Showing 3001 words to 6000 words out of 34659 words

Chapter 2 - Sanadin Kawa Book 1 Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

212

bafillatani da tsayinsa, a Kano yyi Bsc dinsa a fannin Biochemistry, yyi masters kuma a medical Biochem, aiki da bai samu ba tukun yasa yake kasuwancinsa a nan Suleja don family house dinsu na nn, sun hadu da shi ne tana ss1 lkcn ma bai gama karatu ba, ita kanta tasan son da Umar ke mata ya wuce misali ita ma a da tana sonsa sosai amma tunda taga kalan motar saurayin sa'adatu taji duk duniya bbu wanda bata so kamar shi, a da bbu wanda ke mata kyau a maxa kamar shi, amma tun da Husnah ta fara nuna mata wayayyun maxajen IG taga ashe ba ma shi da wani kyau, Elbash ya fi sa kyau da wayewa nesa ba kusa ba, ta turo baki ta rungungume hannu tace "Gani" a hankali yace "Ya jikin?" Tace "Na ji sauki" yace "Allah ya sauwake, ya Ammi fa?" Tace "Tana lafiya" yace "Toh ki gaishe min ita, Xan fita kasuwa ne, just want to check on you" tace "Nagode" dubu biyu ya ciro ya mika mata yace "i wanted getting some fruits for you but it's too early ba su fito ba, gashi ki aiki su Ummi su siyo maki anjima" tace "A'a ka barsa naji sauki ai, thank you" yace "No take it pls dear" ta d'an yi jim kafin ta risina ta karba tace "Nagode" yyi murmushi yace "No thanks baby" juyawa tayi tace "Sai anjima" daga haka ta shiga gida, sakonsa na gaisuwa kadai ta ba Ammi sannan ta wuce dakinsu ta boye kudinta. Bayan an sakko sallar Juma'ah fatima tace ma Ammi xata je gidan wata kawarta da tayi aure Safia, da kyar Ammi ta bari taje kasancewar bata barta taje bikin ba sbda su Husnah, hijab dinta har kasa ne jikinta ta fita gidan sakale da jakarta, ta samu adaidaita ta hau, tana kallon suka wuce hanyar gidan Safia ta turo baki ta kauda kai, sai da ta kai inda xata je ta fito ta basa kudinsa ta shiga gidan, duk da kasancewar gidansu d'an karamin gida da mahaifinsu ya rasu ya bar masu gidan ya fi na su Husnah nesa ba kusa ba, Tsakar gidan kaca kaca ga kwanuka da kaya ta ko ina, Inna mahaifiyar Husnah na xaune tsakar gida tana yankan awara dafaffe, ta duka har kasa ta gaisheta, ta washe baki tace "A'a Fatima daga ina haka" tace "Daga gida Inna" Inna tace "Ikon Allah, Ya su Amina?" Tace "Suna lafiya inna, Husnah na nan?" Tace "Wllh kinga tun safe ta fita ban ma san inda tayi ba, amma nasan baxata wuce anguwar nan ba, ki kira lambarta" nace "Toh" tace "Ki shiga dakinsu ki xauna" mikewa tayi ta nufi dakinsu Husnah na shiga, ita dai tasan a responsible rat will not live in that room don bayan datti, untidiness har da wari yake, ta raba na xauna gefen katifarsu da yyi dukun dukun ta shiga kiran layinta kasancewar tana da sauran bonus, bugu biyu ta dauka tace "Mara kirki sai yau xa ki kirani bayan ko asi bani da shi tun ranan da na bar gidan Ku" Fatima tace "Ke ina fa gidanku ina kika je?" Tace "Kaji ta, ke din ce xa ki xo gidanmu" Fatima tace "Kinga ni ba wani