Showing 24001 words to 27000 words out of 34659 words

Chapter 9 - Sanadin Kawa Book 1 Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

206

sun xo lafiya, kasa cewa komai tayi yace "Fatima" dagowa tayi ta kallesa a sanyaye, yace "Kinsan wannan mutumin?" Kallon Elbasheer dake kallonta tayi, irin tsare ta da yyi da ido yasa ta kasa kwakkwaran motsi xaunen da take, da sauri ta shiga gyada ma kawunta kai kamar kadangariya, yace "Toh ke kika ce ya turo magabatansa?" Lkci daya hawaye ya silalo fararen idonta, Elbasheer ya shafa sajensa a hankali yace "Kawu dama tun farkon da muka fara xuwa akwai maganan da ya kamata muyi da kai, so bana son yin maganar gaban iyayena but....." Fatima ta katse sa da sauri cikin sarkewar murya tace "Kawu nice nace ya turo" kallonta kawun yyi da sauri, "Amma kika ce baki san sa ba jiya da naje can gidan ku" ya tambayeta yana kallonta da kyau, share hawayen idonta tayi cikin raunin murya tace "Ina jin tsoron Ammi ne kayi hakuri" kawu yyi shirun kusan minti daya, can ya kalli Elbasheer yace "Toh kai wani maganan kace xa ka min?" Girgixa kai yyi hade da murmushinsa me kyau yace "Abinda ta fadi xan fadi maka dama kawu...." Kawu bai kuma cewa komai ba, Fatima kam kanta a kasa xuciyarta na mata suya, muryar kawu taji yace "Toh tashi ki je" dagowa tayi da idonta da yyi jajir cikin rawar murya tace "Amma kawu don Allah kar ka fadi ma Ammi xata yi fushi da ni sosai" murmushi kawun yyi yace "Tashi kiyi tafiyar ki" a hankali ta mike ta nufi kofa Elbasheer ya bi ta da kallo har ta fita kofa, kasa shiga dakin maman Hafsa tayi ta takure waje daya kan tabarmar dake shimfide tsakar gidan, ba a jima ba sai ga Elbasheer ya fito, har ya duka ya saka shoes dinsa bai daina kallonta ba, ita kam wasu hawaye masu xafi suka dinga sakko mata, takawa yyi har gabanta ya duka yana kallon ta, ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali, dago kanta yyi ta buge hannun tana shessheka ta mayar da kanta, d'an murmushi yyi ya mike ya fita gidan. Muryar kawunta taji yana tambayeta me take a nan, ta dago da sauri tana goge idonta, yace "Kukan me kika xauna kina yi" kallon kofar dakin maman Hafsa tayi ta tafi gunsa cikin rawar murya tace "Kawu don Allah kada kace ma Ammi ni nace su xo, wllh xata yi fushi da ni" yace "Toh yi wucewar ki ciki ki kira min Aminar" a sanyaye ta juya ta shiga dakin Maman Hafsah, tun da ta shigo Ammi ke kallon ta, a hnkli tace "Wai Ammi ki je in ji kawu" Maman Hafsa tace "Kukan me kike kuma?" Ta girgixa kai kawai, mikewa Ammi tayi ta fita, duk xancen da maman Hafsa keyi ita kam ba apprehending take ba, bata ma san me take cewa ba, har Ammi ta shigo dakin, kai kana ganin mood dinta kasan ba lafiya, nan ta shiga tsara ma Maman Hafsa duk yanda suka yi da kawu, Maman Hafsa da ta saki baki har ta kai aya sannan tace "Bata san shi ba kuma, an shiga uku, a ina aka taba aure haka? A'a gaskiya da sake bari in samu baban Hafsan, don