Showing 21001 words to 24000 words out of 34122 words
Chapter 8 - Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel
magana, tunda na fara tunanina bai katse ni ba.
Ya yi nacin ya yi juyin duniyar nan amma na ki magana har ya gaji ya zuba mun ido da alamun ranshi ya baci, duk kuma sai na ji babu dadi. Wasu hawaye suka zubo min na sanya bayan hannuna ina sharewa. Ya mike zai fita ba tare da ya ce dani komi ba, har ya kai bakin kofa ba tare da ya juyo ba, ban san sanda na samu kaina ina mai cewa cikin rishin kuka “Ka yi hakuri Ya Im, mara ta ce take ciwo!”.
Ya juyo a hankalce ya dawo, hannayenshi duka biyu cikin aljihunshi, ya dube ni sosai, na nutsar da kaina kas, kamar in ce, “Wayyo Allah!” Ya fi mintuna biyar yana kallo na kamin ya ce, “Al’ada kike yi ne ko zaki yi Zaynab?’
Da wata muhimmiyar kunya da haushin kaina mai tsanani suka taso suka kara lullube ni ban san sanda na fashe da kuka ba, yau tozarcin duniya na gama jin shi a rayuwata, da wanne ido zan daga in kuma duban Ya Im? Na wulakanta kaina na tozarta kaina na yi abin kunya.
Imran ya ce dani kamar cikin tsawa, “Ba tambayar ki nake ba za ki sakar min sauti sai kin tara mana mutane a ka?” Na hadiye kukan gaba daya ji kake “mukut”, sai hadiyar rai nake tare da fyace majina da bakin dankwalina. Ya sake maimaita tambayar sa, wannan karon babu alamun wasa cikin maganarshi. Jikina na karkarwa na ce da shi, “A’a, ban ma jima da gamawa ba”.
Ya yi ajiyar zuciya ya sassauta murya ya ce, “To meye abin kuka? Daga na tambaye ki don in san maganin da ya dace in amso miki sai ki bare baki ki fasa min kuka a zaci ma wani mugun abu nake miki, yanzu idan su Azizah suka zo suka ga irin wannan kukan da kike kamar na fitar rai suka tambaye ki me za ki ce musu? Maza share hawayen nan ki mai da mood din ki, mu yi karatun tun ban sa kafar wando daya dake ba”.
Na koma cikin nutsuwata, na share fuskata tas na dauko littafin na budo mishi aikin. Ya zauna gefena yana dubawa, ya ce, “An excellent handwriting! Zaynab haka kika iya rubutu?” Sai yanzu ne na yi murmushi, domin dai ni mutum ce mai son yin abin yabo a yaba mani, yana kara (encouraging) dina.
Cikin dan lokaci Ya Im ya fahimtar dani abin da na kasa har ma da abin da ban sani ba, da dabarun cimma nasara a darasin ‘Physics’ da muke cin kwakwa a kan shi ni da su Azizah. Ji na yi in zamu kwana muna karatun ba zan gaji ba, don kuwa Imran ba dai hikimar koyarwa ba.
Imran S. Bindawa cool ne, reserve! Ga wani lafiyayyen kamshi da ban taba jiba dake fita bakinsa (Albaan mouth-fresh) in yana magana. Sai nake tambayar kaina dama akwai wadanda Allah ya halitta da kamshin baki ne? Ko da yake in ban manta ba ai Iftihal ta ce Yayanta daban yake a cikin al’umma.
A haka su Azizah suka shigo kwanciya suka tadda mu, karfe goma sha daya da rabi na dare, don su tuni har sun yi barci a falon taso su aka yi. Suka saki baki galala! Suna kallon mu don basu zaci har lokacin yana nan ba. To shi kuma sai ya bi duk ya daure fuska, ya buga musu tsawa ya ce duk su dauko nasu littafin.
