Showing 30001 words to 33000 words out of 34122 words

Chapter 11 - Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel

nake ji na sake, freely, cikin walwala da kwanciyar hankali tamkar nan. Bani da wanda ya fiki, bani da wanda nake so fiye dake. Baba Sa’idu bai taba daukar ki matsayin maras hankali ba, ke ce dai kike zaton haka.
Ya sha cewa inda mai hankali a duniya to ke ce, in da wanda zan dage wurin bin maganarsa to ke ce, in da wanda ta san ciwon kanta a duniya to ke ce. Abin da ke damuna kwata-kwata bai shafi abin da ke kike tunani ba. So nake in tambaye ki ashe mu ba Fulanin Gwarzo bane? Kuma meye BARAROJI? Mene ne SADAKA-YALLAH?????”
Inna Rabi ta mike zaune a nutse ta yi murmushi. Ta mika hannu ta latsa makunun wutar lantarki dakin ya gauraye da haske, iare-iren wadannan gorarrakin ita ma ta sha su wurin kishiyoyinta a zamanin kuruciyar ta, ta kuma tabbata watan-watarana za a yiwa Abun ta. To amma ba ta zaci tun yanzu ba, ta dauka sai a gidan aure ko lokacin aure. Ba ta san daga inda ya fara fitowa ba, don haka ta ce, “Shin wa ke ce da ke hakan a gidan Sa’idu?”
Na ce, “Maganar fa ba ta yau ba, tun farkon zamana dasu ne. kuma tun lokacin Baba ya saba musu basu sake ba. Ita Hajiyar ma yanzu ba ta shiga harkata kowa zaman kansa yake a gidan, babu mai shiga shirgin wani. Ita Hajiya Sa’a ta gayawa su Hassan suka samin kahon zuka a wancan lokacin, wai suna kyankyami na saboda mu BUZAYE ne, kazame. Su tofar da miyau, suyi amai wai BARAROJI babu wanda ya kaimu kazanta. Sai nake jin tsoron ko wani ciwo ne hakan abin kyama”.
Inna Rabi ta hasala ta ce, “Ita Sa’ar har tana da bakin gaya mun haka? Tana da bakin ce dake SADAKA-YALLAH ba ta fadin babban? Koma meye ta ce a yanzu ai duniya ce, ita din kuma makaranta ce babu abin da ba za ka gani a cikin ta ba. Wanda bai zo ba ma tana nan tana jiran, kuma tarihi MAIMAITA KANSA yake, sannan kowa ya kwana lafiya shi ya so.
Idan a yau na ga dama wallahi ba za ta kara jin dadi a rayuwarta ba, daga ita har Sa’idun da take takama da shi, domin GIRMANSU YANA HANNUNA, yau ne ko gobe in na ga dama sai in FADAR DA SHI, in ga karshen kudi da boko, wadanda basu da amfani idan babu mutunci a idon duniya.
To amma ba zan yi hakan ba saboda wasu manyan dalilai, akwai ranar da dubunta za ta cika. Tara su nake daga ita har Sa’idun ina jiran ranar da wani a cikinsu zai wulakantaki, ina jiran ranar da zai nuna fifiko tsakaninki da ‘ya’yansa….” Sai kuma ta razana da ta fuskanci ko da wa take magana, Zaynabu ce ba Au ba, da cikakkar budurwa mai hankali take magana ba Kyauta-Abun d ata sani a baya ba ce,.
Ta yi hanzarin gyara zancenta da cewar, “Zaynab mu ba Bararoji bane. Sune ‘yan kasarmu dake daji, mu ‘yan kasar Niger ne ‘yan uslin wani gari DAMAGARAM, amma iyayenmu da ‘yan’uwanmu duk a babban birnin Yamai (Niamey) suke zaune, har yanzu suna can.
Mahaifinmu fitaccen dan kasuwar fata ne da ya yi fice a Niger, kuma mashahurin dan siyasa ne da ya rike mukamai da dama a gwamnatin Damagaram, wanda gab da rasuwarshi yake dan takara mafi rinjayen magoya baya da suka tsaya neman kujerar gwamnatin Damaragam. Duk dangina suna Niamey, ba fakiri ko daya, bamu taba yin talauci a rayuwarmu ba, bamu san shi ba ni da iyaye da dangi na gaba daya. Kaddarar aure da rabon haihuwar ki ya kawo mu Najeriya mu da mahaifinmu da kanwata NURATU da ta bata a hanuna.
