Showing 27001 words to 30000 words out of 34659 words

Chapter 10 - Sanadin Kawa Book 1 Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

209

xa ku yi da El-Basheer in sha Allah, I am wishing you nothing but all goodies that life gat for u Amira, in sha Allah xan koma kano gobe, ban ji dadin baxan ma Ammi sallama ba xan wuce amma idan da rai we shall meet once again in life, I never regret knowing you teemah" content din message din knn, ta tura wayar ta ja bargo ta rufe har kanta.
KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association=ء?

(Home of Experts and perfect Writer's)



*SANADIN K'AWA*


NA


*khaleesat Haiydar*


BABI NA GOMA SHA HUDU




17




5 days later...
Sanye take da Hijab har k'asa tana tafiya kamar me tausayin kasa, ba karamin rama tayi ba sai dai haskenta ya fito sosai, kasancewar bata da kudi gunta kuma Ammi bata yi mata tayin kudin mota ba da kafa take tafiyar xuwa gidansu Nafisa, a 'yan kwanakin nan kusan kullum sai Nafisa ta xo gidansu jiya da yau din da bata xo ba duk sai taji ba dadi har ta nemi ixinin xuwa gidan nasu gun Ammi. A dai dai gidan da Husnah ta taba janta su yi lalle ta ga Husnah tsaye su uku, tayi wani uban haske da alaman lalle suka xo yi, da farko still tayi tana kallon ta ko kiftawa babu, Surutu kawai take xubawa ko full stop babu tana fari da idanuwa, cikin ikon Allah kuwa kamar ance ta juyo suka yi ido hudu, lkci daya Husnah tayi tsit ta wani xaro ido tana kallon ta cike da rudewa, Fatima tayi d'an murmushi ta ci gaba da tafiyarta har ta wuce su. Nafisa tayi murnan ganinta sosai, bayan sun shiga daki tace "Inji dai da ixinin Ammi kika fito amma?" Kai Fatima ta gyada mata tace "Na tambayeta" Nafisa tace "Yauwa, gashi har kin kara kyau da kika fara kwantar da hankalin ki kawata, kinga hasken da kika yi kuwa" murmushi kawai Fatima tayi don gaskiyar Nafisa har wani cool beauty ta kara, da damuwa Nafisa tace "Saura kuma ramar nan da yyi maki yawa, ki daure kina cin abinci plss" Fatima bata ce komai ba, Nafisa ta fita ta dauko mata kunun aya da xobo da suke yi na siyarwa a fridge, Fatima na kallonta tace "Kinsan warce na gani a layin ku yanxu?" Nafisa ta xauna ita ma tana kallon ta tace "A'a" Fatima tace "Husnah" xaro ido Nafisa tayi tace "Kai haba, Husnah? Ta dawo kenan, a ina kika ganta?" Fatima tayi d'an murmushi bata ce komai ba, da sauri Nafisa tace "Amma in ji dai baki ce mata komai ba Fatima" Fatima ta girgixa kai tace "Ban ce mata komai ba" Nafisa tace "Kuma ta gan ki?" Gyada kai Fatima tayi tace "Sosai ma, she was just staring at me may be surprise" Nafisa ta sauke ajiyar xuciya tace "Naji dadin da baki ce mata komai ba wllh" Fatima tace "Toh sai kika tsamman kyaleta nayi wai?" Nafisa tace "Noo ba haka nake nufi ba, but kinsan me