Showing 18001 words to 21000 words out of 34659 words

Chapter 7 - Sanadin Kawa Book 1 Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

207

amsa tana tambayarsa ya aiki, yace "Alhmdllh mama, ya mai jiki?" Tace "Alhmdllh mun gode Allah" Fatima ta kasa ci gaba da abinda take duk jikinta yyi sanyi, ajiye rariyar tayi ta mike da sauri xata wuce daki Ammi tace "Toh ki kawo masa ruwa koh" ta juya a hankali ta nufi gun da suke ajiye ruwa, ta dau cup ta debar masa ruwan, Ammi ta mike ta shiga ciki da cooler din da ta wanke, Fatima ta karaso fuskarta daure ta durkusa gabansa ta ajiye masa ruwan, xata mike ya rike tip din Hijab dinta, tsayawa tayi amma ta kasa kallonsa, jin bai ce komai ba ta dagota kallesa, kallonta yake, ya wara manyan idonsa yana nuna kofin ruwan yace "Is it clean?" A takaice tace "Ban sani ba" ya kai fararen hannunsa ya dauka ya kai baki, kadan ya sha ya ajiye cup din sannan yace "How you feeling?" Bata ce komai ba yace "Toh ci gaba da aikin ki" Tsaki tayi xata mike yace "Don't move, or I shock you" jigum tayi bata ce komai ba, can ta koma a sanyaye ta xauna ta ci gaba da tankaden da take yi, murmushi kawai yake yi shi kadai, can ya kai hannu cikin garin ya dangwala ya shafa mata a kumatun ta, kauda kai tayi ya kuma shafa mata a daya kumatun, hade kai tayi da gwiwa tana jin kamar ta rusa ihu, ya mike yana juya makullin hannunsa yace "Kice da mama na tafi" kofa ya nufa ya fita gidan, sai a sannan ta dago hawayen dake makale idonta ya sakko ita kam ya xata yi da ranta da mutumin nn dake bibbiyarta, bayan kusan minti biyar sai ga almajirai uku sun shigo gidan ko wannensu rike da foodstuff, xaro ido tayi ta mike tace "Daga ina?" Suka ce "A waje aka ce mu shigo da su" da sauri ta fita, buhun shinkafa ne da babban jarkan mangyada da na manja suka yi saura a waje, ta bi motarsa da har ya kusa barin layin da kallo, gabanta na faduwa ta juya ta koma ciki, tsaye taga Ammi tana kallon Kwalin taliya biyu da couscous da ke ajiye tsakar gidan tace "Wannan kuma daga ina" a d'an tsorace tace "Ammi nima gani nayi suna shigowa da su" Ammi tace "In ji wa?" Tace "Wannan mutumin da ya xo" Ammi ta mata wani kallo tace "Baki gaya masa kina da mijin aure bane?" Girgixa mata kai tayi kamar xata yi kuka, strictly Ammi tace "Toh maxa shiga ki kirasa ki sanar masa yanxun nan" da sauri tace "Ammi bai ce yana so na ba, kawai..." Ammi ta katse ta tace "Wuce maxa kiyi abinda na sa ki nace" juyawa tayi ta shiga ciki, ta dauko wayarta da ya kawo mata ranan ta kunna a karo na farko, bbu bata lkci ta nemo lambarsa ta yi dialing, katsewa yyi ya kirata, ta daga ta kai kunne, yace "Kin kunna wayar kenan?" Ta hade rai tace "Malam ka dawo ka tafi da sakon da ka aiko da shi yanxu" yace "Koh?" Tace "Eh" yace "Ohk, but nayi nisa yanxu, anjima da daddare xan dawo sai in tafi da su" tace "Better" daga haka ta katse wayar, ta xauna gefen katifa tayi tagumi, Lambar Umar tayi dialling jikinta a sanyaye, katsewa yyi shima ya kirata.

I don't understand why everyone is looking for Inteesar this days, na fara posting na shi a wattpad now.


KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association=ء?

(Home of Experts and perfect Writer's)