Batan Nuratu ne ya hanani komawa gida, ya hanani neman dangina har yau don ban san me zan ce musu a kanta ba, kuma rashinta ne ya tsomani a halin da har yau kike ganina a ciki ake min kallon MAHAUKACIYA ko TABABBIYA.
Su kuma danginmu basu san inda muke ba, don mahaifinmu rasuwa ya yi a sanadiyyar hadarin jirgi a kan hanyarshi ta komawa gida, ya gaya masu cewar ya aurar dani ba da saninsu ba. Ki taya ni addu’a Allah ya bayyana min Nuratu, ni kuma na yi miki alkawarin a ranar da na ganta a ranar ne zan sadaki da danginki na wurin uwa. Sai kin raina zamanki da su Sa’ar da ke ce dake SADAKA-YALLAH, sai dai ki basu SADAKAR ki wuce.
Idan kika shiga Niamey ko Damagaram kika ce kina neman wani da ya shafi iyalin MAINASARA KANGIWA, ko yaro kankani ya san wannan sunan.
Ki yi hakuri ki kyale ta, akwai dalilin da yasa ba ta son ki, ba kuma za ta so kin ba har abada, illa ta boye hakan a ranta don amfanin kanta, amma ai……” Ta sunkuyar da kanta. Ta dade tana kallon kyawawan yatsun hannunta, can ta dago ta ce, “Ke Zaynab kada ki damu kanki a banza, da dangin Uba ai ake tutiya ba na Uwa ba, ko ta isa ta ce da Malam SADAKA-YALLAH? Ni ta fada ta more, akwai ranar da GIRMA ZAI FADI!”
Na yi shiru ko kwakkwaran motsi bana yi, sauraron Innana nake da dukkan hankalina. Ta ga akwai alamun rashin fahimtar wasu abubuwa cikin kalamanta a tattare dani, sai ta ce, “Ke yi kwanciyar ki don Allah kada ki kara sa wannan shirmen a ranki, na ce dake da dangin Uba ake tutiya ba na Uwa ba.
Kuma ni nan da kike gani, zaman jiran Nuratu nake, amma ba zaman soyayyar Malam Ali ba, ko zaman jiran Sa’idu ya dauko ya bani. Domin har yau Sa’idu bai yi arzikin da zai bani in mance takaicin da ya tusa mini ba, da rayuwarmu da ta gurbata a dalilin son zuciya irin nasa…”
Da maganganun Inna na kwana ina taunawa ina cizawa, ina hurawa a cikin raina. Abubuwa da yawa na kasa fahimtarsu, I’m confused! Da maganganunta masu daure kai da caza hankali, illa na samu kaina a daukan ‘Diary’ dina na rubuta kalmar “MAINASARA KANGIWA” da wasu cikin kalamun ta da ban fahimta ba. Nake fatan duk ranar da Allah ya dawo da Ya Faruq zan sanya shi ya fidda ni duhun da ke cikin su.
Hutuna na wannan karon a Gwarzo na ji dadin shi fiye da na ko yaushe, don muna tare da mutanena su Hafsisi. Ita Indo an sa mata rana da wani malamin su a can Kabon, ita ko sarkin rigima Hafsisi ta ki kula kowa wai ita Faruq take jira, shi kadai take so duk fadin duniyar nan, idan ba shi ba sai dai ta mutu ba ta yi aure ba.
Na yi dariya har da fidda hawaye, na jinjina kai, na jinjina mata, don ni dai tunda nake da Ya Faruq dai-dai da rana daya ban taba jin ya ambaci wata ‘ya mace a duniya da sunan so ba, balle wata Hafsisi. Sanda muke aji hudu ne ma Azizah ta taba rubuta mishi leta wai tana son shi, in ta kare karatu ya gayawa Abba yana son auren ta.
