Showing 6001 words to 9000 words out of 32189 words
Chapter 3 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 3 Complete Hausa Novel
rafinmu nan mai daɗin".
Ya ƙarashe mgnar yana zira rigar.
har ƙasa ta sauƙo cikin jin daɗi tace.
"To Ya Habibi kayi gaba ina binka a baya".
Kai ya gyaɗa mata kana a hankali ya fara taku,
suna isa baƙin ƙofar tayi maza ta buɗe mishi ƙofar da ƙar damanshi ya fara ɗagawa da niyar yin takun fitowan,
ita kuwa tana biye dashi a baya.
Cikin mmki Ummi ta zubawa wayarta ido,
ganin ta....!
*NAKASA BA KASAWA BACE*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
Part 3. Page 1-to-5
_LITTAFINA na KUƊINE ki biya ki karanta ba tare da haƙƙin kowa a kankiba, turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan layin 09097853276 ko kuma kiyi min transfer ɗari ukun ta asusuna na 0005388578 jaiz back Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min screenshort shaidar biyanki ta dai wannan number da nakeyi chatting da ita 09097853276_
Dan Allah ku dena tura min littafina Hukuncin Allah a groups ɗin NAKASA Ba KASAWA BACE, shima na kuɗine kuma wasu basu sayaba, bawai fans ɗin Hukuncin Allah kaɗai bane suka sayi wannan littafin akwai sabbin da a ƙiyasci sunfi ɗari uku da hamsin.
In zaki sayi littafina ki tabbatar kinada App ɗin WPS office.
By
*GARKUWAR FULANI*
Da sauri Ummi ta zuwa wayar ido.
ɗut ɗut haka taji ƙiran ya yanke, da alama network ne ya katse ƙiran, fuska ɗauke da mamaki take kallon screen din wayar, aɗan bayyane tace.
"To meyasa ƙiran kuma ya katse, ko me Zaleeha ke son nunamin?". sake dialing numbern tayi amma taji baya shiga.
Zaleeha kuwa tafi take masa da hannunta, cikin matsanancin farinciki batare da sanin ƙiran da tayiwa Ummin ya katse ba tace.
"Wonderful Ummi kinga Hamma Saif ko, Ummi ya warke yafara takawa da ƙafafunsa."
Ta ƙare maganar tana me ɗaukan laptop ɗinsa, gani tayi gaba ɗaya ƙiran ya katse, tun tsawon mintuna 4 da suka wuce. Fuska taɗan kwaɓe tare da dafe kanta, cikin takaici tace.
"Wallahi Hamma Saif saika sanja laptop wannan laptop ɗin naka bata da kyau."
Tafaɗi maganan tana ɗan bubbuga laptop ɗin nasa.
Hannu yasa ya jawota tare da karɓe laptop ɗinsa, cikin yanayin mamaki yace.
"Dama me kike ƙoƙarin yi?".
Bakinta ta turo gaba, ashagwaɓe tace.
"Waifa connecting vedio call nayi, inason nunawa Ummi tafiyanka shine kuma ashe kiran ya ya katse tun kafin mu fito". Idanunsa ya ɗan zuba mata, ahankali yaja hannunta suka zauna akan gado, cikin kulawa yace.
"Nagodewa Allah ma da ƙiran ya katse, da shikenan yanzu kin ɓatamin plant, kingani ai Allah na ya kamaki." Kallonsa tayi alaman "Kamar ya?".
Kai ya jinjina tare da cewa.
"Yeah ba nacemiki banason Ummi tasan ina takawa, ba Ummi bama kowa banaso ya sani, nafison nayi surprising nasu, shiyasa nace karmu faɗa musu shine wato bakya jin mgnata kike son faɗa musu.
Nafison nayi surprising ɗin su zasufi jin farin ciki Ko bakyason haka?."
Ya ƙarishe maganar yana me ɗan shafa kanta.
Gane nufinsa yasa tayi murmushi tare da cewa. "Inaso mana, amma nasan su Ummi zasuji dadi sosai, Allah sarki Ummi nasan saitafi kowa jin daɗi".
