Showing 9001 words to 12000 words out of 32189 words
Chapter 4 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 3 Complete Hausa Novel
cewa take Zaleeha tayi hoton cikin ta turo mata shike hanawa yace ta bari sai sun dawo, Ameena kuwa yanzu ce mishi take itafa ta tayi kewarsa daga nan yaita mata tsiya yace ta shirya duk randa ya dawo zai bata ajiyan ƙanwar Adeel.
Yauma shirya kansu sukayi cikin kayan sanyi, suna riƙe da hannun juna haka suka fito daga cikin hotel ɗin.
Wani Garden sukaje suka ɗan shaƙata, tare dayin hotuna masu kyau wani a tsaye wasu a zaune wasuma suna kunce cikin korayen shuke-shuken wurin wani a bakin ruwa, kuma duk hoton da zasuyi sosai cikin Zaleeha ke fitowa tim a gabanta, wani hoton da sukayi.
yana zaune ya mike ƙafa ita kuma tana konce tayi pillow da cinyoyinshi, hannunshi ɗaya na kan cikinta ɗaya na kan goshinta, yana murmushi tana murmushi sosai sukayi masifar kyau a hoton sun daɗe sosai a ciki kafin suka fito suka nufi masaukinsu.
Ahanyarsu ta dawowa ne suka biyo kusa da asibitin da Zaleehan ke awu, anan Saifuddeen ke tuna mata cewa.
"Mu dear Gobe nefa dawowanki awu".
Kai ta gyaɗa masa alaman ta sani, murmushi yayi tare da kamo kafaɗunta, cikin kulawa yace.
"Karki damu Insha Allah gobe zan tashi da wuri saina rakoki kinji, duk dama dai kinƙi amiki scanning, bansan daliliba kuma".
Ɗan shagwaɓe fuska tayi akasalance tace.
"To Hamma Saif bagani ba lafiyata ƙalau, scanning ɗin me zanyi, duk abinda zamu haifa zamu ganshi randa ya fito duniya, naga ɗokinka yawane dashi".
Hannunshin yasa ya ɗan shafi cikin tare da cewa.
"Ai basai baki da lafiya za amiki scanning ba, yanzu fa cikinki yayi girma kusan 7 month ake nema, bakya ganin yanda yayi girma da yawa, maybe ma ƴan huɗu zaki haifamin ƴar al'barka". Idanunta taɗan zazzaro, sai kuma ta saki murmushi tare da lafewa ajikinsa.
Shi kuma murmushi yayi a ransa yace.
"Tun yaushema akayi scaninng ɗin, duk dai bawai nayi imani da abinda sukace ba, amman bazan ce miki komaiba zanyi ta miki addu'a Allah ya sauke min ke lfy".
Ahaka suka koma gida, bayan ya saya mata kayan ciye ciye.
Daren yau ma dai soyayyarsu suka sha, yau abun na Saifuddeen harda kukan daɗi, dan kullum sabuwa Zaleehan ke zame masa kodan dama ɗan-ɗanon mai ciki na dabanne, shiyasa akullum yake zaucewa akanta.
Washe gari kuwa kaman yanda ya faɗa, yau da wuri suka tashi, shida kansa ya shiryata dan zuwa yanzu bakomai take iya yi da kanta ba, saboda yanda cikinta yayi girma, idan bakasan watannin cikin ba zaka iya cewa ya cika wata tara.
Har cikin asibitin ya kaita aka mata awu da duk wasu gwaje gwajen da suka dace, suna cikin asibitin kuwa aka soma yi musu dusan dusan ƙanƙara, yanda ta matsa masa cewar tanajin yunwa ne yasa dole suka bar cikin asibitin,
wani restaurant dake kusa da asibitin suka nufa, kafun ma su ƙarasa tuni dusan ƙanƙara ya sauƙa ajikinsu suna shiga cikin. Kasibeyaz Florya Restaurant.