kawata, wllh ni nasan idan Husnah taji wanda xa ki aura sai stroke ya kusa kamata, kai sai ma ya kamata don ita ke mugun son sa ba ke ba, wllh har karamin hauka sai tayi, kuma ina gaya maki sai ta neme ki nan ba da dadewa ba idan ta samu labarin bikin ku da shi, Kai..... Kinsan kuwa Allah plans best Fatima, dubi fa lkci daya mai kudi matashi ya xo neman ki da aure, wanda kuma kusan ince yasan duk sirrin ki ya kuma san ke wacece yasan meye ke din" wani kallo Fatima ta yi mata tace "Yasan meye ni kamar ya?" Dariya Nafisa ta yi tace "Atoh ya kike son ince, ya san ki in and out, kuma ya dage sai ya aure ki, toh ni Allah na tuba me xai wani dame ki? Idan ma Umar ne kar ki manta rabuwar arxiki fa ku ka yi da shi...." Ita dai Fatima bata ce komai amma duk jikinta ya yi sanyi, yanxu fa ita ba budurwa bace wai, Nafisa ta katse mata tunaninta tace "Toh yanxu kin yarda xa ayi dinner din kawata?" Wani kallo fatima tayi mata tace "Allah ya kiyaye" Nafisa tayi murmushi tace "Toh shkkn, amma don Allah ki sake ranki ki kwantar da hankalin ki kin ji kawata" Fatima tace "Tunda ba ke xa ayi ma aure da axxalumi ba ai dole kice in saki raina" yar dariya kawai Nafisa tayi tace "A'a da axxalumi ne baxai sake waiwayo inda kike ba Fatima" kafin Fatima tace komai wayarta dake hannunta ya fara ring, dubawa tayi taga Elbasheer ke kiranta, ita har ta mance rabon da ta ga kiransa a wayar ta sai dai text shi ma ba wai xancen kirki ba kawai text da xai kufular da ita, ta ajiye wayar gefenta, Nafisa tace "Aa ki dauka plss" jin Fatima bata ce komai ba, Nafisar ta dauka tayi picking ta mika mata, Karba tayi ta sa hands free yyi sallama ta amsa can ciki, yace "Ina kika je?" Buds ido ta yi tace "To ka tambayi spies din naka mana" Yace "Sun sani" tace "Toh why are you asking?" Yace "Saboda baki ce min xa ki fita ba" a takaice tace "That's because kai ba ubana bane" Nafisa da duk bata ji dadi ba murya can kasa tace "Kai Fatima..." Elbasheer yyi murmushi yace "Eh amma kuma xan xama mijin ki soon" tabe baki tayi bata ce komai ba, yace "Why putting d call on speaker?" Tace "That's what pleases me" yace "Uhn to ki gaida kawar ta ki" shiru fatima tayi sai taji gabanta ya fadi, kai anya wannan mutum ne ma kuwa, muryarsa ya katse ta "Yaushe xa ki koma gida?" Da kamar baxa tace komai ba sai kuma tace "Idan na tashi tafiya spies naka xa su sanar da kai" yace "Alryt, ki turo min address din inda kike yanxu" tace "Au to ai na xata spies din suna kofar gida ma yanxu haka, to baxan turo ba" yace "OK then..." Daga haka ya katse wayar, hararata kawai Nafisa take yi tace "Baxa dai ki ji magana ta ba ko Fatee" Fatima tace "Ehh baxan ji ba" Nafisa tace "Ae shkkn" mikewa Fatima tayi tace "Xan yi alwala ban yi la'asar ba na fito" daga haka ta nufi kofa Nafisa