*SANADIN K'AWA*


NA


*khaleesat Haiydar*


BABI NA GOMA SHA HUDU




12




Amsa sallamarsa tayi ta gaishesa, yace "How you dear, where did u get a phone?" Shiru ta d'an yi kafin tace "It's mine" yace "But.... You didn't come back with it" ta kuma yin shiru, a hankali yace "Are you there?" Tace "Yeah, are you coming later" yace "Kina bukatan wani abu ne?" Ta girgixa kai tace "Noo, i just asked" yace "In sha Allah dear, xan xo after isha" tace "Allah ya kai mu" yace "Ameen baby" daga haka tace "Bye" bata jira cewarsa ba ta katse wayar. Bayan isha tayi wanka tana daki a kwance tayi nisa tunanin da take wayarta ya fara ring, mikewa tayi ta jawo wayar, sai da gabanta ya fadi ganin number Elbasheer, ta d'an yi jim sannan ta daga ta kai kunne, sallama yayi mata ta amsa, yace "Am outside" ta wani hade rai tace "Toh ni ce maka nayi xan iya kwasan kayan?" yace "Eh ki fito sai ku koma da wa enda xa su dauko kayan" Hija??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????b dinta har kasa ta sa sannan ta fita, dakin Ammi ta shiga ta sanar mata ana kiranta waje, tun da ta fito kofar gida take kallon motarsa, har xata koma ciki ta dauko wayarta ta kirasa sai kuma ta fasa ta karasa gun motar dake a rufe, bata ganin cikin motar saboda tinted glass din, ta jingina da motar ta rungume hannuwanta, sauke glass din motar yyi, ta hade rai tace "Ni baxan shiga ciki ba" yace "Magana xa mu yi, or shud I come out and help u in?" Tace "Baxan shiga ba nace" ya kusa minti daya yana kallonta kafin ya fito daga motar, ya tsaya daga side dinta ya rungume hannayensa shima "Ur dad is late?" Tambayar da ya jefo mata knn Ba tare da ta kallesa ba tace "It's none of ur business...." yayi murmushi yace "Really?" Bata ce komai ba, ya tabe baki yace "Idan baki bani amsar tambayoyina ba kin tuna irin daukar da na maki a gidana na kai ki bedroom, to irin sa xan maki ynxu in sa ki cikin mota" da sauri ta juyo tana kallonsa, ya shafa beard dinsa yace "Kuma ki gudu ciki in bi ki coz i knw dat wil be you next action" ya fada yana kallonta da kyau, kauda kai tayi xuciyarta na bugawa, yace "So now, ranan kince ke marainiya ce, you mean ur dad is late?" Ta xaro masa ido tace "Xaka dawo min da shi ne?" D'an murmushi yyi yace "Allah ya ji kansa" a can cikin xuciyarta tace Ameen, yace "His brothers, uncle, I mean relative in all, where do they stay??" Kamar ance ta juya taga Umar tsaye daga kofar gidansu looking at them, suna hada ido gabanta ya fadi sosai, lkci daya jikinta yyi sanyi, Elbash ya kalli direction din da take kallo, taku kalilan tayi ta isa inda Umar yake don bbu nisa tsakaninsu, ganin har lkcn kallonta yake tayi murmushin karfin hali a hankali tace "Sannu da xuwa" ya gyada mata kai shima da murmushin cikin sanyin murya yace "Thank you" xaunawa tayi kan dakalin da suka saba xama tace "Toh ka xauna" ba musu ya xauna, ta gaishesa ya amsa, har lkcn kallonsu kawai Elbasheer yake, Umar ya kasa cewa komai, mikewa tayi tana kallon Elbasheer tace "Meet my fiance Umar Ahmad" ta kalli Umar tace "Meet Elbasheer a brother of mine, nasan baka san shi ba coz I neva told you anything about him, let me make it brief, shi din yaron yayar Amminmu da na taba baka labari tana Yola ne, then when I was a baby, Ammi was sick, his mum, that's my big mum kenan...." Ta fadi tana nuna Elbasheer sannan ta ci gaba "Breastfed me during that period, I stayed with her till I was a year old kafin in koma gun Ammina, Elbasheer is married with 3 kids now, ynxu ta biyu yake shirin karawa" tana kai wa nan ta koma ta xauna, Umar ya mike yana kallon Elbasheer ya mika masa hannu yace "Ohh it's nyc meeting you Bro..." Elbasheer yyi wani irin murmushi yace "Sure it's nyc" daga haka ya basa hannu sannan ya juya ya shige motarsa ya tada yayi reverse. Fatima ta sauke ajiyar xuciya a hankali, har Umar yace xai wuce bata yarda ta bari damuwar dake xuciyarta ya fito fuskarta ba, kuma bata samu courage din gaya masa abinda tayi niyyar gaya masa ba, ta kuma lura shi ma kamar akwai damuwa tare da shi, don duk a sanyaye yake, duk yanda yyi da ita ta karbi kudin da yake mika mata kin karba tayi har ta wuce ciki, Daren ranan ta nemi bacci ta rasa ita kam sanadin k'awa ta jefa kanta ga halaka, ya xata yi Elbasheer ya fita rayuwarta, tunanin hakan yasa ta dinga kuka daga karshe ta fita ta dauro alwala ta dinga sallah har bacci barawo ya sace ta. Da safe tayi making mind dinta kawai ta amince Umar ya turo idan ya so bayan auren sai tayi