Showing 18001 words to 21000 words out of 34122 words

Chapter 7 - Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel

cikin raina ina cewa, gaskiyan Iftihal ne, gaskiya ne ba mutun irin Yayan ta! Komi nashi mai ban sha’awa ne, hatta furucinsa. Azizah ta ce, “A school ma ba a ce da ita Abu sai Zainab”. Ya ce, “That is good, ZAYNAB, daga yau cikin ku kada wanda ya sake ce da ZAYNAB (ABU)”.
Wannan shine mafarin al’amarin. (Takori).

****

Na kwanta a daren nan ina maimaita kalmar “ZAYANB” da Imran ya ambata, na fadi ya fi cikin carbi, amma ban ji na fadi dai-dai ba irin yadda shi ya furta. Na yi tunanin abubuwan da suka faru a ranar tare da Imran na kasa mantawa. Idanuwanshi suka sanya zuciyata cikin wani sabon al’amari da ban taba tsintar kaina ciki ba. Na yi kokarin in yakice Imran a zuciyata na kasa, inda duk na juya shi ke zuwa cikin idanuna.
Na ji wasu sassa na jikina suna wani irin kaduwa da ban san na mene ne ba. Marana ya kulle tamau kamar zan yi fitsari, don haka na rarrafa zuwa (toilet) na yi ta kakalen fitsarin amma bai zubo ba. Na dawo daki na kwanta a dandaryar carpet, na ware fanka da A.C amma ban daina zufa ba.
Wannan al’amari ya tsoratani, domin wani al’amari ne sabo a gareni da ban taba tsintar kaina a ciki ba, ban kuma san ko mene ne ba. Hawaye ya zubo min ina kallon su Azizah dake ta barcinsu cikin kwanciyar hankali, na rasa abin da ke min dadi, na rasa mene ne shi wannan abun, haka na rasa me zan yi ya gusar min da wannan sabon abu da nake ji cikin jikina har kuma cikin kwakwalwata. Wannan shine mafarin shigar rayuwata cikin gararin da har yau take ciki, cikin halin bakin ciki da dakacen ina ma ba a haifeni ba.
Da ban hadu da Imran ba, watakila da rayuwata ta ci gaba da garawa a yadda take. Wato ba bakin ciki ba kuma farin ciki, sai godiyar Allah. Haduwata da Imran shine silar warwarewar al’amuran rayuwata da na Innana da suka shige min duhu, suke damun zuciyata tun ina kankanuwa. Har ila yau, Imran din ne sanadiyyar rushewar farin cikin rayuwata.
Wata zuciyar ta ce dani, wannan al’amari da ke neman samuna ba alheri bane a tare dani, don haka in nemi tsarin Allah. Wannan ita ce tarbiyyar da iyayena suka dora ni a kai, wato duk wani abu da ya fi karfin iyawa ta, ya fi karfin sani na, ya fi karfin kariyata to in nemi tsari da kariyar Allah, domin shine mai iko a kan komi.
Sai na mike ina layi na yi bayan gida, na dauro cikakkar alwala na yi (brush) na fito na suturce jikina na fara sallah, a cikin sujjada ta ina rokon Allah cikin yi masa kirari da ya yaye min wannan matsala da ya daura min a kan Imran, ya kawo sanadin da Imran din zai bar gidan gaba daya in huta.
Washegari na tashi da azumin tadauwa’i a bakina, kasancewar ranar Alhamis ce dama na kan yi azumi litinin da alhamis. Wallahi sai na ji ni sawai, kaman an yaye mani. Na yi ta yiwa Imran boyo cikin gidan har aka sha ruwa, gani nake kamar idan ya kalli kwayar idona zai karanto abin da ke damuna game da shi, wanda ya hana mani barci daren jiya. Wannan ya faru ne tun ina da shekaru sha biyar a duniya.
A daren Imran da Faruq na zaga gari cikin motar Imran din, Faruq ya ce,
“Yau tun safe ban ga Abu na ba, na shiga sassan Mama ya fi sau biyar ban ganta ba, ina cikin damuwa wallahi”.
