Showing 27001 words to 30000 words out of 34122 words
Chapter 10 - Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel
matsayin wadda ta fi kowacce mace a idanuna ba….” Dariya suka yi suna kokarin ficewa saboda su dai basu saba jin irin wadannan maganganun ba, balle kuma daga bakin da suke matukar girmamawa.
Ya ce, “Ku yi zaman ku ayi hirar da ku, watakila in ci arzikinku ta amshi kokon bara na, in kun tafi ko kallo na ba za ta yi ba. Ku taimaka ku tambaya min Zaynab, shin kalamanta masu tsada na sayarwa ne? Ko-ko kwalliyar da na yo mata ne bai burge ta ba in koma in sako?”
Suka sa dariya gaba dayansu, nima kaina ban san sanda na murmusa ba, still ban juyo ba na ci gaba da abin da nake, kamar in ce da shi shin ba yanzu ka gama cewa ba kwalliya ke sawa a so mutum ba?
Ya karaso ya amshi abin sharar a hannuna yana cewa, “Kawo nan in karasa miki ko kya zauna mu yi zance?” Ya dubeni cikin idanun shi cike da abubuwa da dama, na yi hanzarin zama a gefen gado saboda kafafuna dake neman kayas dani. Iftihal ta ce, “Hala baka taba zuwa zance wurin Mami ba?” Ya ce, “Eh, yes, ban taba ba, ita ne take zuwa”. Ta girgiza kai ta ce, “Ko da na ji”.
Ya dube ta bayan ya aje sandar ya ce, “Me kike nufi?” Ta ce, “Na ga baka iya bane, duk da ban taba yi ba na san ba haka samari ke gayawa ‘yammatan wai sun zo zance gatse-gatse ba, abin babu ko dadin ji”. Ta zura da gudu Azizah ta rufa mata baya ita ma ta ce, “Gaskiya idan baka koyo zance ba, ba za a karbe ka ba”.
Ya zauna a gefena na yi saurin rufe fuska da tafukana ina dariyar su, ya ce, “Da gaske ne ban iya ba Zaynab?”
Na girgiza kai ba tare da na bude fuskar ba. Ya ce, “Wallahi ko ki bude fuskar nan ko in sumbaci hannun ki”. Da sauri na bude. Ya ce, “Ashe dai yanzu an san ni wane ne, da kar ki bude mana”.
Na tsuke fuska gami da baki gaba daya, ya yi dariya ya ce, “Yi hakuri don Allah saki bakin kada fushin ki ya lahanta ni, ya jawo min asara ya dai-daita zuciyata”.
Na yi wani irin murmushi a raina na ce, “Ni kuma fa? Da ka sanya tawa zuciyar cikin wata irin wahalalliyar rayuwa da wani al’amari mai wahalar bayyanawa”. Ya ce, “Zaynab don Allah?” Tare da rausayar da kai gefe tamkar marayan da ya rasa uwa. Na ga in ban yi da gaske ba mutumin nan zai yi galaba a kaina, sai na juyar da kai gefe ba tare da na ce komi ba.
Ya sake kankan da murya ya ce, “Zaynab don Allah!” Wallahi na ji wannan kira har cikin kwakwalta ta, kaina ya sara,z uciyata ta yi wani irin bugu da karfi. Na kai hannu na dafe kai da kirji duka a lokaci daya. Roko nake kawai Allah ya kawo sanadin da Imran zai tashi ya rabu dani, in ji da abun da ya dame ni.
Ya sake kaskantar da murya tare da sakkowa bisa gwiyowin sa, ya daura kai bisa gefen gadon ya sake cewa, “Don Allah Zaynab…” Duk dauriyar da nake yi abin ya ci tura, wai yau Imran dake wahalar da rayuwata ne yau ke roko na da gwiwoyinsa a kasa. Tsinkayen Anti Rose ya tabbata kenan. Ba zan iya jure ganin shi cikin wannan halin ba, ban san sanda na ce, “Me kake so Imran?”