me xai ce haka, ae sai jama'a su ce don ba shi ya haifeta ba shi sa xai yi haka, haba fisabilillah" tana kai wa nan ta fita, Ammi tace "Tashi mu je" mikewa Fatima tayi kamar jiri xai dibeta suka bar gidan da Ammi, har dare daga ita har Ammi kana ganinsu kasan suna cikin damuwa, damuwar da ta ga Ammi ta shiga ya fi daga mata hankali Wanda hakan yasa ta kasa daina Kuka, misalin karfe goma kiran Elbasheer ya shigo wayarta, har ya gama ring bata dauka ba shi ma bai sake kira ba, kwana tayi sallah tana rokon Allah ya wargaza plan din Elbash a kanta, sai bayan da tayi sllhn asuba bacci me nauyi yyi awon gaba da ita, hakan kuma bai hanata tashi karfe bakwai ba. Da rana ta shirya ta samu Ammi a daki ta durkusa tace "Ammi don Allah xan je gidansu Nafisa in dawo yanxu" Ammi tace "Toh" naira dari Ammi ta bata kudin mota, a sanyaye ta mike ta fita gidan. tayi sa'ar samun Nafisah don xata fita islamiyya a lkcn, Nafisa na ganinta da mamaki tace "Baki da lafiya ne fati?" Nan da nan idanuwanta ya kawo hawaye, Nafisa ta ja ta suka shiga daki ta durkusa gabanta da damuwa tace "Subhanallah, me ke damun ki Fatima, what happened?" Fatima ta fada jikinta tace "Na shiga uku Nafisa, na ja ma kaina, Husnah ta sa na cuce kaina" Rikicewa Nafisa tayi tace "Ki gaya min me ya faru don Allah" Sai da tayi kuka mai isarta sannan ta labarta ma Nafisa komai, tsuru Nafisa tayi tana kallon ta, girgixa kai tayi ta dafe kai tace "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un... Don me xaki boye gaskiya Fatima "Why did you hide the truth from Ammi, kin yi making babban mistake, yanxu ki tashi mu je ni da kaina can mata bayanin komai don a dakatar da mugun nufinsa a kanki" girgixa kai Fatima tayi da sauri tace "Aa bana son ta kuma fushi da ni...." Kasake Nafisa tayi tana kallon ta, a fusace tace "Kina nufin aurensa xa ki yi kenan" Fatima ta hadiye abu da ya tokareta da kyar tace "Allah xai ruguza manufarsa, Allah baxai yarda ba," Nafisa ta dafe kanta tace "Toh don me yasa baki bude text din Umar ba ki ji abinda xai ce maki" Ta girgixa kai a sanyaye tace "Baxan iya ba Nafisa, dama ke nake son ki duba min gashi na mance wayar a gida" Nafisa tayi shiru duk jikinta ya mutu, a hankali Fatima tace "xan koma Nafisa nace ma Ammi baxan dade ba" Nafisa tace "Baxan jima a makaranta ba yau, xan biyo nan gidan ku, in sha Allah baxa ki auri mugun nan ba, ki dai ki je sai na xo anjima" A tare suka fita bayan Fatima ta shiga dakin Ummansu ta gaisheta, sai da Nafisa taga ta hau adaidaita sannan ta dau hanyar makaranta a sanyaye ta na tunanin mafitar da xata nema ma kawarta. Fatima na isa kofar gidansu taji d'an hayaniyar mutane cikin gidan, gabanta ya fadi sosai ta shiga ciki da sauri, turus tayi tsakar gida tana kallon Akwatunan dake jibge tsakar gida guda daya daya har goma, matan anguwansu da suka shigo na ta yabawa ana sa albarka.
KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association=ء?