Abinci me rai da lafiya sukaci acikin restaurant ɗin kana suka sha zazzafan tea mgnin sanyi, yau basu wani ɓata lokaci awaje ba suka koma masauƙinsu.
bayan sunyi sallan Ishane Saifuddeen ya ƙira Ummi vedio call, inda ya saita vedion har Zaleeha dake gefensa ma tana hango Ummin, hira sukayi sosai kaman suna gida, dan har Hayatuddeen saida yazo sukayi hira.
Bayan sunyi sallama ne, Saifuddeen din yayi musu connecting game suka soma yi, ahaka bacci ya ɗaukesu dukansu.
Wayewan garin yau kuwa basu fita ko ina ba agida suka zauna, Zaleeha kuwa sai faman zuba masa raki take, tana masa mitar cewa cikin na mata nauyi, shi kam tarairayanta kawai yake. Haka dai suka shafe kwana huɗu basu fita wani yawo me tsawo ba sabida sosai cikin Zaleeha ya girma, aranan da ya rage saura kwana uku su koma Nigeria ne, suka shiga wani babban super market, dake kan Cobblestone street instanbul.
Sayayya sukayi sosai harda na ban mamaki, dan Zaleeha ita kanta saida tasha mamakin yanda yayi ɓarin dukia wajen sayan kayan babies, har saida ta kasa haƙuri cikin gajiya tace.
"Hamma Saif kayannan sunyi yawa, me zamuyi dashi? sai kace wanda zan haifi ƴaƴa dozin dozin, gaskiya arage sunyi yawa over". Batare da ya yarda sun rage kayan babies ɗinba yace.
"Kikasani ko dozin-dozin zaki haifa mana". Hararan wasa tayi masa tare da cewa.
"Chab ai kuwa ni ba ingine bane."
Dariya yayi, sannan ya ci gaba da ɗaukan abun da yake so, tare da cewa.
"Ni kam ingine yara dozin-dozin na zuba miki, kin san dai NAKASA BA KASAWA BACE". dariya tayi tare da cewa.
"Na yarda Nooryart na sani wlh NAKASA Ba KASAWA BACE, ni kam ai ni naga zahiri tunda a nakashen aka amshe budurcin harda sumar dani sau biyu, ga ɗan karen naci".
Signal ya mata da girarshi ɗaya kana ya lakaci hancinta sannan sukaci gaba da sayayya,
kaya suka saya niƙi niƙi.
Bayan sun gama sayan duk abinda suke sone Hamma Saif ɗin ya ƙira ɗaya daga cikin ma aikatan hotel ɗin wanda suke da motocin taxi, bajimawa kuwa yazo ya kwashesu da kayansu ya maidasu masauƙin su.
Gombe Nigeria. Hayatuddeen ne keta faman shirya kansa, cikin riga da wandon tsadaddiyar shadda, yayi kyau matuƙa gashi ya murza hula me kyau akansa, kallon kansa yayi amadubi, murmushi ya sake dan ganin yanda yayi kyau.
Ɗan makullin motar dake ɗaya daga cikin motocin Hamma Saif wanda ayanzu shike amfani da ita ya ɗauka, afalo ya samu Ummi da Raleeya, ganin yanda yayi kyau yasa Ummi cewa. "Masha Allah Autana kaga yanda kayi kyau kuwa, sai ina haka?". Wani irin sanyi yaji aransa, sakamakon jin Umminsa ta yabesa. Kansa yaɗan sosa, cikin ƙasa da murya yace. "Ummi gidan Baba Bello fa zanje, na kai masa gaisuwa amadadin Hammana kinsan yau jumma'a".
Murmushi Ummi tayi cike da jin daɗi tace.
"Masha Allah to adawo lafiya, hakan yana da kyau sosai ai, maza kace musu ina gaishesu." Cikin jin dadi yace. "Insha Allah Ummina zan faɗa musu."
Kallon Raleeya yayi cikin tsokana yace.
"Adda Raleey how far naga baki taya ba, kodai kina baƙinciki da kyawun da nayi ne, dan kinga nafi Ya Ahmad kyau". Hararan wasa Raleeya ta watsa masa, kwafa tayi tare da cewa.
"Oho kadai ɗanyi kyau kaɗan. Amman ko rabin ya Ahmad bakayi ba a kyau yaro, daga Hamma Saif sai Ya Ahmad a kyau".