Imran ya yi murmushin da shi kadai ya san dalili yin abin shi, amma bai ce komai ba.
Ya yi parking a wani katafaren shopping complex suka shiga tare, shi Faruq ya dauka biskit din nashi zai saya da baya rabo da saye. Don haka shi ya yi wani barin can daban yana saye-sayen shi. Kafin ya zagayo inda Imran yake, ya ganshi ya cika kwando taf da kayan shafa na mata (designers) yana jujjuya kwalbar turaren cool-water watau (Davidoff) a hannun shi, turare ne mai sanyin kamshi na ‘ya macen da ta san sirrin da ke cikin turare.
Sai daga baya ne ya dauki kayan shaving din shi da biskit din nashi na (Hob-Nobs) ya yi gaba ya bar Faruq da baki bude. Mamakin Faruq yaushe Imran ya yi budurwa bai sani ba? Ina ya je shi kadai ba tare da shi ba har suka hadun?
Imran S. Bindawa, tamkar ya san me Faruq din ke sakawa a ranshi, sai ya yi murmushi ya kanne mai idon shi daya cikin tsokana, ya ciza lebbanshi masu sulbi, ya matso dai-dai kunnenshi ya ce,
“Don’t be nervous mana (kada ka ji tsoro) ba kowa na sayawa ba face kanwata, ZAYNAB”.
Ya yi gaba ya barshi nan yana mai son convincing zuciyarshi ta yarda da abin da take ji, amma zuciyar ta ki yarda, karyatawa take da cewa, ba ZAINAB ya ce ba ZUBAIDA. Da Imran din bai yi gaba ya barshi ba, da ya ji irin hautsinawar da ‘ya’yan hanjin shi ke yi, da kukan da akuyar cikinsa ke yi. Ya kuma ga kallon firgicin da ya bishi da shi da gumin da ke ta yankowa daga kowanne sako a jikinshi.
Ya shiga gyada kai tamkar kadangare yana girgizawa, yana gayawa kanshi cikin lallashi cewa, ba da wani nufi Imran ya fadi kalaman shi ba, ba da wani nufi Imran zai yiwa Zainab kyauta ba, abin da yake kokarin fahimta ba shine ba. Zumunci ne kawai da alkhairi irin nasa, domin shi mutum ne mai alheri ga kowa ma ba Zaynab kadai ba.

Abinci ake ci bisa makeken dining din gidan, to amma me? Imran idanun shi kyar bisa kyakkyawar fuskar Zainab, tana kai lomar ta a nutse ba irin su Aziza ba hannu baka hannu kwarya. Idan tana tauna kumatunta duka biyu da tsakiyar habarta lotsawa suke ciki sosai. Komi nata a yangace amma naturally ba wai tana sane take yi ba, yana tafiya ne da halittar Ubangiji.
Sanye take da doguwar riga fara sol, ta matse dogon gashin kanta daga tsakiya da farin ribon ya sakko ya kwanta lamban bisa dogon wuyan ta kamar na barewa. Zainab a mike take sosai ga kuma alamun ‘mace’ dake neman bayyanuwa a jikin ta daga yanzu zuwa kowanne lokaci. Ya kasa cin abincin sai ko juya cokali cikin farfesu?
A bangarena, nima ba cin abincin nake yi ba, bugun da zuciyata ke yi a duk lokacin da na ga Ya Im, na yau har ya fi na kullum. Kaduwar da sassan jikina ke yi yanzu, wane na daren jiya. To a haka aka kare cin abincin ba tare da na ci wani abin kirki ba, haka tunda na dukar da kaina kasa ban dago ba. Idan akwai abin da nake son gani, nake kuma gujewa ganin nasa, to Imran ne. ba don komi ba sai don abin da hakan yake haddasa min a cikin gangar jiki da tsokar zuciyana baki daya.