Tun lokacin ya kirata kamar abin arziki, ya kwakkwada mata mari ya ce kuma ba shi ba, ko wani daban ta sake cewa tana so sai ya gayawa Abba, in yaso a cire ta makarantar ayi mata auren da Shehu direba dai amma ba da shi ba. Tun daga lokacin ko da wasa Azizah ba ta kara shiga shirgin sa ba, shima kuma sai ya rage wasan da yake dasu duka.
Na ce, “Hafsisi in za ki ji shawarata, ki samu wani mai sonki tsakani da Allah ki yi auren ki ya fiye miki alheri, don shi wannan Ya Faruq da kike gani ko zancen aure baya yi, kuma nan da shekaru biyu ma albarka ya dawo. Azizah ma bai karbeta ba balle ke?” Hafsisi ta kulu, ta kawon duka ta ce, “Me Azizar ta fini ban da Turancin banza, nima yanzu meye ban sani ba a Turacin?” Na ci gaba da dariyar da ta kara kular da ita, cikin zolaya na ce, “Turancin ma ba fa fiki ba”. (maganar da na zo ina dana sani da ban yi ta ba).
Budar bakin Hafsisi sai cewa ta yi, “Ba wani nan, ai dama ba tun yau na san kin fi son su Azizah dani ba, saboda su masu kudi ne kuna samu a jikinsu kuna ci ke da Malam da Ya Faruq din naki. Duk kun ki mahaifarku kun je kun tare masu a gida saboda tsabar kwadayi. In dai don dan abin da ake ikirarin Malam ya yiwa Alhaji Sa’idu ne da yana karami, ai yanzu ya biya shi har da riba, tunda har Makkah ya kai shi sau ba iyaka. Kada dai kuke mantawa a kullum an ce, inda kwadayi…..” Ta murguda baki ta yi tafiyarta ta barni da baki bude.
Maganganun Hafsisi sun haifar min da ciwon kai, na dade ina maimaita kalamanta a zuci. Babu shakk duk abin da ta fadi gaskiya ne, kuma kalamanta duk shigen na Innana ne. Sai na ji wasu dumammun hawayen tausayin kaina masu zafi sun digo a kan yatsun kafata. Mafari kenan da Hafsisi ta daina yi min magana, ta dauki gaba dani, ta shiga nuna kyashin ta dani muraran.
Tun daga lokacin na ji Sokoto ta fice min a rai, na rika gudun cikar kwanakin hutuna. Na alkawartawa raina ko da na koma gidan Baba Sa’idu da na kare makaranta ko kwana daya ba zan kara ba zan dawo gida.
Don haka a komawata wannan karon su Azizah sun ga sauyi da yawa, gaba daya na yi sanyi, na mai da kaina bare a cikinsu. Na daina amfani da kudin da Baba yake bamu sai dai in ajiye kawai. Shima don ina jin nauyinsa ne amma da na ce ya daina bani.
Na rage cin abincin gidan, idan na ci da karfe biyu bana kuma ci sai dare, na daina karin kumallo, don a ganina duk hakan yana cikin kwadayin abin hannun su. Daga baya ma in an tashi daga makaranta sai na dinga shiga restaurant din makaranta in saya in ci, in mun dawo ba zan ci na gidan ba. (Na manta cewa shi kansa kudin da nake sayin ai daga aljihun Baban yake fitowa). Su Azizah dai na kallon ikon Allah sun rasa ta cewa, sai Iftihal ce rannan ta ce, “Anti-Abu dai ta zama waliyyah”.
Ranar wata alhamis mun dawo daga makaranta, a harabar gidan muka tadda Hajiya ta yowa wata kyakkyawar budurwa rakiya, ga wasu ‘yammata uku suna takewa budurwar baya sun rike mata jaka, za ta yi shekaru ashirin da shida. Baka ce amma a goge take, ko ina a jikin nan nata sumul-sumul, ga sullubebiyar mota ta (end of discussion) baka sidik sai daukar ido take.
Tsayawa fasalta sittirun da ke jikinta ma bata lokaci ne, sai jifa mu take da wani irin murmushinta kamar madara, da hakoranta kamar kankara. Ta yafito mu da hannu muka je ta kama hannunmu mu duka tana tambayar mu ya ya shirye-shiryen (WAEC).
