Showing 15001 words to 18000 words out of 34659 words

Chapter 6 - Sanadin Kawa Book 1 Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

205

sauwake nace!" a hankali tana wasa da yatsunta tace "Ameen nagode" murmushi yyi ya nufi zaure bai kuma juyo ba har ya fita gidan.

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association=ء?

(Home of Experts and perfect Writer's)



*SANADIN K'AWA*


NA


*khaleesat Haiydar*


BABI NA GOMA SHA HUDU




10



A hankali Ammi ta mike tana kallon ta, Fatima ta kasa kallon inda mahaifiyarta take har ta iso kusa da ita ta juyo da ita a sanyaye tace "Fatima" sai a sannan fatima ta kalleta hawaye na sakko mata tace "Na'am" Ammi da ita ma hawayen farin ciki ya cika idonta tace "Alhmdllh, Allah mun gode maka" Xubewa nan kasa fatima tayi cikin rawar murya tace "Ki yafe min don Allah Ammi, I've failed u plenty times kiyi hakuri Ammi I have learnt my lesson" Ammi ta dago ta suka shiga dakin ta ta xaunar da ita ta goge hawayen idonta tace "Tel me what happened daughter kar ki boye min komai" shiru fatima tayi ta hadiye wani abu da ya tsaya mata a rai, is she to tel her mum that she went to Elbasheer's house and was raped by him? Ta girgixa kai hawaye na sakko mata tace "Noo" Ammi da ita ma hawayen ke xubo mata tace "No what, ki gaya min me ya faru ina kika je?" Ja baya fatima tayi don bata san abinda tace ya fito fili ba, Ammi ta kwantar da murya tace "kada ki ji komai Amira, tell me everything I am ur mother" gyada kai tayi da kyar tace "Husnah ce ta sa in je gidansu wani Instagram frnd dina Ammi, I....i never knew him...." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai tace "Don Allah don annabi Ammi kiyi hakuri" Ammi da lkci daya jikinta yyi sanyi ta dake tace "Ina jin ki" Cikin rawar murya Fatima ta ci gaba da gaya ma.mahaifiyarta abinda ya faru daga fari har karshe, bbu kuma abinda ta boye mata, ganin irin kallon da Ammi ke yi mata ta kasa ci gaba ta dinga kuka kamar an aikota, cike da karfin hali Ammi tace "Go on" ta hade kanta da gwiwa tace "Ni ban san abinda ya watsa min ba Ammi kawai na daina jin komai na daina ganin komai" Ammi da idonta ya sauya launi ta kasa cewa komai, tana shessheka ta ci gaba tace "Ban san abinda ya min ba Ammi, kawai dai har yanxu kaina na min ciwo har da cinyana" ta fadi hakan tana bude lap dinta, kusan waje biyu ne yyi ja a cinyar nata, Ammi bata iya tace komai ba sai hawaye da take sosai, can tace "Waye ya fita gidan nan yanxu?" Gaban fatima ya fadi ba kadan ba ta rasa abinda xata ce, da kyar ta nemo abun cewa cikin rawar murya tace "Shine ya gan ni a hanya ya dawo da ni gida" Ammi ta mike tana mata wani kallo tace "Ba baki nake maki ba Amira, amma