masa bayani tasan shi din mai fahimta ne xai fahimce ta, kilan ta hakan kadai ne Elbasheer xai daina bibiyarta. Islamiyya ta koma da duk xuciyarta ba fashi, idan ta tafi tun biyu sai shidda da rabi take dawowa, bata yi mamakin daina xuwan Elbasheer ba don addu'a da tsayuwar daren da take yi duk na Allah ya rabata da shi baxai fadi kasa a banxa ba, kullum musamman don shi da Husnah take tashi yin sallahn dare, kuma Alhmdllh damuwarta ya ragu sosai, har tayi ma Umar xancen ya turo in 2wks time wanda hakan ya sa shi murna ba kadan ba. Yau ma kamar kullum ta fito gida karfe biyu saura sanye da hijab da nikab dinta don tafiya makaranta, ita kadai ke tafiya kan hanyar sai daidaikun mutane, 206 da ta hango daga can bayanta yana tahowa yasa ta tsaya, tun jiya da safe da take diban ruwa a waje ta lura da motar gashi glass din tinted baka ganin wanda ke ciki, yau kuma Wajajen Sha daya Ammi ta aiketa gun mai kayan miya taga motar batun da safe da ta fito bbu motar kuma duk layin su bbu mai mota, haka kawai taji gabanta na faduwa, ta tsaya motar ya wuceta tana karanto addu'o'i a xuciyarta, maimakon taga motar ya wuce kawai sai yyi parking, kasa motsi tayi a gun, aka bude motar ya fito, wani matashi ne ya fito motar, ya sakar mata murmushi yace "Sannu yan mata ina xuwa haka?" Ta hade rai tace "Matar aure ce malam" ya sa hannu a aljihu yace "Koh?" Bata kai ga cewa komai ba ha kalli left, right, back and front kawai ya rufe bakinta da handkerchief din ya bude motar ya turata ciki, atishawa ta dinga yi, lkci daya kanta ya fara juya mata. A hankali ta bude idonta ta dafe kanta da yyi mata nauyi, lkci daya ta mike xaune a firgice tana bin dakin da take da kallo, it look so familiar, rawa jikinta ya fara yi ta fashe da kuka tace "Wayyo na shiga uku na lalace" bude kofar dakin aka yi ya shigo, tana ganinsa ta ja baya ta takure waje daya jikinta na bari tace "Na shiga uku, don Allah don annabi kayi hakuri...." Ya karaso gabanta hannunsa rike da goran ruwa da glass cup yyi wani murmushi yace "maimaita abinda kika fadi ma saurayin ki ranan" ta toshe bakinta tace "Wayyo na shigo uku" ya mata wani kallo yace "Repeat it now" ta sakar masa kuka mai ban tausayi tace "Ina hada ka da Allah kayi hakuri, me kke so daga gareni ni dai na shiga uku, Husnah ta ja min, wllh ni ban san ka ba, ban taba sanin da kai a duniya ba, Husnah ta sa nayi following dinka a Ig ta takura min sai da na maka magana wllh duk ita ce ta sani komai ba yin kaina bane... Ni marainiya ce bani da kowa banda Ammina... Idan ma nayi maka komai ka yafe min kaji tausayina ka rabu dani don Allah" Tana kuka sosai ta kare maganar, yyi wani murmushi yace "I never knew you baby, you introduced ur life to me, ke kika shigar min rayuwa...." Cikin rawar murya tace "Toh kayi hakuri ka yafe min" Wani murmushi ya kuma yi ya bude ruwan hannunsa ya xuba a glass ya mika mata yace "Drink" ta girgixa kai da sauri tace "I am nt thirsty" ya jefa mata wani kallo yace "Karba ki sha nace" hannunta na rawa ta karba ta kai baki ta fara sha, bata sha da yawa ba ta mayar masa, karba yyi ta hade kanta da gado ta dinga kuka tana tausayin kanta, ranan da ta fara haduwa da Husnah har xuwa ranan da ta hadata da Elbasheer a media ta dinga tunani, taji duk ta tsani kanta yarda da biye ma k'awa da tayi, a hankali ta dago kanta jin an bude kofa, sauke idonta tayi har ya iso gabanta ya ajiye mata wani envelope, kallon envelope din kawai take, yace "Check it content" a hankali ta kai hannu ta dauka ta bude ta ciro abinda ke ciki, kasa daina kallon hotunan tayi lkci daya komai nata ya tsaya cak, "What?? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" abinda ta dinga maimaitawa kenan a rikice, yayyage hotunan tayi jikinta na rawa tace "Na shiga uku....." Ta fashe da wani matsanancin kuka, murmushi yyi yace "I have more of them, kuma copies din Umar yake kowa? Mind u.... I knw him so well, he is a biochemist, product of Buk, both Bsc and Msc, also staying at suleja...." Sakkowa tayi daga kan gado ta durkusa gabansa cikin tashin hankali tace "Don darajar iyayenka kar ka min hka, ka rufa min asiri kar ka min haka" tana fadin haka ta hade kai da tiles tana rusa kuka, tana Allah wadaran biye ma k'awa da tayi a rayuwarta gashi ta kai ta ga halaka ta lalata rayuwarta, durkusawa yyi yana kallonta yace "Then ki sallamesa da kanki ba sai ni nayi hakan ba"
[9/30, 5:45 PM] Itz B Y Ebrahm: KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association=ء?