Karfe tara na dare ana falo har Abba ana kallon network news amma ni ina uwar dakinmu dukunkune cikin bargo, ga littafin assignment dina a gabana na kasa hassala komi sai fama da abin da ya dameni. Zan so in samu wani ya fassara mun ma’anar wannan abu dake damuna.
Abin bakin cikin shine, ni bani da kawa, su Azizah duka yara ne na girme su, ni kaina ban san mene ne ba balle su da na kere sosai a shekaru. Kaduwar da jikina ke yi shi ya haifar mun da zazzabi da sarawar kai, haka abin da na dauka ciwon mara ke karuwa mini. Ga (assignment) din da na tabbatar in ban yi shi na bayar a gobe ba na rasa C.A dina na darasin physics, amma bai dameni ba kamar wannan ciwon Imran da Allah ya dora mini. Hawaye masu zafi suka soma biyo kuncina, na kara kudundunewa tamkar curin alkaki, haka al’amarin yana kara habaka a tare dani.
Imran sanye da farar shirt (DKNY) da shudin wandon (Jeans) ya shigo falon, ya zauna ana kallon da shi ba don kallon ne ya kawo shi ba. Ya mike tsaye cikin damuwa ya zura hannunshi cikin aljihun bayan wandon shi kamar mai laluben wani abu, yana kallon su Azizah suna ta shewar su, ya hanga ya duba iyakar ganin shi bai ga mai rikirkita shi ba a ‘yan kwanakin nan.
Cikin mamakin rashin ganin ta da yake cikin jama’ar gidan a dan tsukin ya ce, “Azzy ina Zaynab ne?” Iftihal ce ta amsa masa da cewa, “Tana can daki an ba ta assignment ta kasa shine take yi tana kuka”. Ya ce, “To ku baku taimaka mata in kun iya?” Iftihal da Azizah suka dubi juna suka kama baki, can kuma suka hadu suka tintsire masa da dariyar su ta ‘yan biyu mai ban haushi. Ya shaka, ya kulu, kadan ya rage ya yi kwallo dasu.
“Mama ki ji Yaya Im don Allah, mune ma masu koya ma Zaynab karatu?”
Mama ta ce, “Zainab ce malamar su Azizah ai, in ta iya su koya a wurin ta, in ba ta iya ba duk haka suke lalacewa”.
Hajiya Sa’a ta kyabe baki, saboda neman fitina babu wanda ya sako ta cikin zancen su, amma sai cewa ta yi, “Ai tsiyar ‘ya’ya mata kenan duka tumaki ne, duk ba kwakwalwa sai ta shashanci”.
Mama ta wani irin juyo ta dube ta, ta bude baki za ta yi magana Abba ya daga mata hannu ganin yadda yaran suke kallon su, ta yi shiru tana ciccika tana batsewa, kiris take jira ta yi kuka.
Wannan dabi’ar Hajiya Sa’a ne, babu yadda za ayi a zauna da ita a tashi ba ta san abin da za ta ce wanda zai bakantawa Azumi ba, ko da kuwa ta cikin ruwan sanyi ne. Ita kuma Azumin ba hakuri, ba ta barin ko ta kwana da an tabo ta za ta hau suyi sama suyi ta yi kamar sa cinye juna.
Shi kuma Abban ya zuba ma takarda ido yana rubutu kai ka ce dabbobi ne ya aje ko dagowa baya yi balle ya san suna yi. Ya kan ce cikin zuciyarshi mace daya ce ta ishe shi duba a duniya, mace daya ce ta isa ya daga ido ya dube ta ya ji sanyi a zuciyarsa kuma ta yi mai nisan da har abada ba zai kamo ta ba.
Ta tafi da duk wata soyyarshi a kan diya mace. Don haka duk wata mace kallon ta kawai yake a dage, a kaskance, a hagunce, ma’ana ba ta da abin da za ta burge shi da shi har ya bata muhimmin lokacinsa a kanta. Sai zaman aure domin neman lada gami da kariyar kai daga dattin zina, da rainon ‘ya’ya wanda wannan daman dole ne.