kati me yawa gareni ba, wllh ba wasa nake ba, Inna tace tun safe kika fita" cike da farin ciki Husnah tace "To to Gani nan xuwa ban yi nisa ba" daga haka ta katse wayar, Fatima ta tabe baki, kafin minti goma sai gata ta shigo dakin ta rungume ta tace "Wayyo Ashe da gaske ne, welcome besty" Fatima na kallonta tace "Ina kika je tun safe" Husnah tayi kasa da murya tace "Kinga saurayin Sajida ne yace xai kai mu outing yau, tun safe muke jiransa har yanxu shiru ni har na fidda rai Wllh kilan ma karya ya shirga mata" Fatima tayi dariya tace "Kuna da aiki, ni ba wannan ba, kinsan wnn Elbash din yyi following dina back har mun yi chat" Husnah ta xaro ido tace "Kice Wllh" Fatima ta fashe da dariya tace "Wallahi" wani uban tsalle ta doka tace "Bani in sha kawata, garin yaya" Fatima na murmushi ta bata wayar bayan ta bude IG dinta ta shiga DM dinta da Elbash, Husnah ta nutsu tana karanta messages din, lkci daya ta hade rai tace "My God, to ai tsokanarsa kike ta yi Fatima, dubi fa irin maganganun da kike ta gaya masa marasa dadi" Fatima tace "Uhm ai d'an rainin wayo ne shi yasa nake basa amsa dai dai shi" Husnah ta dafe kai tace "No that was not our plan fa besty, ke da xaki dinga lallabasa" Fatima tace "Tabdi, ya raina ni kenan, ke bari kiji yanda yake jin kansa fa nima haka nake jin nawa kan" Husnah ta fashe da dariya tace "Ke a wa" ta hade rai tace "Ni a mutum" Husnah tace "Yanxu har yace ki basa photo ki ki, haba Fatima you want to spoil d plan kenan" Fatima tace "Ke dadi na da ke baki da jan aji wllh" Husnah ta saki baki tace "Jan aji a wannan xamanin, ai kam xa ki ja har ya tsinke Wllh" Dariya Fatima tayi tace "Koh" Husnah tace "Wllh da gaske, yanxu don Allah ki tura masa hoton" Fatima tace "Tabdi bayan nace masa A'a" Husnah tace "Wllh sai kin tura, to don me dama nasa kika yi following dinsa tun farko" daga haka ta dau waya tace "Bari in duba gallery din muga ko akwai hot pics" tabe baki tayi bayan ta dudduba tace "Ba background me kyau a hotunan, jira akwai wata da muka hadu a IG kusan shekara daya kafin wayata ta lalace, yar masu kudi ce Wllh, idan kika ga gidansu sai kin yi suman tsaye, kinga irin flowers da motocin gidansu kuwa, kusan duk sati sai na je gidan Wllh, amma fa da nisa daga nan don kusan dari uku ne kudin mota xuwa da dawowa, yanxun ma can xa mu je kiyi hoton har kaya ma xata iya ara maki na sani, Allah yasa kin fito da kudi don ni ko taro bani da" Fatima ta saki baki tace "Husnah???" Mikewa Husnah tayi ta dagata tace "Dallah muje kada yamma yyi" daga haka suka fita tace "inna bari mu je gidan wata kawarmu mu dawo yanxu" Inna tace "Toh Allah ya kiyaye hanya, A kula da titi, Fatima kar fa ki wuce daga can ki dawo ki kai ma mamarku awara" Fatima tace "To inna na gode" daga haka Husnah ta ja ta suka fita gidan xuwa inda xa su hau mota.
[9/18, 8:37 AM] Abue Saleh Kurami: KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association=ء?

