Showing 33001 words to 34122 words out of 34122 words

Chapter 12 - Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel

na ce, “Sorry plz, ban ganka bane na gaji ne sosai. Muna barka da zuwa”.
Da daddare muna falo muna ta hirar pepermu ta yau, ya shigo yana balle links din hannun shi yana tambayar Mama ina abincinsa. Gaba daya muka rude mai da labarin zuwan Mami, muryata ta fi ta kowa karadi, ina kara kuranta kyawun Mami da kurzanta kirkin ta, duk sai ya sha kunu ya bi ya daure lallausar fuskar nan tam, alamun ba wargi. Amma bamu fasa ba, kamar ma zuga mu yake. Hajiya na gefe tana ta murmushin jin dadi, ta ce, “To kai ka ji ‘yan kannen naka ma sun yaba da ita”.
Ya dago fuskar nan a murtuke kamar hadari, ya kulu iyaka. Ya hade giran sama da na kasa a take ya koma (previous IMRAN) mai gigita kannensa. Na yi mamaki da bai daka mana tsawa ba. Ya zube min manyan idanun shi a mamakance, ya ce cikin gatse da wata murya mai kama da ta mai ciwon makogaro, “Har da ke Zaynab, kema kin yaba da Mami?”
Da sauri na gyada kai ina dariyar nan da Malam Bahaushe ke kira (yake), na ce, “Wallahi kuwa Ya Im na yaba, a very simple lady, ba ta da girman kai”. Ya sakar min hararar da ta kada min ‘ya’yan hanji, ya ce, “Tunda haka ne ki hadata da Faruq man, kin ga shima baya da girman kan, amma ni ta yi mun tsufa sai yarinya (sweet 16) zan dauka, yadda nake (fresh) din nan in na auri kaman Mami ‘yar (28) ai na ci baya……”
Iftihal ta toshe baki kada dariyar da ta zo mata ta fito, Azizah da Hajiya suka daure fuska wato sun ga samu suna neman ganin rashi. Ni ko na yi tsuru-tsuru don duk maganar nan da yake idanunshi a kaina yake yin su, kamar da ni kadai yake magana a falon.
Ya ci gaba da cewa, “Shin ma wai ita Mamin da ta zo ne ta ce muku na ce ina sonta? ‘Yar ajin su Faruq ce fa, daga kawai tana gani na ina zuwa wajen sa ta like min kamar kaska, amma ni wallahi bana ra’ayin bakar mace a rayuwata, ni baki ita baka, muyi ta haifar bakaken ‘ya’ya me aka yi kenan?
Ko Annabi (S.A.W) ya ce in kai baki ne ka auri fara, in kai fari ne ka auri baka, sai ku haifi ‘ya’ya masu kyau. To kin ga shi Faruq fari ne sol, watakila za ya iya maneji da ita su jera kafada, ko ya ya Hajiyata?” Ta dunkule hannu ta sakar masa dakuwa, ta ce, “Ungo nan, babban banza kawai, ka tsaya kana irin wannan maganar da kannen bayanka ko kunya baka ji, sahorami, shashasha, kada ka auretan mana wa ya yi asara? Ka san dai ba za ta rasa mai so ba, don ba ta yi kama da ‘yan kananan gida ba”.
Ya yi dariya ya ce, “Allah yasa Obasanjo ne Babanta ba Abdulhadi ba, barawon dukiyar al’umma, tunda ya hau kujerar Sokoto ko kwatami bai yiwa al’ummarmu ba, sai baitil malin mu da yake ta handamewa yana kaiwa kasar waje. Ku saurara nan da sati za ku ji shi a hannun EFCC. Don haka sai ku samo min ‘yar sabon Gwamna, tunda ku ke da idon zaben mata ni bani da shi.
Amma wannan bana yi, bana so a kai kasuwa, kada nima ina kwance ina shan amarci na ga sammacin Farida….” Ta dauki filet din da ta gama cin gasasshen nama a ciki ta maka masa, ya kauce ya fice da gudu-gudun sa yana kara gaya mata, “Ko da yake Hajiya ki yiwa Hassan din ki kamun ta, gashi nan ya dauko tsawo kwanan nan zamu yi kafada da shi, in har da gaske surukuta kike so da ita”.
Da haka Imran ya kashe zancen Mami a gidan amma ban da a zuciyata. Kullum Mami tana nan like cikin raina har mafarkinta nake anyi musu aure da Imran, sai dai ko alama ba wanda na bari ya gane halin da nake ciki.
A wannan zuwan da Imran ya yi, gaba daya ya canza mana, ya dawo YA IM din sa, mai son kannensa da son kula su, ko da yake ma mu yanzu bama zaman gidan, kullum safe da yamma muna makaranta.
Ni kuwa in na shige daki tun karfe shida na yamma bana kara fitowa balle mu hadu a hirar falo, zan fiddo littafina in tisa karatu sai gobe kuma, in sha lemo in ci biskit in yi kwanciya ta zuciyata kal babu wani Imran a ciki.
Na danganta canzawar shi da dadewa da ya yi bai ganmu ba. Ya dauki annual-leave din shi ne na watanni uku. Allah-Allah nake mu kare jarrabawar in yi gidan ubana in huta da wahalar rayuwa, zancen zuwa jami’a da su Azizah ke yi babu shi a wajena, sam bana ra’ayi.
A can falo Imran cike yake da mamakin rashin ganina a gidan, ya damu su Azizah da tambaye me nake yi a daki ni kadai, sai su ce a takaice “Karatu”. Ya ce, “Ku bakwa karatun?” Su ce, “Muna yi mana, amma bama iya irin nata. In ta yi (seat) dinmu daya muna kwafe”.
Don haushi ya rasa mai zai ce musu, ya dade yana kallon su kamin ya mike ya rufe ido ya balbale su da fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, wai zai kai su ga hukumar makarantar ayi musu daurin shekaru biyar na (malpractice).
Sai Azizah ta mere baki ta ce, “Wallahi Ya Im yadda ka je haka za ka dawo, don kuwa duk (invigilators) din samarin ta ne, har wajen zaman mu suke kawo mana amsa, ita ce dai ba ta karba, amma wallahi har principal saurayin ta ne. shima GG da ya sata wankin kashi yanzu in zai rabu da duk abin da ya mallaka zai yarda, in har Zaynab za ta daga ido ta kalle shi…..”
Allah sarki, ba ta san yadda zuciyar shi ke tafasa da kalamanta ba da ko kusa ba ta fara ba, da wannan sabon abu da yake ji game da rayuwar Zaynab. Ya ga ba ta da alamun yin shiru balle tunanin dasa aya, idanunsa a rufe gam, ya nuna mata kofa cikin kakkausar murya ya ce, “Ku wuce ku bani wuri mutanen banza kawai tambadaddu, jakai, dabbobi da basu san ciwon kansu ba….”
Ya kware ya shiga tari ba kakkautawa saboda takaicinsu da ya kasa amayarwa, suka fita suna yi mai dariyar kwarewar da ya yi, wai masifarsa ce ta kwarar da shi. Amma Iftihal gorar ruwan (eva) mai sanyi ta dauka a firij ta koma ta kai masa, daga nesa-nesa ta ajiye mai ta zura da gudu. Suka zo suna kyankyasa min yadda su kai, na ce, “Kan ku kuka tonawa asiri, idan ya gayawa Abba fa?”
Mu karasa a littafi na 2
Takori

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login