(Home of Experts and perfect Writer's)



*SANADI???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?N K'AWA*


NA


*khaleesat Haiydar*


BABI NA GOMA SHA HUDU




16




Bata kuma kallon inda kayan suke ba tayi wucewarta daki ta kwanta, tayi iya kokarin ganin ta kauda damuwar ranta lkci daya kuma bacci ya dauketa. Cikin bacci taji ana tashinta ta bude ido a hankali ta ga Nafisa xaune gefenta, mikewa xaune tayi, Nafisa tace "Ke akwatuna nake gani a waje, na waye?" Fatima ta d'an yi murmushin karfin hali tace "Nima yanda kika gansu haka na gansu Nafiee" Da mugun mamaki Nafisa tace "Toh wa ya kawo su?" A takaice Fatima tace "Elbasheer" Nafisa ta dafe kai tace "Lallai gayen nan really mean it, what did u think will be his main purpose of wanting to marry you Fatima? Wllh am just afraid no one knw his intention fa, yanxu haka xa ki yi shiru kiyi ta boye gaskiya a maku aure da wannan mutumin?" A hankali Fatima tace "I don't knw his intentions, and I don't want to knw, ni dai abinda na sani shine in dai ya kuskura yyi making mistake din aurena I will make life miserable for him the way he is making mine right now, ni yanxu na daina sa ma kaina damuwa in sha Allah, I am just waiting in ga iya gudun ruwansa" Nafisa tace "Ikon Allah, to me Ammi ta ce da ta ga akwatunan?" Fatima ta girgixa kai tace "Ni tun daxu da na dawo daki na shigo nayi kwanciyata kawai, na gaji da kuka Nafisa, did I deserve all this?" tana magana ne hawaye cike manyan idonta, Nafisa ta lumshe ido da damuwa tace "Kukan ba shi ne mafita ba Amira" Shiru fatima tayi a ranta tana tunanin farkon ranan da Husnah ta tilastata ta yi following din Elbasheer, Muryar Nafisa taji tana cewa "Har yanxu kuma bbu labarin Husnah koh? I saw her mum yanxu da na shigo tare da su Ammi" wani murmushin takaici Fatima tayi tana kallon Nafisa tace "Trust me Nafisah, I promise Husnah will surely pay for all I passed through, ban kyaleta ba, ita ma xata ji in da dadi ko babu" share hawayen dake sakko mata ta shiga yi wasu na kuma sakkowa, Cikin sanyin murya Nafisa tace "Noo, don't cry anymore Besty, kinsan abinda nake tunani..... Wllh sai nake ga kamar Elbasheer shine mafi alkhairi a gare ki shi yasa duk hakan ke faruwa... Kinga kuwa in har haka ne kam a sanadin k'awa kin ga jarabawa sannan kuma kin hadu da abokin rayuwar ki...." Katse ta Fatima ta yi cikin rawar murya tace "Idan kuma ba haka bane ba fah?" Nafisa ta sauke ajiyar xuciya tace "Hakan ne ma in sha Allah, beside ina tunanin kamar son ki mutumin yake tsakani da Allah banda haka taya xai yi ta bibiyar macen da ya ri ga da ya ka keta mata hadi?" Hakan da Nafisa ta fadi yasa fatima ta rushe da kuka sosai tace "Toh ni cewa nayi ina son sa Nafiee" Nafisa tace "Noo, da baki son sa tun farko baxa ki je gidansa ba duk da xugin Husnah, may be da can you have soft spot for him a xuciyar ki" Fatima ta girgixa kai muryarta na rawa tace "Nooo" Nafisa ta kamo hannunta tace "That's just it Friend, wannan mutumin ya riga da ya san ki a mace kuma yake ta bin ki yana son auren ki, sannan ki tuna fatima idan har ba shi din ya aure ki ba da wani idon xa ki kalli mijin da xai aure ki bayan ya gano ke ba budurwa bace, a kaddara Umar ne, me xa ki ce masa, me kuma xai dauke ki tunda bbu Wanda kika fadi ma gaskiyar abinda ya shiga tsakaninku da mutumin" Fatima