Showing 9001 words to 12000 words out of 34122 words

Chapter 4 - Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel

zauna tare. Sai da Malam ya yi mata alkawarin in Allah ya yarda WATARANA Zaynabu-Abu gidansu za ta koma baki daya, sannan ta hakura suka tafi.
Inna na daga gefe ta ce, “Me kake nufi da da wannan alkawarin? To kada Allah ya yarda! In ma wani mugun nufi ne kuke da shi a kaina da Zainabu, kaida Sa’idun naka, to Allah ya fiku. Bani da kowa sai shi, don haka da shi na dogara. Na kuma tabbata zai fiddani da Abu daga kutunguila da sharrin Sa’idu”.

Muna bakin motar Baba Sa’idu yana kara yi mun nasiha a kan muhimmancin kula da sallah a kan lokacin ta. Ya ce, “Zaynabu in kika kyautata sallarki, dukkan aiyukanki za su kyutata. A kullum ki yi kokari ki fi karfin zuciyarki, kada ki yarda ta fi karfinki. Ki kiyaye wadannan tsokokin guda biyu ‘harshe da zuciya’. Idan kika iya musu za ki iya ma dukkan rayuwarki. Idan suka yi kyau, dukkan al’amuranki za su yi kyau.
Ki ci gaba da yi ma Innarki biyayya, kada ki taba yarda da kallon da ake mata na cewa ita din ba ta da hankali. Idan akwai mai hankali a duniya to ita ce, tana da kirki tana da alhairi yanayin rayuwa ne ya maida ta hakan.
Kada ki yarda da yin mu’amala ko yaya take da namijin da ba muharramin ki ba, har sai kin san kanki, har sai kin san ke din WACE CE? Kada ki dinga sa abubuwa a ranki har su dameki kamar Innarki, ta fiya kullaci! Domin hakan lahani ne ga lafiya da kwakwalwa. Jeki gida Allah ya bamu alkhairi”.
Na juya ina tafiya sannu-sannu, har na kai bakin kofar gida na sake juyowa, shima Baban bai shiga motar ba kallona yake. Na dawo da sauri, da na tuna ban yi masa addu’ar da na saba ba, na ce,
“Baba Sa’idu Allah ya kaika lafiya”.
Ya ce, “Amin Zayanabu, Allah yai miki albarka….”. Muna dagawa juna hannu ni da Iftihal direba ya ja suka tafi. Ban koma gida ba sai da na ga bacewar su cikin rairayi da kurar da ke bisa hanya.
Dawawo ta kenan har zan shiga dakin Inna, amma jin muryar Malam yana ta fada yasa ni dakatawa ba don na so ba.
“Kin dauka har yanzu Zaynabu yarinya ce ne? Irin abubuwan da kike nunawa Sa’idu a gabanta zai sanya ta sanya ma kanta ayar tambaya. Abu anyi shi ya wuce shekara da shekaru ya wuce amma kullum sabo kike mai da shi.
Rabi kullum kina girma amma kina mai da kanki baya, idan don kin ga ba ta yin magana ne kike yi masa hakan a gabanta, ni na gaya miki wataran za ta tambaye ki dalilin haka, me za ki ce mata?
Allah ma muna mishi laifin da ya fi wannan ya yafe mana, balle ke mutum dan adam? Wace ce ke da ba za ki yi afuwa ga wanda ya saba miki ba? Inda Allah baya yin afuwa a garemu, da tuni bai nade duniyar ba saboda dimbin sabon da ke cikin ta? Ina jiye miki ranar da ABU ZA TA JUYA MIKI BAYA A KAN SA’IDU, wannan a rubuce yake! Don haka ki sanyama ranki salama….”
Na yi hanzarin juyawa na koma soro ina ta yarfe gumi da hawaye. Ni ZAINABU ABU wace irin rayuwa ce wannan? Babu ranar Allah da za ta fito ta fadi, ba’a yi musayen yawu a kaina ba. To ni din WACE CE? Kenan ba daya nake da sauran ‘ya’ya su Hafsisi ba, tunda kuwa ban taba jin an samu sabanin ra’ayi a kansu ba.