Kallonta yayi cikin nutsuwa yace.
"Saitafi kowa kuma, kice dai saitafi kowa kuma ya fiki".
Ya ƙarishe mgnar cikin tsokana.
Ɗan hararan wasa ta jefa masa, ido cikin ido tace. "Hmmm saidai ita ɗin ne kaɗai zata fini amma ba kowa a duniya da zai fini jin daɗin samun lfyarka, kai bakasan cewa aduniya daga Ummi asonka sai ni ba, bayan Ummi babu meyi maka irin son danake ma, saidai duk sauran mutane su biyo bayana." Dariya yayi, har saida dimples ɗinsa suka lotsa, cikin son tsokanarta yace.
"Ummm ashe ana sona kuma aka gudu, aka tafi can wata duniya".
Ɗan dukan wasa ta kai masa, cikin kulawa tace. "To nasan kaine? ai da nasan kaine bazan gudu ba, kuma ai duk kaine ka jawo, da ace tun alokacin ka nunamin real face dinka, ai bazan gudu ba, zan zauna atare dakai, kuma dama ai ni ba tsananka nayi ba, kawai dai dan inada wanda nake sone mara saje kai kuma na ganka da saje kuma ka ƙara dari da kyau da girma da kwarjini da ƴar ƙiba kuma kana bisa kujerar mulki ya zanyi in ganeka"
Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
"Duk a cikin shekara ɗayan nayi waɗannan abubuwan da kika lissafi?".
Sajenshi ta shafa tare da cewa.
"Eh mana, sai dai duk sanda naga idanunka sai inga kamar na sansu". Idanunsa yaɗan juya, cikin kulawa yace. "Hahhh to ina wanda kikeso ɗin?".
Da hannunta ta nunasa alaman gaka.
Yana murmushi yajawota jikinsa ya rungumeta, tabbas yanason Zaleeha so me tsanani, yanajin ƙaunarta sosai acikin ransa, yayi imani itace macen da ta dace da rayuwarsa, itace kuma dai-dai da tsarinsa, duk da kasancewar Ameena ta shigo cikin rayuwarsa, alokacin da baya buƙata, ta kuma zauna dashi da lalurarsa, hakan shiyasa ya bata wani babban gurbi a rayuwarsa.
Amma Zaleeha itace tauraruwarsa har gaban abada.
Hira suka ɗan taɓa kaɗan, jin ana ƙiran sallan magriba ne ya sashi ɗauro alwala ya wuce masallacin.
Sultan Ahmed Masjid dake kusa da masauƙin nasu, itama Zaleehan alwala tayi sannan ta zo ta gabatar da sallah, koda ta idar bata tashi akan sallayan ba, saida tayi sallan isha, yau kam batajin zuwa restaurant cin abinci, zatace Saifuddeen ɗin ya musu order kawai, dan sosai sanyi ya shiga jikinta aƴan kwanakin nan shiasa ma batason sake fita.
Kayan jikinta ta cire, sannan ta saka wata ƴar ficikar rigar bacci, wanda da ita da babu duk ɗaya suke, tana kammala shafa fitinannen turarenta Saifuddeen ya turo ƙofar ɗakin ya shigo. Murmushi suka sakarwa juna, hannunsa ya buɗe mata babu musu kuwa taje ta shige jikinsa, cikinta yaɗan shafa, tare da yi mata alaman "Yunwa ko?".
Kai ta gyaɗa masa alaman "Eh." Waya ya bugawa masu kawo abinci hotel ɗin, inda ya gaya musu favorite ɗin da za'a kawo musu.
Ko mintuna goma ba ayi ba kuwa saiga abincin nasu ya iso.
Ɗaurata yayi akan cinyarsa, shi da kansa ya ciyar da ita, saida ya tabbatar ta ƙoshi sannan shima yaci, koda suka kammala brush sukayi sannan suka kwanta rungume da juna, da yake agajiye suke shiyasa basuyi wani abu ba, saidai Saifuddeen da jarabarsa ta kasa barinsa, dole haka saida ya mammatse ta, har saida taji breast ɗinta na mata zogi, haka sukayi bacci, bakinsa na kan nipples ɗinta.
