Showing 27001 words to 30000 words out of 32189 words
Chapter 10 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 3 Complete Hausa Novel
Hayatuddeen ma dake laɓe duk yaji komai, haka ya dinga tsalle da rawan murna, har yanaji ajikinsa cewa shikenan ya gama mallakan Zarah, Insha Allah Zarah tasa ce. Haka su Saifuddeen suka ƙirasa suka sanar masa komai da Baban Zarah'n yace.
Yayi na'am da hakan shima, saboda yasan hakan al'khairi ne agaresu, domin shima bayaso ya ɗauko maganan aure batare daya fara aiki ba, so yake shima ya tsaya akan kafafunsa, kaman yanda Hammansa ya jajirce wajen samarwa kansa dukiya ta halak, haka shima yake fata, bayason ya dogara da kowa da kansa yakeson tsayawa akan ƙafafunsa, duk da yasan cewa shiɗin me gata ne gaba da baya, amma hakan bazai sa ya kashe zuciyarsa ba, amatsayinsa na Namiji dole ne agaresa ya nemi na kansa.
Alhamdulillahi yau tsawon sati guda kenan da nemawa Hayatuddeen izinin fara zuwa zance gidansu zarah, kuma ayaune jumma'a yakeson zuwa gidan su Zarah'n. Yau gaba ɗaya abokan nasa suna nan cike agidan su, anan falon Ummi suka baje sai ciye ciye suke, sun girma amma sam wani lokaci halin nasu na yarinta na nan, yanzu ma Zaleeha ne tayi musu farfesun kaji suke ci, sai zuba santi suke, wasu daga cikinsu kuwa tsokanan Hayatudeen suke, acewarsu waidan zai fara zuwa zance yau shiyasa gaba ɗaya yakasa koda zamane, abinci ma ya kasa ci na kirki.
Khamis ne ya dubesa, cikin salon tsokana yace. "Hayatuddeen ango." Murmushi Hayatuddeen ɗin yayi tare da cewa. "Maganarka haka take soon insha Allah". Dariya sukayi dukansu, Imran ne yace.
"Nima dai Insha Allah zan biyo bayanka Hayatuddeen, dan wallahi nima inason aure".
Khamis ne yace.
"Kuji Imran fa, to waye bayason aure? ai kasha kuruminka wata ƙila ma ni na riga Hayatuddeen aure, dan dama ni suke jira".
Dariya sukayi dukansu, Zakariyya dake tauna tsokan kaza abakinsa ne yace.
"Dukan ku kallon ku nake dan duk saina rigaku aure, nima ba zama zanyi ba, dole zan faɗawa Baba Malam cewa aje anemamin aure". Dariya Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Lalle ma guys ɗinnan wato duk kishi kuke dani, dan kawai kunji anbani babe shikenan sai kuka tashi hankalinku, kai Zakariyya kana maganan aure bayan ko budurwa baka dashi." Murmushi Zakariyya yayi tare da shafa tarin sumar kanshi, cikin jin kai yace. "Kuna wasa dani guys ɗinnan, tun yaushe kuma na samu matar aure, ko kunason cemin kun manta da Zaytoon ne?" Idanu Hayatuddeen yaɗan zaro cikin mamaki yace.
"Wai kana nufi Zaytoon beauty kakeso, ƴar fada ce fa".
Dariya sosai Zakariyya yayi tare da cewa.
"Am so what dan ita ƴar sarki ce, nidai inasonta kuma itama tana sona kuma wallahi Insha Allah Saina aureta, nasan Baba Malam zai shigemini gaba, kuma kasan age mate ɗin Zarah'n ka ne, dan itama yanzu take shekaranta na kusa dana ƙarshe a secondary school, ni dai kam zama corper yayimin amfani a rayuwata dan yacillani zuwa school me daraja, har na gano gwanata." Dariya sukayi dukansu, Zaleeha dake jinsu itama dariya tayi, dan tajima da sanin labarin Zaytoon awajen Zakariyya, kasancewar baya ɓoye mata komai nasa, kafun yayi komai saiya faɗa mata.