ta hade kai da katifa tana kuka a hankli, Nafisa tace "Kiyi hakuri ki bar ma Allah komai, bayan wannan kuma ni ban san me xan ce maki ba kawata" Fatima ta dago kanta tace "Toh me xan ce ma Umar" Nafisa ta yi shiru bata ce komai ba, Mikewa Fatima tayi ta dauko wayar ta ta mika ma Nafisar tace "Ki duba text din da yyi min ban duba ba har yanxu" Nafisa ta amshi wayar ta shiga messages ta bude, dai dai nan kira ya shigo wayar, Nafisa tace "Lah ga shi ma ya na kira" Karban wayar Fatima tayi ta na kallon screen din gabanta na faduwa, can ta daga ta kai kunne bata ce komai ba, Sallama yyi ta amsa a hankali sannan ta gaishesa, yace "Lafiya lau Amira, ya gidan da su Ammi" ta sauke idonta kasa tace "Lafiya lau" yace "Hope baki yi fushi ba I didn't call all this while, I even sent you a text msg jiya da daddare ban san ko kin gani ba" shiru ta d'an yi kafin ta girgixa kai tace "Ban gani ba" yace "Ohk, ban ji dadi bane kwana biyu, I was even hospitalized but Alhmdllh yanxu" tace "Ayya ban sani ba, Allah ya sauwake" yace "Ameen, shi yasa na maki
message but baki gani ba" tace "Uhn, Allah ya sauwake" yace "Amin nagode" shiru ta yi, yace "Toh shkkn dear anjima xan shigo ki gayar min da su Ammi" ta kalli Nafisa kafin tace "Allah ya kai mu" sallama yyi mata ya katse wayar, bude text din tayi taga sanar mata kawai yyi ba shi da lafiya yana asibiti, Nafisa tace "Ikon Allah, toh yanxu ya xa kiyi da Umar Fatima?" Fatima bata ce komai ba na kusan minti daya, lkci daya wasu sabbin hawaye ya cika idonta a hankali tace "Nafisa I will tell him everything idan ya xo anjima" Nafisa tayi tagumi, Fatima na goge idonta cikin sanyin murya tace "Ai da na ji maganan Ammi tun lkcn da take kkrin rabani da Husnah da duk hakan bai faru da ni ba, da naji maganan ki nacewa in raba kaina da Husnah da...." Kasa ci gaba tayi Nafisa ta rungumeta tace "Irin taki kaddarar kenan Amira, so just accept it.... All is well in sha Allah" Sai kusan magrib Nafisa ta wuce bayan ta tabbatar ta kwantar ma kawarta da hankali ta kuma fadi mata abinda ya kamata ta fadi ma Umar idan ya xo anjima. Fatima na idar da sllhr magrib ta shiga dakin Ammi don xuwa lkcn bbu kowa gidan, xaunawa tayi duk jikinta a sanyaye, Ammi dake kan darduma cikin sanyin murya tace "Fatima yanxu kawunnan ki sun kyauta kenan, an taba aure haka kamar a film, yanxu ya suke son ayi da Umar, Umar ya cancanci haka? ban san da idon da xan kallesa ba, kawunnan ki basu taba min komai ba amma wannan karan sun min, ina tunanin da mahaifinku na raye baxai taba bada 'yar kai tsaye haka ba" Fatima ta hade kanta da gwiwa xuciyarta na kuna kukan ma ta kasa, duk tausayin mahaifiyar tata ya cikata, tasan ita ta ja mata wannan bakin cikin da take ciki..... Ammi da ke share hawayen idonta tace "Yanxu me yan anguwa xa su dauke mu, masu kwadayi da son abun duniya da kai kai inda Allah bai kai mu ba, banda haka sayar da ke nace xan yi da xa a kawo maki akwatuna har goma, amma komai ya faru ke kika jawo mana, kika yarda kika biye ma k'awa mara tarbiyya, me kwadayi da dogon buri mara godiyar Allah, da yake ke din ma makwadaiciya ce da dogon burin kika biye mata kika ja ma kanki abun kunya kika kai ma namiji kanki da mutuncin ki har gida Fatima, me na rage ki da shi, duk kokarin da nake maki bakya gani sai da kika watsa min k'asa a ido...." Fatima