Showing 9001 words to 12000 words out of 34659 words

Chapter 4 - Sanadin Kawa Book 1 Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

210

Husnah tace "Toh ba Matsala" Dari biyar fatima ta bata kudin mota kamar yanda ta bukata kafin ta je karbo kayan, sannan ta rakata ta hau adaidaita don komawa gida. Tun da ta shigo Ammi ke hararata sanin ba daga inda ta aiketa ta dawo ba, ita dai ta lallaba ta shiga daki, bata fito ba sai kusan magrib ta yi alwala ta koma ciki. Bayan isha Husnah ta kirata a sace ta fita waje, Husnah ta ce "Amma fa gobe xa mu mayar masu kayan su bana son fitina don da kyar aka ban, yanxu a ina xa mu hadu sai mu shirya?" Fatima tace "Mu hadu gidansu Nafisah" Husnah ta yamutse fuska ta ce "Wannan me shegen sa idon gwara dai mu canxa waje" Fatima tace "A'a ni dai nan xa mu hadu" Husnah ta tabe baki tace "Toh shkkn har da kayan kwalliya a ciki, sai dai goben" Fatima tace "Allah ya kai mu" daga haka ta shiga gida da sauri ta wuce daki. Tunane tunane kawai take har kusan karfe goma, duk kiran da Umar yyi mata kin dagawa tayi, duk ta ma rasa abinda ke mata dadi, can ta dau wayarta ta shiga kiran Elbash, bai daga ba har ya katse, ta ajiye wayar ta ja tsaki tayi kwanciyarta, can har ta fara bacci kusan sha daya sai ga kiran sa, da kyar ta daga don bacci ne sosai idonta ta kai kunne ta lumshe ido tayi masa sallama cikin sanyayyen muryarta, ya amsa yace "I saw ur missed cal" tace "Uhn, I called to ask if I can come tomorrow?" Yace "Are you serious?" Tace "Uhnn" yace "Sure you can come Allah ya kai mu" kai kawai ta gyada masa bata ce komai ba, yace "Seems you are sleepy, good nyt sleep tight" bata ce komai ba ya katse wayar daga wajensa sannan ta ajiye wayar har lkcn bata bude ido ba. washegari misalin karfe takwas da rabi ya kirata ta daga, daga daya bangaren yace "When are you coming?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Later" yace "Alright when you are ready you let me knw" tace "Ohk" ya katse wayar, haka kawai taji gabanta na faduwa ta tashi ta je ta ci gaba da abinda take, kafin karfe goma Husnah ta kirata ya kai sau Ashirin, takaici ya isheta don ita har lkcn bata san karyar inda xata yi ma Ammi tace xata je ba, daga karshe wani plan ya fado mata, safiyya ta kira a waya tace mata don Allah ta kira Ammi tace mata xata rakata kasuwa siyayya, tasan Ammi na jin kunyarta baxa ta hanata fitowa ba, da kyar Safiyyar ta yrda bayan fatimar ta shirga mata karyar ba ko ina xata ba banda gidansu wata kawarsu Naja'atu, Safiyyar ta kira Ammi nan da nan kuma Ammi ta amince Wanda hakan yyi sanadiyyar barin Fatima gidan bayan Ammi tace mata suna dawowa ta taho gida, a boye ta fita da ledan da Husnah ta kawo mata jiya da daddare duk da bbu kayan da ya burgeta cikin kayan don haka ne ma yasa tasa atamfarta Mai kyau da Umar ya siya mata ya bada a dinka, ta daura well ironed hijab dinta fari a kan kayan don baxa ta sa kayan da Husnah ta kawo mata ba, tana kan adaidaita ta kira Husnah, Husnah tace "Ke ni ina nan kusa da gidansu nafisa ana min lalle kema ki shigo idan kin iso a maki, ko haka xa mu je da fararen hannu ba kyan gani" takaici ya ishi Fatima ta katse wayarta, tana isa gidansu Nafisa ta kuma kiran Husnah, Husnah ta fito da hannun lallenta da bai gama bushewa ba, da Kyar da kyar ta lallaba Fatima ta ja ta xuwa gidan lallen, nan aka xana mata lalle ita ma a fararen hannunta bayan ta cire hijab dinta ta linke, sosai lallen ya haska fararen hannunta yyi kyau sosai da kyar ta yarda aka yi a daya hannun don cewa tayi ita a hannu daya kadai take so, ba su suka fita gidan lallen ba sai kusan karfe biyu bayan sun yi azahar a nan Fatima ta biya dubu daya kudin lallen nasu, a hanyar xuwa gidansu Nafisat Husnah tace "Wani kayan xa ki sa a ciki?" Ta yatsina fuska tace "Ke ni fa kayan nn na jikina xan bari" da mugun mamaki Husnah tace "How? Why??"
[9/18, 8:37 AM] Abue Saleh Kurami: KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association=ء?