ke kam kinyi hasara kin cuce kanki kin yaudara kanki, saboda bin umarnin k'awa kika je kika yasar da mutuncin ki a titi, kuma in dai ni Amina ina numfashi baxan taba barin a cuce Umar ba, wllh yafi karfin ki nesa ba kusa ba ynxu yanxu, don haka maxa ki san inda dare yyi maki" Ammi na kai wa nan ta fita daga dakin. Har magrib fatima bata daina kukan da take ba a dakinsu, duk taji ta tsane kanta, ta tsani Elbash, ta tsani Husnah, ji take kamar a dauke ranta ta huta, a haka Umar ya shigo gidan, da da ne Ammi xata ce ya shiga ya dubata amma yau bata yi masa tayin hakan ba har ya gama xamansa tsakar gida tare da ita suna hira jefi jefi kafin ya bar gidan shi ma duk a sanyaye yake rashin ganin fatiman. Washegari da xaxxabi sosai ta tashi ga kanta dake mata axaba kamar xae tsage har lkcn kuma sai dai bata tashi ba amma tana tashi sai jiri ya kusa kwasheta, har rana ko leko dakin Ammi bata yi ba, da kyar tayi karfin halin fita ta yi wanka ta wanke baki ta dauro alwala ta koma daki tayi sallah, xuwa yamma banda rawar sanyi bbu abinda take, Ummi ta shigo tace ana kiranta a waje, Hijab kadai ta iya xurawa kan xani da ves dake jikinta tayi karfin halin fitowa tsakar gida, Xaune yake kan tabarmar dake a shimfide ya tankwashe kafa, fararen hannunsa rike da makulin mota yana jujjuyawa, tun da ta fito yake kallon ta ko kiftawa babu, Ammi dake bakin murhu tana duba girkinta ko kallon Inda take bata yi ba ta mike ta nufi daki, ita kam tsaye tayi bakin kofa xuciyarta na bugawa ga wani jiri da take ji na neman kada ta tun da ta kallesa sau daya bata sake kallon inda yake ba, ita dai ta shiga uku, me kuma ya sake dawowa yi, tunanin hakan yasa hawaye cika idonta, what did this man still want from her? Elbash ya juya ya ga har Ammi ta shiga daki, lkci daya ya mike ya nufeta, kawai ganinsa tayi gabanta, bbu abinda ya taho memory dinta sai ranan da ta fara ganinsa a gabanta a can gidansa sai take ga kamar abinda ya faru ranan ne xai sake maimaita kansa, bai ankaraba sai gani yyi ta yanke jiki tun kan ta kai kasa yyi saurin rikota yana mata kallon mamaki, Kan tabarma ya ajiye ta ya nufi buta da ya gani ya dauko ya debi ruwan ya shafa mata a fuska, a hankali ta bude ido ta mike xaune da sauri ta takure waje daya jikinta na rawa tace "Kayi hakuri plss, stay away from me am begging you" bai ce komai ba, ita kam har lkcn jikinta bari yake, ya fi minti daya yana kallonta kafin ya mike, dai dai fitowar Ammi, yayi kasa da murya yace "Mama tana xaxxabi ne sosai ko xa mu je asibiti" Ammi tace "A'a daxu likita ya xo duba ta ai" yyi shiru kafin yace "Faduwa tayi yanxu, da dai muje asibitin" Da alama Ammi bata son musu da shi don daga karshe ce masa tayi