ta hade hannayenta tana shessheka tace "Don Allah ki yafe min Ammi, kiyi hakuri ki gafarceni" Ammi dake kuka tace "Babu wani yafiya da za ki ce in maki" kasa cewa komai Fatima ta yi banda kuka, taji duniyar tayi mata xafi, da ma ta gode Allah a yanda ya bar su bata yi hange hange ba, da kyar tayi karfin halin tashi ta koma dakinsu tana jin mugun tsanar Elbasheer, kiran Umar ta gani har uku a wayarta, don a dai dai lkcn ya katse, sake bugowa yyi ta dauka nan ya sanar mata da yana waje, ta fita ta wanke fuska sannan ta dawo ta sa hijab ko Ammi bata gaya ma ba ta fita. Kanta a kasa ta isa gun dakalin da yake xaune ta xauna, murya can kasa ta gaishesa ya amsa yana kallon ta yace "Are you okay Fatima" ta gyada masa kai tace "Yeah" duk abun nan bata yarda sun hada ido ba, tace "Ya jikin?" Yace "Alhmdllh naji sauki, ya su Ammi?" Tace "Suna lafiya lau" da damuwa yace "but you look depress tell me what's wrong dear, ki gaya min don Allah" tayi iya kkrin ganin bata fara kukan dake cin ta ba, tace "Ina son muyi magana da kai pls" kallon ta kawai ya tsaya yi kafin yace "Toh ina jin ki" sai da ta gama gathering din courage dinta gaba daya cikin sarkewar murya tace "Umar kayi hakuri... you knw God plans best, may be we where neva destined to be together...." Mikewa yyi da sauri yana kallon ta, ta ki yarda ta kallesa, a hankali yace "Ban gane ba Amira, what did u mean" ta hadiye abu da ya tsaya mata tace "So nake ka hakura dani don Allah don annabi, don darajar mahaifanka, Allah kuma xai baka warce ta fi ni" muryarta na rawa ta kare, kallonta kawai yake ko kiftawa bbu, ta hade hannayenta tace "For Allah's sake kada kace min A'a kuma kada ka tambayeni me yasa, just tell me so be it" Sosai idonsa ya kada, ya kauda kai na kusan minti biyu, tana sheshsheka tace "Kayi shiru Umar, talk to me plss, ka min abinda nake so, Allah xai mayar maka da mafi alkhairina, for Allah's sake ka min abinda nake so idan har son gaskiya kke min" Juyowa yyi yana gyada kai cikin cracky voice yace "Shkkn Fatima, Allah ya sa hakan shine mafi alkahiri, Allah hada kowa da rabonsa, amma ina fatan xan iya ci gaba da xumunci da su Ammi koh?" yana kai wa nan ya sa hannu ya share hawayen da ya taru idonsa, ta girgixa masa kai hawaye na sakko mata tace "Har ni ma ba da su Ammi kadai ba" kai kawai ya iya gyada mata, cike da karfin hali ta durkusa kasa tace "Nagode Umar, amma ka yafe ni don Allah kar ka bar ni a xuciyar ka" kai ya gyada mata nan ma da karfin hali yace "Na yafe maki" tashi tayi ba tare da ta sake kallonsa ba tace "Nagode sai da safe" daga haka ta wuce ciki da sauri, fadawa kan katifa tayi ta dinga kuka kamar an aikota, tun daga ranan da ta jona rayuwarta da Elbasheer take kuka ita da a da sai tayi watanni bata yi hawaye ba, har dare ya raba ta kasa bacci, tana son tashi ta dauro alwala tayi sallah amma duk jikinta yyi mata nauyi, haske wayar ta yyi ta jawo a hankali tana kallon screen din, message din Umar ne ya shigo, jikinta yyi mugun sanyi ta tashi xaune a sanyaye ta bude message din, "A duk xaman mu Fatima idan har na taba saba maki cikin rashin sani ko akasin haka kiyi ma Allah ki yafe min, nima kuma na yafe maki duk da baki taba min komai ba, ina maki fatan alkhairi a rayuwa, Allah kuma ya albarkaci rayuwar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login