(Home of Experts and perfect Writer's)



*SANADIN K'AWA*


NA


*khaleesat Haiydar*


BABI NA GOMA SHA HUDU




6





Fatima tace "Da gaske da shi xan je" Husnah tace "Ji walakanci, ban gane da shi xa ki je ba, ba ga kaya can na kece raini ba na aro mana" Fatima tace "Toh ni basu min ba tunda ba biki xan je ba, I prefer wearing my hijab" Husnah da ta saki baki tana kallonta tace "Tabdi, amma wllh baki da hankali Fatima...." Fatima tace "Na ji" daga haka ta ta shiga gidansu Nafisa, Nafisa dake wanke wanke ta taso da sauri tace "Lah, Fatima kece gidanmu yau" Fatima tace "Eh mana tunda ke baxa ki xo ba" Nafisah tace "Allah sarki ba haka bane Fatima, har yanxu jikin Umma sai a hankali kinga ko islamiyya ma bana xuwa yanxu" Fatima tace "Ayya, wllh ban sani ba da na xo gaisheta, kuma ko shekaranjiya sai da Ammi ta tambayeni jikinta nace da sauki" Nafisa tace "Ai kam sai dai a gode Allah, daga ina ku ke haka" Fatima ta kalli Husnah da ta nemi kujerar tsugunne ta xauna tace "Daga gida mana" Nafisah ta kalli Husnah ita ma tace "Sannu Asma'u ya su inna" bbu yabo bbu fallasa tace "Alhmdllh" Fatima ba ta da kawar da ta wuce Nafisah a da, tun da suka hadu da Husnah a bikin wata kawarsu Husnah ta nace mata har suka fara kawance Wanda lkci daya Husnah tayi nasarar kusan raba ta da Nafisah don a dalilin Husnah sai da suka yi fada da Nafisah sbda yawan bata shawara da take kan tarayyarsu da Husnah ganin bata da kamun kai, Nafisah yarinya ce me hankali da natsuwa, sosai Ammi ke son alakarsu da Fatima, sai dai tunda Fatima suka hadu da Husnah kawancensu ya ja baya sosai da Nafisah a cewarta Husnah ta fita wayewa, Husnah da ta daure fuska ta mike tace "Kinga fa yamma nayi Fatima tunda ke baxa ki canxa kayan ba ni bari in canja mu wuce" Nafisah tace "Ina xa ku?" Da sauri Husnah ta karbe tace "Xumunci" Nafisah bata ce komai ba, Husnah ta shiga dakinsu Nafisar rike da ledan kayan da ta karba hannun Fatima, fatima ta mike ta bi ta ta shiga dakin shiga don kara gyara fuskarta, Tsaye Nafisah tayi bakin kofa tana ta kallon su ganin uban kwalliyar da Husnah take da shegen kayan da ta saka, tuni fatima ma ta gyara fuskarta ta xauna tana kallon Husnah har ta gama sannan suka fito tana kallon Nafisah da ta kasa daina kallonsu tace "Anguwa xa mu je sai mun dawo Nafee" Shiru Nafisah tayi, can ta ce "Ohk shigo mu d'an yi magana fatima" Husnah ta bi Nafisah da harara, Fatima ta bi Nafeesar suka koma dakinsu, Nafisah na kallonta da damuwa tace "Ina xa ku fatima?" Fatima ta yi dariya tace "Ke ba ko ina fa xa mu ba, gidan wata kawarta xa mu" Nafisah tayi shiru, can tace "Toh shkkn, amma ki dai kula pls kinji" Fatima tayi 'yar dariya tace "Toh Ammi" daga haka tayi ficewarta tana cewa "Sai mun yi waya" a bakin soro ta tarda Husnah tana cika tana batsewa, tana dariya ta ja ta suka bar gidan, masifa Husnah ta dinga yi tana xagin Nafeesah har suka isa bakin titi, a nan Fatima ta kira Elbash, ya katse ya kirata, tana dagawa ta sa a handsfree tace "Yanxu. xan fito" yace "Ohk don't stress ur self send the address of where you want our driver to come and pick you" tace "Ohk" daga haka ta katse kiran, tana xaro ido tace "Ke ina na sani a Abuja da xan tsaya driver ya xo ya daukeni" Husnah ta kwace wayar tace "Bari in sa address din gidansu Sadiya" hakan tayi bayan ta tura suka hau mota xuwa cikin garin Abuja, tun basu karasa gun ba wani number ya Kirasu yace Elbash ne ya turo sa ya daukesu kuma ya kusa address din da ya basa, Fatima tace "Alryt sai ka iso" cikin sa'a suka isa dai dai gun kafin shi ya karaso, Husnah tace "Ke kirasa kice a bakin titi xai jira kar ya karaso nan ya gan mu a tsaye" da sauri Fatima ta kirasa ta sanar da shi abinda Husnah tace, yace "Ai ina bakin titin ma yanxu haka" tace "Toh jira yanxu xan taho" daga haka ta katse wayar, da kafa suka karasa har bakin titin, ta kuma kiransa yyi mata describing din irin motar da ya xo da shi, Fatima da ta hango mota irin Wanda yyi describing din mata ta katse wayar sannan ta nufi motar Husnah na biye da ita, kallon mutumin dake cikin motar kawai take tana mamakin wai driver cos he didn't look like one, kallo daya yyi masu ya dauke kai tace "Da kai muka gama waya?" Ya kuma kallonsu yace "Eh ni ne Wanda Dr ya turo in yi picking din ki" Tace "Ohk" ya kalli Husnah yace "Wacece ma a cikin ku tukunna?" Tace "Ni ce" ya kalli Husnah da ke wani yauki yace "Ohk mutum daya yyi instructing dina in dauka so ban san ko ya xa ki da kawar nan ta ki ba" da sauri tace "Noo tare muke kuma rakani xata yi" ya girgixa kai yace "Kin taba ganin inda yaro ya tsallake maganar uban gidansa" Rasa abun cewa Fatima tayi mamaki ya cikata, can ta kalli Husnah da ta marairace, Husnah tace "Amma bawan Allah aminiyar ta ce ni fa, ka kirasa ka kara masa bayani rakata kawai xan yi ko da baxan shiga ciki ba" Yace "Ba umarnin da ya ban ba kenan, sai dai ta kirasa ita ta gaya masa" Fatima ta hade rai tayi dialing numbersa ya katse ya kirata, tana dagawa ta sa a handsfree tace "Hey, am coming over with my frnd fah, and...." Katse ta yyi saurin yi yace "Nop that was nt our deal, beside