ta bi ta da ido, wayarta ta dauka bayan ta fita ta duba call log dinta, El tayi saving number Elbasheer da shi, Nafisa ta shiga gun message da sauri bayan ta sa numbersa ta fara typing din address din anguwarsu ta kuma sa karfe biyar da rabi xata koma gida daga haka ta tura masa yana tafiya kuma tayi deleting ta ajiye wayar da sauri, tasan ko kadan anguwarsu bbu wuyar ganewa kuma har da number din gidan tasa masa.... Fatima na idar da sallah Nafisa ta tilastata ta sha xobo don tace bata son kunun aya, a duk hirar shawarwari kawai Nafisa ke ba Fatima don saura wata daya kacal bikin, karfe biyar na wucewa Fatima tace "Xan wuce Nafiee kar Ammi tayi fushi" Nafisa tace "Ki jira biyar da rabi sai in raka ki" Biyar da rabi saura minti biyar wayar Fatima ya fara ring, kallon wayar ta dinga yi ganin Elbasheer ne, Nafisa ta dauka tayi picking ta mika mata, Fatima ta kai kunne, yace "Gani a kofar gidan" da mugun mamaki tace "Wani kofar gidan?" Yace "Kin fini sani" Nafisa ta karbi wayar ta katse tace "Wai me?" Fatima tace "Rainin wayo mana" Nafisa tace "Toh Allah ya kyauta tashi ni dai mu je in raka ki" daga haka suka fita Fatima ta shiga tayi ma Umma sallama sannan suka bar gidan da Nafisa, sosai gaban Fatima ya fadi ganin motar Elbasheer a waje ta kasa ci gaba da tafiya, sauke glass din motar yyi yana kallon su ta cikin bakar spec din idonsa, Nafisa ma kallonsa take don bata taba ganinsa ba sai lokacin... Ya bude motar ya fito, Nafisa dai ta saki baki ta kasa daina kallonsa don bata taba tunanin Elbasheer ya kai haka a reality ba, sanye yake da kananun kaya, bakar shirt din jikinsa ya haska sa sosai ba kadan ba, rungume hannayensa yayi, Fatima ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, ta rasa gane me yasa in dai ta gansa sai taji faduwar gaba, Nafisa ta yi karfin halin rike hannunta ta ja ta suka karasa gun sa, yyi murmushin da ya bayyana white set of teeth dinsa yace "She looks surprise.... Which reveals ke kika turo min address without her knowledge kenan" Nafisa ta xaro ido a rude, Fatima ta hade rai tana kallon Nafisar, shafa kansa yyi yace "Anyway I am Bashir Ahmad, can I knw u beta?" ya fadi yana kallon Nafisa, cike da karfin hali tace "Nafisat Musa" yace "Nyc, she is ur frnd kenan" ya fadi yana nuna Fatima, nafisa ta gyada masa kai, yace "Good, amma bakya fada mata gaskiya koh" Nafisa tace "Na me?" Yace "Rashin ji da take mana" Fatima dake hararansa tace "Kai dai ne mara ji, don duk rashin ji na bana cutar mutane kuma bana shiga rayuwar mutane" wara ido yayi yace "Really? Sai xuwa gidan frnds din ki maxa da ku ka hade a media koh?" Narai narai tayi da idanuwanta, ya wara ido yana kallon Nafisa da ta daure fuska yace "Look she started fa, kuma ta wani marairaice min xata yi kuka, sai mu