toh, tare da Ummi suka wuce asibitin, ita dai fatima har lkcn a tsorace take har suka isa wani asibitin kudi, ya juya yana kallonta fuska daure don da kyar ta yrda suka taho, hawaye ya cika idonta tace "Don Allah kayi hakuri nasan allura xa a ce xa min, ni kuma ina tsoro, am fine pls" tun da ta fara magana idonsa ke kanta, ta sa hannu tana share hawayen idonta, yace "Amma ranan da na maki can gida baki samu bakin cewa ba kya so ba" da sauri ta kallesa, ya hade girar sama da ta kasa yace "Ina ke maki ciwo yanxu?" girgixa kai tayi tace "Ba ko ina" yana kkrin bude kofa yace "Okay to mu je su dubaki" tace "A'a don Allah kayi hakuri" ya juyo yace "Then tell me what's making u sick" tana goge idonta a hankali ta hade hannayenta biyu tace "I want you to stay away from me pls, kar ka sake xuwa gidanmu ina hada ka da girman Allah" muryarta na rawa ta kare maganan, yyi shiru yana kallonta, ta hade kanta da gwiwa tana kuka a hankali, bai ce komai ba ya tada motar ya fita harabar asibitin, wani babban pharmacy ya nufa, ya siya mata drugs sannan ya dau hanyar gidansu, suna isa kofar gida ya kalli Ummi dake bayan mota yace "Ya sunanki" tana wasa da yatsunta tace "Ummi" yyi murmushi yace "Wani class kike?" Tace "Primary 6" yace "Good" ledan maganin ya mika mata ya ciro dubu daya ya kara bata yace "Kai mata maganin gida, wnn kuma ki siya biscuit" maganin kadai ta karba yace "Take the money" still bata karba ba ya kamo hannunta ya sa mata sannan ya ce "To shiga gida" ba musu ta bude motar ta fita, Fatima xata fita ita ma ya rikota, juyowa tayi tana kallonsa, sosai gabanta ya fadi, tayi saurin sauke idonta ta warce hannunta daga nasa, dage glass din motar yayi, a tsorace ta xaro ido tace "A'a don Allah ka bude min in fita plss ka bude" har lkcn yana kallon kwayar idonta yace "Me yasa xan daina xuwa gidan ku?" Ta hadiye abu da kyar tace "Aa toh ka dinga xuwa" murmushin da ya bayyana beauty point dinsa yyi ya kamo hannunta a hankali yace "Ke kika nuna min hanyar gidan naku ai kuma xa ki ce in daina xuwa" ta ki daga kanta, ta kwace hannunta a hankali, shiru yyi na kusan minti daya yana kallonta, jin shirun yyi yawa ta dago tana kallonsa, shafa beard dinsa yyi yace "What exactly is making you still sad?" Bata fuska tayi sai kuma ta fashe masa da kuka, da mamaki yake kallonta, muryarta na rawa a hankali tace "You took away my pride, you raped me" kallonta Kawai yake kafin yace "You brought the pride to my door step, ke kika kawo min kanki har gida" hade kanta tayi da gwiwa tana kuka sosai, sai da tayi me isarta ta dago ta rike kofar motar cikin rawar murya tace "Ka bude min" bude lock din yyi ta bude motar ta fita, ya bi ta da ido har ta shiga gida.