I didn't tell my family u are coming with a frnd" kasa cewa komai tayi, Husnah da kiris ya rage hawaye ya xubo idonta tace "But I am her frnd fa wllh" yace "I didn't announce she's coming with a frnd to my mum with siblings" Fatima ta ja tsaki kafin tace komai ya katse wayarsa, Ta mayar da wayar jaka tana kallon Husnah tace "Mu wuce gida...." Da sauri Husnah tace "Gida kuma" Fatima tace "Yeah I am nt going anymore" Jan ta Husnah tayi da sauri xuwa gefe tace "Ka ji sha sha sha xata tona mana asiri, ke baki ga irin motar da aka xo daukar ki cikinsa ba, bbu xancen mu koma gida, kawai shiga ku wuce ni na hakura xan shiga gidansu Sadiya in jira ki, amma ki min alkawarin komai kika samo raba dai dai xa mu yi baxa ki boye min ba" Fatima tayi shiru tana kallon ta, Husnah ta kwantar da murya tace "Don't say no plss besty this is d only opportunity we have wllh, in dai ni ne na hakura wllh kije" daga haka ta ja hannunta xuwa gun motar tana kallon Wanda ke xaune maxaunin driver tace "Toh shkkn Allah kiyaye hanya, she will go alone tunda bai son in bi ta" daga haka ta ja Fatima xuwa front seat ta bude mata ta sa ta shiga ta rufe motar tana kara lekan motar, Driver ya ja motar Husnah ta dinga daga ma Fatima hannu tana murmushi, Fatima dai bata ce komai ba amma banda faduwa bbu abinda gabanta ke yi har suka yi nisa daga inda Husnah take. Tafiyar kusan minti sha biyar suka yi Fatima ta kalli drivern a karo na farko tace "Wai ba mu isa gidan bane har yanxu?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Eh" wayar drivern ne yyi ring ya daga ya kai kunne, yes kadai ne abinda ya dinga cewa har ya katse wayar, ganin sun kara tafiyar kusan minti goma tace "Ka ga in har haka gidan yake da nisa naga yamma ya fara yi kawai drop me let me be going back home" yace "Mun kusa daga nan bai fi tafiyar minti biyar ba xuwa gidan" bata kuma cewa komai ba, sai bayan wani minti goman suka shiga wani layi, tun dai tana kirga kwanan da suke sha har ta gaji ta hakura, kana ganin anguwannin kai kasan sai wane da wane, ko ina tsit sai haushin karnuka a wasu gidajen, ta rasa me yasa xuciyarta ke bugawa gashi ta kasa tsayar da takamaiman addu'a a xuciyarta, gaban wani ubansun gida yyi horn bbu bata lkci aka bude katon gate din drivern ya ja motar bai xame ko ina ba sai parking space, ya bude motar bayan yyi parking ya fito, a hankali ita ma ta bude ta fito tana kare ma kantamemen gidan kallo, can ta kalli Wanda ya bude gate din, ko Kadan bai mata kama da mai gadi ba, Drivern yace "Mu je" bin bayansa tayi kamar me tsoron taka kasa har suka isa main parlor din gidan, bbu kowa parlorn sai sanyi Ac da karar sa hatta TV a kashe yake, cool scent ne ke tashi a parlorn, ya nuna mata kujera ya wuce sama, bayan wasu mintuna ya sakko kasa ya nufi kofa xai fita ta mike da sauri tace "Wait, am I to sit here all day?" Ba tare da ya juyo ba yace "They are coming" daga haka yyi ficewarsa ya ja kofar, kasa xama tayi duk gabanta ya ki daina bugawa, ta kalli agogo taga har karfe biyar, lkci daya kawai ta yanke shawarar ita ma ta fita kawai bata kai ga aikata hakan ba taji taku stairs ta juya da sauri, idonta ya sauka kan fararen kafafuwansa don da alamar 3qtr ne jikinsa, ta kasa daga kai ta kallesa tayi saurin dauke kai xuciyarta na mugun bugu, tuni kamshin turarensa ya gauraye ko ina na parlorn, duk yanda ta so juyowa ta direction dinsa kasawa tayi har lkcn kofa kawai take kallo, kawai ganinsa tayi tsaye gabanta suka yi ido hudu, kaii Ashe photo bai masa adalci ba don ba ainahin kyansa yake fitarwa ba, this is just d definition of *Handsome* keenly yake kallonta kamar me examining din abu a tare da ita, da sauri ta juya cikin sarkewar murya tace "Ur... family members?" Bata Ankara ba sai ji tayi ya juyo ta xaro ido a rikice tace "What???" Ya d'an cije lips dinsa yana mata wani kallo daga sama har kasa yace "Fatima Muhd, the daughter of the former minister of education right?" Ta hadiye wani abu da kyar ta girgixs masa kai ba tare da ta san tayi hakan ba tace "Nop, I lied about that" wara ido yyi yace "Really?" Ta gyada kai, wani murmushi yyi yace "Amazing" cikin rawar murya tace "Ur family members pls, I want to apologize and leave it's getting late...." Juyawa taga yyi yana yar dariya, ji tayi komai nata ya tsaya, lkci daya taji sanyi na shigarta, bata yi wani tunani ba ta nufi kofa da sauri ta murda handle ta ji sa a rufe, still tayi a wajen ta juyo a hankali tana kallon sa xuciyarta na bugawa, murmushi taga yana yi yana kallonta, ta fara girgixa masa kai cikin tashin hankali, kamar an tuna mata wayar hannunta ta daga da sauri ta shiga kkrin dialing number, taku hudu ya iso inda take ya warce wayar tana kallo ya kashe sannan ya karasa kan kujera ya jefar, sai a sannan ta fashe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku don Allah don annabi ka rufa min asiri am begging u in d name of God" tana magana tana jijjiga handle din kofar, ji tayi ya fixgota har sai da suka yi karo tana jiyo saukar numfashinsa fuskarta, tsayar da kukan da take tayi lkci daya ta sauke masa mari fuskarta daure tana huci.