yi tare ai..." Kawai ji suka yi ance "Fatima...." Duk suka juya suka ga Husnah da kawayenta biyu an zizara masu lalle a hannuwa, baki sake take kallon Fatima da Elbasheer a rude kamar idanuwanta xa su fito, sake jakar hannunta da leda tayi ta isa gaban Fatima tana xaro ido tace "Fatima wannan ba Elbasheer din nan bane na Instagram, me ya xo yi nan, me ya kawo sa nan, wajen wa ya xo...." Ae bata rufe baki ba Fatima ta sauke mata wani wawan mari bata bar ta ta farfado ba ta kuma sauke mata wani sannan ta cakumota iya karfinta tace "A ina kika san bni?" Husnah da ta rude ta dinga salati tana cewa "Innalillahi, Kika mare ni, ni kika mara Fatima, mari na kika yi? to wllh xaki gane baki da wayo, sai na halaka ki yau, sai na...." Kamar kiftawar ido har Fatima ta kai ta kasa tana duka iya karfinta kamar an aikota, cixo da haurin da Husnah ta dinga kai mata tana ihu hakan kuma bai yi hindering fatima daga jibgarta yanda ta so ba Nafisa da ta rikice ta dinga rikesu tana salati, shi kansa Elbasheer sakin baki yyi da farko don abun just happened all of a sudden, kawayen Husnah kuwa banda shewa bbu abinda suke suna ja baya suna cewa kar Husnah ta yrda, tuni yan anguwa aka taru wajen, ganin Nafisa ta kasa raba su Elbasheer ya sa hannu ya janye Fatima daga kan Husnah, dukan hannunsa ta dinga yi ta fashe da kukan takaici cike da masifa tace "Ka sake ni malam, ni wllh ka sake min hannu, ka kyaleni inyi maganinta" Husnah da ta samu ta mike baki duk jini ido a kumbure tayi kukan kura ta yo kan fatimar, da sauri ya janyeta ya mayar da ita bayansa yana ma Husnah wani kallo, Fatima ta fashe da sabon kuka tana son kwace kanta ta koma gun Husnah tace "Ni ka bar ni don Allah, plss ka sakeni..." ya dawo da ita gabansa ganin da gaske komawa take son yi kawai ya dagata, xaro ido tayi a rude tace "Nooo, stop it plssss ka ajiye ni mutane..." xagawa yyi yana dauke da ita ya bude front seat ya saka ta ciki ya rufe motar ya danna lock, Nafisa ta sauke ajiyar xuciya, Husnah kam duk ta gigice ta dinga xagaye motar tana kumfar baki "Ba dan ni din ba xa ki san sa, ina ce ni na fara sanin sa kafin ke, ina ce ni na kawo maki shi har gida, ina ce da kyar ma kika yarda kika yi following din nasa ke me aji, Fatima har ni xa ki ci ma amana, ki bi ta bayan gida kina haduwa da Elbasheer, macuciya axxaluma muguwa ko kunya baki ji ba kina hulda da saurayin da ni na hadaku kawai kuyi xumunci ta waya, to wllh wllh yanda na hada ku haka xan rabaku in sha Allah" Elbasheer bai kuma kallon inda take ba don har kansa ya fara sara masa sbda hayaniya, ya bude driver seat yana shiga Husnah ta yo kansa da gudu yana ganin haka ya rufe motarsa ya dage glass, yyi igniting key ya ja motarsa.
KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association=ء?