Washegari kuwa koda sukayi sallan asuba, bacci suka sake komawa, dan ita Zaleeha yanzu kwata-kwata bata gajiya da bacci.
Basu suka tashi ba kuwa sai ƙarfe 9.
Kaman jiya da dare haka yau ma aka kawo musu break fast, bayan sunci abincin ne, Zaleeha tasa masa daru kan cewar lallai sai dai yazo suyi wanka a swimming.
Biye mata yayi suka shiga swimming pool ɗin, wanka sukayi haɗi da zazzafan romance. Sunjima acikin ruwan kafun suka fito, anan falo suka zauna inda tayi pillow da cinyansa. Wani latest film yasa musu a laptop ɗinsa suka kalla.
Suna cikin kallone bacci ya ɗauketa, akan gado ya shumfuɗeta, sannan ya ɗauki wayansa dake ta faman tsuwa, ganin sunan Ishaq na yawo akan screen ɗin wayar ya sashi amsa ƙiran da sauri.
Daga can Ishaq ya saki dariyan mugunta, cikin salon tsokana yace. "Kaga Kurma me maganan dare, wallahi kana sha'aninka, wato kasamu yar mutane kana mata sambatu ko". Dariya Saifudddeen ɗin yayi tare da ɗan shafa sumar kansa, yace "Wallahi Ishaq kai banza ne ni ba abinda nayi". Dariya Ishaq ɗin yayi, tare da cewa.
"Eh mana, dole ai kace haka, to duk dai bawannan ba ya ƙarfin jikin naka, nasan zuwa yanzu ansamu cigaba." Kai yajinjina kaman Ishaq ɗin nagabansa yace.
"Ansamu cigaba sosai ma."
Cikin jin daɗi Ishaq yace.
"Alhamdulillah abun da muke fata daso kenan, to ya Zaleeha fatan dai baka sake mata magana cikin dare ba".
Murmushi yayi tare dakai dubansa gareta, har yanzu baccinta take sha. "Meza afasa kaida kasani, saidai danaga tana ƙoƙarin min bankaɗa awajen Auntynta na faɗa mata cewar ina magana." Dariya sosai Ishaq yayi tare da cewa.
"Masha Allah ai hakan yayi."
Hira suka ɗan taɓa kaɗan da Ishaq ɗin sannan sukayi sallama, Ishaq na katse ƙiran ya tashi ya koma falo, numbern Ameena yayi dialing bugu biyu kuwa ta ɗauka.
Hira suka sha sosai da ita, sai faman faɗa masa yanda tayi missing ɗinsa take, haka dai ya biye mata saida suka kwashe minti 30 suna waya, sannan daga bisani sukayi sallama, jin zaman shiru ya ishesa ne, ya sashi ɗaukan Laptop ɗinsa ya fara gudanar da wani aiki. Haka dai awannan rana babu inda sukaje, duk agida suka wuni.
Washegari kuwa tun da sukayi break Zaleeha ta matsa masa akan cewa tanaso taɗan sake zaga gari, da yake shima yana da buƙatar hakan shiyasa baiƙi ba, dan yanaso yaɗan tattaka ƙafafunsa, yasan da haka zai ware.
Kusan shiga iri ɗaya sukayi, koda suka fita sunyi kyau gwanin ban sha'awa, kasancewar ba wani tafiya me tsawo zasuyi ba,
shiyasa basu nemi mota ba, idan suka ɗanyi tafiya me ɗan tsawo, sai ya ce ta tsaya, shida kansa yake miƙewa akan kekensa, ahankali yake ɗan taka ƙafafunsa, cikin ikon Allah kuwa sai gashi yana ɗan iyayin tafiya me tsawo, idan yayi tafiya me nisa kuwa sai itace zata biyosa da wheelchair ɗinsa, Alhamdulillah dan bayajin ƙafar nayi masa zafi.
Bayan sati uku yawanci suna fita suyi tattakin.