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association=ء?

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU

11

Cikin dare bata jira shawarar kowa ba ta mike ta dau maganin da Elbasheer ya siya mata ta sha don wani mugun xaxxabi take ji, har kusan asuba bata yi bacci ba sai bayan da aka yi sllh taji dama dama sai a sannan bacci ya dauketa. Da safe ko kafin ta fito Ammi ta gama duk aikin gidanta, jiki ba kwari tayi wanka ta wanke baki ta tafi daki ta shirya sannan ta fito ta debi kunu kadan ta sha ta kuma shan magani ta kwanta. Yau ma kamar jiya haka aka dinga xuwa ana ma Amminta jajayen dawowarta duk kuma me son ganinta sai dai ya leko daki ta gaishesa ya wuce, ciki har da yan uwan mahaifinta duk sun xo, da rana Ummi ce ta kawo mata Danwake, yunwan da take ji yasa ta cin kadan a cikin danwaken, ko minti biyar bata yi da tura plate din ba amai ya taho mata, a nan tsakar gida ta dinga kwarara aman, ko kallon inda take Ammi bata yi ba, can kuma ta mike ta wuce daki, dai dai shigowar Nafisa gidan, da sauri Nafisa ta nufeta tace "Subhanallahi sannu Fatima" ita ta taimaka mata ta kawo mata ruwa sannan ta wanke gun aman, daga ta tayi suka nufi daki, ta durkusa kusa da ita tace "Sannu Fatima, jiya da rana da na xo kin fara bacci ban tashe ki ba na wuce ya jikin?" Fatima ta mike xaune tana kokarin maida hawayen idonta tace "Da sauki" Nafisa tayi tagumi tace "Wllh ban san abinda ya faru ba knn sai jiya Murja ke gaya min" shiru Fatima tayi, can ta kalli Nafisa dake kallonta da tausayi cikin sanyin murya tace "Nafisa na cuci kaina, had it been I didn't neglet any of ur advice all this wouldn't have happen to me" Nafisa ta kamo hannunta da damuwa tace "Don't worry besty, we do always learn from our mistake, Alhmdllh tunda kika dawo gida lafiya" Fatima ta fashe da kukan takaici tace "Not this type of mistake Nafisa, I was raped...." Ja baya Nafisa tayi da mugun mamaki tana kallonta, kuka ta sakar mata ita ma tana kallonta tace "Innalillahi, How?" Where?" Fatima ta hade kanta da gwiwanta tace "Husnah.... She ruined my life, had I known..." Hawaye na sakko ma Nafisa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" bbu abinda Fatima ta boye mata tun daga farkon haduwarsu da Elbash har karshe, yanda take kuka haka Nafisa ke kukan, daga karshe ita ta daina kukan ta dinga lallashin Fatima har ta samu ta nutsu, Nafisa tace "Baki ce masa kada ya sake xuwa gidanku ba kuma?" A sanyaye Fatima tace "Tsoronsa nake ji, har ce min yake xai gaya ma Ammi abinda ya faru" Nafisa ta hade rai tace "Toh ya fadi mana, duk ya sake dawowa wllh kiyi masa koran da baxai kara tuna hanyar gidan nan ba, macuci da shi" Fatima dai tayi shiru bata ce komai ba amma har lkcn hawaye ya kasa daina sakko mata, cikin rawar murya tace "Toh don Allah ki gaya min yanda xan yi da baxai sake dawowa ba, wllh tsoronsa nake ni Nafisah" Nafisa tace "Tara masa jama'a xa ki yi idan har ya sake dawowa" Nafisa bata bar gidan ba sai kusan magrib bayan ta tabbatar ta kwantar ma kawar tata hankali, ta kuma bata duk shawarwarin da ya kamata. Washegari da safe ta fito tsakar gida, ganin Ammi bata gama aiki ba ta fara hada kwanuka xata wanke, Ammi dake shara tace "Ni ban sa ki ba, ki tafi ki shirya mu wuce asibiti yanxu" Har suka isa asibitin kusan karfe goma Ammi bata ce mata komai a napep ba, amma kana ganinta kasan tana tare da damuwa sosai, duk jikin Fatima yyi sanyi sanin ita duk ta sa mahaifiyarta a damuwar nan, duk iya kokarinta na ganin bata bar hawayen dake makale idonta ya sakko ba ya tashi a banxa don hawaye sosai ta dinga yi har aka xo kansu a ganin likita, series of tests aka yi mata bayan Ammi tayi ma likitan bayanin komai wanda sai da ta kashe ya fi dubu takwas a take, daga karshe magunguna aka hada mata da allurai bayan an tabbatar bbu wani matsala, aka kuma basu