A take kowacce ta shiga taitayinta barci ya nemi inda ya fito. Karatu ya dawo sabo, ya hadamu gaba daya yana koya mana, bai kyale mu ba sai da ya tabbatar mun gane, ya bamu aiki muka gwada mai a kan idonshi ya gani, sannan ya fita ya ja mana kofa, ko kallon mu bai kara yi ba.
Azizah tana ta korafin ita dai da Abba bai ce Imran ya koya min karatu ba, gashi nan yanzu ya jawo mana masifa sai ya mai damu wasu alhuda-huda, su kam sun shiga uku kenan. Iftihal dake ta fi kowa son Ya Im cikin gidan ta ce, “Ai ba zama zai yi ba, baki ji Abba ya samo masu aiki ba? Yanzu haka next week in ya tafi duk da fadan shi ke da kanki za ki yi kewar shi”.
Sai na ji duk hankalina ya tashi, Imran zai tafi aiki, ina? Ni kuma ina zan sanya rayuwata? Kasancewana tare da shi a yau na wani lokaci mai tsawo, ya kawo sauki 50% cikin ciwon zuciya da gangar jikina, ya wanke wani babban kaso na ciwon shi dake damuna, ya kuma kara gina wani makeken al’amarin da ya wuce na jin shi a gangar jiki kadai, maimakon haka, sai ya shigo har cikin bargo da kasusuwana.
Ni kaina na san yau idan na ce idanuwana sun ga barci, to wannan karya ne. cikin kowanne juyina IMRAN ne, cikin kowanne kiftawar ido IMRAN ne, cikin kowanne zama da tashi IMRAN ne, cikin kowanne kwanciya da mikewar kafa IMRAN ne, cikin kowanne mafarki da ido biyuna shi din ne dai kadai ya mamaye, ya babbake yayi babakere a ko ina, bai barni da ko sako daya da zan sanya tunanin kaina ba.
Da safe na sanya (uniform) dina cikin sauri ne saboda makarar da na yi, su Azizah tuni sun gama suna diniing suna karyawa, wannan ya samo asali ne da rashin isasshen barcin da na samu daren jiya, bayan sallar asubahi kuma wani nannauyan wahalallen barci ya yi awon gaba dani mai cike da mafarkai na ni da Y Im cikin wata irin rayuwa mai dadi, da kyar Mama ta tashe ni.
Na ja cambas na daura na juya a hankali ina kallon kaina a mudubi. Ban yi mamakin ‘yar zabgewar da na yi ba cikin ‘yan kwanakin nan da duniyar Imran ta sanya ni gaba. Banda su Azizah shiriritattu ne ya dace su fahimto sauyuka da dama a tare dani, to ita kanta Mamar su haka take, ko cikin dare ba ta rabo da call na emergency case, don haka ba ta samun nutsuwar da har za ta fuskanci kananun abubuwa kamar wannan.
Na ci gaba da kallon kaina cikin mudubin, ba wata kwalliya na yi ba ban da mai da farar powder da na shafa, amma ni kaina ina alfahari da ‘yar zagayayyar kayatattar fuskata, wadda in ba son kai irin na dan adam ba, zan iya cewa alhamdulillahi, babu abin da Allah subhana bai kawatata da shi ba.
Fararen idanu, giran ido kakkaura, dogon hanci da tsararren baki mai daukar hankali. Idan kuma aka yi maganar zubin halitta abin sai shukrah ga Maqagina, domin ko yaro dan shekaru biyar ba zai iya yi min kallo daya bai maimaita ba.
Farina kuwa ba fari ne sol ba, ja ce ni kalar uslin Abzinawa na Damagaram. Ko a farce ba za ka ce na hada jini da Bahaushe ba, domin komi nawa har yatsun kafata irin na Inna na Rabi ne.
Na dauki jakata (school bag) na rataya a kafadar hagu, nasa kai zan fita, Imran na sawo kai zai shigo sai muka yi karo garam, da goshinmu, kasancewar nima ba baya ba ce wurin tsawo zamu yi kafada da Imran, illa ya nuna min kaurin jiki.