Ya dago da hanzari ya dube ni da idanunshi da suka kada suka yi jawur, ya ce, “Zaynab muyi aure shine kawai abin da nake so. Na san kema shi din kadai kike so, duk wannan turjiyar wahal da kanki kawai kike yi, ba kuma solution ne ga problem dinki ba, wanda ni na san shi ba tun yau ba. Illa in ce ke jaruma ce na kuma yaba da jarumtakar ki. Duk wasu experiment da na yi a kanki baki fadi ko daya ba. Wallahi Zaynab ba tun yau nake son ki ba, tun ranar da na fara ganin ki, na dauko ki a sume baki san inda kanki yake ba, tun baki mallaki komi ba.
Na ci gaba da rainon son har kawo sanda kika fara zama mutum, na kuma yi nufin bayyana shi gare ki. A lokacin ne na fahimci kema kin kamu da sona, amma ba irin son da ni nake miki ba, naki ragagge ne wanda sha’awa ce ginshikin sa.
Sai na yi tunanin idan na ci gaba da nuna miki son da ni nake miki, wanda ya sha bamban da naki ba mamaki wata rana ki rinjaye ni na afka irin nakin, muyi abin da ba dai-dai ba. Kuma a shekarunki na wancan lokacin hakan babban hatsari ne ga rayuwar ki. Na yi tunanin abubuwa da dama a kanki a wancan lokacin, musamman inda kika samo wannan al’amari, duk da tarbiyyar da kika taso a kanta, wadda iyaye da dama ke son ‘ya’yansu suyi koyi da ke.
Babu irin zargin da ban yi ba a kanki a lokacin, musamman sani da na yi bakwa kallace-kallacen banza, ba kwa karatun banza. (Excuse me pls) a lokacin sai na ji na kasa yarda da ke, don sai na ga idan kin so ni nta wannan siga, kowa ma za ki so shi da hakan, musamman wanda ya fini. Babu kuma namijin da za ki nunawa hakan ya iya kawas da kai a kanki, ba yabon kai ba sai dai-daiku masu tsananin tsoron Allah, domin ba karamar baiwa Allah ya yi miki ba. Daga baya ne na fahimci abin a halittarki ne nature”.
Na yi tunanin idan har da gaske nake ina kaunar ki, to abin da zan yi in nuna hakan shine in yi ignoring dinki, ba don na daina son ki ba, sai don in yi kokarin daura ki a kan sahihiyar soyayya, ba wadda za ta zamo nakasu ga rayuwarki da mutuncinki a idanuna ba.
Ha horas dake ta hanyoyi da dama domin ki azabtu ki koyi kaunata, kuma alhamdulillahi na yi nasarar hakan. Duk wasu experiment (gwaji) da na daura ki a kai kin haye su, na san a yanzu kina sona, kina kaunata kwatankwacin yadda nake kaunar ki.
Don haka Zaynab don Allah ki yi hakuri ki fasa duk wani ramuwar gayya da kike son yi a kaina. Ban yi da wata manufa ba illa don amfanin kanmu gaba daya. Ban yi don in wulakanta ki ko in tozartaki ba, illa don in samawa kaina kyakkyawan matsuguni a zuciyarki. Ki yi hakuri ki daina wahalar damu haka, we need each other Zaynab plz stop this childishness. Na gaji Zaynab, na yi hakuri na yi juriya kema kin yi, to ki hutar da zuciyoyinmu su samu abin da suke so, tun baki sa na rushe ginin da na dade ina yi ba”.
Hawaye ne na ji sun fito min sur-sur, na yi azamar dauke su kada ya gani, amma ya ganin. Ya dawo gabana a kasa ya zauna dirshan, ya kama hannuna na dama ya rike cikin nashi, ya ce cikin karyayyar murya, “Kuka Zaynab, why? Idan akwai abin da ya bata miki rai cikin kalamai na ki dubi Allah ki yafe mani, ban yi da niyyar in bata miki ba, na fada maki gaskiyar abin da ke zuciyana ne domin wanke zargina da kike da wulakanta ki.
