Showing 3001 words to 6000 words out of 34122 words

Chapter 2 - Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel

bautar aure. Na kuma sha jin Malam na cewa, ‘abin da iyaye suka yi a kuruciyarsu shi ‘ya’yansu suke maimaitawa, wato barewa ba ta gudu danta ya yi rarrafe…..”
Ya yi hanzarin katseni ta hanyar girgiza kai da cewa, “A’a, zamani ne ya sauya Abu. ‘Ya’yan yanzu bama koyi da iyayenmu sai da Bature. Da muna koyi dasu da abubuwan da ke faruwa a yau basu faru ba. Kuma Da a yau ka haife shi ne amma halinsa a duniya yake daukar abinsa. Ki kiyaye nasihar Inna Rabi Abu”.
To a haka rayuwarmu ke tafiya, cikin rufin asirin Allah da tarbiyya ta gari. Lokacin da Ya Faruk ya zana jarrabawar fita sakandire, lokacin ne ni kuma na zana ta kammala firamare wato (Gwarzo Special) da nake zuwa. Malam mutum mai hanyoyin ma’aikatan gwamnati da dama. Akwai wani almajirinsa wanda ya tashi a gidansa, a yanzun kuma yake Farfesa a Jami’ar Danfodio wato (UDUS).
Asalin dangantakar Malam da Proffessor Sa’idu shine, an kawo mai shi almajiranci daga wani kauye a Katsina. Da Dagacin yankin Gwarzo ya nemi da a kai yara makaranta, a wancan lokacin babu waanda Malam ya tuna ya kuma yiwa sha’awar yin boko kamar (Sa’idu-Baki) yadda sauran almajirai ‘yan’uwansa ke kiran sa kenan saboda bakar annakiyar daudar shi. Ya fi kowa datti cikin almajiran, haka ya fi kowa kazanta, inda duk ya wuce warin dauda da zarnin fitsari kawai za ka ji, amma haka nan Malam ke son shi fiye da sauran almajiran, don a cewarsa; Sa’idu duk ya fisu hankali.
Kullum ya je makarantar bokon ya dawo abincinshi na nan cikin kwano Rabi ta ajiye mishi, sai kuma yai mata ‘yan aike da ba a rasa ba. A yadda Ya Faruk ya gaya mini, Inna Rabi ma na son Sa’idu, kuma da yake yana da cutar (ulcer) sai ba ta wasa da abincinshi, ko ba ita ce da girki ba in Sa’idu bai samu abinci ba sai ta daura mai tukunya ko ta jika mai garin rogo ta zuba zuma a ciki ta ba shi, haka duk ‘yan tsummokaran yaran gidan da Malam ke riko in sun tsufa ba ta suke ta bawa Sa’idu.
Da sallah kuwa babba da karama, sababbi take dinka mishi, haka in zai je kauyen su Bindawa za ta hada mishi tsarabar Gwarzo niki-niki ya kai wa Innarshi da kudin motar zuwa da dawowa. Shima in zai dawo duk tsarabarshi ta Katsina su Aya da sauransu duka na Inna Rabi ne, don haka a bakin jama’ar gidan, Sa’idu dan dakin Inna Rabi ne.
To ilimin boko dai babu matsayin da baya kai mutum a rayuwa, don bayan sakandire gaba dayan karatun Sa’idu a waje ya yi shi da taimakon gwamnati da ke daukar dawainiyar karatun dalibai a wancan lokacin. Yau Sa’idu-Baki shine da matsayin V.C watau (Vice-Chancellor) Proffessor Sa’id Salisu Bindawa, na Jami’ar Danfodio baki daya.
Kuma anyi sa’a shi Sa’idun irin mutanen nan ne da basa manta alkhairin da aka yi musu komi kankantar shi. Balle shi yana ganin Malam da Rabi, matsayin wani tsaninshi na duk abin da ya zama a rayuwar shi, tunda iyayen da suka haife shi kasa rike shi suka yi saboda talaucin su da rashin dogaro da kai, suka turo shi almajirancin da ya zame mishi gata ba tare da sun kara bi ta kan rayuwar shi ba, sai dai shi ya neme su.
