatsine fuska hajiya babba tayi tareda gyara zaman siririn farin spece d'inta, batareda tace uffanba tad'auki jaridarta tacigaba da karatu.
Sukam 'yan matannan sai kallon wulak'anci sukema Aysha da gwaggo bintu kanta.
Wajen mintuna 3 babu Wanda yakuma cewa komai, yaran kowacce tana latsa waya, babbarce taketa latse-latse a laptop.
Wayar hajiya babba dake gefenta tahau wringing, d'aya daga cikin 'yanmatan tayi saurin d'auka, cikin ihun murna tace, "lahh ya khaleel ne.
Atare sauran sukace haba dai?.
Kafin tabasu amsa hajiya babba ta kwace wayarta tanata zuba murmushi, akunne takara tareda fad'in my lovelyson kana lfy........
Harara Husnah tamakama su gwaggo bintu, tace Malam kibamu waje haka ko.
Gwaggo bintu tace yihak'uri 2.
Tsaki Hasnah tayi itama, gwaggo bintu taja hannun Aysha suka fita.
Yanzuma ran Aysha ya sosu sosai, Dan takula wad'annan basuda kirki.

Har yanzun samarinnan nata hirarsu, 'yan matanma sunkoma inda suke, Dan haka surutu yak'aru sosai a falon.
Harsun Aysha suka nufi d'ayan 6angaren basu saniba, sunkusa shigewane suka tsinkayi muryar 'yar k'aramar yarinyar tana fad'in maman yara Ammah bata nan, taje Jigawa tun jiya, yanzu daddy da Aunty suka tafi d'akkota a airport.
Ayya Noor d'in Aunty ngd, ALLAH yadawo dasu lfy.
Daga nan gwaggo bintu suka fice, 6angarensu Na 'yan aiki suka koma, suka tarar Har yanzu su iya hama Na kallon film abinsu.
Sulalewa Aysha tayi takoma d'akinsu.
Babu dad'ewa gwaggo bintu tashigo itama, takalli Aysha tace idan barci kikeji tashi naraki wajen kwananki, Dan tare zaku ringa kwana da Bishirah.
To gwaggo, Aysha tafad'a a sanyaye.

Bayan gwaggo bintu taraka Aysha d'akin Bishirah tabarosu.
Cikeda fara'a Bishirah takalli Aysha, tace zoki kwanta mana, ko bak'yajin barcine?.
Guntun murmushi Aysha tayi, tazo bakin katifar ta zauna a d'arare.
Bishirah tace yasunanki?.
Aysha!.
Aysha tafad'a atak'aice.
Sunanki mai dad'i cewar Bishirah tana dariya, tace nikuma sunana Bishirah, iya hama ce Mamana. Kema aiki aka kawoki ko?.
Kallonta Aysha tayi, ahankali ta girgiza mata kai alamar a'a, saidai k'asan ranta tana mamakin shegen surutun bishirah.
Bishirah tayi murmushi, tashi tayi daga kwanciyar datayi, tadafa kafad'ar Aysha, cikin murya kasa-kasa tace nasan son kud'imsu iya bazai bari abarkiba, kema cikinmu zaki koma.
Gaban Aysha yafad'a, tayi shiru tanabin Bishirah da kallo.
Bishirah tayi 'yar dariya takoma ta kwanta, tana fad'in ki kwanta, saboda tunda asuba zamu tashi.
Aysha da mamakin surutun Bishirah yacikata, tazame ahankali ta kwanta, harta lumshe idonta saikuma tabud'esu akan Bishirah, muryarta a sanyaye tace Dan ALLAH kibani labarin gidannan da abinda yak'usa.
Nakasa fahimtar komai, musamman yawan Matan gidan da yaransu, harma da mabanbantan halayensu.
Dariya sosai Bishirah tayi, cikin dariya tace aii bazaki gane komaiba Aysha agidanan saida bayani, wannan shine zaisa kizauna dakowa lfy, kisan halin kowa da yanda zaki zauna dashi.
Tagyara kwanciyarta zuwa rigingine.

Bayan takalli Aysha tace, "kibini bashi wata rana zan fad'amiki, kamar yanda Nima iya tafad'amin.
Cikin rashin jin dad'i Aysha tace, " miyasa ba yanzuba?.
Saboda bamuda lokaci isashshe, gobe yaran gidan sunada makaranta, Dan haka k'arfe 4 Na asuba za'a tashemu, mukwanta Dan musami isashshen barci, namiki alk'awarin ranar weekend zanbaki tarihin gidan *_Alhaji ABDALLAH JIGAWA._*
Gyad'a kai kawai Aysha tayi, amma taso tasan komai tun ayaud'in, tayi addu'ar barci tagyara kwanciyarta, sadai ganin bishirah batayi addu'arba abin yabata mamaki, bata mata maganaba talumshe idonta, saboda gajiyar hanya darashin isashshen barci nafargabar baringida akwan biyun baya, yasaka barcin saurin d'aukarta yanzun..........πŸ–Š





Fan's kubini bashi a page 4. Yasin nagajiπŸ˜’, kamarma nadaina buk d'in, dannaga kamar baya muku dad'i🀨??.
Comments d'inku shine alamun nuna jin dad'inkufaπŸ€₯.
zan tsaya anan harsai naga comments naku ehe😏.





*I love you my sweet fan's*😍
[8/7, 7:36 AM] Aisha Galadima: *_Typing_*πŸ“²



🀰
*_CIKI DA GASKIYA.......!!_*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_



*_Bilyn Abdul ceπŸ€™πŸ»_*


*_NIKA'DAI WRITER ASSO......._*😜


*Sadaukarwa*
_My sweet dady_
(ALLAH ya gafarta maka)🀲🏻



*_part 1_*
(littafi na d'aya)πŸ“•


0⃣4⃣


Kamar yanda Bishirah tafad'a kuwa hakance ta kasance, k'arfe 4am iya tazo ta tada bishirah, amma banda Aysha daketa barcinta.
Aysha bata farkaba saida wasu masallatan suka fara kabbara sallahma, ahanzarce ta tashi tana ambatar addu'ar tashi daga barci, kallonta takai gefenta inda bishirah take kwance, amma saitaga wayam, tunowa da firarsu ta daren jiya tayi, tagirgiza kai cikin takaicin rashin 'yanci da talaka ke fuskanta ak'asarnan, barcinma bazakayi isashsheba, saida tsayayyen lokacin tashi domin hidimtawa wasu, ganin tunani zaisata makara sallah yasata mik'ewa, bata 6ata lokaciba tafad'a toilet d'in dake d'akin ta d'auro alwala.
Bayan tagabar da sallarta tayi azkar a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login