lokacin da xa su dawo a sake mata tests din sannan suka wuce gida. Bayan kwana biyu fatima na debo ruwa da yamma daga tap dake kusa da kofar gidansu kasancewar bbu ruwa gidan kuma Ummi na makaranta, Ammi dake girki a tsakar gida tace "Ki bar ruwan haka nan" Fatima tace "A'a ya kusa cika Ammi yanxu xan gama" daga haka ta fita, xuwa lkcn bbu laifi Ammi na kulata sosai kuma tana jan ta jiki, wanda hakan yasa ta fara mance komai, gashi kuma Elbash din bai sake xuwa gidansu ba, yanxu dai damuwarta Umar, tasan baxata taba aurensa ba kamar yanda Ammi ta gaya mata a baya, ko da Ammi bata fadi hakan ba ita dama ta kudira a ranta baxata iya aurensa ba kuma don bata san da idon da xata kallesa ba, tana kkrin daukar ruwanta da ya cika taga mota ya shigo layin, tun daga nesa ta dinga kallon motar har ya iso kofar gidansu yyi parking gaba da inda take, lkci daya kuma ya bude motar ya fito, sanye yake da Gezna sky blue dake ta faman kyalli, ya rungume hannayensa yana kallonta, gabanta yyi mugun faduwa tayi saurin dauke kanta tana kiran Allah a xuciyarta, nufota yyi ya tsaya dai dai inda take yace "Wannan katon bucket din kike dagawa superwoman?" Hade rai tayi ta juyo tana kallonsa tace "Malam ka fita rayuwata na hadaka da Allah, stay away from me, I hate seeing you, ka fita rayuwata ka kyaleni" a tsawace ta kare maganar cikin fushi, kallonta kawai yake kafin yace "Ohh really?" Tsaki ta ja ta juya xata dau ruwanta ta wuce ciki yace "Toh wai ma na ce maki gun ki na xo?" Wani kallo ta watsa masa yyi wani murmushi yace "Rashin kunyar dai?" Bata tanka sa ba ta dau ruwanta da sauri ta wuce ciki, tana juyewa ta shiga daki ta xauna ta dinga rusa kuka, ita kam ta shiga uku Husnah ta ja mata, har aka kira magrib tana daki, daga bisanni ta fito a sanyaye ta daura alwala ta koma ciki, tana idar da sllh ta shiga wanka. Bayan ta gama shiryawa ta sa hijab ta wuce dakin Ammi, Ammi da ke kan darduma ta bi ta da ido har ta xauna, Fatima tayi kasa da kanta a hankali tace "Ammi don Allah ina son xuwa gun Umma a Kaduna" Ammi dake ta kallonta tace "Saboda me?" Kasa dagowa tayi sbda hawayen da ya cika idonta, Ammi tace "Tell me ur problem Amira" hade kai tayi da gwiwa cikin rawar murya tace "Ammi bana son in xauna nan kuma, don Allah ki bar ni in tafi" Ammi da jikinta yyi sanyi tace "Fatima" sai a sannan Fatima ta dago tana kallonta, ta nuna mata kusa da ita ta dawo, Ammi tayi kasa da murya tace "Ki gaya min meye damuwar ki har yanxu? Ba nace kada ki sake sa ma kanki damuwa ba" A hankali tace "Ammi ni ma ban san me yasa nake haka ba" Ammi tace "Ki dinga azkar din ki kan lokaci ki kuma dage da karatun Qur'an kin ji" ta gyada ma Ammi kai sannan tace "Baxan je ba kuma Ammi?" Ammi tace "Bani da kudin mota yanxu, ki bari sai na samu kudin" a hankali tace "Toh Ammi nagode" sannan ta mike ta fita dakin ta koma nasu. Yau Friday Fatima na xaune tsakar gida tana yi ma Ammi tankade tayi nisa gun tunanin abinda xata gaya ma Umar ya rabu da ita ba tare da yasan komai akan abinda ya sameta ba, cikin kwanakin nan tausayinsa take ba kadan ba, kusan duk dare sai ya xo gashi ta rasa ta inda xata fara hakan yasa ta shiga damuwa sosai, yau kam ta dau kudurin dole ta sanar masa ya nemi wata kawai. Washegari ta yi iya kokarin ganin ta kauda duk damuwar ranta har yamma, Ammi dake wanke wanke tana lura da ita tace "Tunanin me kike?" Da sauri ta dago kan ta ce komai wani yaron makwabta ya shigo wai ana sallama a waje, Ammi ta sa Hijab tace "Toh a shigo" Fatima sai kallon kofar xauren take taga wanda xai shigo, da sallama ya shigo gidan hannunsa rike da makullin mota, sanye yake da shadda milk kala, kallonsa kawai take ko kiftawa bbu, ya karaso yana kallon Ammi da ta amsa masa sallamar sa ya xauna gefen tabarma da fatima ke xaune ya gaisheta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login