[7/11, 3:57 PM] +234 706 160 2791: Sai ta sa kuka a hankali tana cewa,
“Ni ban ce kada Abu ta yi karatu ba, amma duk makarantun Kano a rasa wadda za a sai an tsallaka na Sokoto? Bana son Abu ta gusa daga kusa dani ne ko ya ya, ina tsoron abin da ka je ya zo. Bana son abin da zai bata ran Abu, bana son abin da zai illata mutuncinta. Duk wannan kaunar da take mishi ai don ba ta san shi din wane ne ba, wane irin azzalumi ne?
Kai ma ka sani da daga ranar ba ta kara ganin sa da GIRMA. Ina kokarin in kare GIRMANSA a idanun ta, in kare nata a idanun duniya, amma su basa gani, ai shi kenan, ga ku ga Abun nan ka ba shi ya tafi da ita, sai dai duk abin da ya biyo baya daga baya kar ayi kuka dani”.
Ta fita tsakar gida ta bar mishi dakin.
Wayewar garin wadda ta kasance Juma’a sai ga iyalin Farfesa, wato matan shi guda biyu sun zo da kansu, ya turo su kara baiwa Inna Rabi hakuri ta ba da Abu. Uwargida Haj. Sa’a da Amaryar ta Haj. Azumi, dama dai tuntuni babu shiri tsakanin Haj. Sa’a da Innana, gaba ce mai tsanani a tsakaninsu, don haka tana shigowa ko dakin Innar ba ta kalla ba dakin Inna Dubu ta shiga.
Tana tafiya kai a sama, kai a dage kai ka ce wata matar shugaban kasa ce ba matar Sa’idu ba. Nima dai tuntuni Allah bai hada jinina da Haj. Sa’a ba, saboda girman kanta, mace ce mai dagawa da yawa, na tsani mutum mai girman kai da wulakanta talaka, to ita kuma halin ta kenan, ko ruwan gidan bai isa ta sha shi ba, da ruwan ta na roba take zuwa a bayan mota da sunkin abincinta cikin foil-paper, in ta ji yunwa sai ta je motar ta ci, ta sha, sannan ta dawo.
Tabarmar gidan kuwa babu wadda ta isheta zama, sai dai ta zo da katuwar darduma mai laushi irin ta zuwa picnic din nan ta baje a dakin Inna Dubu, ta kishingida suna kwasar hira da yake ‘yan’uwan juna ne. An ce asalin ta ma a nan gidan Innar ta rike ta, Malam ya aurawa Farfesa, amma da yake Hajiyar birni ce shi Farfesa bai san hakan take yi ba in ta zo garin.
Yawanci za ka samu wanda tushen sa talaka ne futuk in Allah ya yi mishi arziki rana daya, shi ke yin irin haka, ba wanda ya tashi ya kuma girma cikin arzikin ba, kamar amarya Hajiya Azumi kenan. Mace ce mai saukin kai, faram-faram da daraja kowa da zama ko mutunci ya hada ta da shi.
Hajiya Azumi tamkar kawa take da Rabi, don basu fice tsararrakin juna ba, in da akwai wani da ya shafi Farfesa da Inna Rabi ke kulawa to Azumi ce, ina mamakin hakan, tunda kuwa ko ‘ya’yan da ta haifa ita Azumin basu tsira daga kiyayyar Innar ba (su Iftihal), amma ita in ka gansu suna hira rimi-rimi sai ka rantse da Allah Ya da Kanwa ne.
Wannan na daga dalilin da yasa Farfesa Baba Sa’idu ya turo ta ga Inna Rabi, don ya san tana ganin mutuncinta fiye da na kowa nashi.
Sun nitsa da hirar duniya Hajiya Azumi ke gaya mata makasudin zuwan nasu takanas nata ne, ta ce, “Ashe ni ba zan iya rike Abu tamkar su Aziza ba Rabi? Na yi mamaki da Alhaji ya ce dani wai ke kika ki amincewa da zaman Abu tare damu, wallahi kin ji na rantse Iftihal kullum ba ta zance sai na Abu, haka dan’uwanta, ba yadda za a zauna a mike bai ambaci Abu ba.