Murmushi kawai yayi, sannan ya fice daga cikin falon.
Yana zuwa ya shiga motarsa, kai tsaye gidan Baba Bello ya nufa, aƙofar gida ya taradda Baba Bello'n, da alama fita zaiyi, bayan sun gaisane yake tambayan Baba Bello'n, ina zaije?". Nan Baba Bellon ke cemasa zaije gaishe da ƙanwarsa ne wato Maman Zarah, saboda kwana biyu bata ji daɗi ba mura ke damunta, wani sanyi yaji aransa jin cewa Baba Bellon gidansu Zarah'nsa zaije, nan take yacewa Baba Bellon ya shigo motan ya kaisa.
Hakan kuwa akayi, saidai koda sukaje gidan, bayan ya sauƙe baba Bellon, cewa yayi shima zaije ya gaishe da Maman Zarah'n, sosai kuwa Baba Bello yaji daɗin haka, saida sukasa aka musu iso, sannan suka shiga cikin gidan. Ababban falon gidan suka zauna.
Cikin nutsuwa kuwa Zarah ta shigo hannunta ɗauke da tray wanda ke ɗauke da ruwa asamansa.
Agabansu ta ajiye, cikin girmamawa ta gaishe da Kawun nata, fuska asake Baba Bello ya Amsa mata,
ganin idon Baba Bello'n yasa ta gaishe da Hayatuddeen saidai bata yarda ta kalleshi ba. Amaimakon ya amsa mata gaisuwan nata, sai ya gyara zamansa tare da cewa.
"Meyasa wayan baya shiga, always idan nakira baya tafiya, meyasa?". Ƙin amsa masa tayi, asanyaye ta juya zata bar falon, cikin ƙara jadda da mata yace.
"Badake nake magana ba, me yasa wayar bata shiga".
Ɗan ƙaramin bakinta ta ɗan tura, cikin ƙasa da murya tace.
"Sace wayan akayi." Batajira ya sake cewa komai ba ta juya cikin sauri tabar falon. Dai-dai lokacin kuwa Mamanta ta fito, amatuƙar ladabce ya gaishe da matar, wanda take da kwarjini, fuska asake kuwa ta amsa masa, tana me yaba haibansa, dan kallo ɗaya zaka masa kasan cewa yaro ne, amma kuma akwai cikar haiba da hankali, ga girmama na gaba ga nitsuwar. Da bata gane aro nitsuwar yayiba,
Shi kuwa Hayatuddeen sosai ya danne rawan kanshi ya nitsu a gaban surkarsa a gaba in Allah ya nufa.
Bayan ya gaishetane ya tashi ya fita, bayan sunyi da Baba Bello cewar zai jirasa amota.
Turkey Instanbul. Yau ya rage saura kwana ɗaya rak su koma Nigeria, hakan ne yasa suka sake fita zaga gari, wani park me kyau sukaje inda suka yi hotuna masu kyau, take kuwa ta watsasu ashafinta na IG da kuma Whatsapp status ɗinta. Kowa ya gani kuwa sai ya mata comment, dan sunyi kyau matuƙa. Bayan sun dawo gidane Saifuddeen ya maƙale mata kaman ƙaramin yaro, yau sosai ya jigata ta, har saida tayi laushi kafun ya barta, ihu da sambatu kuwa ta shashu, har mamakinsa take dan abun nasa kullum gaba gaba yake, matuƙar zaiyi sex da ita to sai yayi ihu da kukan daɗi, gashi ko da yaushe jarabansa ƙaruwa take.
Washegari da safe ƙarfe 8 dai-dai jirginsu ya tashi daga ƙasar ta Turkey zuwa Nigeria sosai taji kewa da begen ƙasar hakanan taji kamar tace su koma su ƙara wata biyu a nan sabida zamansu a garin wani sashine na daɗin tarihin rayuwarsu.
kafun su tashine kuma sukayi waya dasu Ummi, inda suka ƙara musu 1 hour akan lokacin da zasu iso, dan so suke su musu surprise.