(Home of Experts and perfect Writer's)



*SANADIN K'AWA*


NA


*khaleesat Haiydar*


BABI NA GOMA SHA HUDU




3






Duk yanda Fatima ta so hana Husnah su je gidan warce ta kira da kawarta kin saurarenta tayi haka ta tilastata sai da suka hau mota suka dau hanyar gidan kawarta da suka hadu da a IG me suna Sadiya, Allah ya so ta fito da kudin da Umar ya bata daxu da safe, Tafiyar kusan minti talatin da wani abu suka yi kusa da cikin garin Abuja kafin su iso gidan, sun dade bakin gate don sai da mai gadi yaje ya sanar da xuwansu kafin su shiga gidan, tunda Fatima taga irin kallon da yan gidan ke ma Husnah jikinta yyi sanyi kana gani kasan sun gaji da xuwanta, Sadiyar ma sama sama ta kula su bayan ta fito kafin ta kawo masu ruwa da kayan flour, tuni Husnah ta sauka kasa ta fara cin abubuwan dake gabansu, Fatima ta ki cin komai don duk ranta ya gama baci, Sadiya dai na xaune tana kallo a Tv don duk yan gidan da suka tarar a parlor sun bar parlorn, Husnah ta cika baki da cake ta ce "Kawata mun xo neman wata alfarma ne gun ki don Allah...." Sadiya ta kalleta tace "Toh ina ji" Husnah ta kora cake din da drink ta mike tace "Toh ina xa mu je muyi maganan?" Tashi Sadiya tayi ta fita balcony Husnah ta bi ta tana kashe ma Fatima da ta hade rai ido, bayan sun fita nan ta gaya mata abinda yasa suka xo, har da risinawarta tana roko, Sadiya da ta d'an yi jim tace "Har da kaya?" Husnah tace "Hoto kawai xata yi wallahi" Sadiya tace "Shkkn ba matsala" amma kana jin ynda tayi furucin kasan takaici ne ya isheta, dakin mai aikinsu ta kai su, Husnah na rike da hannun fatima da taki sake fuska tana bin ko ina na dakin da kallo tana cewa maa sha Allah, Allah ka bamu irin haka, suna ta xaune dakin sai ga Sadiyar ta shigo da kaya hannunta da abun kwalliya, nan ta mika ma Fatima kaya na Riga da skirt da kayan kwalliya da mayafi, ta juya xata fita Husnah tace "Ki yi hakuri ki d'an ara mana wayar ki xai fi kyan hoton kuma xa mu yi wasu a nan" Sadiyar ta kalleta sannan ta xauna dakin tace "Toh idan kun gama sai in mata" har Husnah ta gama yi ma Fatima kwalliyar kallonsu Sadiya take, a xuciyarta kuma addu'ar shiriya da Allah ya raba su da karya take barin Fatima da ta yi mata kyau sosai, ba laifi Husnah ta iya make up sosai don ba karamin kyau Fatima tayi ba duk da bata yrda ta cika mata kwalliyar ba, Sai washe baki Husnah take ganin yanda ta fito da kawartata, ta juya ta kalli Sadiya tace "Toh dauketa hoton kawata" nan Sadiya ta mike don daukar Fatima hoton, sosai Fatima tayi mata kyau sai dai taki sakin fuska, kusan biyar ta dauketa a daki, Husnah tace "To ya isa haka mu je waje" tana rike da hannun fatima suka fito compound, nan ma sadiya ta dinga mata hotunan, Husnah na nuna masu background, sae jaraba take wai fatima ta tsaya dososo taki murmushi, Fatima ta galla mata harara tace "Ke kar fa ki dameni wannan din da nake fa, ni na ma gaji ki rabu dani" ba shiri Husnah ta ja bakinta tayi shiru, Sadiya dake ta kallonsu ta d'an yi murmushi tace "Toh wannan na karshen dai ki daure ko dariya kiyi xae yi kyau sosai" Fatima bata san lkcn da tayi dariyar ba a haka Sadiya ta dauketa Wanda duk hotunan babu Wanda ya kai sa kyau, Husnah sae murna take, a nan kuma aka gama daukar hotunan suka koma ciki Sadiya ta tura masu duk hotunan a wayar Fatima, Fatima ta mayar da kayanta ta linke na Sadiya ta ajiye tana kallonta tace "Sister nagode sosai" Sadiya tace "A'a ki tafi da su na bar maki" nan Husnah ta canxa fuska sae dae bata ce komai ba, sai da suka tashi tafiya tace "To ni baki bani kayan ba Sadiya ko na maki wani