Ba fa dauke miki ita zamu yi kwata-kwata ba Innarmu, duk hutu tana nan a dakinki. Kaunar Baban su Aziza da Abu Allah ne ya hada ta, mai zai sa ki kasa ganewa? Ba a san me Allah zai mai da Abu a nan gaba ba, a dalilin karatun nan har al’umma su amfana da ita”.
Inna ta yi murmushin da bai kai zuci ba, ta ce, “Ni abin naku ku da mijinku ya daina bani haushi ya koma bani mamaki”. Azumi ta ce, “Mamakin me kuma Innar Abu?” Ta ce, “Mamaki mana. Yar daya jallin jal da Allah ya bani kun sa mata kahon zuka, kun dage sai kun rabani da ita duk da bataliyar ‘ya’yan da Allah ya baku, saboda hadama ko saboda mene?
Ku daina cewa don Abu ta yi karatu za ta je gidan ku, kawai ku fito fili ku ce kuna so ku kwace ta ta zauna tare da ku, in makaranta ce har Sokoto ce za ta gayawa Kano karatu?” Azumi ta yi dariyar cin nasarar ganin ta fara samo kan Innar, ta ce,
“Ayya Innar Abu! Ke din ce kin iya haihuwa, Abun taki abar so ce ga kowa, ga fara’a ga farin jini, yarinya ce mai shiga ran mutum farat daya.
Idan aka samu irin su Abu suka yi ilimi mai zurfi suna da matukar amfani ga al’umma, su kuma zamo ababen alfahari ga iyaye. Ba kya gani komi nata, nutsuwar ta da takun rayuwar ta daban ne da na sauran yara? Ki daure ki bamu Abu, da yardar Allah na tabbatar miki ba za ki yi dana sani a kan hakan ba”.
Shima Faruq tunaninsa daya ne da na iyayen dakinsa, don dai baya son Inna Rabi ta kullace shi ne kamar yadda ta ji haushin Malam da ya sanya baki. Yana ganin in an bar Abu a kauye, ba ta dandani rayuwar birni irin ta su Iftihal ba, ba ta kuma yi karatu mai tsada ta goge irin Aziza ba, an tauye mata hakki, duk kyawun nan nata da yalolon bakin gashinta maras gyara, a kauye za ta kari rayuwar ta, watakila ma a dauka a baiwa wani gardin kauyen yadda aka yiwa su Halima.
Shi kuwa mai farin ciki ne da duk wani ci gaban kanwar sa tilo. A dan zaman da ya yi na shekaru biyu da iyalin Farfesa, sai ya rika tambayar kansa shin su rayuwa suke, ko ko a daji suke?

Rayuwar gidan Vice-chancellor Proffessor Sa’idu Bindawa, a bar kauna ce a bar sha’awa, a bar so ga kowa. Irin rayuwar nan ce maras takura da rashin sanya ido, kowa ya yi abin da ya zaba ma rayuwar shi kamar a Turai.
Wannan na da nasaba da zaman da sukai na shekaru goma a kasar Ingila inda shi Farfesa ya yi karatu tun daga digirin farko har PhD, inda dukkan su suka fara karatu. Ba rikici ba hargitsi, babu tsana balle tsangwama a tsakanin ‘ya’yan su.
Ba wai dukiya ce ta yi yawa ba, ko facaka ake da kudi, illa rayuwa ta rikakkun ‘yan boko ziryan, komi akwai isasshe, ga kan kowa a bude ilimi ya wadaci kowannen su. Hajiya Sa’a ma’aikaciyar gidan talabijin ce na (NTA), inda ita kuma Azumi take (gynaecologist) a General Hospital na Sokoto. Gidan Proffessor yana cikin Jami’ar Usman Danfodiyo, wanda ya fi gaba dayan gidajen Malaman Jami’ar kyau da tsari kasancewar shi gidan V.C baki daya.
Inna Rabi dai sun taru har Malam sun tattamketa da jijiyoyin ta, musamman ita Haj. Azumi. Duk wata hujja da Innar ta kawo ta soketa, ta ce ba ta amince za ta iya rike mata Abu kamar yadda ta dauki Innar Uwar ta ba.