Ban sani ba ko kina daya daga cikin mutanen da ke son a fada musu karya don a faranta musu. Na fada miki iyakar gaskiyata ne domin ki fahimce ni, ki tsayar da zuciyarki wuri daya….”
A nan ma ban ce komi ba sai hawayen dake ta bilbilo mini. Ya yi duk iya kokarinsa don jin wata kalma daga bakina na ki cewa komai, sai hawayen dai da nake ta fitarwa ina sharewa kamar an sunce famfo. Daga karshe sai haka ya fita ya kyale ni yana cewa, “Na baki kwanaki biyu ki yi shawara da zuciyarki Zaynab, ba zan takura miki ba. Na kuma yi alkawarin yin biyayya ga duk hukuncin da kika zartas garemu”.
Kuka nake ba don komi ba sai don farin ciki da bakin ciki duka a lokaci daya. Kuka nake na farin cikin zuciyata yau ta tabbatar da abin da take shakku a kan shi, yau ta same shi. Kuka nake domin bakin cikin ba zan iya auren Imran ba, domin tsira da mutunci da martabana da na iyayena.
Kwanaki biyu duk hanyar da na san zan ga Ya Im ina kauce mata. Shima bai matsa da lallai sai mun kebe din ba. Za su yi ta hirarsu shi da su Ifty da Mama ba tare da na tofa ko uffan ba. Ranar lahadi ne da daddare ya ce in je in kawo mishi wayana, ba musu na dauko har layin da na cire na kawo mishi. Ya dubi Mama ba zato na ji ya ce, “Mama na kawo miki karan Zaynab”.
Cikin son fahimtar mene ne tsakanin Imran da Zaynab din suke share junansu ta ce da shi, “Me Zaynab din ta yi maka dan Abba? A sanina yau shekaru dai-dai har shida babu wanda ya taba budar baki a gidan nan ya ce ga laifin Zaynab, ko ya ce ta bata mishi sai kai yau. Amma ban sani ba ko Zaynab din dana sani, mai kirki mai addini, mai girmama na gaba da ita da tsantseni cikin al’amuranta ta canza hali ne. tunda ni ba zama nake yi ba”.
Ya yi murmushi ya ce, “Ba ta canza ba, tana nan a Zaynab dinta da kika sani. Cikin kyawawa halayenta sai ma abin da ya karu. Waya ce na basu kowa yana amfani da shi amma ita ta rufe nata, ko kunnawa ba ta yi ta raina kenan?”
Ta girgiza kai da sauri ta ce, “A’a, Zaynab ba ta rainuwa, ko kiyashi ka ba ta a matsayin kyauta za ta ce nagode, Allah ya kara budi. Watakila dai akwai dalilinta na rufewar amma ba wannan ba”. Ta juyo ta dube ni tana murmushi, na sarda kaina kasa nima ina murmushi cike da jin dadin yabon da take yi mun.
Ta ce, “Ina sauraron dalilin ki na rufe wayar da Imran ya baki Zaynab, don in yi hukuncin adalci a tsakaninku”. Na ce a hankali, “Mama firgita ni take, karar ta na damuna, musamman in ina barci”. Suka kyalkyale da dariya ban da Imran, kallona kawai yake cike da matsanancin so da kauna. A hankali ya ce, “Ai ana canza tune din, ko kuma ki sanya shi a silent ba za ya ke firgita ki ba, ko kuma ki sanya kiran sallah for your own convience”.
Ranar litinin Allah-Allah nake mu fito paper in nemi Anti Rose, kuma da yake paper din Islamic Studies ne bana jin wuyar sa, nice farkon fitowa. Gudu-gudu sauri-sauri na bita hanyar fita ganin tana kokarin juya motar ta domin tafiya gida. Na daga murya tun karfina daga nesa ganin cewa duk saurina ba zan iya cimmata ba, na ce, “Anti Rose”.
Ta dakata kamar tana nazarin ta inda kiran sunan ya fito, kana ta yi hanzarin juyowa ta dube ni. Lokaci guda ta kashe motar ta fito. Sai murmushi nake ita ma murmushin take min tun daga nesa. Tana karasowa inda nake kuwa ta ce (tana mai nuna ni da dan yatsanta) “Akwai daddadan labarin Imran a bakin Zaynab dina”.