Hira sukayi sosai. Haka dai yamma nayi suka watse, Inda ya rage saura Zakariyya shi kaɗai, dan shine zai raka Hayatuddeen ɗin wajen Zarah.
Da Misalin ƙarfe huɗu na yamma kuwa suka nufi gidan su Zarah'n, bayan kowannensu yasha kwalliya cikin tsadaddiyar shadda me kyau.
Koda suka isa gidan su Zarah'n, har cikin falon Babanta akayi musu iso, saida aka kawo musu kayan taɓawa kafun Zarah'n ta samu isowa, tayi kyau sosai abunta cikin shigar riga da zani na atamfar dake jikinta, inda ta yane jikinta da mayafi me kyau, masha Allah tayi kyau sosai, haka Hayatuddeen ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta.
Aladabce ta gaishesu, Zakariyya ya amsa mata fuska asake, idanu ya kashewa Hayatuddeen alaman zaɓin nasa yayi sosai, sannan ya tashi ya basu waje dansuyi zancen su cikin salama. Ganin Zakariyya ya fita ne yasa Hayatuddeen ci gaba da kallon Zarah'n yana sakin murmushi. Jin shirune yasa Zarah taɗan ɗago kai ta saci kallonsa, ganin ita yake kallo yasa ta kawar da kanta gefe tana murmushi. Shiɗin ma murmushin yayi, cikin salon jan hankalinta yace.
"Sannunki da zuwa Amaryata".
ɗago kai tayi taɗan kallesa da mamaki, dan bata tsammaci tun daga yanzu zai ƙirata da sunan amarya ba.
Ganin ta kalleshi ne yasa cikin ƙwarin guiwa yace. "Yess ke amaryata ce, ko kina musu da hakanne ƴan mata, sarauniyar murguɗa baki".
Dariya ne yazo mata amma saitayi murmushi, cikin ranta wani irin daɗi takeji, dan tabbas ta kamu da soyayyan Hayatuddeen ɗin, dan bakaɗan ba yake burgeta, musamman idan yana juya idanunsa like Hamma Saif, abun yana mata kyau sosai. Ganin yanda take ta rurrufe fuskane yasa Hayatuddeen soma yi mata hira, wani lokaci tayi murmushi wani lokacin kuma maganan nata baya wuce.
"Eh ko a'a". ahaka dai sukayi hiran ƙarfe 5 dai-dai ya mata sallama ya tafi, koda yazo tafiya ledan da Ummi ta basa wanda yake cike da kayan shafa ya bata, ƙin amsa tayi kwata kwata, hakanne yasa ya ajiye mata anan cikin falon ya tafi.
Ko acikin mota hiran Zarah'n sukayi shida Zakariyya, ahaka har suka isa gida Hayatuddeen yanata zumuɗi kamar ance masa gibene auren...!
By
*GARKUWAR FULANI*
Littafina na kuɗine biya ɗarinki uku kacal ki karanta ba tare da haƙƙin kowa a kankiba turo katin mtn na ɗari uku ta wannan layin 09097853276.
Koda suka ƙarasa gida kuwa, nan cikin falo suka zauna, tare da soma fara bawa Ummi labarin irin karramawan da akayi musu agidan su Zarah'n, sosai Ummi taji daɗi dan taji ajikinta cewa tayi sa'an surukai na kwarai, saidai fatan Allah ya nuna mana lokacin biki.
Haka dai suka ɗan taɓa hiransu a falon Ummin, kafun daga bisani Zakariyya ya tashi ya tafi, inda Hayatuddeen ya rakasa har waje, saida ya shiga motarsa sannan ya dawo gida.
Tofa haka rayuwa ta kasance, tun daga wannan ranan sai ya zamana duk ƙarshen sati Hayatuddeen yakanje zance gidan su Zarah, Masha Allah kuma dan yasamu karɓuwa sosai awajenta, haka ma iyayenta, tun bata sakewa dashi har ya zamana ayanzu sun zama tamkar wasu abokai saboda shaƙuwa.