Malam Ali ya dubi wadannan kasaitattun mutane, basu kyamaci nashi ba sai shi? Ba wannan yake ji ba, illa tattalin mutunci da martabar Zaynabu Abu, wanda muddin ta gusa daga kusa da shi da Rabi, ba mamaki ya FADI a nan gaba. Abin da suke ta mummukin sa a tsakanin su shekara da shekaru ya fito duniya ta sani; GIRMA YA FADI!
To amma shi kansa zai so Abu ta yi ilimin da watarana zai ganta haka a kasaice kamar su Hajiya Azumi, ko ko ta rika taimakon al’umma kamar yadda Sa’idu ke yi ta fannoni da dama, ba wai ta hanyar kudi ba kadai.
A yau matasan da ke neman aiki a garin Gwarzo in dai har suna da takardun nasara masu kyau (graduates) na diploma ne ko NCE, ko ko babban digiri, wurin shi suke zuwa ya hada su da Sa’idu, kamin dan lokaci za su zo suna gode masa, suna sanar da shi an samar musu aiki da albashi mai tsoka.
Haka masu neman gurbi a jami’o’i saboda yadda gurbin karatun jami’a ya zama a wannan kasa tamu, sai ga masu iyaye a gindin murhun. Almajiran Malam da Sa’idu ya ya samarwa gurbi a jami’o’i ba za su kidayu ba, don haka al’ummar Gwarzo kullum cikin amfana da Sa’idu suke, tare da shiwa Malam Ali albarka saboda ci gaban da ‘ya’yansu ke samu a dalilin sa.
Haka matasa wadanda Allah bai basu daman yin karatun ba, yana hadasu da gwamnati su samu taimakon sana’o’i na dogaro da kai. Wannan dalilin da wasu da yawa da ba zasu fadu ba, ya karfafa shi da ya barsu su je da Abu, to amma bai yarda a yiwa Abu aure nan kusa ba, sai ta mallaki hankalin kanta, ta san WACE CE ITA?

To ga ‘yan bokon, wannan ai ba wani abu bane da har sai Malam din ya fada, su dama basu da burin da ya wuce ayi ta bokon har a kure shi in ana kurewa. Da wannan ZAINABU-ABU ta koma Sokoto, gidan Baba Sa’idunta.

***
ZAYNABU-ABU MAI TAGWAYEN SUNA!
A duk yadda dan Adam ya samu sauyin rayuwa ko y ya ne, imma ta fannin abinci, suttura ko muhalli, ya kan samu sauyin zuciya dana surar gangar jiki gaba daya. To hakan ce ta faru dani a gidan Baba Sa’idu.
Duk da irin sabuwar rayuwar da na budi ido na samu kaina a ciki, hakan bai hana ni tuno gida ba da wadannan mutane guda biyu; Malam da Inna Rabi. Sai kuma na samu kaina da jin haushin kaina mai tsanani na wautar da na yi na amince da zaman gidan Baba Sa’idu, bayan a da shine babban burin rayuwata, wato na ganni kusa da Baba Sa’idu.
Dalilin kuwa shine, kwata-kwata tsarin rayuwarsu ya sha banban da tawa, da irin rayuwar da na taso a cikinta. A ganina irin wannan rayuwar bata dace dani ba; ‘yar mallam jikar mallam.
Rayuwa wadda babu Allah ko daya a cikin ta sai rayuwar tsurar ta. Sai a kwana a wuni ba a ambaci Allah ba, balle a ja carbi, sallah ma ba kowa ke yi a kan lokaci ba, balle ayi maganar jam’i, don shi Baban ma kwata-kwata baya zaman gidan. Idan ya tafi cikin makaranta tun karfe takwas na safe sai shida na yamma yake dawowa cikin gidan, haka nan kullum yana bisa hanyar meeting ko seminar a Abuja ko Lagos da sauran manyan birane.
Ban taba ganin mutum (busy) irin Baba Sa’idu ba, bautawa bokon yake da karfinsa, lafiyarsa, lokacinsa da aljihunsa, yayin da jami’ar Danfodiyo ke kara bunkasa da samun ci gaba (inaudiably) a dalilin kwazo da sadaukarwa irin nasa.