Na yi saurin ja da baya ina ta faman ba shi hakuri don ni har ga Allah ban ji tahowar shi ba, kasancewar shi mutum mai nutsatstsen taku, duk na gigice saboda yadda ya yi min jiya na dan fara shakkun sa, da alama dariya na ba shi. Ya ce, “Ni ne mai ba da hakuri Zaynab, kin kwana lafiya?”
Kalaman shi sun matukar bani haushi, wannan rainin hankali ne, kuma kamar son jin halin da mutum ke ciki ne, wanda shi din ba zai maganta mini ba, ba sai ya kyale ni in ji da ciwona ni kadai ba?
“Don haka maganar na kwana lafiya ko ban kwana lafiya ba, ba damuwar ka bane….”
Magana nake a zuci, ban san cewa har ta fito fili ya ji ba. Ya yi murmushi kamar bai ji ni ba, ya sake matsowa gareni ya russuna ya dauko min jakata da ta fadi a dalilin karon mu ya miko mani, ya sake cewa,
“Kin kwana lafiya Zaynab?”
Wannan mugun mutum ne, bani da zabi ban da na daga mishi kai domin ya gama kashe mun jiki da fitinanniyar muryarshi. Ya ce, “Amma ni kin ga ban kwana lafiya ba, Zaynab saboda ke!”
Ya ci gaba da mugun murmushin, yana magana ne kasa-kasa yanda in har akwai wani cikin dakin bayan ni dake kusa da shi, duk kasa kunnen shi ba zai ji abin da yake fadi ba. Na kyabe baki na ce, “Allah yai maka magani”. Dariya ya yi ya ce, “Ya yi mana magani baki dayanmu za ki ce Zaynab. Ba gara ni ba, amma ke maganin naki ai mai GIRMA ne, wanda ni kadai ke iya maganta miki, kuma ba zan yin ba, saboda ni mai hankali ne sabanin ke da kuruciya ke dawainiya dake”.
Ya sake jifana da mugun murmushin, sannan ya miko min ledar da ke hannunshi, tuni na yi suman tsaye. Wani takaici ya zo ya tokareni a kahon zuci kamar in yi aman zuciya don bakin cikin maganganun da ya yaba mani. Bai kuma bani damar in yi magana ba ya juya yana cewa,
“Ki yi maza ki tafi makaranta kin zauna nan kina shirme, tun baki tafasa ba kenan wannan in kika kara shekaru uku a gida ban san me za ki zama ba, gara Abba ya tattaraku da zarar kun kare makarantar nan ya ba wani mai tsautsayin sadakar ku. Balle ke Zaynab irin jarababbun matan nan ne wallahi (nympho), duk wanda ya aure ki ya shiga uku”. Ya juya zai fita yana mun dariyar keta, na ga idan na bari ya fice ban yi wani abu ba na fadi ba nauyi. Idanuna suka ciko da kwalla, bayan kadawa da suka yi suka yi jawur na ce, “IMRAN!”
Tunda yake yaran gidan baki dayansu babu wanda ya taba gigin kiran shi da Ya Imran ma balle IMRANAN gabagadi. Iyakacin kowa YA EM, don haka ya hanzarta juyowa cike da mamaki ya dube ni, da na wulwula ledar da ya bani na maka masa, niyyata ta fasa mun wannan bakin dake tozartani, ta illata wannan halittar da ke jan zuciyata ga abin da yake goranta mun a kanshi.
Amma sai ya yi saurin dukawa ledar ta wuce ta saman kanshi, kayan shafar da ke ciki kowanne ya yi nasa wuri. Na yi murmushi na ce, “Baka da abin da za ka bani Imran, kamar yadda baka da maganin da zai yi maganin ciwo na, don ‘yan mazan naka da kake tinkaho, bai yi isar da zai isar da jarababbiya kamana ba. Amma ka san ina da surar da in maza dari nake so a rana zan samu, kuma daga yau zan fara, Allah za ka yi nadamar wadannan kalaman da ka gaya min”.