Bayan wata ɗaya da bashi zarah ne ya soma service ɗinsa.
Sannu ahankali kuma yake tafiyar da service ɗin nasa yanda ya kamata, dan dukansu acikin Gombe suke service ɗinsu, Khamis da Imran ne kawai aka turasu kudu, amma suma suna ɗan leƙowa gida time to time.
Haka dai rayuwa ta miƙa, kwanaki da watanni na wucewa, yayinda abubuwa da yawa na faruwa, rayuwa tayiwa kowa daɗi.
***
BAYAN SHEKARU UKU. Alhamdulillahi rayuwa ta cigaba da tafiyawa familyn cikin kwanciyar hankali da salama, abubuwan daɗi suna ta faruwa.
Ta ɓangaren Saifuddeen rayuwa ta miƙa masa sosai, budi da alkhairi suna ta shigo masa, ya sake haɓaka yazama babban me arziki da rufin asirin Allah ya tabbata NAKASA BA KASAWA BACE.
Inda acikin shekarun da suka wuce ɗinne, Zaleeha ta koma taci gaba da aikinta.
Ta kuma sake samun ciki ta haifi ɗanta na Miji, wanda yaci sunan Aleeyu, inda akayiwa Baffa Ali takwara, ana kiranshi Haydar.
Ranar da Haydar ya cika shekara biyu ta kuma haifi ƙanwarsa, Wacce Saifudddeen ya yasa mata suna Aysha, ana kiranta Aish itama yanzu shekaranta ɗaya cib.
Yanzu yaran Zaleeha biyar Khareem Khasim Khausar Haydar autan Aish.
Bayan Zaleehan ta haihu kusan da shekara ɗaya ne Ameena ma ta haifo ƴarta mace me kama da ita sak,
Yayinda yanzu yaran Ameena uku Adeel Abbi Rahma.
farincikin da familyn sukayi nasamun ƙaruwa ba ɗan kaɗan bane.
Ɓangaren su Khareem da Ƙaseem Da Khausar Haydar kuwa sun ƙara girma sosai, yayinda asalin kyawunsu ke ƙara bayyana, zuwa yanzu dukansu babu wanda ba a sakashi a makaranta ba, Khausar kuwa kullum ƙara girma take, ga wani irin fitinannen kyaun da take tasowa dashi, kowa ya ganta saidai kaji yana cewa.
"Masha Allah." dan yarinyace me shiga rai, gata da yawan fara'a. Adeel ma ya sake girma abunsa, still kuma har yanzu komai nasa Amminsa ne, Zaleeha ta zama kamar itace ta haifesa, dan komai nasa yana wajenta, akoda yaushe kuma ko unguwa zataje matuƙar basu da school to yana naniƙe da ita.
Abbi ma da Rahma suma yawanci sashin Zaleeha suke,
ba abun dake ƙara sanya su jin daɗi kaman yanda kan ƴaƴan nasu suke ahaɗe, basa taɓa kyarar juna, kowani yaro yana son ɗan uwansa. Akuma cikin shekarun da suka wuce ɗinne akayi bikin Zakariyya da amaryarsa ƴar Sarki wato Zaytoon, wanda suke ƙira da Beauty, saboda kyawunta, Zaytoon yarinyace me hankali da nutsuwa, ga kuma iya girmama nagaba da ita.
Zuwa yanzu Zakariyya da Hayatuddeen harma dasu Khamis sun tsaya akan ƙafafunsu, dan kuwa Zakariyya baiyi aure bama saida ya tabbatar da ya zama cikakken lowyer ya kama office ɗinsa na nusamman, inda koda ya tashi Aure wanda tare akayi dana Ya Habu Yaya Ahmad ne ya saya musu wasu haɗaɗɗen gida anan cikin G.R.A ɗin, basu kuma da wani nisa da gidan Baba Malam, gidajene me kyaun gaske.