Ta kama hannuna har staff-room, babu kowa duk suna dakin jarabawa, muka zauna a kujerun dake fuskantar juna ta ce, “Hurray Zaynab, bani in sha”.
Na yi murmushi na zayyane mata dukkan abubuwan da suka yi ta faruwa tun dawowar Ya Im, ban rage kalma daya ba. Ta ce, “Thank God! Na kuma gode miki da baki yi saurin amsawa ba. Hakan ma wani abu ne da zai kara miki matsayi a zuciyarsa. Ki ci gaba da kin amsa bukatar shi har sai kin koma gaban iyayen ki. Idan ya biki ya cika mai kaunar ki Zaynab, sai ki nuna mai matsayin ki na cewa ke talaka ce, kasa da shi. Kina gudun wulakanci. Idan ya ce ya ji ya gani yana son ki haka, Zaynab ki yarda da Imran ku yi auren ku, ina muku fatan alkhairi”.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Mun baro Katsina ranar Lahadi, kai tsaye muka zarto Kanon Dabo, yaro ko da me ka zo an fika, mai Dala da Gwauron Dutse, tushen Maguzawa ta Dabo tumbin giwa. Kwanan mu biyu a gidan Baba Sa’idu na Kano dake Sultan Raod sannan muka tattaro muka yo Gwarzo.
In ba don idon Abba ba, da Hajiya Sa’a da iyalanta ba za su Gwarzo ba iyakacinta Kano, domin ita a gareta takura ne zaman kauye ai sai dole. Amma shi Abban baya ganin haka. Kar ku yi mamakin jin cewa Hajiya Sa’a ‘yar Gwarzo ce ‘yar kanwar Inna Dubu da aka rike a gidan Malam Ali, domin iyayen Dubu talakawa ne futuk amma duk sun rasu. Don haka Dubu ta daukota ta rike. Shi kuma Abban a rayuwarshi ba shi da kamar Malam Ali, a shirye yake kuma da ya bata da kowa in dai a kanshi ne, daga ‘ya’yan shi har matan shi ya sha gaya masu wannan. Don haka wannan lokacin take taka-tsan-tsan.
Ita dama ‘yar dakin Innar Faruq ne, don haka can suka sauka da ‘ya’yanta. Ni da su Mam, ‘yan biyu da Gambo muna dakin Innana dake ta faman makale ni kamar ta maishe ni ciki. Yau abin da sauki tunda kuwa ban ga ta hana su Iftihal shiga dakinta ba, ko don ganin idon uwarsu ne, oho! Ko kuma ‘yan mutuncin ne a kanta? Na danganta hakan da dokin zuwana da take, domin na yi dadewar da ban taba yi ba har watanni shaida ban zo ba.
Rabi da Mama sun barke da hirar yaushe gamo wadda duk rabinta labarin rayuwata ne da ke burge kowa, yake kuma baiwa kowa sha’awa a can Sokoto. Ta ce, “Zaynabu-Abu uwar addini ce, ban taba ganin yarinya Abida (mai ibada) irin Zaynabun ki ba”. Inna ta kara janyo ni ta rungume tana murmushi dadi ya cika ta. Don ba abin da take so a rayuwarta irin ta ji ana yabon Abun ta, Kyautar ta, Kyautar Allah (kamar yadda take cewa).
Sai na samu kaina da kara godiya ga Allah da ya kare ni daga aikata ZINA, kamar yadda zuciyata da gangar jiki ke so, har suka so su ja ni. Wannan ya samo asali daga addu’ar da Malam yai min a sanda aka haifeni a al’aurata, domin kariya daga aikata zina. Aya ta ( ) cikin Suratul-Maryam. (Don haka iyaye a dage da kula da ita wannan addu’ar a yayin da aka haifi yaro, to insha Allah ba dai ya aikata zina a rayuwarshi ba).