laifi ne" Sadiya ta yi murmushi tace "Bari in dubo maki to" daga haka ta tafi dakinta ta dauko mata wani kayan ta bata, Husnah ta dinga godiya har da durkusawa tana washe baki, Fatima da takaici ya isheta ta fice daga dakin suna biye da ita, a bakin gate Sadiya ta basu dubu daya kudin mota Fatima ta mata godiya ta fita ta bar Husnah dake ta godiya kamar wata marokiya ta dau hanyar titi, da gudu Husnah ta kamota tace "Kinga masu kirki koh, kuma ace duk sati baxan dinga xuwa nan ba, ko don irin cimarsu ni bbu Wanda ya isa ya hanani xuwa wllh" Fatima dai bata tanka ta ba har suka shiga mota xa su koma Suleja. Sai kusan karfe biyar da rabi suka isa gidansu Husnah, Fatima da duk hankalinta ya gama tashi tace "Kinga baxan shiga ba xan samu adaidaita daga nan in wuce gida nasan Ammi na can tana jirana na dde sosai, sai mun yi waya" Husnah ta rikota tace "Toh amma banda masa bakar magana plss, ki kara editing hotunan ki tura masa masu shegen kyan ciki plsss ki rufa mana asiri mu ma mu faso gari kwanan nan" Fatima tace "Naji ni dai sai mun yi waya" daga haka ta wuce da sauri ba tare da ta damu da dubu dayan da aka basu da Husnah ta boye a jaka tun daxu ba, adaidaita ta samu ya kaita har kofar gida, Ammi dake tuka tuwo tana xaune kan kujera kusa da coal pot bata ko amsa sallamarta ba, a sanyaye ta durkusa nesa da ita tace "Don Allah don annabi Ammi kiyi hakuri nasan na dde sosai, kinga dambu tace in tsaya in koya mata bata iya ba kuma shi xata yi, shine kawai na tsaya na girka mata, kiyi hakuri Ammina" Ammi ta kalleta tace "Toh ni na ce maki wani abu ne Fatima" Fatima tayi shiru bata ce komai ba, Bude ledan da ta shigo da tayi ta fiddo kayan ciki da mayafi tace "Gashi Ammi ta bani, nace ta bari na gode amma ta ki saurarana" Ammi tace "Allah ya saka da alkhairi" Fatima ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "Ameen" sannan ta mike ta shiga cikin dakinsu tana murmushi. Ita ta karasa sauran aikin gidan Ummi na taya ta, suna gamawa ta daura ruwan wanka ta koma daki, sae kusan shidda ta fito tayi wankan ta daura alwala ta shiga daki, Ta gama shafe shafenta ta saka doguwar riga ta dau wayarta ta hau saman gado ta bude data, IG ta shiga ta duba DM dinsu da Elbash taga har lkcn bai ce komai ba, ta d'an yi jim, sai kuma ta tura masa "Are you ready to listen to why I followed you and went ahead to ping you?" Daga haka ta fita ta koma WhatsApp, sai da taji kiran sllh ta kashe data ta mike, tana idar da sllh tayi azkar dinta sannan ta fita xuwa dakin Ammi, Ammi dake xaune Da Ummi da Yusuf suna cin abinci ta kalleta, xaunawa tayi gefen Ummi, Ammi dai bata ce mata komai ba tana jiran ta ji me ya kawota sanin bata shigowa sae idan abu ya kawota, Ita kanta she was uncomfortable can kuma ta mike xatah fita Ammi tace "Kin ci abincin ne?" Fatima ta kalleta tace "Shi xan je in ci ynxu" Ammi dai bata ce mata komai ba har ta fita, ta rasa irin yar tata, bata taba ganin yar da ke kin sakewa da uwarta kamar Fatima ba, Fatima ta debi tuwo kadan da miyar kubewa ta saka cokali ta wuce daki, har ranta ta tsani cin tuwo, ta gama jagwalgwa shi ta tura gefe ta dau wayarta ta bude datan ta, message din Elbash ta gani yace "I am not interested" tsuru tayi tana kallon message din, can tayi murmushi tace "is that so??" ya bude message din yaki cewa komai, bayan kusan minti sha biyar tace "u knw something I already knew about you even before chatting u up?" bayan wani lkci yace "That's ur cup of tea..."
[9/18, 8:37 AM] Abue Saleh Kurami: KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association=ء?