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association=ء?

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*



7

Kauda kai yyi na kusan second biyar, can ya juyo a hankali, xata bar wajen ya rikota bata Ankara ba sai jin ya sauke mata tagwayen mari da yasa ta fara ganin dishi dishi tayi, bata gama recover ba ya fixge Hijab din jikinta da karfi, wani ihu ta saki da karfi ta durkushe wajen tana kare jikinta tana kuka a rude tana cewa "Na shiga uku, don Allah kayi hakuri...." Ya dagota taki tashi tsaye banda rawa bbu abinda jikinta yake, cixo ta galla masa a hannu ya buge bakin, ya dagata cak, cakumosa tayi tana jijjigasa cikin tashin hankali tana kuka tace "Ka fitar da ni daga gidan nan yanxun nn, ka fitar da ni nace, get me out of here" bata rufe baki ba ya kuma sauke mata mari da ya sa ta fara ganin duhu, ya shaketa, kasa cewa komai tayi don lkci daya taji numfashinta na sama, kamar wata yar baby ya dauketa ya wuce sama da ita, bai direta ko ina ba sai kan gadon bedroom din da ya shigar da ita, kin sakesa tayi ta rungumesa gam ko ina na jikinta na rawa cikin kuka mai taba xuciya tace "Don Allah don annabi don darajar iyayenka Elbasheer don't, wllh ni ba yar iska bace kar ka min haka ina rokon ka ka rufa min asiri I am a nobody" har wani daukewa numfashinta yake tsabar tashin hankali, da manyan idanuwansa da suka sauya kala yake kallonta ya turata da karfinsa har sai da ta fada kan gadon cikin Husky voice dinsa yace "Noo you must display that talent of yours na rashin kunya ga wa enda baki sani ba a media, 1st u called me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login