Ya dago ya dubi Imran idanunshi sun kada sunyi jazur da tunanin wani al’amari mai GIRMA da ya taba zuciyarshi, ya ce da karfi, “Dan Abba! Jeka koyawa Zaynab assignment”.
(Kuskuren da iyaye ke yi kenan, musamman iyaye ‘yan boko da attajirai, kan dauki kebantuwar ‘ya’yansu mace da namiji baligai ba a bakin komi ba duk a cikin wayewar ne, wanda ko Annabi (S.A.W) ya fadi mana kebancewar mace da namiji, na ukun su shaidan ne, musamman ga ita Zaynab, da Abban ya yi tunani bai dace ya yi hakan ba, tunda shi da bakinsa ke yi mata nasihar mu’amala ko ya ya da namijin da ba muharraminta ba).
Tamkar ya yi mai susa a inda ke yi mai kaikayi, da sassarfa ya nufo dakinmu. Har zuwa lokacin kwance nake kudundune cikin bargo ga littafin a gaban filon da na ta da kai da shi, idanuwana cike da hawaye amma basu kai ga zubowa ba.
Daga bakin kofa ya dakata ya tokare a jikin kofar da hannunshi na dama kafafunshi na daga waje ya ce,
“Zaynab mene ne haka? Cewa aka yi in baki iya assignment din ba korar ki za ayi daga makarantar?’
Shiru na yi masa tamkar da littafin yake magana, don ban san me zan ce masa ba. Shirun shine mafi alfanu. Ganin haka ya karasa shigowa dakin gaba daya, ya ce, “ki tashi na ce, ki tashi ki zauna Allah tun ban kwaye bargon ba”. Nan ma ba amsa, sai ido da na bishi dasu, luuu! Wadanda suka kankance suka yi jawur, tamkar an gumbuda musu barkono.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Ya yi tsai da ransa cikin son karantar me ke damun Zaynab? Ko me Zaynabu ke ciki? Ba tare da tunani ba kuma ya janye bargon ya wancakalar. Subhanallahi! Ba shiri ya mai da mun abuna saboda kananun (minis) da ke jikina.
Ya juya mun baya da sauri cikin rawar murya yana fadin, “Ki tashi ki sa kaya in koya miki assignment din. Ki tashi tun baki yi sanadin da na idasa kai hannu gareki ba, wannan hawayen da kike zubarwa Zaynab ba zan iya jurarsu ba. Zaynab ya kike so in yi da raina? Kin hana mun ganin kyakkyawar fuskarki, kin haramta min jin lafuzan ki masu taushi, kin hana mun barci yanzu ma a ido biyun kina so ki mai dani wani zararre, haba Zaynab! Ke wace irin yarinya ce mara tausayi da halin ko in kula……..”
Baki na saki galala! Ina jin abin da ko a mafarki ban taba yin na zan ji hakan daga Imran ba, ko a tunani, ban yi na wai Imran zai taba fadin hakan gareni ba even in my imaginations! To ko shima irin ciwon nawa ke damunsa? Bai san halin da nake ciki duk a kansa bane? Bai san duk wannan kukan ba na assignment bane na rashin abin da zuciya da gangar jiki ke so ne, wato shi YA IM, da nake ganin har abada ba zan samu ba.
Still bai juyowa ba ya saki wata irin ajiyar zuciya ya ce, “To ni yanzu Abba ya ce in zo in koya miki karatu, me kike so in je in ce masa? Baki da lafiya ko-ko bakya jin magana?”
Da sauri na lalubi jallabiyana na zurma, na daura mayafin ta cikin wani irin dauri maras fasali, cikin dasasshiyar murya na ce, “Ka yi hakuri Ya Im, bani da lafiya ne”.
Da sauri ya juyo ba tare da ya yi tunanin nasa sutturar ko ban sanya ba, ya tako da sauri ya zauna a gaban gadona. Ya kai hannu goshina, “me ya same ki?”