Hayatudeen ma dai buri ya cika dan yanzu haka yana aiki a babban branch ɗin U.B.A Bank, wanda duk wata yake ɗiban 300k amatsayin Salary'nsa, Alhamdulillahi dan yanajin daɗin rayuwarsa, dan ba a iya aikin bankin ya tsaya ba, Hamma Saif ya ware masa dukiyarsa wanda yake na gadonsa ne, bai karɓa ba saidai yace aci gaba da juya musu kaman yanda akeyi adacan baya.
Soyayya kuwa shida Zarah sai abun da yayi gaba yayinda ita kuwa har ta fara karatu a F,C,E Zaytoon kuma na G.S.U.
Sosai Hayatuddeen ke rawan ƙafa wa bikin dan kuwa yanzu har ansaka ranan biki, ankai lefe anyi komai, ko awajen lefe baƙaramin bajinta yayi ba, dan setin akwatuna 16 yayi mata, kowanne shaƙe da kaya masu kyau da tsada, abun saidai ace masha Allah.
Khamis ma ya zama doctor yana aiki awani babban privet hospitall wanda yake mallakin Babansa ne, sai su Imran, Sulaiman, Isma'il, suma kowannensu ya kama aikinsa haiƙan, masu aikin gwamnati nayi haka ma waƴanda suka faɗa kasuwa sunayi, Abun dai saidai ace masha Allah kuma duk sunyi aure Hayatuddeen ne kaɗai ya rage.
Yau ya rage bikin Hayatuddeen saura sati ɗaya rak, inda gaba ɗaya familyɗin suke ta hidima da kuma shirye shiryen biki, sunyi anko yafi kala shida, kowa ji yake da auren na Hayatuddeen, Saifuddeen da kansa ya biyawa Hayatuddeen ɗin sadaki naira 200k, inda kuma yasa aka sake gyaran gidan nasu, tuni dama shi ya rushe ɓangarensa ya maidashi gidan sama inda tura karshine a sama,
Adeel da Khareem Khasim Haydar da Abbi kuwa ya bar musu sashinsa na da ɗin dan yace yafi son duk motsin yaransa a kunnensa, yaran matan kuwa ko wacce tana tare da uwarta duk dama duk sunfi zama a sashin Ummee.
Kasancewar asama nan cikin sashin Ummi inda su Raleeya suka tashi, nan Hayatuddeen zai zauna da Zahrah'n sa, hakan yasa aka sake ƙawata wajen, aka sabunta komai na wajen ya zama sabo dal, ranan da akazo akayiwa Zarah'n jere kuwa ba ƙaramin kyau sashin ya ƙara ba, dan sosai iyayenta suka kashe mata kuɗi wajen saya mata tsadaddun furnitures da kuma kayan kitchine, kowa yaga jeren kuwa sai ya yaba.
Yau take laraba inda za a gudanar da haɗaɗɗiyan Kamu, da yamma kuwa da misalin ƙarfe huɗu su Zaleeha suka tafi wajen Kamu, bayan sun tsantsara adonsu me kyau da burgewa, Zaleeha sai sake murjewa take tana zama wata haɗaɗɗiyar mace da ita, sam yanayin girma ko wani manyanta bai bayyana ajikinta ba, haka zalika ko mace ce ƴar uwarta ta kalleta saita kuma dan tasan Zaleeha macece iya mace, kyau, diri, sura, duk ta haɗa, hakanne yasa ko da yaushe Saifuddeen yake mutowa akanta, domin har yanzu bata sanja ba, tana nan a Zaleehanta nada, me kyawun jiki dana fuska, uwa uba zaƙi kamar zuma.
Gurin kamu fa yayi guri, an kawata ko ina dake wajen da haɗaɗɗen decoration, pink nd sky, wato kalan kayan ango da Amarya kenan, wanda suka sha kyau har suka gaji, kallo ɗaya zaka musu kaga zallan dacewarsu da juna, tabbas hayatuddeen yayi dacen mace, dan kowa yasan Zarah yarinyace me hankali, da kuma sanyin rai, baruwanta da wasu ƴan ƙananun fitina.