Kai ba wanda yake zancensu cikin gidan, kowa ya bude baki ZAYNABU…. KYAUTA… ABU.. ...
“Kada ki dinga sa abubuwa a ranki har su dameki tamkar Innarki, domin hakan lahani ne ga lafiya da kwakwala….”. Na tuna nasihar Baba Sa’idu, don haka na yi kokarin mantawa da wannan tunanin kada ya zamomin lahani ga kwakwalwa.

Sati biyu a tsakani sai ga Ya Faruk ba zato ba tsammani. Ai kuwa na kwashi murna ba ji ba gani, na rasa ina naka-saka ina naka-aje da shi don farin ciki, inda duk yasa kafa cikin gidan nan nake mayas da tawa, na like masa tamkar cingam. Shima cike yake da farin cikin ganina, ya kara kyau da tsayi, ga wani irin gogewa da yake yi, jikinshi ya koma irin na Iftihal, mai santsi da taushin gani.
A dakin Inna Dubu muke, na kwanta lamo aikinsa, cikin karamar murya na ce, “Ya Faruk Iftihal ba ta baka sako ka bani ba?” Ya ce, “Ta bani mana, fara kawo salala!”.
Murmushi na yi, “Salalar me kake so?” Ya ce, “Ki daina wannan son jikin kamar mage, musamman kwanciya a jikin maza, ba kowa ne na gari ba, wani maye ne wani dan iska ne…”. Ba ni kadai ba hatta Inna Dubu ta ji kunyar maganarsa.
Ta ce, “La’ilaha illallahu!…..” Amma shi din ko a jikinsa, iyakar gaskiyar shi ya fada zuciyarshi sak! Cikin sanyin jiki na tashi daga jikinsa na koma can gefen Inna na takure, duk raina ya baci.
Bai kara bi ta kaina ba ya jawo jakarsa ya bude ya fiddo damin littattafan yara (junior readers series) na Turanci guda hudu ya miko mini. (An African Night Entertainment, Akin Goes To School, Suger Girl, da The Boy Slave). “Ga shi in ji ta”.
Ya kuma fiddo wani takalmi (cover) rufaffe baki mai tsinannen kyau cikin kwalinsa, shima ya turo mani duk in jita. Ya sanya hannu ya fiddo ‘yar takardar littafin memo ta sha zanen shudayen furanni, ita ma ya miko mani. Na bude cikin zumudi, ga abin da ta rubuta layi daya kacal.

“Abu plz, come soon”.

Shi kansa Ya Faruk ya lura duk dokin zuwansa da nake, ya sagar min da gwiwa, don kuwa tunda na kwashi shirgina na haura kafa na yi dakinmu bai kara jin duriyata a gidan ba.
Da daddare ya saba ni nake kai mishi abinci har dakinsa, amma yau sai Zulkiflu ne ya kai masa, domin Inna Rakiyar da ta kwashe tuwon ta yi kiran duniyar nan na yi kamar ban ji ta ba.
Ganin Zulkiflu ya kawo mai abinci, ya tabbatar Abu dai fushi take yi. Ya yi cilli da jaridar da yake karantawa ya miqe ya shigo cikin gidan har dakin Innata.
A lokacin ina cin tuwo, sai kawai yasa hannu cikin tuwona yana ci, na lura cin nasa har da mugunta ne, domin kan na kai loma daya ya kai uku gunduma-gunduma, nan da nan ya cinye mun tuwon. Na tsame hannuna na koma gefe ina ta kumburi, sai ya fita ya dawo da roba da sabulu gami da ruwa a buta. Ya soma wanke min miyar kukar.
Inna ta ce, “Mulki sai mai shi”. Ya ce, “Kwarai, wannan Princess Diana ce”. Ban san sanda na yi murmushi ba. Ya ce, “To ko ke fa? Baki ga yadda kika yi kyau ba, da wannan murmushin naki mai narka zuciya, da wannan fararen idanun naki irin na Princess Diana, da wannan yalolon gashin naki irin nata. Na rantse da za ta ganki sai ta ce ke kanwarta ce. Duk namijin da Allah ya ba shi ke a matsayin mata, ya yi mai baiwa da rabin addininsa.