Na wuce shi nan dafe da lebban shi yana girgiza kai kamar kadangare yana mamaki na gasken-gaske amma ya kasa magana. Kan mu zo makaranta kiris ya rage in yi kuka a gaban su Azizah, amma na yi kokari na daure na cije ina ta kukan zuci. Hirarrakinsu ko daya ban tsoma baki ba, haka fuskana babu annuri.
A cikin aji ana ta aiki, amma ni ban rubuta komai ba, ashe wai har aikin aji (class work) malamin ya bayar suka yi suka gama ni ban sani ba, na yi nisa a tunanin rashin mutuncin da Imran ya yi mani.
Malamin yana bin kowa yana sa mishi hannu har ya zo kaina, ya ce, “Ke ina aikin naki?” Na yi firgigit na dube shi, a sannan ne Azizah da Iftihal dake bencin bayana suka shiga zungurina da nasu litattafan, na mika hannu ta karkashin bencin na karbo na fito masa da shi kamar daga jakata na fiddo.
Kuskuren da na yi shine, duka biyun na hada masa wato na Azizah da na Iftihal na kuma ba shi ba tare da na duba ba. Ya karba yana dubawa duka biyun, ya daga murya ya ce da ‘yan ajin, “Wace ce Azizah Sa’idu?” Gaba daya aka nuna Azzy da ta yi tsuru-tsuru. Ya sake cewa, “Iftihal Sa’idu Bindawa?” Wata kabila Ngozi ta nuna Ifty.
Ya nuna ni ya ce, “Wannan kuma fa ya sunan ta?” Aka ce da shi, “Zaynab Aliyu”. Ya ce, “To ku taso dukkan ku mu isa wurin principal, yau idan uban ku gwamna ne ya daure ni har sai igiya tai rara. Dabbobin banza ni za ku mai da shashasha! Na zo duniyar na kuma je makaranta tun kan ayi cikin uwarku balle ayi tunanin haife ta, shine za ku mai dani sakarai?”
Su Azizah suka tsugunna a kasa suna ta ba shi hakuri har da hawayensu, don ba abin da suka tsana a rayuwarsu irin a kai su wurin shugabar makarantar a ce sun yi laifi, don ta san Baba Sa’idu farin sani a take za ta gaya masa.
Ni ko ko gezau, don zuciyata ta riga ta kekashe da bakin cikin Imran da ya yiwa zuciyata katutu, don haka don an duke ni gani nake dukan ba zai shiga jikina ba ko da kuwa da bulalar karfe ne.
Ya ga ni ban ba da hakuri ba, karewa ma wani gefen daban nake kallo kai ka ce ba dani ake case din ba, kuma dama shine (discipline master) din makarantar baki daya, kowa ya san Malam GG watu Garba Gumel a wurin mugunta babu na biyun shi duk fadin makarantar.
Ya ce, “Su Azizah su koma su zauna, ni kuma in taso in biyo shi”. Ban yi musu ba na karkade rigata na bishi a baya, Iftihal ta biyo ni tana ta ba shi hakuri ya daka mata tsawa ya ce ta koma mazauninta, ya kuma sanya monitar ajin Suhaila ta yi mai gadinsu, idan suka fito ta kira shi a waya ta gaya masa.
Tafi-tafi ina bin shi kamar jela, ina gayawa kaina na cancanci a hora ni, wauta ce tun farko ta hanani gane Imran ai ba tsarana bane da zan kallafa zuciyata a kansa, don haka kome GG da Imran suka yi min dai-dain su ne.
Wani kazamin (student toilet) ya sani in wanke kana tafiya kana karo da busasshen kashi, zarni kuwa ba a magana. Hankalina ya tashi, na soma hawaye amma GG in ban da narka min zagi ba abin da yake.