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU

18

Rufe fuska Fatima ta yi da Hijab ta dinga rera kuka, shi dai bai ce komai ba har ya bar anguwar, parking yyi yana kallonta da mamaki yace "Sannu drammer Queen, ba ma ki da kunya yarinyar nan, haka kawai kin kama yar mutane kin nakada mata duka snn ki xo nan kin cika min kunne da kuka" cire Hijab din tayi a fuska cike da masifa tace "Toh ina ruwanka??" shafa beard dinsa yyi yace "Lallai, Ashe Bruce Lee xan auro gidana" k'in cewa komai tayi, ya wara manyan idanuwansa yace "Kaddai nima haka xa ki je kina dukana idan aka yi auren" nan ma dai ko kallonsa bata yi ba bare ta tanka sa, murmushinsa mai kyau yyi yace "Ita ce kawar taki da ta baki shawarar ki xo gidana knn" murguda baki tayi taki cewa komai ta kara tsuke fuska, dogon hancinta ya ja ta buge hannunsa, ci gaba yyi da driving dinsa, yana kallon titi murya can kasa yace "But ba girman ki bane dambe a titi, you just downgraded me there, ke kika yi damben amma ni naji maki kunya...." a takaice tace "Toh ai ban ce ka xo inda nake ba" ya kalleta ta gefen ido xai yi magana wayarsa ta fara ring, kallon screen din yyi sannan ya daga tare da yin sallama a hankali, ya d'an buda ido yace "Noo, Sorry mum yanxun xan dawo...." Shiru yyi yana sauraren mum din tasa, can ya kalli Fatima a hankli yace "Noo, Fatima na je picking ne, amma kiyi hakuri xan dawo in maki yanxu" ya gyada kai yace "Alryt" sannan ya mika ma Fatima wayar, kallon wayar ta dinga yi murya can kasa yace "Take.... My mother" da kamar baxata karba ba sai kuma a hankali ta sa hannu ta karbi wayar ta kai kunne hade da sallama cikin sanyin murya, daga daya bangaren aka amsa mata, tace "Ina yini Umma" Matar tace "Lafiya lau Fatima, ya ku ke?" Fatima tace "Lafiya lau ya aiki" matar tace "Alhmdllh dear, ya iyayen naki" tace "Suna lafiya" matar tace "Maa sha Allah, Allahu ya sanya albarka, sai ayi ta addu'a kinji" Fatima ta gyada kai tace "Toh nagode" daga haka matar tayi mata sallama ta mika masa wayar, ya amsa ya kai kunne yace "Thanks mum, will be back anytime soon" daga haka ya ajiye wayar ya ci gaba da tukinsa, sai da suka kusa gida yace "Look... Ki saurareni da kyau on a serious note bbu ruwanki da yarinyar can, you just disgraced ur self few minutes ago...." Bata ko juyo ba bare tace komai, yayi parking kofar gidansu yace "Ni dai na gaya maki, if you like pretend u are not hearing, in Allah ya baki sa'a kin doketa daxu next time try that shit xata nakada maki duka ne ba ruwana...." Sai a sannan ta kallesa tace "Mai dukana sai ruwan sama shi ma idan na so kenan, ita din banxa, ai ba ta ga komai ba yanda ka walakanta ni haka ita ma xan walakanta ta don ita ta ja min" buda ido yyi yana kallonta da kyau yace "Walakancin me na maki" tabe baki tayi tace "Bani da lkcn wannan bayanin" ya daga kafada yace "Karkari kice nayi raping dinki koh?" Ji tayi wani takaici ya rufe ta, ya tabe baki yace "Yeah that's just it, kuma auren ki da nake son yi I keep saying wllh taimakon ki xan yi, It will save u d embarrassment on ur 1st nyt" yana fadin haka ya bude motar yace "kinsan me, idan har baki je kinyi wanka da ruwa me xafi ba yanxu ina tausayin abinda xae sameki kafin gobe, ba ke Bruce Lee ba" bude motar tayi tayi wucewarta ko rufe kofar bata yi ba, ya bi ta da kallo yana murmushi. Tun daga wannan rana Fatima bata sake fita ba tana ta xuba ido taga xuwan Husnah gidansu amma shiru shiru har bikinta da Elbasheer ya rage sati daya, a duk kwanakin nan rana daddaya ne Nafisat bata xuwa, kai har suka saba da Elbasheer dake xuwa gidan jefi jefi da yamma, yawanci ma da ita yake labarinsa, nan Nafisah taga Elbasheer is just perfect, kawai dai ta lura ya fiye tsokana ne, Nafisat mamakin halin Fatima take don har lkcn taki daukar shawarar da take bata don har lkcn taki sakewa da Elbasheer, in dai fatima tasa kanta abu bbu me canxa mata ra'ayi . A cikin satin da ake ta shirin biki Fatima tayi mugun daga hankalinta fiye da baya, abinci ma sai an tilastata take ci, ana jibi biki wani kanin Umar ya kirata, bata ma san shi bane bayan ta daga ya sanar da ita waye, Hijab ta sa ta fita bayan ta dau ixini gun Ammi, gaisawa kawai suka yi ya mika mata envelope wai in ji Umar, ta karba a sanyaye, yyi mata sallama ta koma ciki, tare da Nafisa suka bude Envelope din suka ga kudi ne har dubu Hamsin, duk yanda Fatima ta so danne kukan dake cin ta kasawa tayi, Nafisat ta dau kudin ta kai ma Ammi. Yau juma'ah tun da fatima ta samu labarin an daura aurenta da Elbasheer take kuka, bbu irin lallashin da Nafisa da wasu daga kawayensu basu mata ba amma kamar
Suna d'a d'a tunxurata, sai da wata kawar Ammi tayi da gaske da ita ta hakura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login