Ga dai kyau ga kyan hali, ga hankali da addini. Ga Alqur’ani a cikin kanki. Ga ki da daukar rayuwa da sauki ban san ki da zuciya ba. A kullum kina auna abubuwa a mizani na hankali, ki yi hukunci wanda ya dace, ban san yaushe kika koma bin son zuciya ba….”
Na toshe mishi baki cikin dabara ya cire hannun yace, “Is o.k, mun shirya ko Abuna? Taso maza muje ki gaya mun abubuwan da kika gabatar da bana nan, da kuma shirye-shiryen ki na tafiya babbar makaranta. Duk ‘ya’yan kirki suna makaranta sai ke ‘yar gatan Innarta da Ya Faruq”.
Ya juya ya fita, Inna na ta mamakin mu. Da gudu na juya na je na sako bantena, na dora doguwar riga a kai, na daura karamin hijabi, na bishi muka fita waje muka zauna a kan dakalin kofar gida.
Garin babu hasken lantarki sai na farin wata na daren goma sha hudu. Taurari birjik sun mamaye sararin samaniyar Subhana, sun kara haskakata. Da yake bayan isha ne duk almajiran Malam sun shiga gari bara, don ba duka Malam ke iya ciyar dasu ba saboda yawansu.
Na sanya hannu na lalubo ‘yar akwatuna daga cikin bantena, Ya Faruq na ba na ce, “Ga amana, ka ajiye min. Domin Baba Sa’idu ya ce kada in sake in bari Inna ta kyautar min da zobban nan, a nan gaba za suyi mun amfani”.
Cikin mamaki Ya Faruq ya soma kiciniyar bude akwatun, wani haske da ya fito ya dallare mana idanu ba shiri ya mayar ya rufe, daga inda nake ina iya juyo irin bugun da zuciyarshi ta shiga yi da sauri da sauri.
Ya sake budewa domin tabbatarwa ya fiddo daya yana juya shi a hannunsa, hasken wata da taurari na kara masa walkiya. Ya ce cikin shakakkiyar murya, “Shi…… Baba Sa’idun… ne ya baki wannan da kansa Abu?”
Na ce, “Allah shine, nima da fari na ji tsoro. Amma ya ce kar in sake in bawa Inna, to ni kuma na gaji da boyon su kullum tare dasu nake barci, har bandaki dasu nake shiga, shi yasa na matsu ka dawo”. Ya ce, “To ai nima wannan ya fi karfin in ajje shi wurina ‘sapphire’ ne (shudin yakutu) komai na iya faruwa. Shima Baban ban da abinsa bai dace da ya baki wannan ba yanzu, haba! Sai dai in kai banki”. Na ce, “Banki kuma Ya Faruq, ba kuxi ake ajiyewa a banki ba?” Ya ce, “Wannan ya fi karfin kudi, ya fi karfin zinari da diamond. Ana ajiye (valuable goods) wato kaya masu daraja a banki”.
Ya yi shiru cikin tunani mai zurfi, da alama kanshi ya yi zafi. Can ya ce,
“Gaya mun irin hirarrakin da kuke da Baba Sa’idu?”
Na gaya masa irin nasihohin da yake yi mun ne kadai a kan sallah, sai irin wulakancin da Inna na ke mishi. Na ce, “Abin yana damuna Ya Faruq, shin me yasa Inna ta tsani Baba Sa’idu ne? Me ya yi kullum yake cewa ta yafe mishi tana wulakanta shi?”
Akwai alamun rudewa sosai a tare da Ya Faruq, ya rasa amsar da zai bani, daga bisani ya daure ya ce,
“Ban san yaushe kika koyi sanya ido a kan abin da bai shafeki ba. Ba tare kika tashi kika gansu ba Abu? To ki bisu da yadda kika gansu, nima ban sani ba.
A yanzu haka Farfesa ya turo ni ne da wani al’amari mai girma wanda ban san yadda zan yi in shawo kan Innarki ba, don Malam ba matsala bane sai ita din mai tsatstsauran ra’ayi sa rashin kaunar duk wani al’amari daya shafi Baba Sa’idu. Ya turo ni ne da zungureriyar wasika zuwa ga Malam da ita Inna, kan su bada ke in tafi dake, an samar muku makaranta keda su Ifty.