Mamaki ne ya kama mu na yadda akai ta sanmu har ta san jarabawa zamu yi. Hajiya ta shiga yi mata bayanin mu, wai wadannan Azizah ne da Iftihal (twin sisters) din Imran. Wannan kuma Abu ce kanwar Faruq. Ta ce, “Lah! Ke ce Abun Faruq Aliyu?’ Ta makale ni sosai a jikinta ta sake cewa, “Ina jin labarinki sosai a bakinshi, amma ban zaci haka kike da kyau ba kamar Baturiya. Dan’uwanki ya damu da ke sosai Zaynab, da wuya a zauna da shi bai yi zancen ki ba, ina taya ki murnar kasancewa ‘yar’uwa ga mutum irin Faruq Gwarzo”.
Na lumshe ido wani dadi ya kashe ni. Kowa ya budi baki alheri yake fada a kan Ya Faruq, ban taba jin wanda ya aibata shi ba, dai-dai da rana daya. Haka duk wanda ya san shi in ya ganni zai ce ya sanni, Faruq yana yawan ambato na. wannan ne yasa har abada ban da mutum mai kimar Ya Faruq.
Ta mikawa ta bayanta hannu ta miko mata jakarta, ta sanya hannu a ciki ta damtso kudi da ba ta san adadinsu ba, (American-Dollars) ta fito dasu tsurar su ta raba su gida uku, ta mika mana. Azizah uwar son kudi ta riga kowa amsa, har da mu aka rakata bakin motar ta, ta ja ta fita cikin wani irin ubansun tuki. Azizah ta buga tsalle ta yi cikin gida tana cewa, “Yanzu zan shirya in tafi canji, in Allah ya yarda sai na zama MAMI ABDULHADI”.
Na samu kaina a maimaita sunan Mami Abdulhadi fiye da cikin carbi, na so in ji sunan a baya amma na rasa daga inda na ji shi. A dakinmu na ce da Iftihal “Wai ita wannan Mami wace ce?” Ta ce, “Baki san Adda Mami ba? Diyar Gwamnan Sokoto Abdulhadi Talata Mafara, budurwar Ya Im?”
Wallahi ban san sanda na saki kudin da ke hannuna ba suka tarwatse a kasa, a take na ji na tsane su bana son ganin su kamar yadda na tsani wadda ta bani. Na ji haushin kaina da har na tsaya na kula Mami, wani kululu ya zo ya tokare min a makogaro ko miyau na kasa hadiya.
Su Azizah sun dauka wai mamakin ita ‘yar waye ne ya kamani, don son kara burge ni da tabbatar min da Mami wace ce, Azizah ta zura da gudu dakin Mama ta zo da mujallar ‘OVASION’ da bama gajiya da kallo ta auren Aishah Babangida tana nuna min Mami cikin ‘yammatan Aishah, dama kuma na so in tuno inda na ga fuskar Allah ne ya mantar dani.
Irin rudewar da Azizah ta yi a kan Mami sai na ji ina tausayin kaina, da burin da na daura a kan Ya Im. Yanzu idan ta san ni din ina son dan’uwanta ko ya ya za ta karbi al’amarin? Ni Zaynabu-Abu ‘yar Malam Ali, jikar Mamman Gwarzo, da bamu da komi sai tumaki, sai tsintsaye. Na fara fidda rai da Imran a karo na farko a rayuwata. Na san Imran ya fi karfina nesa ba kusa ba, wai wan ce ‘kwarya ta bi kwarya…..’ Anya maganganun Anti Rose za su taba zama gaskiya kamar yadda take ikirari?
Kwana na yi a ranar nan cike da kishin Mami, ko rintsa ido na kasa, gami da wani azababben son Imran dake kara daidaita zuciyata. Sai dai wannan karon kam kauna ce ta hakika, da har nake jin ko ya ya ne, ko ya nake ba zan iya barwa Mami shi ba.