Ko acikin jirgi liƙe suke da juna, gwanin ban sha'awa.
Sukansu basu san wani lokaci suka ɗauka suna keta hazo ba, suna cikin mood me daɗi jirginsu ya sauƙa acikin garin Lagos Nigeria, lokacin da suka fito daga cikin jirgin, saida suka sauƙe zazzafan ajiyar zuciya, tabbas sunyi kewar ƙasarsu ga wani ɗumi da sukaji ya ratsosu saɓanin sanyin da suka baro, kasancewar sunyi booking flight ɗin da zai kaisu Gombe, yasa basu wani jima a airport ɗin ba jirginsu ya ɗaga zusa Gombe.
Lokacin da jirginsu ya sauƙa acikin garin Gombe wani irin dadi sukaji acikin ransu, tabbas kowa yabar gida gida ya barshi, komai rashin dadin naka naka ne, lallai ko ina kaje da ka dawo tushenka, zakaji wani irin sanyi da salama acikin ranka wannan shine tunanin da sukeyi a lokacin da suke taka steps ɗin jirgin suna sauƙa.
Taxi suka nema, Saifuddeen ne ya gaya masa unguwar da zai kaisu sannan suka kama hanya.
Acan gidansu Saifuddeen din kuwa, yau zuciyoyinsu cike suke da farincikin dawowan su Saifuddeen ɗin, dan hakane ma Ameena ta kashe zuwa aikinta na yau, da kanta tashiga kitchine, ta haɗa musu abinci me rai da lafiya, bayan tagama ko ta caɓa ado, anna falon Ummi suka zauna dukansu hadda su Adda Rahama, jira suke lokacin dasu Saifuddeen ɗin zasu iso suje su tarosu.
Can waje kuwa adai-dai ƙofar gidan nasu kuwa me taxi ɗin ya sauƙesu. Sule driver wanda dawowansa daga masallaci kenan, ganin Ogansa tsaye akan ƙafafunsa yasha mamaki ƙwarai ya kuma yi murna sosai, harda ƙwalla saida yayi.
Shiya shiga kwasna kayan su Saifuddeen yana kaiwa cikin gida can side ɗinsu kamar yadda ubangidashin ya umarce sa.
Shikuwa Saifuddeen yana sarƙe da hannun Zaleeha suka nufi part ɗin Ummi sabida yasan in Ummi taga ana shiga da kayansu zata fito, shiko yafi son ya shiga har ciki ya samesu yaga irin farin cikin da zasuyi.
Abakin ƙofar shiga falon suka tsaya, Zaleeha ne tayi masa alaman cewar ya fara shiga, hakan kuwa akayi ahankali ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga da wani irin taku mai cike da haiba tafiyarsa irin ta RK ta fito ras bakinsa ɗauke da sallama ya shiga.
Jin sallaman sane yasa dukaninsu suka jujjuyo da sauri.
Ganinsa tsaye akan ƙafafunsa yana sakar musu murmushi Yasa su Raleeya da Hayatuddeen fasa wani uban ihu, da wani irin gudu sukaje suka faɗa jikinsa, Ummi da Adda Rahama da kuma Ameena da Ahmad kuwa cikin tsananin farin ciki suka mimmiƙe tsaye cike da zallan mamaki da al'ajabi da kaɗuwa, sukace.
"Lahh hauwalaƙuwata illabih, Alhamdulillah".
sosai suka shiga shock ɗinn ganinsa, wani irin matsanancin farinciki ya cika zuciyarsu, har hakan yajawo taruwan ƙwalla acikin idanunsu. Cikin matsanancin farinciki Ummi ta durƙushe a wurin ta fuskanci gabas sujjadar godiya tayi wa mahaliccinmu ,
kana ta miƙe da jiki na rawa tace. "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Babana kaine kuwa kai nake gani tsaye akan ƙafafunka? Alhamdulillah ko yau ko yau na koma ga mahaliccina burina da fatana da addu'a ta sun ciki, Allah na gode maka yau bani da sauran damuwa a duniya a kan wannan ɗan nawa bawanta mai rauni".