Na tabbata da na karya zuciyar Inna Rabi, fiye da wanda ta samu kanta a gaba dayan tsayin rayuwar ta, wanda ni ba zan ce ga shi ba. Da duk wannan kaunar da take mun, ta koma kiyayya, watakila irin kiyayyarta ga BABA SA’IDU. Sai na samu kaina a mai tambayar kaina, wannan na nufin BABA SA’IDU ya aikata ZINA ne shi yasa ta tsane shi? To da WA????? (Wa’iyazubillahi). Wama taufeeqee illa billahil aliyul azeem…. Kada Allah yasa tunanin nawa na banza ya zama gaskiya, kada Allah yasa tunanin nawa na wofi tabbatacce ne. ya Allah ka fitar mun da wannan mugun tunanin a zuciyata…. Allah ka dube ni, kasa tunanina ba gaskiya bane rudin shaidan ne.
Ba abin da ke dadadawa Innana kamar ganin yadda nake girma da wani irin murjewa, kai ka ce irin Larabawan nan ne na Lebonon. Duk na fi ‘ya’yan Farfesa daukar ido da kwarjini, haka duk kalar kayan da nasa kyau suke min su kuma amshe ni kasancewata jajur, masu tsada ne ko akasi, kai ka ce don ni aka kirkire su. Ni Zaynabu-Abu shiru-shiru ce, bani da kwaramniya, kuma bana sonta. Da wuya ka ga ina magana in ba a kan abu mai muhimmanci a gareni ba.
Sun baro Gwarzo bayan motarsu cike da tsarabobin da suka saba komawa dasu, wato kamar su man shanu, garewanin man gyada, kindirmo, madarar shanu, kwan kaji da na zabbi da sauransu. Wannan karon har kajin gidan gona ishirin Malam ya ba su Hassan, amma an fige an gyara ya kuma ba Haydar takwaransa dan maraki, Abba ya ce a bar shi a nan a kiwata masa.
Ni da su Azizah bamu so rabuwa ba, don dai ina son samun lokaci da Innana ne su kuma sun kallafa ran su a son zuwa Porthearcourt, akwai tambayoyi da dama da nake son in yiwa inna, musamman a kan irin gore-goren da su Hassan ke mani a shekarun baya, wanda wancan lokacin karancin shekaru da rashin wadatar hankali bai barni na kuma waiwayarsu ba, sai yanzu da hankali ya zo mini nake ganin hakan tamkar wani barazana ne ga mutuncina a nan gaba.
Mun kwanta ne da daddare, sauro ya gallabe mu, duk kuwa da maganin sauron da muka kunna da (Rambo) da na fesa, amma ni ko jin cizon suron bana yi balle in sosa, abubuwa ne da yawa ke damuna a zuci. Wurin karfe daya na dare na ja tsuka “Tsut!” don tuno shekarun baya. Ashe Inna Rabi barcinta ba wani nisa ya yi ba, ta ce, “Ke in wani abu ne ya dame ki, ba kya gaya mun? Haka kawai ki bi ki isheni da tsaki cikin dare”.
Maimakon in amsa mata sai tsakin ne (by mistake) ya sake subutowa daga bakina, na ce, “Kai abin ne ma Inna na kasa ganewa wallahi”.
Ta ce, “Can gidan Baba Sa’idun naki, fi sauran-Babanni ne kike da matsala ko-ko satittikan da za ki yi mana ne kike ganin kyashin su, kin baro A/C sauro na cizon ki? Abin da na guda kenan ai tun farko Kyauta na hana tafiyar ki hannun su Azumi, amma Malam bai saurare ni ba, saboda dukkanku baku dauke ni a cikakkar mai hankali ba sai SA’IDU. Sa’idu ya fini GIRMA a idanun ku, komi Sa’idu ya ce shine dai-dai, amma Rabi ai MAHAUKACIYA ce…..”
Wasu hawaye suka balle min, na ce cikin rishin kuka, “Ki daina gaya min haka Inna, wallahi-wallahi a kowanne hali, a kowanne matsayi babu inda ya fiye mun dakin nan naki kwanciyar hankali. Babu inda