(Home of Experts and perfect Writer's)



*SANADIN K'AWA*


NA


*khaleesat Haiydar*


BABI NA GOMA SHA HUDU




13



Kai kawai ta dinga gyada masa hawaye na sakko mata, yace "Good... Tashi in mayar da ke garin ku, there is still time for you to go to d islamiyya u intended going" ba musu ta mike ya nuna mata kofa, ta nufi kofar a sanyaye, ya bi bayanta, suna sakkowa downstairs ta jirasa bakin kofar parlon har ya karaso, suna hada ido ta dauke kai da sauri, ya bude kofar da makulli sannan ta fita tana goge guntun hawayen idonta, parking lot ya nufa ya bude mata front seat yana kallonta, taki yarda su hada ido, a hankali ta karaso tana share idonta ta shiga motar ya rufe, ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar aka bude masa gate ya fita, sai da suka hau kan titi murya can kasa yace "Am... am sorry for making you cry" ko kallonsa bata yi ba ta hade rai, yyi murmushi yana ci gaba da tukinsa yace "I was definitely on my own kika yi following dina a IG kika fara min rashin kunya....." nan ma dai ko kallon inda yake bata yi ba, bai kuma cewa komai ba sai da suka yi nisa sosai yace "Did you want to eat something?" Nan ma bata ce komai ba sai sabon hawayen da ya taru idonta, ya gangara gefen titi yayi parking yana kallonta yace "All this will surely come to an end one day fatima...." Ta fashe da kuka a hankali tace "Ni dai ka gaya min me kke so daga gareni, ka gaya min ko xan iya maka ka rabu da ni na har abada" kallonta ya dinga yi har na tsawon minti daya kafin, ya shafa sajensa murya can kasa yace "Kin tabbata xa ki iya yi min abinda nake so kuwa?" Ta share idonta tace "What again, after you've deflowered me, meye kuma kke so a guna da ya wuce wannan, that's all I have and you took it away, we are not rich, I have nothing again to give" ya girgixa kai yace "Noo, you are talking off hook, the question is straight, ce min kika yi me nake bukata daga gare ki, and I answered xa ki iya min abinda nake so?" A sanyaye tace "Meye shi" yace "Xa ki iya?" Cikin rawar murya tace "But I have nothing to offer you again, ni ba kowa bace" ya hade rai yace "Just answer my question xa ki iya?" Ta make kafada tace "In dai sa6on Allah ne ni ba xan yi ba" murmushinsa me kyau yyi yace "Ba shi bane" tace "Toh meye?" Yace "Xa ki amince?" Tace "Idan naga xan iya amincewa" yace "Noo its a deal" tace "Ina jin ka" yana kallonta cikin cool voice dinsa yace "Kawai ki amince in aureki, shi kenan abinda nake so daga gare ki" wani mugun faduwa gabanta yyi tayi kasake tana kallonsa ko kiftawa bbu, lkci daya ranan da ta fara following dinsa da intentions dinsu na following dinsa ya dawo mata a kai, lokacin da ya daina kulata gaba daya da yanda taji a lkcn duk ta damu taji duk duniya bbu Wanda take so sai shi, ko a mafarki bata taba tunanin akwai ranan da Elbasheer xai bude baki yace xai aureta ba, bata san lkcn da tayi murmushi ba don reverse is d case yanxu, duk duniya bata jin akwai Wanda ta tsana irinsa yanxu, yana juya wristwatch din hannunsa yace "Yeahh, I want to marry you not because you deserve me" tana kkrin mayar da hawayen da ya cika idonta tace "ko da kuwa kai kadai ne namiji da yyi saura a duniya wllh da amince in aure mugu mara tausayi kamar ka gwara na mutu ba aure, I hate you.... I hate d reason i met you, kar ka sake ce min xaka aureni don ni ina da mijin da xan aura kuma na fi karfinka...." Tana kai wa nan ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali, Kallonta kawai yake kafin yace "kika ce kin fi karfina? Did u knw it's a privilege in bude baki ince xan aure ki? Kinsan wanene ni?" Ta dago da sauri tace "Kwarai kuwa nasani, Elbasheer Ahmad kake ko wa? Wanda giyar kudi ke rudarsa ya kuma mance a nan aka samu kudin a nan kuma xa a bar su, macuci sannan kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login