Amma sanin kanki ne wannan ba karamin aiki bane ya hada ni dashi, tunda shima ya buga ya kasa balle ni? Sannan Inna Rabi na ganin mutunci na fiyeda kowa, ina tsoron abinda zai zubar da wannan mutuncin, ya rana na kaunata a zuciyarta. Saidai na gamsu da hujjojin da ya bayar.”
Daidai nan Malam ya karaso ya tadda mu, wani almajirin sa Matt ya rikon masa leda, da alama irin tsira da balanghiga gu da ya saba kawo mana ne duk dare, yana murmushi yace “yaya dai? Wa da ‘yar kanwar shi ana shawara ne?”
Muka yi murmushi dukkanmu tare da sunkuyar da kai kasa. Yace “ku tashi mu shiga gida, bana son zama cikin hasken farin watannan, yana gadar da ciwo”. Muka mike muka shiga gidan gabadaya, shi da Malam suka shige turakar Mallam din, nikuma nayi daki na kwanta.
Inna na bisa sallama tana ta sallah, wannan al’adarta ne na duk daren juma’ah kwana take sallah. Ta kan ce, “wanda ya bari du iya da Kyale-kyalenta ya rudest, ya manta da ambaton Allah da yawa ita tuba a gareshi, haqiqa yana cikin rafkanannu.
Don haka nima ta koya min, har yabi jinin jikina. Sau tari na kan bita muyi ta yi, har sai kafafuna sun sare, yawun bakina ya bushe.
A can dakin Malam me suka ce – me suka ce oho! Was he gari da asuba hi dai naga fuskar Malam babu annuri. Bayan yayi sallar asubah gari yayi Dan shaawa! Haka, misalin karfe shidda na safe ya shigo dakinmu. Inna na bisa sallaya tana lazumi har zuwa lokacin ba ta mike ba, ni kuma ina kwance bisa gado bayan da na ida sallah ban iya na koma ba.
Na dai rufe ido ne kawai cike da tunanin al’amuran rayuwa masu rudarwa, su sanya zuciyar mutum cikin wani hali na rashin sanin tabbas da rashin jin dadin rayuwar ko ta yaya. Ba a rasa ci ba, ba a rasa sha ba, ba a rasa suttura ba amma zukatan al’umma babu dadi. Wannan ita ce hakikanin rayuwar da ke faruwa a cikin gidanmu.

Da alama Malam bai san idanuna biyu ba. Ya ce, “Rabi’atu na zo miki da umarni ne ba yardarki nake nema ba. Ki yi duba izuwa rayuwarki, tun daga farkon ta har karshen ta cikin kunci take. Kina nufin a haka za ki kare ta? Wannan hukuncin da kika yanke na tsanar Sa’idu da al’amarinsa ba shi zai sa ba, ba kuma abin da zai rage sai dai ya kara dagula rayuwar Zaynabu. Ki yi hakuri ki ba shi ita ya sanya ta a makarantar, tunda BAKI FISHI IKO DA ITA BA!
In kin dauki al’amuran rayuwa da sauki, watarana sai labari, za ki ga kamar ba a yi ba.
Ke baki bar zuciyarki ta huta ba, ita yarinya kin hanata amfani da damar da Allah ya bata ta yin ilimi, wanda zai zamo gata ga rayuwar duk da ta tsinci kanta a gaba.
Ya gaya mun hujjojinsa cikin takarda, kuma na gamsu. Ya yi alkawarin duk hutu Abu za ta zo nan tare da Faruku, in ta kare hutun sai a zo a tafi da ita. In kin sanyata a daki kin kulle me za ki yi mata itama me za ta yi miki? Ki duba ki ga duk tsararrakin ta sun wuce ta a karatu, shekarunta goma sha biyu, amma har yau ba ta fara sakandire ba sai yaushe? Sai shekarun karatun sun wuce mata?