Cewa yake, “So nake in ga matsayin ubanki a garin nan, in tabbatar da cikar ki ‘yar masu kudi. Allah yasa ‘Yar Aduwa ne ya haife ki, da kike wannan bunkasar. Kin ganni nan duk kyawun mace da farar fatarta ba ta burgeni, ko da kuwa ta hurul-eeni ce. Ko dai ta yi karatu ko in bautar da ita, bautar da uwarta da ubanta basu taba yi mata ba. Ke ni ko a aljannah bana fatan Allah ya hadani da mace, ba don komi ba sai don cewa ita ba komi bace face fitina a doron kasa, balle irin ku masu narka-narkan…….sai ku lalata mutum in ba ana wulakanta ku ba….”
Na daga idona a hanzarce da hawayena suka kafe karaf, na dubi GG din nan na ‘yan dakikai don ji nake kamar Imran ne yake gaya mun hakan. Ashe dalilin Ya Im kenan na wulakanta ni, kada in lalata shi? Dalilin shi kenan na gaya mun abin da zai bata mun rai in ji har abada bana son mu hada hanya? Sai na ji GG ya yi gaskiya, na shiga kada kai ina mai gasgata kowacce kalma dake fita bakinsa.
Na duka na soma ture busassun kashi da tsintsiya, da wani amai ya taho min gabagadi sai na kwararo shi a kafafun GG kore shar da shi kamar atini, don rabona da abinci tun na safiyar jiya. Ji nake kamar hanjina nake amayarwa.
Ya daka tsalle ya yi gefe yana kara zagina, ya ce, “Wallahi ba amai ba ko hantarki za ki amayar sai kin wanke toilet din nan fes, kamar tuwo na ya fadi in dauka, in ya so gobe a sallameni daga aikin gwamnati. Wannan ba abun damuwa bane ina da makekiyar gonar gado a Gumel, sai in koma gida in cimma sana’ar Uwa da Uba watau (noma)”.
Ya kira wasu dalibai da za su wuce ya ce su dauko mai kujera, ya girkata can gefe daga nesa ya zauna yasa hankici ya toshe hancinsa, lokaci guda kuma yana wanke kafarsa da ruwa a gwangwani da na kwararawa amai.
Haka ba yadda na iya na zage na wanke toilets dai-dai har guda shida, na kuma kwashe busasshen kashi na zuba a dustbin, sannan ya sani a gaba muka nufo ajinmu. Lokacin karfe sha biyu da rabi na rana ya rage awa daya a tashi. Na dauka shi kenan GG zai kyale ni, amma me? Ina sa kai zan shiga ajin ya juyo ya dakatar dani ya ce, “Haka za ki shiga musu aji kina warin kashi? Koma ki shanya kanki a rana har sai warin ya gushe tukunna, kneel down”.
Na koma cikin rana na zube gwiwoyina idanuna a rufe. Tsayin awa guda da rabi sannan aka kada kararrawar tashi. Su Azizah suka rugo da gudu suka rungume ni suna tattabani suna tambayar abin da ya yi mini, ban ce musu komi ba illa hawaye da nake ta sharewa ina fyace hancina da ya toshe don azaba, suka tabbatar ba za su ji kalma ko daya a bakina ba sai suka hakura suka kyale ni.
Muka zo gindin bishiyar dalbejiya inda muke tsayawa Shehu direba ya zo ya dauke mu, shiru-shiru bai zo ba har dalibai suka fara karewa. Su Azizah suka kulu matuka, ni kuwa ta kaina nake da kuguna da ya rike kamar zai balle saboda durkuson da na yi na awoyi da dama.
Sai misalin karfe uku na yamma sannan muka hango hancin motar Abba (Vanquish), muka shiga ware ido cike da mamakin yau Abba da kanshi ya zo daukar mu, to ina Shehun? Ashe dan duniyar ne ka janye da motar da Faruq a kujerar mai zaman banza.
Suka saki baki suna kallon ikon Allah, don ni har zuwa lokacin kaina a durkushe yake, tunda na yi musu kallo daya ban sake dagowa ba. Ya daka mana tsawar da ta firgitamu ya ce, “Da Allah malamai za ku