Amma a dole washegari na shiga tirsasa zuciyar da ta fidda Imran da duk wani al’amarin shi a cikin ta. Ina nuna mata beke da illar dake cikin hakan, ina nuna mata Imran ba alkhairi bane a tare da ita, ina nusarsheta da cewa a kul, Zaynabu! Igiyar rakumi… ta yi nesa da kasa, tsira da mutunci…. ya fi tsira da kudi, abu mai yiwuwa shi ake yi ba mara yiwuwa ba, yaro tsaya matsayinka…. kada zancen ‘yan duniya ya rude ka, kai zai kai nya baro. Amma wallahi zuciyar nan mai laushi da kafiya (delicate but strong) ta ki amincewa, ita dai Imranan nan shi kadai take so by all means. Babu abin da ya dame ta da hujjoji na, ba ta san su ba, IMRAN kawai ta sani. Cewa take Zaynabu-Abu luv, have no boundaries…..
A kwanakin biyun da suka biyo baya, duk rabin hirar su ta Mami ce da kirkin ta. Idan na ji ba zan iya jurewa ba, sai in tafi daki na ci kuka na ya isheni, in sa sabulu in wanke fuska. Kamar wata zautacciya, in saka wannan in kunce da wancan. Daga karshe na alkawarta ma raina ko Imran din nan ne autan maza na hakura da shi, don tsira da mutuncina da na iyayena.
Duk wanda ka ga Hajiya Sa’a ta tashi ta rako gate da kafafunta, to tabbata ya isa, ta san shi din wani ne, za kuma ta samu wani abu a jikinsa, duk da babu abun da Allah bai mata ba ita da mijinta da ‘ya’yanta, ba ta da godiyar Allah ko kadan. Ko a jiya Imran ya aiko mata da sabuwar mota (Hummer Jeep) da gaba dayan albashinsa na wata da watanni, dama ya ci alwashin ita ne za ta fara cin gajiyar iliminsa, amma a yadda take nan-nan da Mami, sai ka rantse ba ta taba mallakar kwandalar kanta ba.
A kwanakin da suka biyo baya ban kara yardarma zuciyata ta tuna Imran ba, na tattarasu shi da Mamin da al’amarinsu na zuba a kwandon shara. A yau muka fara zana WAEC da practical Biology, bamu muka fito ba sai karfe hudu na yamma. Kwakwalwata ta yi zafi, kaina ya yi zafi rau, ga yunwa, gajiya da nannauyan barci a kaina, wanda ban samu na yi ba a daren jiya muna ta karatu.
Don haka mun shigo gida a gajiye lis, muna tafe muna hada hanya, ban lura da bakuwar motar da muka samu ba a harabar gidan. Muka isa falo kowacce na ‘wash-wash’, ni ko dafe nake da goshina, idanuwana a rufe nake tafiya a cikin falon.
Ban ankara ba na ji na yi karo da mutum, kamin wani lafiyayyen kamshin turaren nan na (Boss-Intense) ya bakunci hancina. Na yi hanzarin bude idanuna da suka yi ciki sosai saboda yunwa da wahala, na dube shi yana murmushin nan nasa mai cike da ginshira, a hankali ya ce, “Ya… ‘yan makaranta ba a gani ne?”
Wallahi sauran kadan in fadi a tsakiyar falon sakamakon kafafuna da suka kasa daukar nauyin jikina, saboda yadda Imran ya koma, in da dare ne ba za ki gane shi ba. Ya zama kato, ya zama ‘giant’ ya kara kyau na ban mamaki. Tsayayyun kafadun nan nashi ‘pysique’ na barazanar gabje maza biyar a lokaci daya saboda yadda suka kara habaka har da doro na musamman, na kasaitattun maza.
Ya kara haske ba can ba ‘chocolate’, ya kuma kara murjewa, da gani za ka san naira ce ta zauna da gindinta. Lafiyayyen agogon ‘switch-blustery’ sai walkiya yake cikin lallausar fatar hannun shi, yana sanye da farar shadda kal kamar takarda, dinkin mazan Maiduguri. Na yi gaggawar ba shi hanya, ya yin da shawarar Anti Rose ta zo min cikin kaina kamar karatun sallah. Cikin halin ko in kula

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login