Kamu yayi yanda akeso, inda su Zaleeha sukayi musu ɓarin kuɗi wajen liƙi, Raleeya ma ta taka rawar gani sosai, duk da cewa itama yanzu tana da ciki, wanda dukansa bai wuce 5 month ba, Ahmad kuwa ji yake da cikin sosai, shiyasa ma duk inda zataje yan liƙe da ita, wai bayason wani abu ya sameta.
Adda Rahama ma tazo wajen kamu'n, inda ta nunawa ɗan autan nasu gata sosai, haka dai aka watse a kamu zuciyar kowa cike da farinciki.
Washegari Alhamis kuwa mothers day akayi, wanda Zaleeha ne da kanta ta shiryawa su Ummi, da kuma mahaifiyar Zahrah da sauran dangi, abun kuwa ya ƙawatar sosai, anci ansha sannan angaggaisa da juna, abun dai yayi matuƙa, har akatashi zuciyar iyayen amarya da ango fari tas.
Ranan Jumma'ane da yamma aka gudanar da haɗaɗiyar Walima, wanda acikin familyn su Saifuddeen babu wanda bai samu halasta ba, abun saidai ace masha Allah, yanayin yanda Zaleeha tayi kyau awajen Waliman ne yasa duk inda ta gilma, matan dabasu santa ba suke binta da ido.
Raihana wanda tun ana biki saura sati ɗaya tazo, zuwa yanzu babu wani rashin fahimta atsakaninta da Zaleeha'n, hasalima shiri suke sosai da sosai.
Hannun Zaleehan ta riƙo cikin salon tsokana tace. "Matarnan kizo ki faɗamin wai miye sirrin ne, naga duk inda kikayi idanun matane ke rakaki, wato da wanka da kwalliya kike saye mana zuciyar Hamman mu ko?".
Dariya Zaleeha tayi, tare da cewa.
"Ke zan tambaya miye sirrin ai, gashi sai haihuwa kike amma kinƙi tsufa, then har yanzu banji Saminu yana maganan ƙara aure ba." Dariya suka sa dukansu, Raihana ne takai mata dukan wasa, cikin dariya tace.
"Wallahi dagani ba ƙari."
Haka dai aka tashi a walima bayan anyi wa'azi mai ratsa zuciya, koda suka koma gida yau Ameena itace da Saifuddeen, duk da yasan cewar agajiye take kuwa bai ɗaga mata ƙafa ba, saida suka morewa daren na yau kafun sukayi bacci.
Washegari asabar.
Damisalin ƙarfe sha ɗaya dai-dai dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren Hayatuddeen da kuma Zarah, wanda yasamu halartan manyan mutane da dama, dan har abokan aikin Saifuddeen saida suka halarci ga auren.
Hayatuddeen yasha kyau abunsa cikin farar getzner, gefensa kuwa amininsa kuma ɗan uwansa ne wato Zakariyya shiɗin ma dai yasha kyau abunsa, gasu Imran, Khamis, Isma'il, Sulaiman, duk suma sunsha adonsu, kowannensu yana cike da farincikin auren abokin nasu.
Koda yamma tayi ƙarfe huɗu akaje aka ɗaukowa Hayatuddeen matarsa, wanda Saifuddeen da kansa yaje ɗaukowa autan Ummenshi matarsa, acikin motarsa kuwa akasaka Zarah'n. Direct gidan Ummi aka kawota, inda Ummi da kuma su aunty Mina Goggo Dada, Aunty Kubra, Umman Ishaq, sukayiwa amarya da ƴan uwanta tarba me kyau.
Karfe 8 na dare dai-dai jama'ar gidan suka fara shirin zuwa wajen diner, wanda za'a gudanar a Medugu Hall, musamman