Wani irin shock ya same ni ya kuma taso da lalurar da ke kwance lumus cikin jikina. Jikina ya soma kyarma tun daga kai har yatsar kafata mazari nake. Ai Imran ba yaro bane, na san ya fahimci halin da nake ciki, sai ya yi azamar janye hannunshi a goshina ya ja da baya.
Ya yi murmushi ya ce, “Zaynabu gaya mun irin ciwon da ke damun ki in ji ko zan iya maganin shi. Nima bani da lafiya amma nawa bai yi tsanani kamar naki ba. Kuma ni ina kokari a kullum in fi karfin zuciyata, in hana mata abin da na san ba alkhairi bane a tare da ita, in ce mata a’a, wannan ba dai-dai bane, bana biye mata domin sharrin dake cikin ta Allah ya yi yawa da shi.
Sai ta kai ka garin DANA SANI ta baro, ita ba abin da ya dame ta. In yi hakuri in dauki kaddara, in roki Allah ya kawo mun sauki cikin al’amarina. Ni Imran da kike gani a duk sanda na ji zuciya na neman rinjaya na cewa nake, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’ouun!”
Wallahi sai na ji matsananciyar kunyar shi ta saukar mun, na kuma shiga maimaita “Innalillahi…..” a fili da zuciyata. Wata nutsuwa ta musamman ta same ni, komi nawa ya koma normal, na sunkuyar da kai kasa cike da burin ina ma a ce…. kasar za ta tsage da na shige na huta da kunyar Ya Im, amma shi bai damu ba.
Sharewa ya yi ya bagarar ta hanyar yin zaman direshan a gabana bisa carpet, yayin da ni nake zaune a gefen gado na zubo fararen kafafuna kasa, na tokare gefe da gefena da hannaye na biyu. Imran ya sunkuyo ya leka fuskata muka hada ido, ya sakar mun lallausar murmushinsa cikin son ganin na saki jiki na daina jin kunyar tasa. Na sanya tafukana na rufe fuska ina murmushi.
Ya ce, “ZAY-NA-B”. Yadda ya kirayi sunan sai da tsigar jikina gaba daya ya kara tashi, ban iya na amsa ba. Ya ce, “Maza sauke hannuwanki daga fuskarki, kada ki sa in taba su”. Da sauri na sauke amma har yanzu ban bari mun hada kwayar ido ba. Ya ce, “Na ce ki gaya mun ciwon da ke damun ki, a kalla idan ban baki maganin sa ba zan baki shawara a matsayina na babba wanda ya fi ki shekaru. Idan kin barshi a ranki kin ki fadi, mai yiwuwa ne ya ci gaba da cutar dake ba tare da kowa ya sani ba, wanda a karshe hakan zai iya zamowa illa ga lafiyarki”.
Ya yi shiru yana mai kokarin son mu hada ido amma na ki. Na yi tunanin dukkanin maganganun shi a kan hanya suke, ba wadda babu gaskiya a ciki. Don in ban mance ba Baba Sa’idu ma ya sha gargadi na a kan barin sanya abu a rai illa ne ga lafiya da kwakwalwa.
To amma ni kaina wallahi ba na ce ga hakikanin abin da ke damuna ba, abin ya fi karfin bayyanuwa, ya fi karfin kwatance, ya fi karfin duk kokarin harshe na ya fassara shi. Unxpressable feeling kadai zan iya kiran al’amarina. Wanda in ban da ni da zuciyata da kuma Ubangijin da ya assasa mani shi a ruhi da gangar jiki, babu wanda ya san iyakar sa. Abin da na sani kawai shine, “I need Imran! I need Imran!! I need Imran a tare dani”.
To amma idan na fadi mishi ai kamar na zubar da mutuncin kaina ne, na zubar da tarbiyyar gidanmu, duk da ban san wannan abun mene ne ba? Na san ba abun kirki bane, haka ba abin alheri bane kamar yadda ya fada mani. Don haka na kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login