Kuma Alhamdulillah yanzu tafiyarshi na ɗan nisa,
Yau da yamma suka fito,
koda motarsu ta kawosu tsakiyar garin sai sukace ya koma sai sun nemishi yazo ɗauka su.
anan kan Babban titin Instanbul ɗin suketa tattaki,
suna tafiya ya ɗan kalleta a hankali yace.
"Bari in tashi in tafi har can, kinga can wurin da mutane suka ɗan tarun nan yau sai naje har can sai ki isoni da keken".
Cikin mamaki tace
"Notyart zaka iya, da nisafa".
kanshi ya jinjina mata tare da cewa.
"Karki damu in sha Allah zan iya".
Kai ta jinjina mishi.
alamar to shi kuwa miƙewa yayi a hankali ya fara taku yana tafiya a .
Ita kuwa ido ta zuba mishi da cikinta da yanzu ya cika wata biyar ya fito ras a gabanta.
ya daɗe kafin ya isa wurin da yace ɗin yana isa yaji tana mishi tafi tare da cewa.
"Alhamdulillah Nooryart am hoini".
Da sauri ta fara turo keken har ta iso gabanshi,
tana isa ya zauna tare da sauƙe ajiyan zuciya cikin fidda numfashi yace.
"Kai na ɗan gaji kam".
Sunkuyowa tayi ta ɗanyi kissing goshinsa.
tana ɗagowa kuwa taji anayi musu tafi,
sabida wasu sun lura mara lfya ne,
hannu sukayi ta bawa Saifuddeen suna mishi fatan lfy.
A haka sukaci gaba da tafiya har suka ratso, kan Buzy Turkish street.
Da sauri Zaleeha ta riƙo hannunshi tare da cewa.
"Laaa Hamma Saif kalli can suna gasa masara, muje ka saya min zanci gashesshen masara".
Da sauri ya kalli inda take nuna mishin. Tabbas ɗanyar masara wani ke gasawa a ɗan wani ƙarfe da akayi kamar tukuban gashin tsirai, matane ke ɗan tsastsaye suna saya,
ido ya lumshe mata tare da cewa.
"Muje in saya miki a cicina rumbun gwamnati".
Baki ta ɗan tura shi kuma hannunta yaja suka isa wurin.
Ganinshi bisa kekenshi ne yasa a take aka basu hanya suka isa suka saya ba tare da bin layiba, saida suka isanema sukaga ashe harda dafaffiyar gyaɗa ai kuwa shima sun saya.
Gefe suka ɗan yi inda ake saida abubuwa sauran kayan ciye ciye suka saya, shike riƙe da ledar tana biye dashi a baya.
Suna ɗan dube-duben wurinda zasu zauna su ɗan hutane kuma Zaleeha ta hango mai saida su inabi da tupa,
nan tasa masa daru kan cewa ita lallai saitaci inabi da tupan, shida kansa ya taka da ƙafafunsa inda yaje ya saya musu inabin da tuppan, har yaje sayo ya dawo vedio take masa.
Yana dawowa ya zauna tare da nuna mata saibot ɗin wani babban wurin hutawa.
Nan suka kama hanyar tafiya kaɗan sukayi sai gasu
cikin wani gurin shaƙatawa na Goztepe 60th year park, wurin mai tarihi da kyau.
Acan sukaci masaran dama duk abun ƙwalaman da suka sayo. Sunjima awajen shaƙatawan sai shawagi suke ananne kuma ya dage wajen tattaka ƙafansa, sai wajen yamma gab magriba sannan suka kira direbanshi yazo ya ɗauke su suka koma masauƙinsu, atare sukayi wanka, yayinda tundaga cikin toilet ɗin labari ya sanja salo, sosai suka sha love dinsu acikin bathroom ɗin, yauma haka ya dinga mata sambatu irin wanda bata gane me yake faɗaba, dan itama fitar da ita daga hayyacinta yake.