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

4

"And yours also" ta mayar masa tana murguda baki, har xata kashe data ranta a bace sai ga wani message din nasa "Where did you leave" xaro ido tayi, can tayi murmushi tace "Abuja" yace "Where in Abuja" dariya tayi ta tura masa da cewa "That's my cup of tea alone" ga mamakinta sai yace "Hmm" ta lumshe ido ta bude a hankali ta rasa abinda xata ce masa, can tace "Though it won't be of any use to you I live at Maitama, bye.... catch ya later, I've gat to do better things now" daga haka ta kashe data ta jona wayarta da caji ta fita tayi alwala ta dawo tayi isha ta kwanta ranta fari fes. Washegari tana idar da sllhn asuba ta fita don hura charcoal, ta daura ma su Ummi ruwan wanka, kafin karfe bakwai kaninta sun bar gidan xuwa islamiyya, Tana wanke kwanukan da aka yi amfani da su Ammi da ta fito daga daki rike da tsintsiyar da ta share dakinta tace "Yau baxa ki islamiyyar bane ke?" Ta hade rai tace "Ammi baxan je ba, ko na je malam Suraj cewa xai yi sai na koyar yau" Ammi bata ce komai ba ta kwashe kayan su Yusuf dake kan igiya ta wuce daki, Fatima ta gama wanke wanken ta shiga wanka bayan ta daura ruwan da ta daura a coal, doguwar Riga ta sa ta saka hula, duk da hali na rashi dake tare da su hakan bai hanata tsafta ba, ko da yake kusan gun Amminsu suka gado tsaftar, Komai na gidan xaka gansa tsaf tsaf, sutirarsu kuwa ko wasu masu kudin sai haka don tsaf xaka gani, Fatima bata taba sa kayan da bai da guga hakan yasa ko ina taje ake sha'awarta ta fi da yawa daga kawayen da take bi nesa ba kusa ba, shayi ta sha bata kalli bread din ba sbda bata damu da shi ba, ta dau wayarta ta hau net, murmushi tayi ta kwanta saman gado tana kallon message din Elbash "I won't ask for this again, can I see u facially" gun tura photo tayi tap ta shiga gallery dinta daya daga hotunan da Sadiya tayi mata ta xaba, tsaye take kusa da flowers a gefen parking space, full tayi mata hoton Wanda hakan ya fito da ainahin shape dinta da tsayinta, I don't want to waste time describing Fatima but just get this, she is a damsel, she's more den beautiful, komai na mahafiyarta da dauka, tsayin haske kyau, gashi beauty point, tsayin hanci lips masu daukar hankali, infact everything, ga shegen farin jini sai dai kasancewar locality din arean da suke ba lallai a gano value din kyan nata ba, shi yasa Umar ke bala'in sonta, emojin love tayi amfani da ta rufe fuskarta ta tura masa hoton, har xata ajiye wayar ta fita da cup din da ta sha tea sai ga message dinsa yace "What's this?" Ta mayar masa da cewa "What u asked for" yace "I asked

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login