Su Hafsisi duk bana za su shiga aji uku na sakandire, amma ita ki kama kina mummukewa a daki haba Rabi! Ni mijinki ban ji dadin ki ba, abokan zamanki basu ji dadin ki ba, haka ‘yarki hakuri take da ke, duk da ta san babu wata uwa a duniya mai hali irin na tata uwar. Wannan kaunar da kike wa Abu wace iri ce tunda kuwa ita ba ta ganta ba? Wannan ba so bane, kwarar ta kike yi….. in gaya miki gaskiya in baki barta ta bishi ba za ta kullace ki, ko da ba ta gaya miki ba. Kuma IDAN NURATU CE BA HAKA ZA TA YI BA..…!!!.”
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Wata irin rayuwa ya yi mai ban tausayi da rashin galihu, amma a komi Malam Ali da mai dakinsa sun tsaya mishi. Ko taron iyaye da ake yi a makaranta Malam ne yake wanke kafa ya je a matsayin mahaifinshi da ya rasu tun bai yi nisa da karatun ba. Haka ranar taron iyayen yara Rabi ke shan lullubi ta je matsayin mahaifiyar shi, duk da idan ka dube ta za ka san a haife ba ta haife shi ba.
Don haka a girman Sa’idu, da ci gaban da aya samu a rayuwa, baya da kamar Malam da Inna Rabi. Ka’ida ne duk karshen wata ya zo duba su, ya cika su da abin arziki kamar don su kadai yake nema, baya ga tarin iyalin da yake da shi a can Sokoto.

Na taso cike da dokin, ranar zuwan BABA SA’IDU, wadda a kullum take lissafe cikin kaina. Ba don komai ba sai don na san ranar duk da ya zo, to ni ranar take sallah. Sabbin dinkuna da kayan ‘ya’yan gayu da yake kawo mini kamar shago za a bude mini, cakulet da biskit kamar (super-market) din su gare shi, don haka duk hakorana suka cinye da zaki suka gwaigwaye kamin in soma famfara, sabbin littattafai da sabbin uniform wannan duk wata ne sai ya sake mini, don haka nake daban a cikin yaran gidan dama garin Gwarzo baki daya, babu ‘yar gata kuma ‘yar gayu kama na. Ga kuma kyawun sura.
Ribbon kuwa Baba Sa’idu dozin-dozin yake saya mani kala daban-daban. Ya Faruk ya zauna ya jera min su reras a kaina, in zamo kamar wata ‘yar Turawa, sai ka rantse da Allah Baba Sa’idu bai san ciwon kudinsa ba in dai a kaina ne. Allah ne ya hada jininmu da wata irin kakkarfar kauna, sai dai babban abin da ke bani mamaki, yake kuma sanyaya min jiki shine, duk wannan hidimar da Baba Sa’idu ke min, ko kadan baya burge Rabi, haka ko sau daya koda wasa bata taba sanya hannu ta taba kayan da suka fito daga hannun Baba Sa’idu ba.
Kwankwalatin lemu ne da ni guda talatin, a karkashin gadon Rabi me fameka, kullum sai in ciri daya in jefa a kofi, ranar da suka kare kenan ita ce ranar zuwan Baba Sa’idu. In ina wannan kirgen, Rabi kallona take kawai, sai dai ba ta magana, na san tsabar takaicina ke hana ta magana. A raina sai in ce, “Inna ai ke rayuwarki sai ke, tunda Malam da Ya Faruk ma basa burgeki, shi Baba Sa’idu wane ne da zai maki gwaninta?”
Ni dai haka nan nake son Baba Sa’idu saboda kirkinsa, saukin kai da haibarsa, ba shi da girman kai ko kadan, haka yadda yake sonmu ni da Ya Faruk yake kuma janmu a jiki, ko ‘ya’yan cikinsa basa samun hakan.
Tun karatun sakandire ya so ya dauki Ya Faruk ya koma gidansa ya yi karatu a can Sokoto, Ya Faruk ya ki don a lokacin babu wani babban da namiji a gidan kusa da Malam sai shi, sai ko yanzu da manyan almajiran Malam su Lawal da Harisu suka tasa.
Baba Sa’idu Malam ya dankawa alhakin nemawa Faruk gurbi a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login