Sosai suka gajiyar da kansu hakanne ma ko sallan Magriba agida yayi, inda ya jasu jam'i, suna idar da sallan Isha kuwa sai bacci, sai washe gari da safe ne ya ƙira su Ummi suka gaisa, jin suna gaisawa da Ummi ne yasa Zaleeha ta karɓi wayan suka gaisa, bayan sun yi sallama da Ummin ne ta ƙira wayan Hayatuddeen saboda da da sukayi waya da Ummi basu samu daman gaisawa ba, saboda yana makaranta, koda ya ɗaga wayan kuwa hira suka sha sosai, kasancewar suna tare da Zakariyya, yasa ya bawa Zakariyya wayan suka gaisa, bayan ta gama waya dasu Zakariyyan Ziyada ta ƙira suka sha hiransu. Taji daɗin yanda taji muryan Ziyadan dan da dukkan alama tana samun jindadi da kulawa daga wajen Yaya Ameenu yadda ya kamata, ko dama tasan ya Ameenu zafinshi baya kan matarshi, don ko ita kanta tana mmkin yadda ya zama kamar bawa ga Adda Maryam sai dai in tayi duba da yadda Adda Maryam ke biyeyya a gareshi sai tace ta canci ya mata komai ma, to kuma tasan Ziyada ma irin Adda Maryam ɗince. Yau ma dai basu wuni agida ba, dan ma saidare sannan suka dawo masauƙinsu, tundaga ranar kuwa yawanci kullum sai sun fita , kullum cikin yawon zuwa wajen shaƙawata suke, Alhmdulillahi kuma zuwa yanzu Ƙafar Saifuddeen tana ci gaba da zama normal.
*******
Alhamdulillah yau watansu biyu da sati uku, da zuwansu Instanbul yayinda cikin Zaleeha ya kusa cika watanni bakwai ras.
Yau ya kama saura sati guda kenan su koma Nigeria, acikin watannin da suka shuɗe ɗinne kuma, Zaleeha ta fara zuwa awu nan cikin wani babban asibitin Acibadem Hastanesi Hospital instanbul.
Dake Cikin tsakiyar birnin Instanbull, asibitine me kyaun gaske da tsaruwa komai cikin ci gaba da gwarwa suke mata auwan cikinta da bata dukkan kulawa da shawarwarin yadda zata kula da kanta da cikin dake jikinta.
Sannan kuma acikin watannin sosai sukaji dadin rayuwarsu a Instanbull,
kulawa me tsabta suke bawa juna, shaƙuwarsu ta ƙaru, kodayaushe suna jikin juna suna tattalin cinsu, duk randa akayi dusar ƙanƙara kuwa zama na musamman Hamma Saif yake ta buɗe mishi tirtsetsen cikinsu ya ɗun-ɗuma musu abinda ke ciki daga nan kuma wasa ke sauya salo.
Zuwa yanzu kuwa Saifuddeen yana tsayawa akan ƙafafunsa car, tafiya kuwa babu inda baya zuwa, hakanne yasa shi jingine wheelchair ɗinsa, da ƙafafunsa suke fita suje yawonsu su dawo, wata irin zazzafar soyayyace ta shiga tsakaninsa da Zaleeha me wuyar fassaruwa, acikin ƴan watannin kowanne yasan sirrin kowa, sun zama kaman wasu shaƙiƙan abokai, acikin watannin kuwa kullum sai sunyi waya dasu Ummi, kuma tana ƙoƙarin ƙiran Mama da kuma Mamy harma da Baba Malam da Ziyada, sosai sukejin daɗi, musamman ma Baba Malam da ayanzu yake al'fahari da ita Ummi yanzu ta fara cewa suyi maza su dawo wai kada Zaleeha ta haihu a wannan ƙasar sanyi ya kama mata jiki, Saifuddeen kanyi dariya yace.
"Ummi cikin tai wata bakwai ne".
Takan ce to ba Ameena bakwaini ta haihuba waya sani ko daga gunshine Zaleeha bakwaini zata haifa yanayi dariya yace mata, a a Ummi shi wannan taranni za'a hafo in sha Allah da haka dai suyita hiran cikin suna dariya, Raliya kuwa har