Shi kuwa Saifuddeen da sauri ya ɗan janye su Raleeya daga jikinsa yayi cikin matsanancin kewan Ummin nasa ya ƙaraso cikin falon haɗasu yayi dukansu biyu, wato Ummi da Adda Rahama da ta zama kamar an dasata ya rungumesu ƙam, cikin farinciki yace. "Nine Ummi Saifuddeen dinki ne, Allah yayi ikonsa na warke tun bamu jima da xuwa Instanbul ba, na ɓoye muku ne saboda ina matuƙar so nayi surprising ɗinku sabida ina son ganin wannan farin cikin naku da nake gani yanzu ido da ido." Murmushi Ummi tayi tare da rungumesa ƙam, wani irin tarin farinciki takeji acikin zuciyarta, sosai ranta yayi sanyi, tabbas wannan rana zata shiga cikin ranaku mafi girma na rayuwarta, yana rungume da Ummin ya kashewa Ameena idanu, wanda tun ɗazu kallonsa take tama kasa ɗauke idanunta daga kansa, saboda ba ƙaramin kyau ya ƙara ba, yayi fresh har ɗan ƙiba yayi, da'alama babu wani abun dake damunshi ga tarin farin cikin ganinsa a tsaye ji take kamar ta ture Adda Rahma ta gurbinta a jikinshi.
Zaleeha ce wanda shigowarta falon kenan, cikin sakalci da tura baki tace.
"Wayyo Allah na, dana sani da ban amince maka akan maganan surprising ɗinnan ba, tun da dai gashi kai kaɗai kawai aketa kulawa nikam kamar ba a sanni ba an mance dani". Maganar da takeyi ne yasa gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kanta.
Raleeyace ta rungume ta cikin farinciki tace. "Oyoyo my aunty, i miss you more".
Murmushi tayi itama ta rungume Raleeya, ahaka suka ƙaraso cikin falon, daga kan Ummi har zuwa Ameena saida duk ta bi ta rungumesu, sosai suka yaba da irin zallan kyawun da tayi, duk da cikinta ya ƙara girma, haka ma hips ɗinta sun sake cikowa, ta zama wata babbar mace, ta kara zama cikakkiya abun so ga ko wani namiji.
Anan falon suka zazzauna, suna ahaka kuwa su Ishaq da Mudassir da kuma Salisu dama su Wareesu suka ƙaraso domin lbrin isowarsu da Ahmad ya basu da workewanshi, baƙaramin murna suma sukayi da ganinsa ba, daɗi kam sunjisa alokacin da suka ga yana taka ƙafafunsa.
Hira sukayi sosai a falon Ummi da aminanshi sunyi farin ciki mai tarin yawa anan a take yake cewa Ishaq ya shirya nanda wata biyu shida Rashida zasu tafi India ganin likitan ido, nan duk akayi ta fatan Allah yasa shima a dace, daga nan suka cicci abin gwalamar da Ameena tai musu, sannan suka fito suka nufi cikin Garden ɗin dake bayan part ɗin Ummi dan su ɗan barshi ya gana da iyalansa saida suka fitan.
kafun shida Zaleeha kowa ya nufi sashinsa danyin wanka, ita part dinta ta wuce wanda Zahira da Ziyada da Raliya suka gyara matashi fes-fes.
Shi kuwa ƙiran Ameena yayi yace tazo ta haɗa masa ruwan wanka.
Suna shiga part ɗinsa ya jawota jikinsa ya rungumeta ƙam, anutse ya shiga kissing ɗinta tako ta ina, tare da ce mata.
"I miss You so much cingom ɗina".
biye masa tayi dan itama tayi missing ɗinsa sosai, wata uku cur batare dashi ba ji take kaman shekara uku ne, cikin tsananin jin daɗi tace.
"Miss You too ya Habibi". saida sukayi tsotse-tsotsen su sannan yayi wanka.
Afalon Ummi suka sake haɗuwa, nan cikin falon suka baje, anan sukayi ciye ciyensu.
Haka sukayi ta hira, sai da aka ƙira sallan magriba sannan kowa yaje yayi sallah.
Su Ishaq basu bar gidan ba