Rayuwar gidan rayuwa ce da ke sawa mutum ya manta da Allah, da irin tarbiyyar da ya taso a cikin ta saboda jin dadin da ke cikin ta, sakaci da rashin kwaba ga ‘ya’yan su, abin har ya so yayi yawa.
Duk da haka ina kokari naga cewa ban kaucewa tarbiyyar Rabi ba da koyarwar Mallam. Hakika duk wanda yasan rayuwar Malam Ali da iyalansa, itace rayuwa a bar koyi. Babu abinda suke bari ya shagaltar dasu daga bautar Allah da kiyaye sallah. Kuma babu shakka shima Baba Sa’idu a wurin su ya samu wannan tubalin na kiyaye sallah, domin ya kan ce mun tana hani daga aikata alfasha da aikin munkari. Irin yadda su Iftihal suka ga bana wasa da sallah, ko me muke yi da zarar lokacin sallah yayi zan tsame kaina har sai na bada farali, shine sanadiyyar da suma suka dage, duk sanda nayo alwala suma zasu mike su dauro alwala, wannan ba karamin fa ranta ran Haj. Azumi yake ba.
A ranar dana zo Aziza bata nan tana porthercort hutu gidan Antinta Isaita kanwar Haj. Azumi, Iftihal kuma tana makaranta. Bazan manta ba zugum nayi, na zubawa akwatun kifaye da ban taba gani ba ido (aquarium) kifaye nata gudu a ciki masu ruwan kumfar zinare cikin mamakin ilmi da fasaha na bature, wanda yayi tunanin ya zabo kyawawan kifi masu rai, ya zuba cikin wannan gilashi. Haj. Azumi ta umarci Gaddafi (Gambon su Aziza) kuma autan ta, da ya rakani dakin su Aziza, in yi sallah inyi wanka in kwanta in huta, don kuwa ba karamar tafiya muka kwaso ba ta yini guda cur.
Da nayi wanka na canza zuwa doguwar rigar shadda ruwan makuba, da aka yiwa dinkin babban riga. Haj. Azumi ta kira ni muka ci abinci tare, ni da ita da Ghaddafi, tana mun hiran shirmen Gaddafi cikin sugar Jan ra’ayi na da sake dasu, ga yadda na lura ta fi son Gaddafi fiye da su Aziza, ko don shi kadai ne namiji ban sani ba. Cikin murmushi kuma ta ce,
“Abu ya ya? Za ki zauna dani ne ko ko wajen Hajiya Sa’a za ki zauna wurin su Faruq?”
Ni kam cikin dan lokaci Hajiya Azumi ta saye ni kaf da kirkin ta, ganin ta nake tamkar Inna ta, gata dai ba wata babba ba sosai, ga kuma kissar zama da mutane, komi nata da na ‘ya’yanta burge ni yake, yadda take nan-nan da ni sai ka ce ba ta taba haihuwa ba. Ban san sanda na ce,
“Ni dai da ku zan zauna, waccan matar bata dariya”.
Ta yi dariyar jin dadi ta ce
“Ni kuwa zan gwada miki kauna Abu, ba za ki yi kewar Inna ba insha Allahu. Tuni an sanya ki makarantar su mutuniyar ki, da zarar Azzy ta dawo jibi da yardar Allah za ku fara zuwa”.
Cikin kwanaki biyun shakuwa mai tsanani ke shiga tsakanina da Mama (yadda ake kiran ta a gidan) hatta abinci tare muke ci, in za ta tafi aiki sai ta sanyamu a gaban motar muje in an sauke ta sai direban ya dawo damu.
Fadin murnar da Iftihal ta yi da zuwana ma ba zai fadu ba. Ranar lahadi da Mama ba ta da aiki daukarmu ta yi ta kai mu wajen wankin kai, ta yi mun sayayya mai yawa. A ranar ne kuma Aziza ta dawo.
Farkon ganina da Aziza ban san cewa ba Iftihal ba ce, saboda kamannin su (identical twins). Yara bula-bula dasu kamar hura su ake sai ka ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login